Hausa novels

Wace ce ita (who was she) Page 58 Hausa Novel

WACEC ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

FIFTY-EIGHT📍

Har ze ce masa baze rakasa ba sai kuma yayi wani tinani, yasan halin sudais da shegen wasa da tsokana, yanzu zeje ya sakata a gaba har sai ta saba dashi, gwara ya bisa suna gaisawa da mutanen ciki yace sai sun fito, yana jin kunyar haduwa da umm matuka amma ya gwammaci yabi sudais suje a haka, sannan su abbas ma yasan zasu shigo anjima so gwara yasa ido akan kowa, sauka yayi daga gadon yana fadin;
“Excuse me in shirya toh”….
Sannan ya shige toilet….
Binsa da kallon mamaki sudais yayi dan be taba tinanin deen ze amince ya rakasa babu jan rai babu komai musamman yanda ya gama tsokanarsa yanzu….
Tashi yayi ya koma parlour ya samu guri ya zauna yana latsa wayarsa…
Bayan minti talatin sai gashi ya fito cikin wani dark blue short sleeve kaftan daya bayyana muscles dinsa da kallo daya zaka masa kasan kakkarfa ne, coily gashin kansa daya sha gyara sai sheki yake me daukan hankali, gemunnan ko sai sheki yake gwanin sha’awa kamar mutum ya taba, sai matching shoes da wrist watch daya saka masu shegen kyau, kamshi ko kamar anyi barin turare a jikinsa, gaba ki daya sai glowing yake looking so ravishing, he just look as handsome as ever, kana ganinsa kaga asalin shuwa arab, wasu ma kallon balarabe suke masa saboda yanayin features dinsa…..
Sudais na ganinsa ya mike, washe baki yayi yace;
“Ka hadu fa mutumina shiyasa yan mata ke crushing, wallahi akwai wata yarinya ma da taga na saka hotonka a IG wai na bata numberka ka mata, saif for the ladies hahaha”….
“Zaka wuce mu tafi ko sai na komawata ciki?”…
Deen ya fada yana harararsa batareda ya biyewa wanchan maganar da yayi ba……

Yan matan kadai ne a zaune a parlour sunata shapta abunsu, ko wacce taci gayu da ado kamar zasu gasar kyau, baby tee na cikinsu itama dan tinda ta tashi umm ta fatattakota wai tashiga cikin yan uwanta, lace ne na gani na fada a jikinta an masa dinki riga da skirt na zamani, dass kayan ya zauna mata a jiki dan dama haka yanayin jikinta yake, komai tasa sai yabi ya kwanta, karyane kaga tana yawo a cikin kaya saboda irin karuwan jikine da ita mai daukan kowani kaya, ita kanta tasan tayi kyau dan duk inda tabi a gidan sai an bita da ido, har ta gaji da jin kinyi kyau, inda Allah ya taimaketa ma rigar ta dan sauka kadan amma a hakan ma kowa ya kalleta yasan anyi mace a gurin, English gold din da Abby ya siyamata ta saka sai walkiya yake a wuyarta, kana gani kasan an narka kudi sosai akai, babu yanda siyama batayi da ita akan ta mata makeup ba ta ki, karshe da taga abun ya isheta taje ta samu mami tace ta mata irin wanda ta mata da zataje gurin Abby, a hakanma bata tsira ba saboda mami saida ta kara mata wasu abubuwan, sai hakan ya kara fito da kyanta, ta zama kamar wata celebrity tayi outshining kowa harda masu heavy make up, mayafi me dan girma umm ta bata tace incase in maza sun fara taruwa sai ta saka kar ayita kallonta, amma a inda umm ta bata mayafin anan ta barshi ko tace ma batasan inda ta kaishi ba a ganinta abun cikin gidane ba sai tasa mayafi ba……
Suna tafe zuwa part din mami sudais na gaba deen biye dashi a baya yana waya, bayan sun karaso kofar part din sudais yayi gaba shi kuma deen ya tsaya dan ya karashe official call din da yake……
Sallamar sudais ne yasa hankalin yan matan duka ya dawo kansa banda baby tee da take tsaye tana chargi tana chat da khaleel sunata zuba soyayyarsu abunsu, da sauri sukayi kansa suna yaya sudais oyoyo saboda yanda yake wasa dasu shiyasa kowa na ganinsa yake murna, har suka karaso inda yake be sani ba saboda guri daya daya kafe da ido ko kiftawa bayayi……
Cikin shagwapa hussy tayi waving hand dinta a saman fuskarsa tana fadin;
“Haba yaya sudais ka dade baga ganmu ba shine ko murnan ganinmu bakayi”…
Sai a lokacin ya dawo da kallonsa kansu, murmushi yayi batareda ya bata amsar waccen maganar ba ya nuna baby tee data juya baya yace;
“WACECE ITA?”…..
