Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 36-37 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

      THIRTY SIX – THIRTY SEVEN📍

           Kukan dayaci karfinta ne yasa takasa cigaba da labarin duk ta fada musu kusan komai gameda rayuwarta……

Tinda ta fara labarin Umm take kuka kasancewarta mutum me rauni da tausayi, rungumeta tayi suka hadu sukaita kukan, tashi mami da batasan tana hawaye ba tayi ta hadasu duka ta rungume tana lallashinsu bayan itama kukan take…….

Deen ko yana gefe yana kallonsu, zirgi zirga ya shigayi ya kasa zaune ya kasa tsaye, chan kuma sai ya zube a kasa yayi tagumi yana kallonsu with blank expression, a haka bazaka taba gane yanayin da yake ciki ba saidai shi kadai yasan me yakeji aransa, ashe dama abin tausayin ce ita shiyasa yakejin tausayinta sosai? And he has a lot of questions to ask her right now, sannan a labarinta tace daddy mutumin kirki ne amma bega alamun hakan ba, the fact is that koma menene zeyi finding out, wuyarta kawai ya fara bincike yasan da sannu ze gano komai……Sai ya sake daga kai yaga kuka suke har  lokacin sai abun ya basa mamaki ya kuma rena karfin zuciyar mata, abu kadan sai su zauna suyita kuka?….

       “Haba Umm ke baki dena kukan ba taya zata dena ita?”……

Cewar mami da har lokacin itama hawayenta be tsaya ba amma bata sani ba………

Dagowa Umm tayi tana share hawayenta tace;

     “You’re also crying sis and I understand, I just can’t believe she went through a lot at this very young age?”…..

    “Gaskiya kam, I am even speechless with lots of questions!”……..

Gyada kai Umm tayi ta dago Fatima zainab tashiga share mata hawaye, saida taga hawayen tsaya ya tsaye sannan tace;

      “Sweetheart stop crying pls, komai tsanani maganinsa Allah, ki dauki hakan a matsayin jarabawar rayuwa kuma Allah be manta dake ba yana sane, you have a brighter future Insha Allah, worry not okay?”……

Sai kuma ta kara da;

     “Where are you from, ina family member dinki suke bayan iyayenki sun rasu?”…….

Dan jimm tayi kadan kamar bazatayi magana ba, chan kuma a hankali tace;

      “Bani da family members”……

Dariya mami dake gefenta ta danyi tace;

  “Injiwa? Ai kowa yana da family members sai dai in kin mantasu”…….

    “Okay”……..

   “Permit me to adopt you, I really want you to have a good life?”…….

Umm ta tambayi fatima zainab amma hankalinta na kan Deen da taga ya mike tsaye yana kallonta……

Shiru tayi bata bata amsa ba meanwhile bataso tayi adopting dinta dan daga gani takurawa rayuwarta zasuyi suyita mata kulle, ita kuma ta riga ta saba da freedom, tasan tsap zasu iya hanata shayeshaye musamman yanda Deen ke yawan ci mata mutunci akan hakan, kuma tasan ko sama da kasa zasu hade bazata iya dainawa ba……

      “Meh ka wani tsareni da ido dan nace I want to adopt her?”……

    “Because she’s already adopted!”…….

   “By who?”…..

Mami ta tambaya surprisingly…..

   “I mean yanzu a gurin Alhaji Ibrahim take, adopting her won’t be easy, dole sai komai yayi settling”……

    “The last time I checked kai ka binciko Alhaji Ibrahim has bad intention towards her, toh akanme zata koma gidansa?”……

    “Ba gidansa zata koma ba, aure zan mata very soon saboda shi kadai ze nitsar da ita!”…..,,,

Yana fadin haka ya sa kai ya fita daga parlourn da sauri dan yasan bazasu kare ta dadi ba…….

     “Umm kinji shashasha ko? Tun yaushe ake binsa yayi aure yaki yayi amma yana da bakin cewa aure ne ze nitsar da ita kamar wani ubanta, toh sai ya mata auren mugani”……..

