Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 15 Complete Novel

*ASM Bk2015*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

………Wani babban Eatery mai kyau da tsari ya nufa dasu bayan ya parker Motar a wurin da aka tanada don haka a tare suka fito suka nufi ciki Masha Allah ya dae tsaru Fatuu sai d’an bin wurin take da kallo ta yadda baza’a ga k’auyancinta ba, wuri ya nuna mata suka zauna suna facing juna suna zama sai ga waitress tazo tana sanye da Uniform d’in wurin bak’in skirt sai riga milk tasa yar himar bak’a dama ma’akaitan wurin Mata da Maza ne, Haisam ta nufa cike da salo tace “Barka da zuwa Yalla6ai” ba tare da ya kalleta ba ya d’aga mata kai Fatuu ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah don sai faman rausaye rausaye take, Menu ta mik’a mashi mai d’auke da lists d’in dishes dake garesu bai amsa ba yace ta kawo mashi Fried rice d’an d’aga gira tay jin yadda yake Magana tace “with Beef or chicken yalla6ai” chicken ya bata amsa a tak’aice sai kuma ta k’ara kanne murya tace “to yalla6ai itafa mi za’a kawo mata?” Shiru yay mata jin wata tambaya mara kan gado gata ba sai ta tambayeta ba Fatuu kam har saida tay kaman zatai murmushi cikin ranta take ayyana kyama yi ki gama, har saida ta k’ara tambayarshi sannan idonshi akan waya yay mata nuni da Fatun yace “ask her” d’an ta6e baki tay ta nufi Fatun suka had’a ido tana kokarin bata menu d’in itama tace ta kawo mata babban robar ice cream da shawarma tace Ok ta juya Haisam yay ma Fatun kallon k’asan ido ya furta “Wannan ne zai isheki?” Yar dariya kawae tay bata ce mashi komae ba, bada jimawa ba waitress d’in ta dawo d’auke da k’aton tray wurin Haisam ta fara zuwa ta aje mashi nashi kafin ta nufi fatuu, tana niyyar tafiya Haisam ya tsaidata ta kalleshi sai lokacin suka had’a ido dashi yace ta kawo mashi pepper chicken da soft drink sai ruwa cikin kashe murya ta tambayeshi kaman ya complete chicken ko half yace complete ta d’an juya ido ta furta Ok kafin ta tafi, har ta kawo mashi bai fara cin fried rice d’in ba bayan ta aje mashi tace aci lafiya ta juya Fatuu ta d’an ta6e baki tabita da ido, tana juyowa taga ya turo pepper chicken d’in gabanta ta kalli kazar sai kuma ta kalleshi taga yana sakin wani Murmushin gefe nan take ta gane mi hakan ke nufi dama tasan tunda tay Maganar kaza yace ko tana son ci ne tabbas sai ya siya mata, tura mashi baki tay yay mata alamar ta fara ci shima ya fara cin nashi a nutse, ita kuwa Waitress d’in wuri ta samu can gaba ta zauna ta fiddo wayarta tana lallatsawa can wata ma’aikaciyar ta shigo d’auke da tray ta kai ma wasu bayan ta aje masu ta juya da tray d’in anan ta hango d’ayar zaune ta nufi inda take tana zuwa ta dafa shoulder d’inta tace “Su Billy manya shine kika bar aiki kika zo nan kikai zaune ko” wani d’an iskan kallo tay mata tana d’an Murmushi tace “zaman dole nike zuciya ce taga abunda take so” bud’a ido tay jin abunda billyn tace sai kuma ta juya tana k’are ma wurin kallo nan take idanunta suka sauka kan su Fatuu,

 

“Kice bak’in Farar fata mukae,to ke burgeki sukae kenan shiyasa kikai zaune kina k’are masu kallo”? d’an juya ido Billy tayi tace “ya dae burgeni” da sauri d’ayar tace “yau naga ikon Allah daga ganin Mutum kuma kika sani ma wadda yazo da ita ko matarshi ce ko kuma budurwarshi” d’an ta6e baki Billy tai tace “I don’t care ni dae yayi man ne baki ji dad’in voice d’inshi ba wllh, kuma ma ni ban tunanin wai ko matarshi ce ko budurwarshi nafi tunanin kanwarshi ce ma” d’ayar tace “kanwarshi kuma,haka kawae sai ya d’aukko kanwarshi ya zo da ita nan cin Abinci ko ba wani abu bane hakan ai nasan dae ba ita kadae ce kanwarshi ba”,

