Halysaah Page 104 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 104…Ajay ya gaida Hajja da ta fito daga dakinta rik da bowl a rufe tana kallon sa da Khaleesat, bayan ta zauna tace “Kai kuma daga ina kama an jefo ka?” sai a sannan Khaleesat ta daga kai ta kalleta cikin sanyin murya ta gaisheta, Hajja ta kalli direction dinta tace “Lafiya lau” Sai kuma ta kalli Ajay tace “Ita ce matar taka kenan” Shi dai Ajay bai ce mata komai ba, Haj tace “To Maa sha Allah, Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya” Daga haka bata sake cewa komai ba a parlon, bayan yan mintuna ta mike ta dau bowl din da ta ajiye ta fita daga parion, Jay taje ta sama a daki, bayan ta kulle kofar dakin ta karasa ciki ta zauna kan kujera tace “Na dauko maka dambun naman kuma ban same ka a parlon ba” Shi dai bai ce mata komai ba, ta ajiye bowl din tana kallonsa ta kwantar da murya tace “Kayi hakuri Jawwad, nasan kai me hakuri ne, bazaı ji dadi ba idan ka kullaci dan uwanka akan wannan abu, kun taso tare cikin so da kaunar juna kamar yan biyu rana tsaka wannan abu mara dadi ya gifta, ka fi kowa sanin halin dan uwanka ni ina da yakinin bai san da wannan aure ba shima sai bayan da sarki ya daura masa, sannan kasan yanxu haka in kace zaka sharesa damuwa zai saka ma kansa, ni naji ma kwata kwata yarinyar bata min ba wallahi’ Sai a sannan Jay ya daga kai ya kalleta yace “Me ta maki?” Hajja ta hade rai tace “Me ta maki?” Hajja ta hade rai tace “Me ta min? Yarinyar kamar er jaraba gashi ta dalilint zumuncin da aka gina tale tale na neman rushewa tana neman shiga tsakaninku da dan uwanka, to kuwa ina amfanin irin ta a al’umma? Ai ta zama abar tsoro kenan, dole n sai an aurota cikin Family tunda auren bai yiw da kai ba ba sai a hakura ba, na meye sai an maida aure kan wani Junaid kamar ita din er gwal ce?? Wallahi da sarki yayi shawara da ni bazai aura ma Junaid yarinyar nan ba ko don saboda kai, in ma yace shi bazai zama karami mutum ba to gwara can ya aura mata Walid ko kuma Mukhtar, ko ya nemi wani a dangi ya aura mata, gaskiya ban ga alamar alkhairi tattare da yarinyar ba tunda ta dalilinta komai ya cakude na rasa ta inda zan fara gyaran nan kuma naga ma kamar halarabiva ce ko Idona ne Jay dai bai sake cewa komai ba, cikin nutsuwa Hajja tace “Nasan halin ka na kuma san halin Junaid, nasan Junaid bazai ki yi maka magana ba Jawwad don Allah idan yayi maka kar kace zaka ki kulasa, kayi hakuri ka bar ma Allah komai, kuma ba kowa ya ja sanadin faruwan wannan al’amari ba sai Aseeyah, Aseeyah ita ta ja komai kuma bata kyauta maka ba, amma a yanxu dai ina son ka saka ma ranka salama ka malda lamarin ka ga Allah” Hajja ta fi minti sha biyar a dakin tana kokarin kwantar masa da hankali tana kara jadadda masa kar yace zai yi banza da Junaid, shi dai yaki ce mata komai daga karshe ta bar dakin ta koma parlon ta, tun bata karasa ba take jin kamar muryar Aunty a parlon nata, tana shiga kuwa ta sameta tsaye da Hajlya Aisha suna ci ma Ajay mutunci ya ki ko daga kai ya kaliesu sai danna wayarsa kawai yake karnar ba da shi suke ba, Suna ganinta duk suka yi shiru, da mamaki Hajja tace “Lafiya? Me ke faruwa haka?” Aunty ta zauna kasa don gaida Hajja, Hajja tace “Me ke faruwa nace?” Cikin bacin rai Aunty zata fara magana Hajja tayi wani tunani sai ta dakatar da ita tace “Bana bukatar jin komai yanxu, kawai ke da A’isha ku tashi ku je” Aunty ta mike ta fita daga parlon Hajiya A’isha na biye da ita a baya, ita dai Khaleesat na zaune kamar an dasata inda take mamaki yaki barin ta, she was really shock don bata ga alamar mutunci ba kwata kwata, sosai jikinta yayi sanyi da wannan abu, is it she that will leave with this kind of people in the palace? Auren da har yanxu ba amsan sa tayi ba amma take ganin wannan abu, Hajja na kallonta bayan