Haihuwa Da Hanji Page 2 Hausa Novel
Nannauyar numfashi ta sauƙe sai kuma ta fita daga tsoro ta shiga fargaba, kawu ne! Me ta yi? Jikinta a sanyaye ta miƙe tsaye ta turo kofan ta fito.”Iskancin naki ya kai ina ƙiranki kina ji na ki yi min banza ko? Ko har kin tafi meeting naku na cin ɗanyen naman mutane ne?”Girgiza kai ta yi tana wasa da yatsun ta murya na ɗan rawa ta furta”Ka yi haƙuri kawu bacci na fara ne”Tsaki ya ja yana jefanta da mugun kallo, babu yadda ya iya ne kawai yarinyar ke zaune gidan shi in ba haka ba babu abinda zai sa ya ajiye makashiyar mamarshi da ‘yan uwanshi har ya ke bata abinci tabbas da ana kashe mutum a sha a banza da tuni ya yanke wuyanta ya jefar da gawar daji tsuntsaye sun cinye, duniya in akwai wacce ya tsani ko inuwarta ya gani ya biyo bayanta. “Ba dai a mawankin chan za ki bar mana kwanuka su kwana ba kan safe duk shedan ya bi ya fitsare mana kwanuka? Oh ko so kike duk ki kashe mu ne ki huta?”Lip ɗinta na ƙasa ta ɗan datse a hankali kan ta saki ta furta”Kayi hakuri zan yi”Ya ja tsaki kan ya juya ya wuce ɗakin inna Asabe.Mawankin dai ta wuce akwai ɗan guntun omo haka ta fara wanke wanken idanunta kaman za su cire saboda raɗaɗin bacci har kifewa take yi bisa kwanukan tana tashi sai da kusan duk kowa yayi bacci a gidan kan ta gama kifewa ta wuce nata akurkin sanyi kaman zai kasheta ta shige cikin zaninta bayan ta sauya hijabi zuwa busasshe dukunkune haka tayi baccin. Kaman jiya yau ma dai kowani ɗan adam na kwance yana bacci haka ta fita tsakar gidan ta shiga aikin abincin tallar inna larai.Ba don ba’a sabo da wuya ba zata iya cewa wahala ya riga ya zama jininta, bata san yadda zata fassara rayuwa ba sai dai ta san ƙaddararta mai matuƙar zafi ne da ta kan rasa sanyi ko sama ko ƙasa a duk sadda ta rura wutar ta. Bata da farin ciki ko ɗaya bata da mai tambayar damuwarta ko ciwonta har ma da bukatuwarta waenda suke tare da ita amfana da ita kaɗai suka iya amma ita bayan mafaka da kwanon abinci sau ɗaya a wulakance bata anfanuwa da su ko ta wani ɓangare, manyan su zaga, matasan su daka su kuma hantara yaran su wulakantata bata da bakin magana saboda ita ɗin ta riga ta zama annoba…Eh annoba zata ƙira kanta kaman yadda kowa ke kiranta an haife ta da rashin sa’a tunda tana ciki watanninta basu wuci biyar ba Allah ya karɓi mahaifinta, a wurin haihuwar ta Allah ya karɓi mahaifiyarta ta zama cikakkiyar marainiya daga ranar da ta faɗo duniya, kakarta ta wurin uba ita ce ta raine ta kan madara ta bata tarbiya ilimin addini da boko har ta shekara takwas ita ta sani a matsayin uwa kuma uba, ta samu gata na iya tsawon lokacin da tayi da kakarta har makarantar gomnati na boko ta sanya ta kan kwatsam mutuwa ta yanke wannan ƙauna tun daga sannan aka fara jita-jitar ita ɗin Mayya ce! Kuma duk wanda ta raɓa zai mutu.Tsangwama ya fara yi mata yawa a hannun ƙanwar babanta da ta koma Inna Amina ta sha baƙar wahala kasancewar inna Aminar ma cikin gidan yawa take, mijinta kuma ba wai ya karɓe ta bane zaman dole take mishi