 

“Ke baki san in kud’i sukae ma Mutum yawa ba komae yi yake, ba kamar su daga gani ba cikakkun hausawa bane nafi tunanin half caste ne kuma ai zai iya yuwuwa yafi ji da ita ne acikin k’annan nashi” ta6e baki d’ayar tayi tace “lallai aiki ya sameki to, ki tashi kici gaba da aiki ko inje in kai k’ararki” ta k’arasa Maganar tana kokarin tafiya billyn tay dariya tace “ai na gama da kowa ba abunda zanyi” gyad’a kai tay tayi gaba abunta ita kuma billyn taci gaba da lallatsa wayan tana satar kallon yadda Haisam yake cin Abincinshi a nutse bai ma san tana yi ba,

 

Fatuu na cikin shan ice cream idonta akan tv tana kallon maimaicin shirin dadin kowa da aka fara yi a tashar Arewa 24 hankalinta ya tafi har bata san sadda robar ice cream d’in ta kubce mata ba gaba d’aya ya zube akan after dress d’inta duk ta 6aci dashi da sauri ta mik’e tana d’an yarfa hannu idon Haisam a kanta suka had’a ido dashi ta d’an yamutsa fuska d’an ta6e baki yay tace mashi yanzu ya zatayi ya d’age gira yace “ni nasa ki sake shi” d’an tura baki tay kaman zatai kuka ya bita da ido yana d’an murmushi, duk abunda ke faruwa akan idon billy hakan yasa ta taso ta nufo su tana zuwa cikin kashe murya tace “Subhanallahi 6are maki yay ne?” Kai Fatuu ta d’aga mata tace bari ta taimaka mata ta ciro rigar Fatun tace to, ta kai hannu ta cire Billyn ta kar6a ta juya, duk sai kuma Fatun tajita wani iri da ba rigar don kayan ba k’aramin tighting nata sukae ba hakan yasa tay tunanin tabi bayan billyn in an wanke sai tasa, fita tay daga cikin seat d’in ta nufi hanyar data ga billyn tayi Haisam yabi bayanta da kallo, tunda suke bai ta6a kafeta da ido ya k’are mata kallo irin haka ba bare har ya fahimci yadda jikinta yake ya dae san ba ramamma bace kuma yana jin ana Magana kan structure d’inta kaman can baya lokacin da Najeeb yay Magana kan hakan, dressing d’in ba karamin fiddo mata da shape yay ba don har shatin undies nata ana gani kasantuwar kayan roba ne, a hankali ya d’an juya lokaci guda yay noticing gaba d’aya hankalin mutanen dake wurin ya koma kanta maida idon yay a kanta har takai tsakiyar wurin don kayan basu barinta sauri a hankali take tafiya d’an d’aga murya yay yace “ZARAAH” dakatawa tay lokacin da kiran ya sauka cikin kunnanta Slowly ta juyo ta kalleshi don tasan shine ya kirata da kai yay mata alamar tazo ta juyo ta nufo shi idanunshi a kanta har ta k’arasa kafin tace wani abu yace “Sit and wait for her zata kawo maki ne” d’aga mashi kai tay don dama da tana tafiyar ta lura da yadda ake kallonta alama yay mata taci kazar a shagwa6e tace ai tayi mata yawa yace taci wanda zata iya,

