Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 53 Hausa Novel

*******”Ameer! Yaushe rabon da a gana? Ashe za ka zo?”Ya shafa kanshi yana rike hannun Ammin yace “Ammi abubuwan mu ne sai a hankali amma kuna raina wlh””Da muna ranka ba’a waya kaɗai zaka dinga jin mu ba da kana zuwa shekara nawa rabon da ka waiwayi gida?””Na tuba Ammi yanzu kam zan dinga zuwa, yanzu ɗin ma labarin bayyanar Sameer ya saka ni zuwa dole.”Suka kai zaune, Aisha ta kawo mishi ruwa yayinda jannah ta gaishe shi ya amsa, Abeeha ma ta gaishe shi ganin shi mutum mai fara’a kwarai da wasa ya burge su.”Ammi ina kika samu wasu yaran babu labari?””Ƙannenka ne, Abeeha da Jannah ga wani yayan naku ɗan wajen babban yayana ne Galadima, abokin Sameer ne don tare suka tashi kaman ‘yan biyu a ɗakin nan ɓacewar Sameer bai sa ya bar nan ba anan yayi rayuwa har ya gama secondary ya tafi karatu chan kasashen turawa ya gama da jimawa ya ƙi dawowa”Sannu da dawowa suka sake yi mishi ya amsa da kulawa.”Ammi ina Sameer ɗin? Wani sashe yake?””Ka ci abinci ka dan huta sai kaje yana chan tare da matarsa”Wara ido yayi “Har ma aure yayi abin shi””Eh ya bar ku da gaurantaka”Yayi dariya, Abeeha ce ta taya Aisha presenting mishi abinci kan suka koma suka zauna suna ta jin hirar su da Ammi wanda suke tuna baya tasowarshi da Sameer, hakika zata iya cewa shine na uku a damuwar rashin Sameer don sai da yayi jinya tunda tun ba’a yaye shi ba ya yaye kanshi ya dawo wurinta saboda Sameer sun shaku sossai ta zama sanadiyar raba wannan ƙaunar.Bayan ya gama sashenshi da bai da nisa da nata ya ƙarasa don ana gyarawa akai akai kuma zaman cin abincin nan da yayi ta aika wasu hadiman sun sake kakkaɓewa ya tafi yayi wanka yana fitowa ma yaji ana kiran la’asar don haka sai da yayi sallah ya fita ya tambayi wasu fadawa suka fada mishi inda sashen na Sameer yake ya nufi wurin.”Amir Galadima..!”Rayyan ya faɗa fuskarshi ɗauke da fara’a shima Amir cike da fara’a ya rungume shi suka raba hug ɗin suka tafa irin na mazan dai da aka manta rabon da a haɗu.”Sameer kana duniya ashe? Baka kyauta mana ba! Ka ɓace babu traces? Hankalinmu ya matuƙar tashi har ka bayyana ban daina tunaka ba, saƙon bayyanarka na daga cikin news mafi jin daaɗi da na taɓa ji a duniya”Murmushi kawai Rayyan yake.”Mu isa ciki, wannan labari ne mai tsawo and ka san ban da bakin ba dashi”Suka nufi yana furta “Har yanzu ana nan da baƙin hali”Murmushi yayi yana tuna kalmar Afeefah wai ta mishi shaidar Rashin kirki a baya yace “Tunda matata ma ta faɗa hakan don ka faɗa ba komai bane”Dariya sossai Ameer ke yi har suka ƙarasa parlorn suka zauna, nan hira ya fara don Ameer na daga cikin waenda a bayan ma suka san dariyar Sameer, daga shi har mahaifinshi suna da muhimmanci sossai a rayuwarshi Dukda tun dawowarshi sau ɗaya yaje wurin Galadiman kuma tun da ya kawo mishi maganan Ammi bai sake komawa ba.Ita kam Afeefah jin hirar su yasa ta nemi gyale mai girma ta saka ta ɗora wata alkyabba marar nauyi shara shara a kai ta fito, tayi kyau sossai don ya kasa dauke ido a kanta Dukda bata shafa komai ba, gaisawa