Juyawa hussy tayi taga wacce yake nufi, dariya tayi tace;
“Oh baby tee? She’s umm’s daughter, ita za’ayiwa welcoming party dinnan fa”……
“Ohk ohk, kirawo min ita mu gaisa toh”…..
Ba musu ta tafi tacewa baby tee yaya sudais na kiranta, bata tambayeta waye ba saboda umm ta gargadeta akan ta saki jiki da kowa duka yan uwanta, sannan ita kanta she’s looking forward to knowing everyone, ajiye wayar tayi tabi bayan hussy suka karasa gurinsa……
Tinda ta juyo sudais yayi mutuwar tsaye a gurin, sauran yan matan na masa magana amma gabadaya besan abinda suke cewa ba, in banda masha Allah babu abinda yake maimaitawa aransa, kafeta da ido yayi har suka karaso inda yake……
Cikin sirirriyar muryarta me sanyi da amo tace;
“Ina kwana”……
Wani irin ajiyar zuciya da be shirya ba ya sauke saboda wani yanayi da dadin muryarta yasa masa, murmushi yayi still looking at her yace;
“Kin tashi lafiya dear? Kowa ya ganni ya tawo shine ke kika ki zuwa ko?”….
Murmushin tayi tace;
“Alhamdulillah, bansan ka shigo bane”…..
“Okay, let me introduce myself to you, I am sudais, everyone’s favorite, I hope I’ll be your favorite too?”……
“Insha Allah yaya sudais”….
Ta fada tana barin gurin saboda wayarta dake ringing, tana zuwa taga eesha ce, dauka tayi suka danyi magana sannan ta kashe…..
Tana barin gurin suma suka koma inda suka taso wai sunyi fushi yaki kulasu tin dazu sai ya basu hakuri, yana shirin binsu deen ya shigo, tsit parlourn yayi kamar babu wani halitta a ciki, tsugunawa sukayi suka hau gaisheshi a tare, ko kallonsu beyiba ya samu guri ta daya side din ya zauna, dawowa sudais yayi ya zauna a kusa dashi yace;
“Kai fa baka da kirki wallahi, yara na gaisheka kayi banza dasu idan kuma basu gaisheka ba kace zaka musu masifa”…..
Tin kafin ya karasa deen ya masa wani kallo yace;
“Da suka gaisheni kuma sai ya zama dole na amsa? “…..
Tapping kafadarsa sudais yayi with a serious look yace;
“Mai da wukar boss man, ni yanzu abinda yake damuna yafi karfin kaina”…..
“Me yake damunka?”….
Deen ya tambayesa with so much attention, haka yake ko a wani yanayi yake bayasan wanda yake tare dashi ya kasance cikin damuwa……
“Watace ta sace zuciyata farat daya and I’m very serious saif, kasan dai na saba admiring mata amma bantaba cewa ga wacce nake so ba, amma dagaske wannan sonta nake kuma da aure”…..
Gajeran tsaki deen yaja yana dauke kai, kamar ya share sudais sai kuma ya tabe baki yace;
“Tana da kaya ko babu? Dan nasan ba karamin abu ne ya saka sha’awar aurenta”…..
Dariyar da sudais be shirya ba yayi, sannan yayi kasa da muryarsa yace;
“Kutumar uba wannan ai tafi karfin ace kaya kawai, kai ka ganta ne? Wallahi komai yaji gaba da baya babu inda baza’a more ba, kai ni ban taba ganin kayan daya ja hankalina irin wannan ba”…..
