Halysaah Page 75 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 75…
HALYSAAH PAGE 75…
Ajay na cin strawberry dake gefensa idonsa a kan movie din da ake yi a TV, Jay ya dinga kallonsa kafin ya fixge remote ya kashe Tvn, Ajay ya juya ya kallesa yace “Wai kunne ke ji ko ido? Ina fa sauraronka Jawwad” Jay yace “If you are not giving me ur attention i will leave this parlor, tun daxu ina magana hankalin ka na wani waje daban, what’s all this pls” Ajay ya tabe baki, sai kuma ya juya yana kallonsa direct in the eyes yana ci gaba da cin Strawberry dinsa yace “Oya be fast pls” Mikewa Jay yayi zai bar parlon Ajay ya fixgosa yace “Kai matsala ta da kai kenan banzan zuciya, ba gashi ina sauraron ka ba” Jay yace “Kar ka rena min hankali mana Malam” Ajay dai ya ci gaba da cin fruit dinsa yace “Ka kashe Tv din ai, i am listening” Jay ya koma ya zauna, for peace to reign yasa Ajay ya maida hankali yana sauraron maganar da Jay ke yi masa, can ya ɗan yi murmushi ya jawo grapes dinsa zai fara sha yace “This is weird… All of a sudden sai ka ji bazaka iya zama gida daya da ita ba, why is that? Meye dalilin ka? Da ba apartment daya kake zaune da ita ba some months ago, ko ni ban san gida daya ku ke ba sai ranan da baka da lafiya, meye kuma ya canza ra’ayin ka all of a sudden….” Jay yace “To yanxu bazan zauna ba, period! in zaka kawo Suggestion din yanda za ayi ka kawo ina sauraron ka….” Ajay yace “Ai ni dalilin hakan nake son sani” Jay yace “Ni dai babu ruwan ka da dalilina kawai solution nake nema, just tell me yanda kake ganin ya kamata ayi…. Tunda kaga we are not going to make the mistake of accommodating her again in this House” Ajay yayi shiru, kamar bazai ce komai ba can dai yace “Kai din dai ya kamata ka zauna a apartment din tare da ita, that’s the only solution for now tunda jarabawa za su fara, ko da za a samar mata sabon Apartment definitely sai ya bi ta can din ma kamar yanda ya gano wannan, da mun san haka kawai da a cikin makaranta aka biya mata accomodation to avoid all this, wannan wawiyar kawar tata mara hankali kuma will just worsen the situation idan aka ce taje can gidansu ta zauna, beside no one loves being inconvenience in this state….” Jay ya sauke ajiyar zuciya, after a while ya fixge remote din da Ajay ya dauka yana kokarin kunna TV alamar ya gama maganarsa, Ajay yace “Na fa baka solution din da ka zo nema, ka bar ni in ci gaba da abinda nake yi” Jay yace “I told you staying in the apartment with her isn’t an option Ajay, kaga kenan har yanxu babu solution” Ajay yace “Wai saboda kana gudun ka ci gaba da rungumeta ne yasa ka kasa zama gida daya da ita? To ai wannan norms ne a wajen ku tunda iya runguma ce kawai…” Jay ya dinga masa wani kallo, Ajay yayi murmushi yana gyara zama yace “Ko kuma kawai ka kira gida a daura maku auren, ko ni sai in rakaka ka tare a can apartment din kawai” Jay yace “What is this u are saying?” Ajay yayi dariya yana shan grape dinsa bai ce masa komai ba, Jay dai kallonsa kawai yake, can Ajay ya daga kafada yace “Or better still idan kanwar Baabarta na da Passport kawai ka nema mata visa idan Allah yasa an bata sai ta zo ta zauna da ita har ta gama jarabawan…..” Jay yayi shiru kamar me nazarin abinda Ajay yace, after some seconds yace “What if ba a bata visa din da wuri ba, sannan before Everything is process kasan zai ɗan dau lkci may be kafin nan ma sun fara jarabawan” Ajay yace “To ni iya shawaran da zan iya badawa kenan, ban san kuma yanda zaka yi ba, stop stressing me with ur problem plss” Jay yace “Why not stay in the apartment with her, har zuwa sanda kanwar Mom dinta zata zo” Ajay ya daga kai ya kallesa, can yace “Wa zai zauna a apartment din?” Calmly Jay yace “Kai…..” Ajay ya ajiye fruit din hannunsa yace “Amma ka ma raina min hankali Jay, ni ne zan zauna da ita a apartment din ga ni Bodyguard ko? Can you even hear ur self? kawai sai in koma apartment dinta in zauna gadin ta saboda ni bani da aikin yi, in da gaske neman me gadinta kake ka sa Salem ya koma apartment din da zama mana tunda ya gama masters dinsa, after all she was sharing an apartment kafin ka santa a kasar nan, so yanxu ma zata iya sharing da Salem as her Housemate” Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, har ransa yaji zafin abinda Ajay yace wai ya hada Khaleesat da Salem a gida daya, duk da ba wai Salem na da wani mugun hali bane amma yaji haushin hakan sosai, har Salem din da bai masa komai ba sai da yaji ya fara jin haushinsa a zuciya, mikewa yayi ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Ajay ya taɓe baki ya ci gaba da shan fruit dinsa ya jawo remote ya kunna TV.