suka yi da Ameer cikin natsuwa da girmamawa kan ta kawo ruwa da su snacks ta ajiye mishi, ta kalli Rayyan “Ya Saraki bari na je wurin su Adda Abeeha yanzu za mu dawo”Bai ce komai ba don baya son abinda ke tsakanin shi da mahaifiyarshi ya shafe su dukkansu.Ta juya ta fice, tana tafiya ana jefa mata gaisuwa har ta kusa isa sashen suka haɗu da Fulani Adama, ta ɗan rusuna ta gaisheta “Lafiya ƙalau ya baƙunta Afeefah?”Ta amsa tana ƙare mata kallo ganin yadda ta sake wani kyau da haske.”Alhamdulillah Mama””Masha Allah.”Tana kai nan ta wuce ta itama ta wuce ta nufi wurin Ammin, zaune kuwa ta same su har lokacin ganinta yasa jannah fara cewa “Amarsu ta ango”Murmushi tayi tana sunkuyar da kai saboda Ammi dake wurin ta duƙa ta kwashi gaisuwa.”Lafiya ƙalau Gimbiya Afeefah, ya zaman baƙunta da rashin sabo?””Alhamdulillah Ammi””Masha Allah, yanzu kuwa Mamanku ta kawo min ƙararku sai dai na bata uzurin da cewa laifina ne tunda ku baƙi ne baku wani san tsare-tsaren ba, ni kuma rigimar Sameer ne yasa ban yi maganan ba””Allah ya sa ba laifi muka yi ba Ammi””A kan zuwa gaisuwa ne, ya kamata duk safiyar duniya ku bi ku gaida iyayen naku musamman ke Afeefah da kike matar Ciroma””Ayi mana afuwa bamu san da tsarin ba amma za mu gyara in shaa Allah”Ammi tayi murmushi tana yaba Yadda Afeefar ta iya magana.”Adda Abeeha kitson nan yayi kyau masha Allah””Kin ga nawa ni ma, kitson na da kyau wlh”Jannah ta faɗa tun kan Abeehar ta bada amsa tana nuna mata kanta.”masha Allah duk sun yi kyau””Afeefah zo kema in tsefe miki sai a yi miki tunda duk gobe shigan al’ada za ku yi”Tace “Ai Ammi kaina a tsefe ne”Wacce ta yi musu kitson ta kira aka kawo kayan kitso na musamman itama aka shiga yi mata kuwa suna hirarsu.Dab Magrib aka gama yayi kyau ainun ya amshe ta don har a fuskarta zaka san ta chanchada kitso yadda ya ƙara sheki.Ana gamawa kuwa sai ga wani hadimi ya nemi a sanar da Fulani Afeefah Ciroma ya aiko a yi kiranta, Miƙewa tayi ta kalli su Abeeha “Adda Abeeha ku tashi mu tafi please””A’a yi tafiyar ki muna wurin Ammin mu”Shagwaɓe fuska tayi “Ni kaɗai za ku bari a chan? Ammi kina jin su?””Ba ke kaɗai ba kam, ki faɗi tsakaninki da Allah ko sanin mun taho ma kin yi in ba da kika ji shiru ba?”Hararar wasa take yiwa Abeehar suka yi dariya har Ammi ganin ta kasa cewa komai yasa ta juya zata tafi sai ta juyo ta kalli Aisha da itama sun fara sakewa sossai da juna tace “Ko za mu tafi kawai Aisha?”Aisha ta zaro ido”Ni?? Raba ni da shiga shirgin mijinkin nan yanzu su Adda Jannah suka gama labarin rashin mutuncinshi in je ya zane ni?”Zaro ido tayi “Yaya Sarakin ne bai da mutunci? A kunnenshi to!”Miƙewa suka yi suna ce mata ta tsaya ta ji ta rufa musu asiri su ba haka suke nufi ba tuni tayi gaba tana dariya suma duk dariyar suke har Ammi, saura ƙiris ta ci karo da Zarah suka tsaya suna kallon juna, a hankali maganganun Fulani Adama suka shiga dawo mata kaman yanzu suke yi, barin ma da ta ga kyaun da Afeefar ke ƙarawa ga iya ado kaman sarauniya, ga kamshin ta da in ka shaka zaka san ka shaka ko ita da ta tashi a masarautar bata