Uncategorized

Wasu Cututtuka Guda 4 Da Mutum Zai Iya Kamuwa Dasu A Dalilin Sumbata “kiss”

Cikin wasannin motsa sha’awa, sumbata ko kiss a turance yana gaba gaba.
Bama ga ma’aurata ba har masoya da babu aure a tsakaninsu suna sumbatar junansu. Sai dai kuma wannan dabi’ar yana iya yada cuta daga mai dauke da daya daga cikin cutukan nan ta wannan hanyar.

Wasu Cututtuka Guda 4 Da Mutum Zai Iya Kamuwa Dasu A Dalilin Sumbata "kiss"
Wasu Cututtuka Guda 4 Da Mutum Zai Iya Kamuwa Dasu A Dalilin Sumbata

Cutukan da mutane zasu iya kamuwa ta hanyar musayan yawun bakinsu ko tsotsan harshen su gasu kamar haka a cewar masana.

Cuta ta farko da mutum zai iya kamuwa dashi idan yana mikawa kowa bakinsa shine ciwon Antikuriya da ake Kiran cutar da suna syphilis a turance.

Cuta ta biyu itace cutar Human Papilloma virus a turance, amma basan sunan cutar da Hausa ba.Ita ma cutace da ake daukarta ta hanyar sumbata.

Cuta ta ukunsu itace cutar Herpes wacce itama bansan sunanta da Hausa ba.

Cutar launi biyu gareta. Akwai HSV 1 da kuma HSV2. Ita ma cutace dake yaduwa daga mutum zuwa mutum ta hanyar tsotsan baki.
Na hudu kuma ta karshe cikin cutukan da ake daukansu a lokutan yin kiss, itace cutar Cytomegalovirus.

Don haka sai a kiyaye shan bakunan juna ba tare da sanin lafiyan wanda za a shawa bakin ba.

Back to top button