Khaleesat na zaune tare da Safiyyah bayan sun gama lectures wajen karfe shidda saura na yamma, ita dai sai kallon Safiyyah dake bata labarin yanda Mustapha yace zai nemi Abdul duk inda yake ya basa hakuri don shi baya son fitina a kasar mutane, cikin bacin rai Safiyyah ke bata labarin tana cewa “Mustapha ɓata mana sunan family kawai zai yi a zata mu coward ne matsorata, abun duk ya dameni wallahi, har da cewa in na sake kula Abdul zai kira babana ya gaya masa, ni kuma tsoron old Man dina nake wallahi….” Ita dai Khaleesat kallonta kawai take ba don tana sauraron abinda take cewa ba, infact gaba daya ma bata san me take cewa ba, kawai memories din jiya da daddare ne ke dawo mata a kai, ko karatun ma yau bata san abinda aka yi ba sunan ta zo school ne kawai, kana ganinta kasan she is in a very happy mood today, Safiyyah tace “Wai yau naga sai fara’a kike kamar warce aka biya ma kujeran mecca, meye sirrin kawata, wallahi na zata idan na shigo school zan ga idanuwanki sun kumbura don kuka tunda aikin ki kenan, amma naga sai farin ciki kike kina nishadin ki, yau har da kula Coursemate dinmu a Hall kamar ba ke ba” Khaleesat tayi murmushi tana wasa da zoben hannunta tace “To saboda me zaki ga idona ya kumbura don kuka?” Safiyyah tace “Akan issue din Abdul mana, ai nasan halin ki sai ki iya kwana kina kuka” Khaleesat ta taɓe baki har sannan tana murmushi tace “That was then, I don’t have time for that now Safiyyah, ni fa na ma dena tsoron nasa yanxu, kuma ba abinda ya isa yayi min….” Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace “Nagode tawan, don Allah a wani kasuwan kika siyo liver din nan naki me shegen kyau?” Khaleesat bata san sanda tayi dariyan ba ita ma tace “Allah da gaske i am not afraid of him any longer Safiyyah” Safiyyah tace “Ko ke fa, yanzu tun asali da haka kike ai babu me taka ki kawata, amma naji dadin wanda ya siyar maki da liver din nan har kika samu kwarin gwiwa….” Shiru Safiyyah tayi ta daga kai tana kallon Abdul that is coming toward them, tuni Khaleesat ta hade rai bayan ta gansa ita ma, ta fara tattara reading materials dinta a jaka, ta dau jakar tana kallon Safiyyah tace “Mu je Sophie” A tare suka mike Safiyyah na taɓe baki, Khaleesat na fara tafiya Abdul ya riko veil dinta yana kallonta yace “Don Allah ki bani minti biyar mu yi magana Khaleesat” Ta juya ta kallesa fuskarta a murtuke tace “Let go of my veil Abdul” Yayi kasa da murya yace “Plss Khaleesat, i want to say one or two words, don Allah ki bani lokacin ki ba don ni ba” Fixge veil dinta tayi a fusace kafin ta bar wajen kawai taga ya shige gabanta yana mata magiya yace “Don Allah fa nace maki Khaleesat, ko minti biyu ne ki bani” Safiyyah dai ta koma gefe tana wani dariya kamar taga wawan zama, lallai Abdul ya zama abun dariya yanxu don tsakaninsa da Allah ya marairaice ma Khaleesat, Khaleesat ta juya tana jin zuciyarta na tafarfasa zata bi daya direction din taji ya riko hannunta this time around, bata san sanda ta juyo ta sauke masa mari a fuska ba, cikin fushi tace “Baka da hankali ne Abdul?” a hankali ya sake hannunta don bai ma san hannunta ya rike ba, yana kallonta calmly yace “I am sorry Khaleesat, I didn’t mean to….” Tuni ta juya ta bar wajen kamar zata tashi sama, Safiyyah da ta saki baki hangangan ta bi Khaleesat da kallo, slapping Abdul was the least thing da tayi zaton Khaleesat zata iya yi a rayuwa, Safiyyah ta kalli Abdul da ya zauna inda Khaleesat ta tashi ya rike kansa, bin bayan Khaleesat tayi har sannan ta kasa rufe baki with shock, ita kuwa Khaleesat ta sha kunu Kamar bata yi komai ba tana ta tafiyarta, bayan sun yi nisa a hankali Safiyyah tace “Khaleesat?? Did you just slap him?” Without looking at Safiyyah