irin dressing da daukar ido haɗe da kamshin da Afeefah ke yi, abinda ya sake sa taji kaman da gaskiyar Adama shine dariyar da ta samu duk suke wanda take da tabbacin yana da alaka da Afeefar idanunta ta sauke akan Aisha dake tsakiyar su Jannah sai kawai ta juya ta tafi.”Zarah kin tabbatar za ki iya aikata duk abinda za mu saka ki? Sannan za ki iya riƙe mana sirri?””Mama kin raine ni ne akan kafafunki kaman ɗiyar da kika haifa da cikin ki, har manta cewa ni ɗin ɗiyar dan uwanki nake don ban taɓa neman abu na rasa daga wurin ki ba, don na taya ki yaƙi akan cikar burinki na tsawon shekaru ban faɗi ba sai ma halarci da na mayar. Dukda Na ji Son Ciroma Sameer a raina hakan ba zai hana na isar da Manufarki yadda ya kamata ba””Masha Allah, haka nake son ji yanzu na san ban yi rainon banza ba. Zarah!”Ta amsa “Za ki auri Sameer dole sai dai bana so ko kadan zamanku yayi nisa”Kallonta take da neman karin bayani “Ba haka aka so ba kuma duk Shigowar wannan Afeefar ne ya ɓata mana komai amma a yanzu za mu gyara, za ki shiga a mata ta biyu amma ke za ki haihu za mu yi duk yadda za mu yi mu hana Afeefah haihuwa da Sameer, ke muke so ki sama mana ɗa namiji daga nan kuma za mu shafe Sameer””Mama ko da yaron bai girma ba? To waye zai yi sarautar?””Mahaifinki shine first cousin na sarki kuma yana da ikon yin sarauta zai iya riƙon ƙwarya har dan da zaki haifa ya girma ya bashi kin ga kenan Sarautar gabaɗaya ta dawo gidan mu kaman yadda dama tun chan yake a tarihi aka yi mana fin karfi aka hana mu”Shiru zarah tayi Fulani Adama tace “Ke kar fa ki tsaya wani kokonto don a sarauta babu kokonto ko tsoro, sannan kar ki bari wani soyayya yayi tasiri saboda babu wannan a tarihin jajirtaccun da suka yi mulki, ko ni na auri mai martaba ba don ina so ba sai don burin haifar Sarkin gobe, a yadda ban haihu ba na so kowa ma ya rasa har shi mai martaban ya mutu a haka dole ‘yan uwana su karɓa amma Yarinyar chan Faɗimatu ta lalata min shiri don haka dole ne ta ga ba daidai ba”Waɗan nan sune maganganunsu da Fulani Adama da farko tana wasu-wasi amma yanzu ta ji lallai zata iya, za ta iya aikata hakan ba ɓata lokaci.Afeefah na isa ta samu yana zaune a parlor kafanshi ɗaya a kan daya yana ɗan karkadawa ganinta bai sa ya saki fuska ba tace”Barka da hutawa Ya Saraki””Sai yanzu?”Ya faɗa yana kallonta, tuna irin kirkin Ammi take da irin damuwar da take ciki ko a murmushinta za ka iya fahimta hakan yasa ta miƙe daga inda take ta dawo kusa dashi tare da zame alkyabba da gyalen kanta haɗe da ɗan kwali tace a Shagwaɓe”Wai fushi ka yi na jima Ya Saraki? Kitso fa nayi kalli ka ga bai yi kyau ba?”Ya kasa ɗauke ido a kanta ta mishi kyau da Kitson sossai ya riƙo hannunta”vooɗi masin boɗɗiyel am”Dukda bata ji ba ta ɗan yi murmushi “Me ka ce kenan?””Mai kitson Fulani bata iya yaren ba?””Toh ai bana ji, kaima na yi mamakin yadda na ji kana yi fluently”Ta ɗan kwanta a jikinshi yana sake kallon kitson da ya fidda fatar kanta fesss yace “Tun daga ranar da na bar gidan nan ban sake yi ba sai da na dawo”Ta sa hannu ta zagaye cikinshi kanta na a