Uncategorized

Maganin Jinnul Ashiq (Aljani mai hana aure ko mai kwanciya da matan mutane)

Aljani mai hana aure ko mai kwanciya da matan mutane

ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ

Idan aka ce Jinnul Ashiq ana nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji.

Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma in ta samun cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau’in Aljani shi muke kira

JINNUL ASHIQ 

ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷق

Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne mutum yake yi da su, su shiga jikinsa ba tare da wani dalili ba. 

YADDA MUTUM ZAI GANE YANA DA ALJANIN DARE KU TAƁA BULUN RUBUTUN

Back to top button