ta zauna tace “To ban san sunan kishiyar tawa ba” Khaleesat ta sunkuyar da kanta a hankali tace “Sunana Halysaah” Hajja tace “Maa sha Allah, sunan kishiyar tawa ta yan gayu kuwa” Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace “Amma sunana Jiddah” Hajja tace “Maa sha Allah, kin ga mu mun fi gane wannan ai, you are welcome to the family Jiddah” Mikewa Hajja tayi da kanta ta kawo kayan ciye ciye ta ajiye a parlon sannan ta fita, can main parlor ta tarar da Aunty, Hajja na kallonta tace “Ke yanxu Hafsat saboda rashin kamun kai a gaban surka za ki zubar da mutuncinki ki nerr ki zubar da na gidan nan?” Cike da damuwa Aunty tace “Hajja tun da aka kawo yarinyar nan masarauta Junaid ke bude mata kofofin raina ni, tun kawota har yau yarinyar nan bata taba bude baki ta gaida ni ba kamar yanda sh ma sai ya ga ubansa yake gaisheni” Hajja tace “To ke ma ba sai kin ga uban nasa kike amsa gaisuwarsa ba? Duka duka yaushe har aka kai ta gidan da zata waye ki? Yarinyar da ko kwana uku bana tunanin tayi” Shiru Aunty tay bata sake cewa komai ba wani sabon bacin rai ya lullubeta, Hajja tace “To ki kama kanki, ba ruwana da abinda ke tsakanin ki da Junaid kar ki kuskura ki ce zaki zubar da mutuncin gidanmu a idon duniya, a gaban yarinya babu kunya ki tsaya kina kalaman banza da hofi akansa? Idan matar Walid ce za ki yi wannan iskancin a gabanta?” Aunty tace “Matar Walid ma bazata min haka ba Hajja” Hajja tace “To zageni Hafsat, kare min nima yanda kika kare ma Junaid al ba sabon abu bane” Shiru Aunty tayl sai kuma ta fara bata hakuri kai a kasa, Hajja tace “Aikin banza aikin Hofi kawai, a ko ina ke sai kin malda kanki karamar mutum, gaban yarinya kin zubar da mutunci da girman ki, ina amfanin haka wai kuma matar sarki? Dama haka matan sarakunan su ke? To sam mu ba mu yi haka ba, bama son duk wani abu da zai taba reputation dinmu da na gidanmu komin kankantarsa, amma ke kam taka haye ce ma a jinin sarautar Hafsat” Daga haka Hajja ta juya ta bar parlon, Aunty dai sai huci take tunani iri iri na yawo a ranta, lallai ta gamu da aiki ja wanda ko bacci bai kamata tana yi da ido biyu ba yanxu. Throughout ranan haka Khaleesat ta yini daga ita sai Hajja a parlor, ga ‘ya ya da jikoki da mutanen arziki na ta zuwa gidan yi ma Hajja sannu da zuwa, in an gaisa sai Hajja tayi masu introducing Khaleesat dake gefenta, Khaleesat dai duk a masu zuwa bata ga wanda ya wani bata attention ba, duk kuma a nan ne taga yaran Aunty uku, wata me sunanta da ake ce ma Baby that is just a teenager sai yayyinta Maryam da Khadijah, gaba daya ko bin ta kan Khaleesat basu yi ba, ita dai tana zaune parlon ne amma Allah kadae yasan damuwan da ya cunkushe mata a rai, har take jin da zat: samu wajen da zata yi kuka ta samu relief, Babban damuwarta a yanxu shine wannan aure da aka mata da Junaid, secondly Jay da ta garni shigowar su daxu ya kara destabilizing dinta komai ya dawo mata kamar yanxu yake faruwa, thirdly Aunty, har cikin ranta taji take tsoron matar don bata mance mahaifiyar Abdul ba da abinda tayi mata, she is so afraid of the woman, further more gashi ta lura duk familyn babu alamar akwal wanda zai so ta, kllan sai Hajiya Shafa’atu kawai, duk sai sha mata kamshi kawai suke suna daga mata kai kamar sun ga kashi babu wanda ya bata attention a parion, hatta Hajja is just being neutral babu yabo babu fallasa ce, kuma duk zamanta a parlon sae ya kama Hajja ke mata magana although cikin mutuntawa zata mata maganar, kuma ko ita aka kawo ma abinci sae ta fara dibar me Khaleesat kafin ta ajiye. and the least among damuwarta Junaid, she don’t know why he is being treated this way a gidan nasu, she don’t even know ko hakan tausayi ya bata ko kuma she is just feeling for him, but for now dai duk ba shi ne a gabanta ba, damuwarta kawal Jay….