kafaɗar shi duk tausayi suke bata daga shi har Ammin.”Toh ka faɗa min me ka ce?””Ya yi kyau sossai kyakyawata. Abin da na ce kenan”Tayi murmushi mai sauti tana ƙoƙarin maimaita abinda yace da fulatancin, yadda ta shirmata dole ta saka shi murmushi har ma ya manta da yana kokarin yin fushi ne ta tafi sashen Ammi tayi zamanta.Bayan Magrib ya zo ya ja ta suka fice daga masarautar a wata BMW baƙa ya hana su Gaabɗo Binshi ta chanza zuwa wani blue Abaya da ya karɓeta sossai, shima navy blue Jean ne jikinshi da coffee shirt da ya fitar da hasken shi ainun sai ya saka facing cap navy blue saboda mutane baya so a gane shi a wajen don yanzu sai a fara maganan yana fita da kananun kaya, Sossai ya zaga da ita hannunta na cikin nashi yana driving da hannu ɗaya ba wani hira sossai yake mata ba amma in tayi magana yana kokarin amsawa bar shi dai da kallonta sai kuma pecking expecially bayan hannunta dake cikin nashi.Shopping sossai suka yi suka je suka ci abinci daga nan suka dawo suka sayi popsicle don tace tana so, sai wuraren 9 suka dawo gida hankalinsu kwance shi yayi sallah already ta shiga tayi nata kan ta shirya kwanciya, kaman jiya riga da wando ta saka masu yauki na kayan baccin cream colour da ya amshe ta sossai hannun rigan na singlet ta feshe jikinta yadda ya kamata, tsoron zuwa ɗakinshi take don bata san me zai faru ba kar a yi irin na jiya don ma shi likita ne yana da tarin sani akan yadda zai bi da ita ko da ta gurzu yayi jinyar kayanshi amma tana tsoron zafin don har lokacin tana jinta a kumbure.Gadonta ta hau ta kwanta shiru tana jin kewan jikinshi da har ta fara sabo da hawa, bata yi mintuna talatin ba ya tura kofan ya shigo ganinta kwance ya saka shi murmusawa ya isa gadon ya yaye rufan da tayi “Lallai ma yarinya ni za ki bari kaman gauro?”Dariya maganan ya bata ta kama murmushi Dukda yadda ta so tayi pretending ta yi bacci dole ya dauƙeta suka yi nashi ɗakin daga shi sai wani cotton wandon bacci chest dinshi duka a bayyane haka ya rufeta ciki, yana shafa bayanta yace “Wasu sun ce zazzafar soyayya tana zuwa ne a bazata! Na yarda Boɗɗi saboda a sadda na fara ganinki ban zaci zan so ki kaman yadda nake jinki a yanzu ba, ban san za ki zama abu mafi muhimmanci da daraja a rayuwata ba, I just fell in love with you and am still falling even harder cikin kowani dakika”Tana tare dashi amma tunaninta yake, tana a jikinshi amma kewanta yake bai taba sanin haka so yake ba, bai damu da yaji ta Bakinta ba shi dai ya san yana sonta daga shafata da yake ya nemi zarcewa, za tayi magana ya haɗe lips ɗinsu yana bata wani irin kyakyawar french Kiss da ya gigitata, tuni rigar ta yayi wani wurin ganin da gaske yake yasa ta kawo kuka ta saka mishi mai tsuma rai dole ya haura a hankali zuwa wuyanta yana ajiye wet kisses slowly ya isa kunnenta.”Am sorry boɗɗiyel am! Ki yi haƙuri kaɗan zan yi ba dayawa ba i promise ba za ki ji zafi ba”Girgiza kai take sai dai bai bari ta sake wani yunkurin ba ya shiga wasa da harshenshi a kunnenta, Tsam ta tsume sai da ya tabbatar ta gama rikicewa kan yayi abinda zai yi duk