tana ci gaba da tafiyarta tace “He asked for it, don me zai rike min hannu, ko bashi da hankali ne” Safiyyah da ta bude baki tace “Don Allah wa ya koya maki haka? Dama kin iya haka all this while kike maida kanki rubabbiya ake taka ki yanda aka ga dama? I still can’t believe your action Khaleesat, Omg” Khaleesat ta tsaya ta ciro wayarta dake vibrate, number Housemate dinta ta gani dama kuma she was expecting his call don shi yace ta jira zai zo ya dauketa, tayi picking call din ta kai kunne, after some seconds tace “Eh mun gama tun daxu” Safiyyah dai kallonta kawai take da mamaki har ta gama wayan, sannan Khaleesat ta kalleta tace “He came to pick me, mu je sai yayi dropping din ki tunda hanya daya ne” Safiyyah ta rike haɓa tace “Ni fa na kasa yarda marin Abdul kika yi da gaske, don da bana wajen aka yi ko jikina kunnuwa ne bazan yarda ba, ko ni duk fitina ta bazan yi gigin marin Abdul ba wallahi” Khaleesat ta hade rai tace “Ni dai don Allah mu tafi, kawai yayi ta bibiyata a makaranta yana daga min hankali for what reason? babu komai fa tsakanina da shi yanxu don me bazai bari inyi rayuwata irin na kowa ba, i am fed up with this” Hawaye ne ya ciko idonta ta fara gogewa tana ci gaba da tafiya, Safiyyah dai tayi shiru tana bin ta, don yau kam Khaleesat ta goge mata hadda tasss, a haka suka karasa inda Housemate yayi parking motarsa, yana ganinsu ya sauko daga kujera me zaman banza, Safiyyah na washe baki ta gaishesa ya amsa da murmushi fuskarsa yace “Ya lectures din? Ko kuma ince revision, since exams is around the corner” Safiyyah tace “Alhamdulillah Yaya Jawwad” Juyawa yayi ya kalli Khaleesat, ganin mood dinta nan da nan fara’ar dake fuskarsa ya bace, ita kuwa Safiyyah sai gwale ido take bayan ta hango Ajay zaune driver seat, shi kuwa dama tun da ya hangosu da Khaleesat ya toshe kunnensa da ear pod yana kallon gabansa, Housemate na kallon Khaleesat ya bude mata back seat, cikin sanyin murya ta gaishesa sannan ta shiga motar, ya kalli Safiyyah yace “Tun da hanya daya ce ki shiga mu ajiye ki ko?” Safiyyah na kirkiran murmushi ta girgiza kai tace “A’a akwai wata Coursemate dinmu da nake jira akwai reading material dina a wajenta” Jay yace “Alright Safiyyah sai anjima” Daga haka ya bude front seat ya shiga, Safiyyah ta daga ma Khaleesat hannu sannan ta jefa ma Ajay harara duk da ko kallon inda take bai yi ba, ta juya tayi wucewarta, Allah ya rabata shiga mota daya da fitinannen nan, kila ma tana dosana kugunta a kujeran motar zai ce ta fita, in ya mata haka kuma tsaf zata masa rashin kunya ita kam, to ina dalili, gwara da ta kama kanta taki bin su…. Bayan sun bar school din Jay ya kasa daurewa ya juya yana kallon Khaleesat yace “What happened Housemate?” Khaleesat ta girgiza masa kai alamar ba komai, yace “No there is something, why are you Moody? Tell me pls, wa ya bata maki rai?” Kamar Khaleesat bazata ce komai ba, sai kuma ta sauke idonta tace “He still followed me again today” Ta madubin mota Ajay ya kalleta jin abinda tace, Housemate yace “Sai me ya faru kuma?” Khaleesat tace “Rike min hannu yayi wai in tsaya in sauraresa ni kuma na maresa nayi tafiyata” Ba Housemate dinta ba, Hatta Ajay sai da ya bude baki yana kallonta ta madubi, Jay was totally speechless yana kallonta, can ya juya ya kalli Ajay, Ajay yace “Kika maresa? Saboda baki da hankali zaki maresa? Ana kokarin protecting dinki by all means kina kara jawo ma mutane aiki? nasan wannan baƙar kawar taki ce zata zuga ki ta koma gefe tana kallo, dama kuma nace idan kika ci gaba da mu’amala da ita sai ta ja maki bala’in da yafi karfin ki don ban ga alamar tana da seti ba yarinyar nan, kina er mitsitsiyar ki zaki daga hannu ki mari gabjejen mutumi haka ko