“To kai bazaka ci ba” ta tambayeshi, shiru ya d’anyi sai kuma taji yace taci in ta rage zaici bud’a ido tay tace “ba baka cin saura ba?” Yar harara ya wurga mata tasa dariya ta kai hannu ta fara ci, can saiga billy ta dawo maimakon ta nufi Fatuu sai ta nufi Haisam cikin salo tace “amm Yalla6ai na wanke rigan tana can na shanya under fan don ta bushe da wuri in zaku tafi sai ayi man Magana in d’aukko mata” Slowly ya d’ago da fararen idanunshi tar masu d’auke da bakar kwaya mai baki sosae ya d’aura a kanta har saida taji fad’uwar gaba fuska a sake ya furta mata “thanks” wani far tay da ido ta washe baki tace “u’r welcome” daga haka ya maida idon yana cigaba da cin Abincinshi tay tsaye tak’i tafiya tana kallon sumar kanshi dake ta kyalli tasha gyara duk abun nan idon Fatuu na kanta ta gama kasheta da mamaki kasa jurewa tay tace “kar ki sa ya kware fa” kaman daga sama billy taji Maganar hakan yasa ta juya da sauri ta kalli Fatuu dake kallonta fuskarta ba yabo ba fallasa cikin dabarbarcewa billyn tace “a….am ina jira ya gama ne in d’auke kayan kar nayi tafiya biyu ba wani abu ba” wani kallo Fatun tayi mata cike da rainin Wayo tace “ba zaki kawo rigan ba ai sai ki d’auka lokacin ko” da sauri tace hakane ta manta ne ta juya cike da jin kunya ta tafi, kallon k’asan ido yay mata ta tura mashi baki yay d’an murmushi kawae bai ce mata komae ba, bai cinye fried rice d’in ba Fatuu ta mik’o mashi pepper chicken d’in ya d’an ci kadan daga haka ya yagi tissue ya fara goge hannu da baki tana ganin haka itama ta yaga ta goge tana kokarin mik’ewa taje ta amso rigar yace ta zauna ya mik’e ya nufi cikin wurin don kunya tasa billy ta bar wurin a can daga ciki ya ganta yace ta d’aukko rigar ta amsa da Ok ya juya ya koma bada jimawa ba sai gata tana wani shan k’amshi ta mik’a ma Fatuu rigar da d’an murmushi tace mata ta gode ba tare data kalleta ba tace ba damuwa ta juya taba Haisam bill d’in abunda suka ci ya fiddo Wallet ya biya yay mata kyautar dubu biyar tana Murmushi tace ta gode ya d’aga mata kai kawae ya tashi Fatuu ma ta fito bayan ta saka rigar tana zuwa saitin billy dake tattara kayan da suka yi amfani dasu ta tsaya tace “kiyi Hakuri in kinji haushi na sati mai zuwa ne d’aurin Aurenshi ban so ki wahalar da kanki ne” daga haka tay gaba abunta Billyn ta bita da ido baki bud’e acikin ranta ta fara ayyana to ko Fatun ce zai aura.

 

 

