Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 21 By Ayshercool

Hanyar da ta bi ya bi da kallo, yana tunanin a ina ya taɓa ganin fuskarta.A ransa ya ce “Mahaukaciya ce kenan, Shiyasa aka aura mini ita, haukana ya fi naki” ya fito daga falon ya saka takalmansa ya fice.Jauhar kuwa durƙushewa tayi, ta ɗora hannunta a ka ta ce “Na shiga uku” a take ta fashe da kuka ta ce “Allah ka sanya mafarki ne ba gaske ba, Allah ka sa ba wannan ne mijin nawa ba? A gabana ya kashe wani, Allah Ubangiji ka rufa mini asiri ka dube ni, ya Allah ka dubi maraicina da ƙangin da na baro, ka sassauta mini a nan, ya Allah ka sa ba shi ne mijina ba”. Ta cigaba da addu’ar tana kuka, ta kasa fitowa sai ma ƙara sakata da ta yi a ɗakin tana kuka.A take komai ya dawo mata fes, yadda ta ganshi, ya yi kisan kai, hannunsa riƙe da mutum da wuƙa a gefen cikinsa.”Na shiga uku, ko biyoni yayi ya kasheni, me na yi masa wallahi ban gayawa kowa yayi kisa ba” tayi maganar ƙasa-ƙasa tana kuka.Ko da wasa ba ta yi yinƙurin, sake buɗe ƙofar nan, a banɗakik nan tayi alwalar magariba da ta isha’i, ta kasa addu’a komai, sai fatan Allah ya sa ba wannan ne mijinta ba.Ba ta sake fitowa ba, har garin Allah ya waye.Zaman ɗakin ya isheta, fitowa kuma ta gagareta, sai da ta leƙa ta ga babu kowa a falon, bakinta ɗauke da addu’a ta fito.Ba kowa, ta leƙa tsakar gida, ya rufe mata ƙofar, babu taklmansa kuma a wurin.Ta dawo falon, ya cinye taliya da man da da ta zuba masa tas, ya ajiye komai a wurin, hatta wadda ta ɗan zube a ƙasa bai kwashe ba, jug ɗin ma daban kofin jug ɗin daban.Ta kwashe komai ta fitar tsakar gida, ga sauran kwanukan da ta fara wankewa ta bar su a wurin, komai yana nan.Sai zuciyarta ta fara raya mata, ai ba shi ne mijin nata ba, ya shigo ne kawai ya tsorata ta, sai ta cigaba da addu’a Allah ya ƙara nesanta ta da shi.Ta yi ‘yan gyare-gyaren ta na gida, yaran da suke shigo mata, yau ba kowa duk sun tafi makaranta, ga tsakar gidan wasu irin manyan ƙadangaru suna bin bango, dan haka fitowa tsakar gidanma wahala yake bata, saboda tsoro.Ta datse gidan, yadda babu wanda zai shigo sai ya bubbuga.A jere ta sake jera kwana biyu ba ta sake saka shi a idonta ba, akwai ranar da bai kwana a gidan ba. Bai sake dawowa da rana ba, sai cikin daren nan, idan ya tarar da abinci ya zauna ya cinye abun sa, kafin ta tashi ya fice.Abun ya fara damunta, ga tsoron gidan take ji, sosai da sosai.Wajen la’asar ta ji ana buga ƙofa, ta din ga tambayar waye, amma ta ji shiru.Har zata haƙura da buɗe ƙofar, ta zata ba kowa, aka kuma buga gate ɗin maimakon ƙofar da ƙarfin gaske.A tsorace ta buɗe, aikuwa ya hankaɗo ƙofar, ta kuma kurma ihu, ta kwasa da gudu, ta shiga kitchen ta rufe ƙofa.Sororo ya tsaya yana tunanin, ihun me take yi dan ta ganshi? Ya basar ya shiga ya yi abun da zai yi ya fice.Sai a yanzu ta fara gazgata lallai wannan ne mai gidan, shi ne mijin da aka aura mata.Cikin kuka ta ce “Allah komai ka yi dai-dai ne, Allah ka sanya shi ne mafi alkhairin da nake ta fata”. Ta sanya wa zuciyarta za ta yi ƙoƙarin, danne tsoronsa da take ji, amma abun da ba ta gane na shi ne, ba iya abun da ya faru waccan ranar ne kawai yake ba ta tsoro ba, tsananin kwarjinin sa ne ke ƙara rikita ta.Suna dabarsu, Al’amin yana ta shan sigari, Walid ya ce “Maza, gaskiya abun da ka ke yi baya dacewa, an kai maka mata, amma kullum kana nan kana cakewa, akwai matsala ne?”.Al’amin ya rausayar da kai ya ce “Yarinyar Mahaukaciya ce ashe”Cikin rashin fahimta ya ce “Mahaukaciya kamar yaya?”