“Matsalata da kai baka da lissafi sudais, ni nasan dama ba a banza ka rude haka ba, toh what if in ka aureta nan gaba kaga wacce ta fita kaya sai ka sake aurowa? Haka zaka tayi har ka dawo kana auri saki? Honestly this is not true love, in bazaka so mutum dan Allah ba sai Allah ya baka me kayan that will be your worst nightmare”……
Jikin sudais ne yayi sanyi amma beyi kasa a gwiwa ba yace;
“I know all this saif kuma wallahi tsakani da Allah nake sonta, kasan dai love also comes with lust and I can’t marry someone I’m not attracted to, believe me she’s not the type of person I can use and dump”…..
“WHO IS SHE?”…..
Deen ya tambaya yana kallon ceiling…..
Amsa ya bashi da;
“Over there! Using her phone”……
Juyawa deen yayi daidai lokacin itama ta dan juyo idonsu ya fada cikin na juna, razana deen yayi ya tashi zaune, sai kuma ya kalli sudais cikin wani irin murya yace;
“But you don’t mean what you said right? Are you stupid sudais? Yanzu duk wannan zancen dana biyemaka ina saurara duk akan yarinyar umm ne? Sudais wani kalan highest form of disrespect ne wannan?, baby tee din ka karewa kallo har kasan tanada kaya? Duka duka guda nawa take for God’s sake? Sudais na dauka shirmenka a iya yan waje ne ashe abun naka har ya kai kafara screening mutanen gidan? idan umm taji abinda ka fada how do you think she’ll feel, sudais baby tee din kake fadamin komai yaji za’a wuta a jikinta? Sai kazo ka huta a jikinnata mugani! Wallahi ka bani mamaki, wannan maganganun banzan da kayi kuma ka dauka umm taji ta gama!!!”…
A rikice sudais da hankalinsa ya tashi ganin deen ya juya masa maganganunsa duka yace;
“Listen to me saif, wallahi ba wani abu nake nufi ba, bakaji nace aurenta nake…..”
Buga kujerar da suke kai yayi ya dakatar dashi tun kafin ya karasa;
“Fuck you! Just shut up sudais!”..
Sai kuma ya juyo kan baby tee da tinda suka hada ido bata sake juyowa ba sannan bata bar gurin ba, wata muguwar harara ya aika mata cikin daga murya yace;
“Zaharahhh get out of here!”…..
“You all should leave too!!”…..
Ya daka musu tsawa suma…..
Rigen rigen tashi sukayi dan dama tinda ya buga kujera yayiwa sudais ihu suka sha jinin jikinsu even though basu san meya hadasu ba, zare wayarta a chargi tayi itama tabi bayansu tana zaginsa a ranta…….
“Kai kuma await the outcome of the stupidity you did banza dan iska kawai!!”….
Deen ya fada da karfi yana barin parlourn, bin bayansa sudais yayi yanata basa hakuri ya sauraresa shi kuma yaki har suka karasa part dinsa, yana shiga ya rufe kofa yabar sudais a tsaye a bakin kofa……..
Shigewa cikin bedroom yayi yana rike da kansa, sai a lokacin yaji maganganun sudais na dawo masa, he can’t believe ya zauna yaji wannnan shirmen akan zahrah, da yasan ita yake nufi tin farko da ya taka masa burki amma ya zauna kamar wani mara hankali sudais ya zubo masa duk haukar dake ransa, wani abu ne ya sake fado masa yaji gabadaya duniyar ta masa zafi, abun shine khaleel, tinani yake kila khaleel ma saboda kayan nata ya nace mata tinda tayi zaman gidansu tin bata kai haka ba, dole ya gama kare mata kallo yasan komai, girgiza kansa ya hau yi zuciyarsa na tafarfasa…. Ya dade a zaune a haka kafin ya tashi ya shiga toilet ya kunna shower ruwa na sauka a kansa zuwa jikinsa batareda ya cire kaya ba, yayi hakan ne ko ze samu sauki aransa, yafi 20mins beji abinda yakeji ya ragu ba, kawai ya cigaba da tsayuwa har sai ya samu salama….