a gida hatta abincin gidan bai amince a saka mata ba duk abinda aka sanyawa inna Aminar suke taɓawa a tare, ta samu innar tata da ciki a lokacin kawunta ya ƙi yarda ya ƙarbe ta tunda su uku kawai kakarta ta haifa.Kawu ne babba sai babanta tukuna innar dole dai wurinta take lallaɓa wa rayuwarta.Wata rana inna Amina ta tashi da nakuda babu wani cima mai kyau, babu cikakken kulawa da ya kamata mace mai ciki ta samu, bata taɓa zuwa awo ba ana rayuwa ne cikin wahala haka ta tashi nakudar a gida aka kira unguwarzoma ta ci azaba ko da ta haihu babu rai ita ma bata jima ba jini ya balle mata ko kan a ce an yi wani yunkurin Allah ya karɓi abin shi, ko gawar inna da jaririyarta ba’a binne ba aka sanya Afeefah gaba da zagi, cin mutunci, baƙaƙen maganganu babu irin wanda ba’a jefeta ba a lokacin da take jin tashin hankali da damuwar rashin innarta Aminan.Ta ga mutuwar kaka amma bai kaɗata kamar na inna Amina ba saboda yadda ta mutun a wulakance cikin sakacin miji da kishiyoyi ta yi kuka kaman babu gobe, har jifan ta da dutse ake yi in ta fita a haka kawu ya dawo da ita gidan shi tana da shekaru 10.Matanshi basu karɓeta ba, babu wacce take yarda har yanzu ta shigar mata ɗaki ko na yaransu dole aka buga mata keji don ba shi da maraba da keji aka sanya buhu aka bata taburma saboda kar ta kashe musu ‘ya’ya, bata sani ba ko tabbatar ta mayyar ce ta sa yanzu shekara shidda kenan da dawowarta gidan kawu bayan ɓari da matan suke yi babu wacce ta sake haihuwa, sun yi duka sun yi zagin duk a banza wai an tsikari kakkaura ita bata ma san ta yadda ake yin maitar ba, wani lokaci har ta kan yi adu’ar ya tabbata ita ɗin Mayya ce don tana so ta ba su kyautar kanta duniyar bata da anfani a gareta. bata ƙara zuwa makaranta ba ko na boko ko arabi tun bayan mutuwar kakar ta sai dai ta ga wasu da kayan makaranta, ta zama boyi boyi abin wulakantarwa, abinci wannan da kyar ake bata a gidan kan suka fara ɗora mata tallah ganin tana da wannan farin jinin ya sa suka dage kuma ake kishi a kanta don kaman yadda suke raba kwanan mijinsu haka suke raba ta.Dole kuma a rana idan ta yiwa wannan sai ta yi wa ɗayar idan ta sayarwa wannan ko kwana zata yi waje sai ta sayarwa ɗayar kan ta dawo gidan in ba haka ba ta shiga uku, bata sani ba zata tabbata a haka Ko wani sauyi zai iya shigowa rayuwarta? Ita ɗin Mayya ce da gaske? Har yanzu tambayar da ita karan kanta bata iya amsawa kanta ba kenan bare ta amsawa azzaluman mutanen da suke zagaye da ita. “Ke!!!”A ɗan firgice ta ɗaga kai sai ta ga wani matashi na miƙa mata kudi “tun ɗazu ina ta magana kin yi shiru kaman bakya duniyar? Saka min na ɗari biyar”Abincin ta shiga sakawa shi ne ma na karshe don wuraren sha ɗaya na safe ne, bayan ta saka mishi ya koma cikin matasan da suke tare ya shiga ci ita kuma ta fara tattare wurin cikin natsuwa da sanyinta sai da ta gama zuba komai cikin wheelbarrown tana jiran matashin ya gama ya bata plate sai kawai ta fara jin hayaniya na tashi, ɗago kan da zata yi sai ta ga wannan saurayi ne