.”Kamar yadda na gaya maka, ihu take yi itakaɗai”Walid ya ce “Ko dai tsorata ta ka ke yi? Ki tsaya kun yi magana kun gaisa?”Aminu ya ce “Da wa?””Da amaryar mana” ya ja tsaki, yana mayar da sigari bakinsa.”Wallahi Aminu da ni aka yi wa auren gatan da aka yi maka da na more, haba baka kyautawa gaskiya “Yayi masa shiru, yaƙi ko kallonsa, dan ko zancen auren ba ya son ji, haka kurum ji yake yi kamar an yi masa dabaibayi.Saifu kuwa yanzu ban da gaisuwa, babu abin da yake haɗa shi da da mama da Baba, dama Babar su hafsa Zakkyya ba shiri suke yi ba, ko kallo ba ta ishe shi ba.Sai dai sun fara zancen a kawo ‘yar aiki, dan duk yawan ‘yan matan gidan nan, ba sa iya aikin gidan, girki sai dai a jagwalgwala, wani ya ciwu wani ba zai ciwu ba, gidan nan kuwa wasu lokutan kamar fadar mahaukaciya, dama jauhar ce ana ɓatawa tana gyarawa, yara na cire kaya suna zubarwa tana kwashewa, amma yanzu bata nan babu mai gyarawa.Baba kuwa ƙasan zuciyarsa yana nadamar auren da ya yi wa jauhar, amma ba zai iya nuna hakan ba, ya duƙufa yana yi mata addu’ar samun kwanciyar hankali a gidan aurenta.Cikin dare da ya dawo, ya ji gidan a rufe, bai tsaya jiran komai ba, ya kama katanga ya dira kamar ɓarawo.Gaba ɗaya jauhar a zatonta, itakaɗai ta kwana a gidan, saboda ba ta ji bugun ƙofa ba, ta fito tana ta share-sharenta, ta ɗora ruwan zafin dafa makaroni, saboda su yaya saifu ya sayo mata, taliya makaroni, mai maggi sugar da sauransu.Ta fara bin ɗakunan tana gyarawa. Sai dai ta din ga jin warin taba, ta rasa daga ina take jin warin.Kawai ta nufi ɗakin da yake ciki, ba tare da ta san yana ciki ba, ta afka, a zatonta ita kaɗaice a gidan.Yana kashingiɗe yana zaune yana kaɗa ƙafa yana shan tabarsa, ya zazzage kayansa a kan katifar ɗakin, ghana must go ɗin, ya cillar da ita a tsakar ɗakin. Har da takalma a kan katifar, soson wanka da brush duk suna kan katifar.Ba wannan ba kawai, har da ledoji da kwalayen taba, ga tokar maganin sauro ko ina.Kamar mahaukaciya haka ta juya, ta ɗiba da gudu, sai dai a wannan karon, rufa mata baya ya yi, ya cimmata, tana ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin da ta shiga, ya hankaɗa ƙofar ta faɗi jikinta na wata irin tsuma.Ya zuba mata ido, wanda ya haddasa mata tsuma da karkarwa cikin razani da matsanancin tsoro.Bai ce mata komai ba, sai cigaba da kallonta da yake yi.”Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ban gayawa kowa ka kashe shi ba, dan Allah ka yi haƙuri, ni matar aure ce, ka daina shigo mini gida” tayi maganar wani irin gumi na tsatstsafowa daga fuskarta.Ya sunkuyo saitinta, warin sigarin da ya sha, tana dukan hancinta, sai a lokacin ya gane ta, ya gene a in da ya taɓa ganinta.”Kin ganni na kashe shi?”Ta jinjina kai alamar eh.”Mahaukaciya ce ke? Ki na da taɓun hankali ne?” Ta girgiza masa kai alamar a’a, tana ja da baya.”Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu” ya zaro wuƙa a ƙugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce “Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki”Ta girgiza kai ta ce “In sha Allah ba zan sake ba” ya miƙe, ya mayar da wuƙarsa ya fita ya bar ta.Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ƙara gazgata cewar, shi ɗin ne dai mijinta ba wani ba.Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa ɗakin da ta gano shi.Ɗakin yana nan, kamar mahaukaciya ta buɗe dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari ɗakin yake yi.Ta ɗaɗɗaga labulaye, ta zo ta durƙusa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ƙofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ɗakin tsaf, ta ɗauki brush ɗin sa da toothpaste, ta kai masa banɗakin cikin ɗakin, da bokiti da buta.Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta ɗauki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta ɗan ɗebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana.Gidan su jauhar, akwai maƙwabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ɗauki yaranta, ita ce ta haɗata da ‘yan gidan su, take karɓar shirin dutse tana yi.Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum ɗaya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan.Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata daɗi, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, saɓanin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata.Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. “Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su”Ta ɗan yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa kuɗin da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji.Tana ta tunani, ta ji ana buga ƙofa, cikin murna ta tashi, ta san baƙi tayi sa ɗebe mata kewa.Anty lubabtu ta gani, maƙwabciyar su, da ƙanwarta wadda take karɓar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba.Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu.Ta ce “Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nikaɗai, ba wanda yake leƙo ni”.”Ki yi haƙuri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur ‘yan gidanku da ‘yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, ‘yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ɗan daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana”.Ta ɗan rausayar da kai ta ce “Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran maƙwabta, ni kaɗai nake wuni”.Samira ta ce ‘Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?”Tayi murmushi ta ce “Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?””Taɓ kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?”Jauhar ta ce “Eh mana, zai din ga ɗebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi”Anty lubabtu ta ce “Jauhar iyayen neman kuɗi”.Samira ta ce “Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka”Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da ‘yan kayan buƙatu.Jauhar ta ji daɗin hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la’asar, sannan suka tafi.Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan haɗin sa, ta zauna ta shirya salak ɗin nan, ta juye miyar a tukunya, ta ƙara soyata tayi mata gyare-gyare ta ƙara mata su maggi da kayan ƙamshi ta kammala komai. Ta ɗebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta ɗebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta.Tana aikinta, tana jin radiyo a mp.Ta bawa yara kuɗi, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi.Ta gama aikin, ta share kitchen ɗin, ta kwaso sharar abun da ta ɓata, ta fito kawai ta ga Al’amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce “Yi haƙuri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba” tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo.Ta daɗe a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lallaɓa ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi.Ba ya falo, ta shiga ɗaki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa ɗakin da yake.Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, banɗakin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa.Ya gama wankan, ya ɗora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ɗaya ƙasa, sannan ya zaɓi wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba.’yar siririyar muryata ya ji a bakin ƙofar ɗakinsa, tana ta sallama.A fusace ya ce “Meye ne?”