Daki daya suka shige suka rufe kofa saboda tsoron kar ya biyosu ya musu wani abu, harda baby tee da sukace sai ta shigo itama karya biyota dan babu ruwansa da bako rashin mutunci ze mata, gashi dama ita ya fara kora….
Sun fi 20mins babu wanda yace komai kafin finally raihan tace;
“Gaskiya guy dinnan yanada case, yanzu me muka mishi daze koremu haka?”…..
“Kardai ki zagar min shi toh, I love him regardless”….
Cewar ilham tana hararar raihan……
“Wai ke bazaki dena wannan wasan ba? Yaya saif din kikeso, wake up from your dream baby”….
Cewar siyama tana dariya….
“Toh meye a ciki dan ina sonsa, nifa wallahi yana burgeni, ina samun soyayyarsa nasan hankalina kwance saboda babu wacce ze kalla sai ni kadai, ko matsowa gurinsa kukayi nasan tsap zaku sha mari, a yanda nake da kishinnan kuma ai ya saukakamin da baya daukan nonsense bare wata ta gane min abuna tace tanaso”……
Karap baby tee da bata tanka musu ba tinda suka fara tace;
“Saif din? Kawai saboda mutum ya matso kusa dashi sai ya maresa?”….
“Dan Allah ki rufamana asiri kar yazo wucewa yaji kince masa saif, wallahi abinda yafi mari ma zeyi idan kika sake kika matsa kusa dashi”….
Cewar hassy tana toshewa baby tee baki, ita dama haka take tsoro ne da ita kamar farar kura…..
Haushi ta bata ta janye hannunta daga bakinta tace;
“No this is a joke! Be isa ba!”….
Wani irin kallo ilham ta mata dama tanajin haushin yanda take da ji da kai tace;
“Toh ko zaki gwada ne?”…..
Smirking baby tee tayi tace;
“A nawa? I love challenges!”…..
“Allah ko? You would soon hate challenges kuwa! Ko nawa kikeso, we can make it a deal naga kina wani ji da kanki”…..
Cewar ilham data kasa boye abinda ke ranta….
Murmushi me ma’ana baby tee tayi tace;
“Lol! Nawa ne a bank account dinki? And which type of phone are you using?”…..
“I have up to a million and this is an iPhone 12 Pro max!”…..
Tabe baki tayi tace;
“Not bad, I can accept them, matsawa kusa dashi kawai kikeso nayi ko?”….
“No hugging dinsa nakeso kiyi muga karshen loving challenge, na miki alkawari kuma I’ll empty my bank account for you plus this my phone idan yayi hugging dinki back ko be tureki ba because I know he’s gonna push you away ya hada miki da mari kuma”……
Dariya baby tee tayi tace;
“It’s alright, just get ready to lose everything you have soon”….
Dakatar da ita ilham tana dariya itama tace;
“Wait I have another condition”…..
“Go on”..,.
“So nake kiyi hugging dinsa a cikin mutane lokacin da ake barbecue, nasan lokacin yan mata da samari an cika, and what will you give me in return if he push you or slap you?”…..
Wani devilish smile baby tee tayi tace;
“What do you want?”……
“How much is in your bank account too? And na ganki da latest Samsung a hannu in taki ce ina sonta itama….
“Tawa ce! I don’t know how much is in my bank account, just mention any amount in million”…..
Wani irin shegen kallo ilham ta mata na irin me kike takama dashi haka sannan tayi murmushin mugunta tace;
“5m! In muka hada da wayarki we’re talking of almost 8m, are you sure you’re ready to risky all that?”….
“Deal accepted!”….
Ta fada tana shirin barin dakin…..
Dakatar da ita ilham tayi da fadin;
“Gaskiya banyarda da haka ba, mu yiwa hassy transfer ta rike komai, duk wanda yayi wining deal din sai ta bashi, kar inyi winning ki ki bayarwa”…..
“If you say so”
Baby tee ta fada tana dawowa dakin…..
“Ni dai kar wanda ya min transfer! Dan Allah kar kuyi, haba ilham nasan so kike kawai kici mata kudi, baby tee be kamata ba this is more like a gambling game karkiyi please”….