Suna barin wurin Zoo and park ya wuce da ita bayan ya yankan Masu ticket suka shiga, wurin namun daji su zaki, giwa da dai sauranau suka fara zuwa suna kallo cike da nishadi daga baya suka koma wurin liluna ganin tayi tsaye tana murmushi yasa yace taje ta hau wanda take so amman sai cewa tay ita kunya take ji har saida ya d’an bud’a ido alamar mamakin yau Zaraah ce da kunyar hawa lilo, ganin ta toge yasa yace suje su hau tare cike da mamaki ta bishi ya biya masu irin mai juyawa suka hau suna facing juna sai faman dariya take shidae murmushi kawae yake yayinda Mutane keta bin su dana mujiya don a zaton mafi akasari ba hausawa bane, daga baya suka sauka ta hau swing ya d’an rinka turata can kuma ya k’yaleta taci gaba da yin abunta yaja gefe yana kallon yadda take yin sama tana dawowa, sosae Fatuu ta samu nishad’i anan yay sallar la’asar a Masallacin wurin sai wuraren k’arfe biyar saura sannan yace mata su tafi gidan Abbas bayan sun fito yace suyi ma Abdul shopping a Supermarket d’in wurin, leda biyu sukae yace d’aya tata ce tay mashi godiya kafin suka wuce, suna kan hanya ya kira Abbas d’in ya tambayi yana gida yace mashi a’a yana kan hanyarshi dae ta komawa daga Jami’a yace Ok su had’e yana kan hanya shi da Zaraah, suna dab da shiga gate d’in Estate d’in shima Abbas ya iso suka shiga tare a bakin gate duk suka tsaya Abbas ya fito ya bud’e masu gate d’in suka shiga shima ya koma Mota ya shiga, bayan duk sun parker Motocin suna fitowa Abbas ya nufeshi yana fad’in “the latest Ango” shidae murmushi kawae yake ya bashi hannu sukai shaking kafin ya maida idon kan Fatuu yace “Mom Zarah barka da zuwa” da d’an murmushi tace mashi yauwa yace “kin rako ango zaga garin bankwana kenan” shiru tay still da murmushi akan fuskar Abbas yace su shiga suna shirin juyawa sai ga Abdul ya fito da gudu ya nufi Fatuu ta rungumeshi yana ta dariyar Farinciki itama dariyar take mashi ta d’agoshi Haisam yace ta d’aukko abunshi tace to ta bud’e back door ta fiddo ledan kayan kwalama da suka siyo mashi ta mik’a mashi ya amsa yace nashi ne tace eh cike da murna yace “thank u so much Aunty Zarah I love u” gaba d’aya suka sa dariya Abbas na fad’in ba dole kasota ba tunda ta kawo maka abu da sauri yace “No Daddy wllh ba saboda su bane ina sonta tana da kirki kuma tana da kyau” murmushi duk suka yi Abbas yace “yau da alama Mom Zarah ta tafi da hankalinka shiyasa ko ta baban naka bakayi ba balle ka gaidashi ko” da sauri ya nufi Haisam yana fad’in “Good Evening Baba Zakee Ango” gaba d’aya suka sa dariya daga haka suka nufi ciki hannun Abdul cikin na Haisam, cike da Farinciki Feenah ta tarbi Fatuu don sun kwana biyu basu had’u ba bayan sun gaisa tace bari ta shirya table dama Abbas d’in bai ci Abincin rana ba shima tana shirin mik’ewa Haisam yace mata a koshe yake tace ma Fatuu ai ita zata ci ko tace mata a’a itama a koshe take ganin yamma ne tasan dole sunci Abinci yasa ta k’yalesu Abbas ma yace ba yanzu zai ci ba, d’aki Abdul yaja Fatuu wai suje suyi game su ci kayan dad’in data kawo mashi Feenah ma tace baza’a barta ba da ita za’a ci tabi su Abbas na dariya yana fadin da girmanta zata cinye ma yaro abu, bayan barinsu parlon hirar tafiyarsu Haisam d’in gobe suka shiga yi can ya tambayeshi yadda akai suka koma Normal da Mom Zarah anan ya bashi labari yace ba abunda yake tunani bane kawae ta damu da tafiyar da zaiyi ne don basu ta6a hirar Aurenshi da ita ba so abunne yazo mata unexpected kuma gashi bazata je bikin ba, da mamaki Abbas ya tambayi dalili yace mashi zasu fara final Exams ne Next week d’in, shiru Abbas yay kaman mai tunanin wani abu lokaci guda ya tuna da ba Next week ake fara Waec ba sai Upper week wato sati na sama nan take ya fahimci Fatun k’arya tay ma Haisam hakan kuma ya tabbatar mashi da zarginshi akanta duk da ba zargi bane duk alamu sun tabbatar da son Haisam take kawae shima don bai da experience kan hakan yasa yak’i fahimta shiru yay kawae bai ce komai game da hakan ba sai da sukayi Magrib sannan sukae masu sallama suka rako su gaba d’aya har bakin Mota anan Feenah ke ce ma Fatuu “Mom Zaraah sai mun had’e Abuja ko” Abbas yay saurin cewa “Mom Zaraah bazata samu zuwa ba don lokacin sun fara Waec” kallonshi fatuu tay suka had’a ido ya saki wani murmushi da yake akwae haske sosae sam Feenah bata ji dad’in hakan ba haka ma Abdul daga haka suka shige Mota Abbas nace ma Haisam sai sun had’e goben suka tafi bayan ya bud’e masu gate, akan hanyarsu ne yake ce mata zadae ta raka shi Airport gobe ko tunda da yamma zai tafi har saida gabanta yay wata kalan bugawa kafin da k’yar tace mashi eh ai bazata ma je Makarantar ba ta fad’i mashi hakan ne don kar yama zo daukarta, tambayarta yay dalili tace mashi ba komae kawae shiru yay bai ce komae ba har suka iso gidan ba wanda ya k’ara tankawa, jiki a mace tace mashi ta gode ya jinjina mata kai kafin yace ta d’auki ledan baya tace to, bayan ta d’auka ta nufi gida ko juyowa batayi ba ya bita da ido har ta shige ya lura da canjawar da tayi nan take zuciyarshi ta ayyana mashi saboda zancen tafiya da yayi mata ne d’age kanshi yay a fili ya furta “I too gonna miss u Zaraah” iska ya d’an fesar ya d’ago ya kai hannu ya ja Motar.