    “Rabu dashi mami he’s not serious, in banda rashin hankali irin na saif antaba cewa zaayiwa mutum aure without someone on ground?”…..

     “Inaga siyo mata mijin zeyi, ni yazo ma inji a wani stand yake, nace yaje gidansu eesha banajin yaje”…..

    “Kai, Allah dai ya shirya, nidai yaya sai inga kamar gwara a barshi ya kawo wacce yakeso da kansa, kina gani wacce ya damu da lamarinta ma ba kyaleta yayi ba inaga wacce kwata kwata baya bi takanta, tsoro nake kar ayi aure ya dinga cutar musu da yarinya da wannan zafin zuciyar tasa”….. 

        “Kinfi kowa sanin halinsa Umm, I’m sure ko zaa bashi nan da ten years baze kawo wacce yakeso ba, toh haka zamuyi ta zuba masa ido ba aure?”……..

     “Hakane kuma, Allah ya tabbatar da alkhairi……

Fatima zainab na jinsu tayi kamar bataji, dan tsaki tayi aranta tace ashe aure ma zaa masa shiyasa itama yakeso ya mata auren dole kenan, aiko gwara tin wuri tasan inda dare ya mata dan zama a gidan ba nata bane……..

Haka suka cigaba da mata tambayoyi kala saidai kememe ta kasa basu kwakkwarar amsa kuma har cikin zuciyarta bata saniba, kamar dai wacce tayi losing memory dinta haka take basu amsa……….

Deen befi 30 mins da fita ba sai gashi ya dawo dauke da wata bakar leda sai envelope guda biyu a hannunsa…….

Umm ya mikawa envelope daya, ta karba batace komai ba ta hau karanta content din……..

      “Yaushe kukayi magana da Max Saket din?”……

Umm ta tambaya after reading the content finish…..

     “Jiya mukayi magana, na fadamasa kina nan, yace kiyi assisting dina mu fara mata start up medication kafin muje chan”……,

Gyada kai Umm tayi cikin gamsuwa……

      “What’s going on Doctors? A mana bayani we’re left behind”……

     “It’s about the transplant yaya, a Max Super Speciality Hospital, Saket, New Delhi zaayi”…….

     “Masha Allah, Allah yasa a dace, yaushe zaayi?”……

     “Ameen, in four weeks time, kinsan sai anbi wasu process kafin ayi main deal din”……

     “Nagane, Allah ya bata lafiya”…..

Tashi fatima zainab da bata gane kan zancensu ba tayi ta bar parlourn, dakin da aka fara kaita randa ta fara zuwa gidan ta tafi ta kwanta tana tinanin yanda zata bar gidan ta kuma bacewa rayuwarsu gabadaya yanda duk neman da zasuyi bazasu ganta ba, sai kuma tinanin halin da khaleel yake yanzu ya fara damunta, tasan duk inda yake hankalinsa baa kwance yake ba..…….

Bin biyanta da kallo Deen yayi kamar ze lasheta har saida ta bace masa daga gani sannan ya dawo da kallonsa kan su mami, sai a lokacin yaga yanda suka tsaresa da ido, cikin borin kunya yace;

     “Sai kusan yanda zaku mata fada ta dena shayeshaye, dan in bata dena she’s at more risk”…….