Hassy ta fada har zuciyarta…
“And who cares?”….
Baby tee ta fada tana murmushi….
“Kingani ko? Tana ta cika baki shine zakice a bari, toh gaskiya sai anyi, siyama ke bada account dinki ayi transfer din in hassy bazata bayar ba”…..
Da yake siyama yan abi yarima asha kida ne, babu bata lokaci tace suyi transfer sannan su miko wayoyinsu, duk wanda yayi winning kuma zata mika masa duka…..
Sai a lokacin baby tee ta tina sababbin wayoyi ne a hannunta haryanzu bata saita mobile app dinta ba so ba dama tayi transfer har na 5m, mikawa siyama wayarta tayi tace;
“Take the phone sai ki bani account number dinki insa a miki transfer a kudin ajiyana, I don’t want to touch my personal money”…..
Wani irin kallo duka yan dakin suka bita dashi suna tinanin ta ina ta samo kudin duka ita da akace ba’a dade da gani ba, sun san dai umm nada kudi but it’s so soon ace harta bata wannan uban kudin and they have no idea who her father is, su sun dauka ma zasu zo su ganta duk sai a hankali, sai sukaga classy babe me tsinannan ji da kanta….
Karba siyama tayi tace;
“Yayi hajajju, I love your courage mehn!”….
Sannan ta rubuta mata account number a paper…..
Karba tayi ta fita batareda ta kulata ba, bedroom dinta ta koma ta bude bedside drawer ta dauki iphone 14 pro max dinta da Abby ya kawo mata tareda wanchan Samsung din, dauka tayi ta kunna sannan ta fita daga dakin, kalle kalle tashigayi tana neman inda zatayi making call batareda kowa ya jita ba, dama Abby zata kira saboda kullum in sukayi waya sai ya jaddada mata akan fadamasa duk wata bukatarta kota me cece amma kullum sai tace bakomai, so this is the right opportunity for that, fita tayi daga part din gabadaya ganin babu inda zatayi waya safely anan, garden ta nufa straightly ta tsaya gaban wani flower tana dialing number Abby, saidai kash akayi rashin sa’a numbersa a kashe, sau uku tana kira still numbersa a kashe, dafe kanta tayi tana tinanin umm is her next option, tasan zata bata amma dole sai ta amsa query, kuma bata isa ta fadi gaskiyar abinda zatayi da kudin ba, juyowa tayi da nufin komawa ciki kawai ta hangoshi a zaune dan nesa da inda take, sarai ya ganta amma yayi kamar be ganta ba, dakewa kawai tayi ta karasa inda yake…..
Zama tayi a kusa dashi wai ta danyi practical kafin main deal din, kawai taga ya dauke kai kamar besan anyi halittarta a gurin ba, matsawa ta sakeyi kamar zata shige jikinsa, ya mata wani irin kallo yace;
“Meye kikeyi hakan? Sanyi kikeji ne?”….
Janyewa tayi kamar zatayi kuka tace;
“Shine ka tureni?”….
Zaro ido yayi yaja hancinta yace;
“Ni yaushe na tureki baby girl?”….
Wani irin sanyi taji aranta ta sake matsawa kusa dashi harda dora kanta a kafadarsa wai duk a cikin practical din sannan tace;
“Aro nakeso ka bani dan Allah yaya”….
Be rukota ba sannan kuma be janyeta ba yace;
“Aron me? Ni fa bana bada aro amma fadi abinda kikeso naji?”……
“5 million nakeso, wallahi zan dawo maka dashi, I just need to do something urgently”…
“Me zakiyi dashi?”…..
“Wani kaya muka hada kudi mukayi joint order shine kayan sukazo yanzu, toh babu kudin shipping din a kasa shine nakeso mu ara sai mu bayar da zaran munyiwa mutane supplying an bamu kudin mu”…..
Ta shirya masa karya kai kace dagaske ne…..
Murmushi me kayatarwa yayi ya mintsine ta a hannu yace;
“Iyeee anmatan umm ashe upcoming CEO ce, I’m glad seriously, ni kyauta zan baki inyaso sai ki karba in kun hada kudin, bani account number dinki insa a miki transfer from one of my company’s account, I can’t transfer because I haven’t set my app”…..