.Ta razana ta ɗan shigo daga bakin ƙofa ta tsuguna, ta ce “Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da kuɗi dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka”Ɗan shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu daɗi da bai haɗu da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta.”Ga kuɗin” muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi.”Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware” ta tashi ta ce “Kuɗin fa” banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin ɗakin.Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa kuɗin, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce “Ke!” A razane ta waiwayo.”Kwashe kuɗin nan ki bar nan” jiki na rawa, ta ɗauka ta ce “To bar mini ka yi” mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar ɗakin.Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi.Ta na shigowa yana fitowa daga ɗakin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ƙarasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce “Fita zaka yi, ga abinci” ta juya ta koma kitchen ta ɗaukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ɗora a kan wani plate ɗin ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al’amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba.Maimakon ya ɗebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya buɗe flask ɗin, ya juye salad ɗin a ciki, ya ɗaga flask ɗin miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma.Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi ɗaya, ɗaya kuma ta zuba masa ruwa.Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata.Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa ‘yan gidansu, suka zaɓa su aurar da ita ga shi? Gaba ɗaya yanayinta kalar ‘ya’yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan.Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba.Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da faɗuwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba.Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula ‘yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama ɗaya, dama taliya leda guda yake cinyewa.Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet ɗin ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin.A hankali ta ce “Na shiga uku, miya a kan carfet ɗina” da sauri ta kwashe kwanukan, ta ɗebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma ɗakinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar.Ya watso su duka gaba ɗaya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ƙara gaba.Ta sake gyara masa, ta kwaso wanda ya cire, da wanda ta kwashe na wanki ɗazu, ta fito ta jiƙa su zata wanke.Ta koma ta sake sharo falon, sai dai ta ga leda a in da Ya tashi, ta ɗauki ledar, ta taɓa ta buɗe, tana tunanin ko ita ta ajiye wani abun, amma ta ga wani abu kamar ganye a ciki, ta sinsuna ta kasa gane ko menene, kuma a iya tunanin ta, ba ta ajiye ba. Ta samu wani wurin ta ajiye, ta cigaba da aikinta.Sallama aka din ga rangaɗawa a ƙofar gida, ta wanke hannunta ta ce “Waye”Ya amsa da “Ni ne” ta saka mayafi, ta fita ta leƙa.Wani jibgegen ƙato ta gani, jiki duk a murɗe, duk bai kai girman Al’amin ba ba.A ɗan tsorace ta ce “Sannu”Ya ce “Yauwwa, matar gidan tana ciki ne?”Ta ce “Eh meyafaru?””