dafe da ƙirji yana tari sossai da sossai har filate ɗin ya faɗi ƙasa abincin ya tarwatse ya bi abincin yana tumurmusa a ƙasa, kan kace kobo wurin ya cike da mutane wasu na cewa ya mutu wasu na cewa da sauran ranshi.”Me ya ci ne? Me ya same shi?”Abin da mutane dayawa ke tambaya kenan, ita dai Afeefah na kafe a wurin ko motsi ta kasa sai gangar jikin da mutane suka yi wa zobe kwance ta zubawa idanu kaman daga sama ta ji Muryar wani na cewa “Daga fa sayan abincin yarinyar chan kun ga bai ma gama ci ba…! Ku taimaka mu kaishi asibiti kar ya rasa rayuwarsa kumfa ne a bakin sa”Cikin jimami ya ƙarasa Wata murya taji tana cewa “hohoho asshaa dama na san aje aje sai ta fara yiwa mutane dauki ɗaiɗai shiyasa ban taɓa sayan abincinta ba, yarinyar da riƙaƙƙiyar Mayya ce an ce ma ita ce mataimakiyar shugaban Mayu yanzu?”Ko motsi bata iya ta yi ba taji an damketa zuciyarta kaman zai fito waje ba na tsoron abin da mutane zasu iya yi mata ba sai na tsananin tsoron mutuwa, mutuwa na daga cikin abinda a yanzu yake gigitata dole duk mai imani ya tsorace mutuwa a yanzu yaron nan ke mata magana a yanzu ana cewa ya mutu? Ta yaya? Meyasa sai da ya sayi abinci a hannunta?Wani mai ƙirar ƙarfi ya hankaɗata tsakiyar mutanen “Ke tsallakeshi sau uku ki sakar masa kurwa yanzu wallahi ko mu sheƙa ki barzahu..”Yayi maganan da karaji yana zaro wuƙa mutane suka fara kananun maganganu masu zaginta na yi, wasu har labari suke bayarwa na ta kashe iyayenta ai maitar gado ne tun a ciki ta fara kisa, hawaye masu zafi ne suka shiga gangaro mata a sadda take tsallakeshi a dole, kalaman da suke shiga kunnuwanta sun yi mata girman da ba zata iya ɗauka ba, abin tashin hankalin ma shine yaron bai tashi ba, ya tabbata ya riga ya rasa ransa ko kan ta gama fahimtar kanta har tayi wani yunƙuri an rufe ta da duka, ko yunkurin kare kanta bata yi ba don a yanzu ita ma ta fi ƙaunar mutuwar da rayuwa, da kyar wasu dattijai suka kwace ta fuskanta har ya fara sauya kamanni wasu sassa na jikinta na zubar da jini, kwanukan inna larai da kulolinta an yi daga daga da su, ko kasheni ka ɗaukanta (lalitar kuɗi) bata gani a jikinta ba.Wani irin deep kuka take yi mai taɓa rai, dattijon ta kalla”Don Allah baba ka bar su su kasheni kawai nima ina so in huta, don Allah ku bar ni su kasheni”Abin da take ta maimaitawa kenan tana gunjin kuka ya riƙo hannunta”Ki natsu yarinya babu mai kashe ki, shima kwananshi ne ya ƙare ya mutu kiyi hakuri ki tashi mu raka ki gidan ku”Cikin in-inaa take cewa”in naje gi..gidan ma ba..ba tsira z..Zan yi ba kuɗin inna larai da kwanukan ta duk babu”Ta sake rushewa da kuka, tausayinta ne ya kama su suka haɗu suka tasa ta gaba har gidan, kawu suka fara nema ko da ya fito da kallon tsana ya shiga bin ta.”Yau kuma magana kika janyo min ko? Kayan uban wa kika sata ko uban wa kika kashe??” Dattijo ɗaya daga ciki yace “A’a malam labaran ya kamata ka fara tambayar raunin jikinta ne amma damuwarka wani abu daban? Ka san yaran zamani da kansu a koyaushe baya gayamusu daidai akwai