suka samu natsuwa cike da tarin soyayya da tsantsar kulawa kuma bata ji zafin kaman na farko ba, a tare suka yi wanka yau ma nade da towel kawai suka shige bargo yana sanya mata albarka a kunnenta haɗe da godiya.Washegari da safe kaman yadda Fulani Adama ta faɗa bayan ta gama mishi abin kari ya ci ya fita ma wurin mai martaba ta shirya ta nufi wurin Ammi don da gaske su jannah basu kwana sashen ba, bayan sun gaisa suka dunguma wurin Fulani Adaman suka gaisheta Madarar shanu ta basu akan su ɗuma ciki sabo ne da zafin shi, ita Afeefah bata sha amma don kar su yi laifi Jannah ta karɓa ta sha, Abeeha ma ta Sha Afeefah na ta wasa dashi har suka ce zasu tafi suka ajiye mata suka fice, sauran sashen suka je suka miƙa gaisuwa kan ta koma sashenta su jannah suka koma wurin Ammi.Bacci tayi sossai sai azahar ta tashi ta shiga shirya mishi abinci inda ta haɗa mishi White Rice da kidney sauce sanin yana son abin sossai, bata ma gama shiryawa ba ya dawo ɗakinshi ta kai ta ɗale kafafunshi yana ci yana bata har suka gama ta fitar da kwanukan. Bayan Magrib aka zo shirya ta zuwa wurin Taron da Matasan Fulani suka shiryawa Yariman nasu na murna.Kayan saƙi ne Fari aka bata ta shirya ciki a ƙasan rigan ta saka bodyhug mai dogon hannu fari ƙal kan ta ɗora rigan ya zauna mata sossai ta ɗaura zanin a ɗan sama kaɗan suka shiga cika mata kayan adon Fulani bayan an yi mata dauri mai kyau, goshinta, wuya, hannaye har kafa kayan ado ne irin na al’ada sai aka ɗora mata alkyabba fara kal tayi kyau sossai tana ta kallon kanta tana murmushi, bayan sun fita tana nan zaune sai gashi ya shigo.Miƙewa tayi tana kallonshi kaman yadda yake kallonta da tarin ƙauna, farin wando na saƙi shima shine jikinshi sai wani farin shirt kan rigar sakin har da hula yana rike da sanda yayi kyau har ta rasa wani irin kyau za ta ce yayi, wayanta da bata taɓa daukar ma hoto ciki ba ta ɗauko ta ja shi gaban door size mirror ta shiga yi musu mirror selfie, ya biye mata sossai akwai wanda ya ɗora sandar a wuyanshi ya riƙe da hannu ɗaya ya ɗan karkato ya ɗora hannunshi ɗaya akan cikinta bayanta na jingine a kirjinshi sossai posture ɗin yayi kyau amma bai yi dariya ba sai ta Shagwaɓe “Kayi murmushi mana Ya Saraki ka ga fa shiyasa ake cewa baka da kirki”Bai san yayi murmushin ba ta ɗauka duk hakwaransu waje da ya gaji ya ja ta suka fice tana kallon hotunan nasu na karshe daga ma baya ma shi ta mayar wallpaper wayan ya karɓa yayi air dropping shima ya mayar nashi wallpaper ɗin, sun isa katoton zallar filin taron dake cike da haske an kawata wurin da kujeru.Kusan kowa a wurin shirye yake da kayan saƙi na fulani sai a wurin suka haɗu da Jannah da mijinta shi Rayyan sun haɗu tun da ya fita da safe ita ce dai Afeefah sai lokacin ta ganshi, wurin yayi kyau sossai kujeransu na a haɗe, gefe yan mata da ƙwairen Nono da wasu kananu masu kyau a tsaftace wanda shine za’a sha a taronMatasa da yan mata cike da wurin kida da fulatanci na tashi daga wannan ya kare za’a saka wannan wasu na soyayyarsu yayinda Afeefah ke bin komai dake gudana da kallon burgewa, wasan