Ɗan je ki ce mata ana sallama da Boss”Ta yatsuna fuska ta ce “Waye hakan?””Mai dogon zamani nake nufi, ba shi ne maigidan ba?”Jauhar ta ce “Ba wani mai irin sunan nan a gidan nan, ba sunansa kenan ba”Ya ce “Kee, ni fa nake rako shi har gidan nan, ki ce mini ba sunansa kenan ba?”Ta tsuke fuska ta ce “To shikenan idan ba ka yadda ba”ta mayar da ƙofa ta rufe.Walid ya koma gefe ya kira Al’amin ya ɗaga ya ce “Ya mai laya”.Walid ya ce “Na kiyayi mai zamani, maza na zo gidanka wata ‘yar cika, ta leƙo ta raina mini hankali, na kusa kwarfeta, na ƙyaleta ne kar na kwafsa””Wacece ya aka yi?””Kai na zo nema, ina ta jiranka, yaran nan za su karɓi kaya su rarraba, ba ka zo ba, na biyo ka gida, wata jar yarinya nunar rana mai kama da ‘yan china ta ce mini wai ba mai irin sunanka a gidan, na ce mata mai zamani wai ba gidan ba ne”Al’amin ya ce “Ita ce matar gidan fa””Kai haba maza, wannan ɗin?””Yarinyar da ta suma, na ce ka saka a kaita Asibiti”Walid ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, maza ka sha kwana wallahi, dama ita ce, kaga rabo, wata ‘yar caras beauty ka ji muryarta”.”Kai dalla malam, ka buga mata ƙofa, ka ce ta duba in da na tashi, na bar leda ta baka, ka tsaya shirme”.Walid ya ce “To meye na yi mini masifa kuma, na ga dai auren dole aka yi maka” katse wayar walid ya yi, yayi ashar ya ce “Ina da wannan, ai kan a ganni a ƙofar gida, sai an sha wuya, kai Aminu kamar ba biladam ba” yayi maganar yana bubbuga ƙofar gidan.Kamar ba zata buɗe ba, ta sake buɗewa cikin mamaki ta ce “Malam lafiya?” “Ya ce ki duba in da ya tashi, ya manta leda ki bani””Shi wa?”Cikin mamakin yadda take neman raina masa hankali ya ce “Maigidan””Dan Allah ka yi haƙuri, bai bar mini wannan sallahun ba”Ya ce “Saboda bai bar miki sallahu ba, ba zaki bayar ba?”Ta marairaice ta ce “Idan na baka ya dawo, ya ce mini ba shi ya aikoka ba, kaga bani da abun da zan ce masa”.Ya ce “Gaskiya ne, shikenan” ya juya ya tafi, ta mayar da ƙofar ta rufe.Duk da kayan suna da nauyi, haka ta zage ƙarfinta a kan kayan nan, ta wanke su.Sai a lokacin ta kalli window, ta ga mpn da ta ɗaukko masa ta ce “Na shiga uku, da ya ganta fa me zan ce masa?” Ta ɗauka ta mayar masa ɗakinsaAl’amin kuwa duk in da ya juya, sai dai ya yi gyatsa saboda yadda ya ƙoshi.Walid ya je ya samu Al’amin, ya  din ga yi masa mitar yadda jauhar fafur ta hana shi saƙon nan. Yayi ya gama, bai ce masa komai ba, sai sakace da yake yi, yana cigaba da jin ƙamshin miyar da ya ci a hannunsa.”Yanzu mai zamani shikenan yau b za a sayar da kaya ba? Saboda ka yi aure ‘yar yarinya ta hana aiki yau?”Al’amin ya kalle shi ya ce “Ƙila”Yayi tsaki ya ce “Yauwwa, na haɗa maka da mp ɗina a kayanka, ka kawo mini kayata kafin ita ma ta ce taka ce ba zata bayar ba”Al’amin ya tuna ya ganta a kan window, kuma ya ga yadda ta gyara masa ɗakin, ya tabattar ɗauka tayi ta kunna.A ransa ya ce ‘Ashe ba tsoron ki ke da gaske ba'”Malam magana nake yi maka, a kawo mini mp ɗina. Yunwa ma nake ji, ko zamu je cin garau-garau ne?”.Aminu ya miƙe ƙafa ya ce “Sai ka dawo”Walid ya fice yana tunanin asarar da za su yi, na rashin sayar da kayan nan yau, ya san ko zasu dambace da Al’amin, ba zai koma gidan nan ya ɗaukko kayan ba.Ƙarfe tara na dare ya shiga cikin unguwar, tare da su liti, da Walid, sai dai ba su shiga cikin gidan ba, suka zauna a barandar kusa da gidan, suka din ga hira suna shaye-shaye.Jauhar kuwa kamar a cikin falonta suke shaye-shayen, saboda yadda duk gidan ya gauraye da wari.Yau da gari yayi haske ta fito, a falo ta tarar da shi, a kwance a kan doguwar kujera.Ta durƙusa ta ce “Yaya ina kwana” waiwayowa yayi ya kalleta ya kawar da kansa, sai dai ba ta tashi ba.Har ta fitar da ran zai amsa ya ce “Lafiya”Ta miƙo masa leda ta ce “Ga abun da ka manta jiya, wani ya zo ya ce ka aiko shi, ni dai ban bashi ba. Na ga kamar ganyen shayi ne, ko na ɗiba na dafa mana tea?” Afujajan