tsoron tsayinsa baki ji ba, da kika maresa sai ta fara hailing din ki ko…” Kuka Khaleesat ta fara yi a motar kamar jira take, Jay ya juya ya kalli Ajay yace “Look Ajay, no one is above mistake, we all make mistake, don haka ba gigitata zaka yi ba, she is frustrated shi yasa tayi hakan, so we shouldn’t blame her….” Ajay ya wani kallesa sannan ya maida dubansa kan titi bai sake tofa nasa ba a cikin motar, Jay ya kalli Khaleesat dake kuka, cikin kwantar da murya yace “Ki kwantar da hankalin ki Housemate, babu abinda zai maki in sha Allah, i am giving you assurance, marinsa da kika yi kuma baki yi kuskure ba shi ya ja ma kansa” Ta gefen ido Ajay ya kallesa bai dai ce uffan ba, Ita dai Khaleesat kuka kawai take a hankali har suka isa apartment dinta, sauka tayi daga motar ta nufi kofar apartment din ta bar su cikin motar. Jay ya kalli Ajay yace “You are not suppose to scold her that way, she is already frustrated, cikin kwantar da murya ya kamata ayi mata gyara, beside ita yarinya ce fa har yanzu” Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace “A’a, sha’awar gado ce” Jay bai sake ce masa komai ba a motar, bayan kusan minti daya ya kallesa yace “Ka shiga ciki… let me get some food from the restaurant for her, kai nasan zaka yi sorting kanka out, there is everything available at the kitchen” Ajay yace “Wait pls, ni kaji nace maka na amince da tsarin ka ne da kake wannan bayanin?” Jay yayi shiru yana kallonsa, can yace “Pls ka daina maido da magana baya Ajay, i tot we are done with all this, nayi ma Aunty Farida magana daxu tace bata da passport, but getting a passport isn’t an issue, Visa ne babban damuwan yanxu, kasan baza a samu da wuri haka ba” Ajay yace “Yanzu me kake nufi? Shikenan ni sai inyi inconveniencing din kaina in takura rayuwata just to please you? Bayan ka fi kowa sanin ba ko ina nake zama comfortably inyi rayuwa ba, You know how irritating everything can be to me, why not consider me?” Jay yace “I will make the apartment very Comfortable for you to stay, beside i will be coming around too, wata daya ne fa an gama exams din….” Ajay yace “To wai ba na baka shawaran kawai kayi ma mai martaba magana a daura maku aure ba? What are you still waiting for?” Jay yace “Me yasa kake mantawa da Mamina ne? I didn’t birth my self, har yanxu fa Mami bata san komai kan wannan maganar ba, i need to speak to her about it face to face ta yanda zata fahimce ni… After their exams dama tare za mu koma Nigeria, so i can speak to Mami” Ajay ya ɗan yi murmushi ya shafa gashin kansa bai dai ce komai ba, Jay dake ta kallonsa yace “Meye ma’anar hakan?” Ajay ya daga hannu da sauri yace “Nothing….. Just wishing you luck” Jay bai sake cewa komai ba kuma bai fasa kallon Ajay ba, after some seconds yace “Ban taɓa nuna ina son abu Mami taki abun ba ko da bai mata ba, she is after nothing but my happiness, bata da kowa sai ni, farin cikina shi ne first priority dinta, kuma kai ma kasan da wannan, you can attest to that” a hankali Ajay ya jinginar da kansa jikin kujeran motar keeping silent…..
Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence 07087865788
We sell all kind of spices like grand masala, 7 mixed spice, all purpose spices, Mandy spices, biryani, pepper soup spice, ginger mix, Curry, suya spice and tsire mix all at affordable prices
Siyan daya ko sari, contact +234 803 298 6552 for more info
Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence 07087865788
We sell all kind of spices like grand masala, 7 mixed spice, all purpose spices, Mandy spices, biryani, pepper soup spice, ginger mix, Curry, suya spice and tsire mix all at affordable prices
Siyan daya ko sari, contact +234 803 298 6552 for more info