Kankame hannunsa tayi a kirjinta tana mika masa paper dake hannunta sannan tace;
“Thank you so much yaya, nima kasan sabon waya ne ban riga nayi setting app dina ba, kace suyi transferring to this account…
Lallabawa yayi ya zare hannunsa daga kirjinta jin ya fara shiga wani yanayi sannan yayi murmushi ya karbi paper yayi typing account number din a inbox dinsa ya turawa cashier dinsa with short message a kasa, ba sufi 5mins ba sai ga cashier din yayi responding da done sir, kunna datansa yayi yaga ya turo masa receipt din ta WhatsApp, dawo da kallonsa kanta yayi yace;
“Bani numberki in tura miki receipt din sai ki tura musu”….
Da sauri ta karanto masa number cike da farinciki, tana zaune harya tura mata sannan ta mike tace masa zata wuce, ruko hannunta yayi yace;
“Dan Allah let me be the first you tell your problems before anyone, and don’t hesitate to tell me when you need anything okay?”…..
“Insha Allah”….
Sannan ta bar gurin, binta da kallo yayi harta bace ma ganinsa…..
Komawa gurinsu tayi, tana shiga sukasa ihu wai siyama taga alert, tana jin haka kawai ta fice ta barsu sai hyping dinta suke….
Around 2pm aka fara barbecue, kafin 3pm yan mata da samari sun cika harabar gidan, dake manyan suna cikin gida, mutane ne kala kala a cikinsu harda friends din ilham sosai dake dama ita a abuja suke zaune, haka sauran ma kowa zaka samu da gayyarsa, wasu kuma samarin familyn ne sukayi inviting yan matansu da abokansa da ire irensu duka……
Ko wacce ka kala sai sheki takeyi kowa ya dau wanka na kece raini, wannan na wane wane, kowa sam barka…..
Suna zaune sun kasa sun tsare suna jiran fitowar deen, har abbass ilham ta kira ta tambaya a boye ya tabbatar mata da saif ze fito, baby tee ma na zaune looking so breathtaking tana jiran fitowarshi duk abinda ze faru ya faru, deep down she’s feeling so nervous saboda uban mutanen dake gurin kar hakan yasa ya tureta kamar yanda suke fada fa, kuma ko a gaban mami da umm yana mata masifa bare tarin mutane haka, duk sai taji ta karaya gabadaya itada take da hope da, abu daya ne yake dan kwantar mata da hankali inta tina 5m din data bayar ba kudinta bane sai taji asarar da zatayi da sauki…….
Kamar a mafarki sai gashi ya fito yana taku kamar wani sarki, nan da nan kallo ya koma kansa baga yan matan ba baga mazan ba, kowa sai fadar irin haduwarsa yakeyi, duk inda kabi maganarsa akeyi, abu sai ya zama kamar shine star din event din, tabo baby tee ilham tayi tace;
“Your time has started, ki tabbatar kin rungumeshi yana tsaye sannan ta gaba bata baya ba”…..
Mikewa baby tee tayi gabanta na faduwa amma a haka bazakace tana tsoro ba, tana barin gurin eesha ta karaso gurin….
Baby tee na tashi sai kallo ya dawo kanta kuma, deen na tafe yaji wani yacewa na gefensa;
“Kai kaga wata chika, wai gaskiya yarinyar nan ta hadu”….
Haka kawai yaji hankalinsa be kwanta da wacce ake magana akai ba, juyowa yayi daidai lokacin ita kuma ta karaso inda yake, yana shirin yin magana kawai yaga ta rungumeshi a bainan-nasi!!! Kankace me guri yayi tsit kallo ya koma kansu….. Dagowar da deen zeyi sukayi ido hudu da khaleel da be dade da karasowa ba idonsa ya masa mummunan gani…… Hakan yake da eesha itama da taga abun kamar almara…..
Saboda bakin cikin ganin khaleel deen besan sanda yayi hugging dinta back ba, sannan ya dauketa chak suka bar gurin….

Back to top button