Be jira cewarsu ba ya ajye ledar dake hannunsa shima ya fita……

             Saida daddy ya saukewa khaleel lafiyayyun maruka guda biyu sannan ya nunasa da yatsa cikin bacin rai yace;

     “Ni zaka tozarta khaleel? Ni ni! Ni mahaifinka dana nuna maka gata fiyeda kowa a cikin ya’yana shine zaka rufe ido saboda mace kana nema ka tona min asiri? Why are you so stupid for love? Akanka aka fara soyayya ne khaleel daka bari hankalinka ya gushe akan wacce ko damuwa batayi dakai ba, ko kunya bakaji ajika da mahaifinka akan mace? Mata gasunan dayawa kamar pure water sai wacce ka zaba ma, kai da a tinaninka zan barka ka auri fatima zainab ne? Ina take da tarbiyyan da zaa zauna da ita a matsayin mata?, kai bama wannan ba bazan taba yarda ka auri yarinyar da bata da asali ba, a titi fa na tsintota khaleel, a titi fa! Tana rike da sigari a hannu, wannan kakeso in bari ka aura? Allah ya kiyaye wallahi, gwara tin wuri kasan inda dare ya maka ka nemo yar mutunci ko yar gidan uban waye namaka alkawarin zan aura maka ita, damuwata kawai ka rabu da yarinyar nan!!!”……..

Khaleel zeyi magana kenan daddy ya dagatar da shi da fadin;

     “Kamin shiru mallam! Yanzu abinda nakeso kayi shine muje police station ka janye case din chan a sakar min mutane na right away, sannan ka fitomin da fatima zainab duk inda ka kaita!!”….

     “Ka gama? Nace ka gama?”……

Khaleel ya fada da karfi……

Shiru daddy yayi yana kallonsa ganin dan daya haifa na daga masa murya yau akan mace, macen ma mara galihu……

     “Toh yanzu zanyi nawa, kabani mamaki daddy! Mamakin da baki baze iya furtawa ba, it’s so sad ace inada heartless father irinka!, meyasa ka taimaketa in kasan ba tsakani da Allah zaka riketa ba, toh bari kaji ko a gidan karuwai ka kamata da wani wallahi zan aureta a haka, idanma duka kayan shayeshayen duniyarnan kaga tanasha ina sonta a haka, wayace maka na damu da sanin wacece ita ko tarbiyyarta, infact ko yankani zata nayi kullum zan zauna da ita a haka wallahi, abu daya nakeso kasani baka isa kasa in rabu da itaba, kana gani kuma zan aureta just watch and see, and maganar mutanen dana sa akama stop dreaming zaa sakesu dan saina gama bincike na kuma tonawa mugaye asiri, ita kuma mara tarbiyya ba ruwanka da ita therefore karka kara tambayarta!!!”……..

 Kawai sai ji khaleel yayi an saita masa bindiga akai…

      “Duk son da nake maka bazaisa in zuba ido ina kallonka ka batamin aiki ba, so are you ready to do as I say ko in kasheka?……

Daddy ya fada yana kara saita ma khaleel bindiga akai abu kamar a film…..

Wani irin dariya khaleel ya fashe dashi, cikin halin ko in kula ya dawo da bindigar saitin zuciyarsa……

      “Go ahead and kill me, dan Allah ka kasheni daddy! Shoot me here zanfi saurin mutuwa dama zuciyata is already weak kiris kawai take jira ta buga, ka kasheni nace, ka kasheni!!!”…..

Hannun daddy ne ya fara rawa yayi saurin cillar da bindigar a chan gefe sannan ya juya ya shige ciki……

Sosai gumi ke karyo masa daya tina yanda ya saitawa khaleel bindiga akai, khaleel fa! His favorite! Ya akayi ya bari zuciya ta dibe shi haryayi wannan deadly attempt din, yasan yanzu khaleel zena kallonshi da abin bayan shi ba haka yake nufi ba, so yayi kawai ya tsorata shi ko ze bashi hadin kai amma it seems his coward khaleel ya zama brave yanzu, da sauri ya juya ya koma parlourn dan ya bashi hakuri ya lallabashi, saidai ko kafin yaje khaleel ya bar parlourn, neman bindigar daya cillar ya hau yi itama ya rasata…. 

Cikin rashin sanin abunyi ya kira alhaji habib ya fadamasa abinda ke faruwa, shawara ya basa akan suyi kidnapping khaleel su boye har sai komai ya daidaita tinda yasan daddy baze yarda a kashe khaleel ba, sosai daddy yayi na’am da shawarar har sukayi making arrangement yanda abun ze kasance…..