 

 

Next Day……..

 

Bayan sallar juma’a misalin k’arfe 3:30 sun gama shirin tafiya tsab Hajiya tasha adon lifaya haka ma Saude tana sanye da doguwar rigar Atamfa da babban gyale don da ita za’a tafi Tk kuma zai tafi garinsu ne gobe daga can zai tafi tare da iyayenshi, gaba d’aya Tk ya gama fita da kayayyakinsu yasa acikin Mota, lokacin da suka k’araso parking space Gwaggo ta shigo cikin gidan tana ta sauri ta nufesu tana fad’in ayi Hakuri ta taushe hannu don ta sanar da Hajiyar zata raka su dama suna haka sai ga Haisam da Abbas sun fito daga part d’inshi sun nufo parking space din Haisam na sanye da wani d’anyen bak’in voile haka hular kanshi da takalman kafafunshi da agogon hannunshi suma duk bak’ak’e ne wato shigar complete black yay just Ma sha Allah, suna isa Abbas ya gaishe da Hajiya don bai shiga wurinta ba sannan ya gaishe da gwaggo tanata fara’a ta amsa Haisam ma ya gaishe da ita har zai bud’e Mota sai kuma ya dakata ya kalli gwaggo yace “Zaraah fa?” shiru ta d’anyi Hajiya tace “wllh nima inata son in tambayeta nasan dae yau ba islamiyya ai”, ganin duk ita suke jira tayi Magana yasa tace “d’ana Haisam kar ka damu mu tafi kawae” jimm yay haka Abbas ma Hajiya tace “wani abu Dije, ina Fateemar take?” Da yar damuwa tace “tana can tun jiya da daddare take abu guda yau ko Makaranta bata je ba sai aikin kuka ba irin lallashinta da ban yi ba amman a banza tunda ba jin Magana take ba” yar dariya Hajiya tayi sai kuma ta d’an girgiza kai tace “Allah sarki kinsan yadda sabo yake dole ta shiga damuwa Yayanta Handsome zai tafi gashi ba samun zuwa bikin zatai ba ko ni banji dad’in hakan ba itace ya kamata ace k’irjin bikin” gwaggo tace “to amman ai saitai hak’uri tunda kukan ba canja komae zaiyi ba kuma don an tafi ai ba shikenan an rabu ba ko” gyad’a kai Hajiya tayi tace suje kawae duk suka shiga Jeep d’inta Tk na niyyar shiga wurin driver don ya jasu Haisam ya tsaidashi yace ma Abbas ya kaisu shi zai taho tare da Tk d’in ya d’aga mashi kai da murmushi kan fuskarshi ya shiga mazaunin driver ya tashi Motar suka tafi, kallon Tk yay yace ya shiga shi kuma ya zagaya ya bud’e mazaunin driver d’in ya shiga daga haka yaja Motar Suka tunkari gate Officer na mashi Allah ya tsare sai ya zo suka wuce, A daidai gidan su Fatuu ya taka burki yace ma Tk yana zuwa,bud’e motar yay ya fita ya maida kopar ta rufe ya nufi cikin gidan…………….

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button