wani yaro da ya sayi abincin ‘yar wajenka yana cikin ci sai Allah ya turo da ajalinshi a take ya tafi shine suka yi yunkurin kasheta a cewar su ita ce ta cinye kur…”Tuni ya katse su “Ai da kun barsu don ni baku burge ni ba sam, da kun barsu don ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba ita ce nan ta kashe shi, sai ki shiga ai ki jira zuwan iyayenshi tunda ba kowani mahaukaci bane zaki mishi asarar rai ya barki ki sha ba””Ashshaa amma….””Babu ruwanku! Tunda kun kawo ta zaku iya tafiya” ya cigaba da mita kaman zai ari baki yarinya ba jari zata kawo mishi ba, ba auruwa za tayi ba babu wani amfanin da take mishi sai cin abincinshi amma kullum bacin ranta ya fi na kowa a ranshi.Dattijan suka juya suka tafi ita kam kanta ƙasa zuciyarta na wani irin karta, hawaye kuwa sun ki kafewa a idanunta kafafunta da suka matuƙar yi mata nauyi take kokarin ɗaga wa ta shiga cikin gidan taji an fusgo ta har tana taga taga zata faɗi wuyan hijabin jikinta aka shaƙo “Ina kudina da kayana?”Kakari take don ko numfashi ta kasa shaƙa, idanunta da suke manya suka sake fitowa ainun sun rine sun chanza gabaɗaya.Inna larai ganin zata yi kisa ya sa ta Hankaɗata bata damu da kokawar saisaita numfashin da take tayi ba ta daka mata tsawa “nace ina kuɗina?””In…nn..a B..ban san ya ak…a yi ya fice daga ji..jikina B..”Hayewa ruwan cikinta tayi ta shiga ɗirkarta kaman an aiko mata ita “kaman kuwa yadda ya fice baki sani ba haka sai na rabaki da numfashinki baki farga ba, wlh dukan kuɗina yau sai na yi miki shi”Ko karfin kare kanta bata dashi sai da dukan yayi yawa ne kawu Labaran da ke kishingiɗe yana sakace haƙorinshi ya fito ya ɗaga inna larai “ke kar ki yi min kisa a gida”Yana kai nan ya juya ya bar wurin ta cigaba da sababi da zage zage karshe ta tafi ta barta nan yashe.Yaran gidan bayan sun gama kwasar dariya kowa ya kama gabansa Inna Asabe ma na girki tana zaginta da tsine mata don yau ta yi mata asarar tallar yamma tunda yanzu ko ta fita ba su da tabbacin akwai mai sayan abin hannunta irin wannan suncewar zani a kasuwa da tayi musu, ta fi mintuna goma a kwance a wurin kan da rarrafe ta shiga akurkinta ta faɗi bisa taburma tana kuka kaman ranta zai fita.Ko mintuna biyu bata yi da shiga ɗakin ba tana yashe a inda take ta soma jin hayaniya tamkar ana yaƙi, idanunta sun kumbure ko iya buɗewa da kyau bata yi, bata san ya aka yi ba sai ji tayi an janyota tamkar tsumma an fitar da ita, sama sama take jin mutane na ta hayaniya tana hangar sanduna da makamai na tashi sama ana ikirarin kasheta kaman yadda ta kashe musu ɗa matashi, bata san ashe rigimar har su kawu ya shafa ba don sun rantse in ba’a fita da ita ba gidan gabaɗaya za su ƙona, tashin hankalin da bata taɓa shiga ba ta shiga a ranar, bata san ya aka yi ‘yan sanda suka iso wurin ba don ana ta janta tamkar kaya ko takarda Muryar kawu na ihun kar su ƙona masa dukiya ita suke so don haka ga ta nan su kashe ta. Fusgar ta aka yi aka wulla ta motar ‘yan sanda suka ja suka yi ofishin su da ita…