Daddy na shiga ciki khaleel ya dauki bindigar daya cillar ya fita, fita daga gidan yayi a kafa yanajin kansa kamar ze fita, abun ya masa yawa wai shege da hauka, ga fatima zainab be ganta ba ga lamarin daddy da besan a ina zeyi categorizing dinsa ba, tayaya baze shiga damuwa ba, sai ya rasa me zai dafa yaji dadi…………

Yana cikin wannan hali kiran sameer ya share wayarsa wanda rabon su da yin waya sun dade, dauka yayi ya kara a kunne……

      “Guy ya ake ciki ne?”……

Cewar sameer daga daya barin…..

     “Hala kashigo kasarne, naga ka kira ni da number Nigeria”…….

      “Eh wallahi na shigo, jiya na shigo”…

     “Ohk kana kano kenan?”…..

     “Nop ina abuja”…..

   “Ah haba, kana ina ne inzo in danyi clearing head dina dan na rasa inda zanyi dama”……

    “Subhanallah! Meya faru, ina base dinmu, bari in turo maka address”….

    “Kaidai sai nazo, yauwa turomin”….

        “No wahala”…..

Sameer na ajye wayar ya tura masa address din, sai ya zauna zaman jiran zuwan khaleel, yana abuja tun wanchan lokacin amma ba wanda ya sani, yana zaune shi kadai yanaji kamar damuwar duniya akansa aka sauke, tin bayan yusuf yace su hadu washegari da rana be kara samun nitsuwa a rayuwa ba saboda yusuf din bezoba kamar yanda ya fada, haka yayita sintirin zuwa gurin kullum amma har rana me kamar ta yau Yusuf be zoba,!sai ya rasa waye me gaskiya tsakanin Deen da Yusuf, hakan sai ya dagula masa lissafi kawai ya mayarda giya abin shansa, haka ze zauna yayita sha tin safe har dare yayita maye abinsa shi kadai, at first ya dauka competition yakeyi da khaleel sai yanzu yagane santa yakeyi da gaske,  ganin kamar illata kansa zeyi without any action ya sashi yanke shawarar kiran khaleel dan yasan dole ya samu information akanta a gurinsa…..

Yana zaune khaleel ya shigo parlourn da sallama, kallon parlourn yayi disgustingly yace;

     “Kaidai anyi kazami wallahi, daga zuwa harka bata guri?”…….

      “Man bazaka gane bane, nagaji ne sosai wallahi”..

     “Kaika sani ai”……

     “Naji meya faru”…….

   “My girlfriend is missing”……

   “Wifey din? Since when?”…..

   “Eh ita, yau”….

Dan jimm sameer yayi yana lissafi, indai har yau ta bata it means Deen baya tareda ita kenan?”……

     “Yau yau ta bata kodai tintini ta bata?”……

   “Ko yau da safe muna tare, nina kaita school da kaina”……

    “Wow”

Sameer ya fada yanajin ba dadi a ransa na yanda ya zargi Deen da daukanta, ashe tana tareda khaleel be sani ba, kenan kuma Yusuf karya ya dinga masa, inba karya yake ba meyasa ya nemesa ya rasa toh?….

       “Wow zakace ma? Ince maka wifey ta bata kacemin wow?”……

     “Sorry nigga, wallahi I was just shocked ne, ya kamata mu nemota duk inda take gaskiya, karka damu I gat you”..,,

    “Thank you”……..

    Tana kwance a bedroom din mami sun sata a tsakiya kamar yanda sukayi randa bata da lafiya, a lokacin tara na dare ya wuce, likimo tayi kamar me bacci saidai idonta ko alamar bacci babu, so take suyi bacci ta tashi ta gwada fecewe, har karfe goma shiru sunata dan hirarsu Umm nata shafa mata kai daga bayanta, lokacin harta fara fita hayyacinta saboda batasha regulars dinta ba tin safe, tasan kuma in bata sha ba ba zaman lafiya, tsap saita birgice musu, ita kuma bataso ta kara creating wani scene din dan bataso ta daga musu hankali ganin yanda suka damu da lamarinta sosai…….