kiwo da shanu aka fara inda aka ajiye shanu aka shirya Matasa biyar aga mai dabarar da zai iya tada shanu tsaye, sossai wasan ya kayatar bayan an gama shi aka yi shaɗi sai wasan Matasa na sanda, aka yi rawa kala daban daban su dai basu tashi ba Dukda ta so ta tashi amma ganin gogan ya ƙi bada dama sai ta natsu an saka waƙar wani mawakin Camero Jaamali Na Lara saftata ya waiga ya kalleta tace “Me ake cewa?”Ya ce “Zan fada miki sai mun je gida”Kai ta gyaɗa amma da aka kira wata mawakiyar Fombina Rukayya aka saka waƙar ta sai ya waiga ya kalleta “Akwai inda zan fassara miki amma da sigar namiji zuwa mace”Kai ta gyaɗa.”kin san me amshin ke cewa?”Ta girgiza kai “Ni fa ko zo in kashe ki aka ce ba sani zan ba bare na shirya guduwa”Murmushi mai kyau yayi hannunshi na cikin nata yana wasa dashi a yadda suke maganan kallo ɗaya zaka musu ka san masoyan Juna ne kuma exchanging kalamai suke don fuskarsu a sake musamman ita dake ta doka murmushi.Ya fara yi mata”Mi ɗon yidi ma a anda mi don yiɗi ma na? Mi ɗon yidi ma Yideyel am nder bernde am.(Ina sonki baki san ina sonki Ba ne? Ina sonki masoyiyata har cikin zuciyata)”Sossai take blushing tana jin kidan wakan na mata daaɗi barin ma rawan da Matasan suke. Bai sake magana ba sai da aka zo wani wuri yana wasa da hannunta idanunshi a kan fuskarta yace “Ki ji! Yiide ma nde nangi am mi warti bumɗo!(Sonki da ya kama ni na zama makaho)Yiide nangi am mi warti ginnaɗo..!(Sonki ya kama ni na zama mahaukaci)Waru nangam giɗɗo am saklare hosi am!(Zo ki riƙe ni masoyiyata jiri/hajijiya ya kama ni)Mi ɗo numa ma jamma be nange mi nyamataa!(Kina cikin tunanina dare da rana bana iya cin abinci)Mi ɗo numa ma nange be jamma mi ɗanataa!(ina aikin tunaninki rana da dare bana iya bacci)”Hannunshi ta sake gimtsewa tana sake faɗada murmushinta ta ce cikin yanayin ‘yan koyo”Mi ɗon yidi ma a anda mi ɗon yidi ma naa mi ɗon yidi ma yideyel am nder bernde am”(Ina sonka baka san ina sonka bane? Ina sonka masoyina har cikin zuciyata)”Da gaske ko a waƙa?”Yayi tambayar yana ɗage gira daya cikin saloTa saki murmushi “Da wanne kayi kai?””Na taɓa miki wasan ina sonki? To ina sonki Afeefah! idan na kalle ki sai na ga cikakken kwanciyar hankali zuciyata ta samu natsuwa, kin kasance Abar alfarina!”A hankali in a whisper tace “Nima da gaske nake, ina sonka har cikin raina zan kuma zame maka macen da zata baka duk wani so da kulawar da ba’a taɓa baka irinshi ba, zan zame maka macen da ba zata taɓa ɓata maka da gangan ba, zan zama mai baka goyon baya a dukkan lamuran rayuwa, zan zama mai maka uzuri kuma zan kasance haskenka a duk sadda duhu ya nemi mamaye maka hanya, the girl you never want to argue with but communicate things out, the girl who love you for you ba don kudi ko mulki ba”Miƙewa tsamm yayi “Tashi mu tafi”Bai jira cewarta ba ya janye ta don tana cigaba da maganganun nan zai iya tafka abin kunya a bainar nasi duk nema take ta rikita shi ko ta kan Abeeha da ya hanga da Ameer yake so yayi magana bai bi ba ya buɗe mata ta shiga ya zagaya ya shiga aka ja su sai gida.

Back to top button