ya kalleta, tashi ya yi zaune ya ce “Da me zaki dafa tea ɗin?” Ta nuna masa ledar tana sunkuyar da kai ta ce “Naga kamar ganyen shayi ne, sai na dafa mana ko jallof ɗin taliya ce?” “Wiwin zaki dafa a matsayin shayi, saboda mahaukaciya ce ke?”Da sauri ta kalleshi ta saki ledar da sauri, sai dai ba ta ji daɗin mahaukaciya da ya kira ta da ita ba.”Dan Allah ka yi haƙuri, ban sani bane”.”Jiya mai laya ya zo, ya ce miki yana neman mai dogon zamani, kin ce ke baki san shi ba, to ni ne mai dogon zamani, idan kuma jami’an tsaro ne suka ce miki Viper ni suke nema, idan ki ka cigaba da yi musu rashin kunya kuma, za su sassaraki ne a banza su bawa karnuka namanki”Shagwaɓe fuska ta yi zata yi kuka ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, dan Allah ka bashi haƙuri, ba zan sake ba, dama ban san me zai yi maka bane, shiyasa na ce masa ba kai bane ba shiyasa”Ya saka hannu ya ɗauki ledarsa ya tashi zai fita ta ce “To karin kumallon fa” ko waiwayowa bai yi ba, ya fita.Bayan fitarsa, ta je ta kwaso kayansa da ta wanke, ta ninke su tsaf, ta shiga ɗakinsa, tana shirya masa kayan, ta fito masa da guda ɗaya da zai saka, ta ɗaukko bedsheet tana canzawa katifarsa, kawai ta yi karo da wata irin zabgegiyar wuƙa.Gabanta ya faɗi wuƙar kawai abun tsoro ce.”Innalillahi wa Innalillahi raji’un, jikinta na rawa ta hau kuka, ta kai hannu za ta ɗauka””Idan ta ji miki rauni, ke ki ka sani”.A razane ta ɗago jikinta na tsuma.”Fita ki bar mini ɗaki, bincike ki ke yi mini ko?”Ta girgiza kai ta ce “A’a wallahi, bedsheet zan canza maka na ganta, ba bincike nake yi maka ba””Fita to”Ta ce “To, ga kaya na fito maka da su, wanda zaka saka”.Ya sake tsuke fuska ya ce “Ki fita na ce” Ta zo fita, ta kasa saboda yana tsaye a wurin.Yayi tsaki ya bata hanya, ta fita har da tuntuɓe, a tsakiyar falon ta ga ledar buredi, da sugar da madara da Lipton.Ta lallaɓa ta fita ta kunna gas, ta ɗora shayi.Buga gate ɗin gidan ake yi da ƙarfi, ba shiri ta tafi ta buɗe.Wani matashin magidanci ta gani, a tsaye ya kima uwar hula, ya rufe kunnuwa.Ta gaishe shi cikin ladabi, ya ce “Ina matar gidan?” Mamaki take yi, meyasa mutane suke neman matar gidan idan suka ganta.”Lafiya?””Eh, megidan muke nema? Sunana malam lawan, ni ne mai wannan gidan na kusa da ke”Jauhar ta yi murmushi ta ce “Allah sarki, baban su halimatu? Ai suna shigo mini”.”Eh, mai unguwa yana neman mijinki, ƙararsa muka kai”Ta ce “Subhanallah, laifin me yayi muku?””Au jira zamu yi sai ya yi kan mu ɗauki mataki, an ce mana mutumin banza ne, kuma da ya zo bai yi mana sallama ba, bamu san da wani irin mutum zamu zauna ba, jiya an hanamu sukunk da warin wiwi, ya tara mana ‘yan iska a layi. An gaya mana gawurtaccen ɗan daba ne da ya addabi in da yake, aka yi masa aure mu aka kawo mana bala’i. Gara aje a zauna da mai unguwa da ‘yan sanda, ko ya tashi, ko ayi yarjejeniyar zaman lafiya da shi”.Jauhar ta ce “Haba malam, bai yi muku komai ba kuma sai a kai shi wurin ‘yan sanda, ina laifin mai unguwar ma, in sha Allah ba zai sake sha muku komai a layi ba, kuma ba zai cutar da kowa ba ma. In sha Allah wataran sai labari zai daina”.”Ke rufe mini baki kan na kwaɗe ki, nasiha zaki yi mini, ba zamu zauna da mutumin banza da wofi ba wallahi, ya lalata mana yara haka kurum ba”Motsi ta ji a bayanta, tana waiwayawa ta ganshi a tsaye, ashe duk ya ji abun da malam lawan ke faɗa.Da sauri ta leƙa ta ce “Ka tafi kar ka bari ya ganka”ta waiwayo ta rufe gate ɗin tana kallonsa.”Ya tafi kar ya bari na ganshi ko? To ke bari na yi miki abun da zan yi masa”.

Ayshercool 08081012143

Back to top button