Around 11 taji tsit lokacin sunyi nisa a bacci, tashi tayi sadap sadap ta fita daga dakin, fitilolin parlourn duka a kashe sai ko ina yayi duhu, tafiya ta cigaba dayi dan zata iya gane kofar fita….

Ji tayi tayi karo da wani abu kamar dutse, janyewa tayi da sauri ta cigaba da tafiya, sake karo tayi da abu sai kuma taga ko ina na parlourn yayi haske……

Kallon nighties din dake jikinta Deen yayi, gashi ba dankwali a kanta sai gashinta ya zubo gwanin sha’awa, sosai ta mishi kyau har tsigar jikinsa na tashi, lumshe ido yayi cikin husky voice dinsa da yanayin daya fara shiga yace;

     “Ina zaki? Meyasa bakya jin magana?”…..

   “Abu zan siya”…..

   “Codeine? Haka zaki fita kamar wacce zata club? Da kinfita wani ya ganki a haka wallahi baze kwana lafiya ba, ki kiyayeni!”……..

     “Toh in dauko hijabi inje in siyo, yanzu zan dawo”

    “And you thought I can ever believe you?, bama wannan ba wa kike tinanin ke barki ki cigaba da shayeshaye!”………

     “Nifa saina sha, in ban shaba bazan iya bacci ba, dan Allah ka bari inje in siyo”……

Dariya yayi yana jinjina wautarta wai sai tasha, ashe zataga karfin ikonsa yau…….

     “Naji! Kinada kudin da zaki siyane yanzu?”……

    “No, zaka aramin? I promise to pay back”……

    “Allah ya kiyaye in arar da kudina a siya kayan maye!”…….

     “Toh ka barni in fita, ni nasan yanda zanyi a bani kyauta”…..

Cillata kan three sitter dake kusa dasu yayi, cikin bacin ran daya taso masa lokaci daya yace;

     “Uban me zakiyi a baki kyauta? Dama kinsaba ne?”……

Shiru tayi tana rarraba ido da addu’ar Allah yasa su Umm suzo su kwace dan batada strength din rigimar dayake nema……

Gashinta ya fuzga ya dagota yana huci yace;

      “Answer me, me kikeyi ake baki abu kyauta?”…..

    “Babu, can you kindly leave my hair? You’re giving me headache”…..

Ta fada cikin zazzakar muryarta dake fita a hankali….

     “Gashin dokin kike cewa a saki, toh bazan sake ba sai kin bani amsar tambayar dana miki”…..

Hannunta ta dora akan nasa dake kan gashinta, ta shiga masa tafiyar tsutsa…..

     “I said nothing! Ka sakeni”……

Kamar wani robot haka ya sake mata gashin, sai ya kasa dauke hannunsa daga kan nata, shi kadai yasan irin tasirin da abinda take masa yake masa…….

Komawa tayi ta zauna ya bita kamar wanda ake controlling ya zauna a gefenta…….

Ganin kamar yayi laushi ne yasata dora hannunta akan kirjinsa tashiga balle masa botir din gaban riga tana fadin;

     “Let’s go get it pls”…..

    “Okay”….

Ya fada murya chan kasa……

      “Zaka aramin kudin in siya?”…,

    “Zan baki kyauta, ko nawa kikeso”….

    “Toh muje ka bani”…..

   “No ba yanzu ba”…..

    “Okayyy”…..

Ta fada tana karasa unbuttoning rigar gabadaya, nan faffadan kirjinsa me dauke da kwantaccen gashi ya bayyana, shafa gashin ta hau yi da dukka hanneyenta…… 

      “Asssshhh pls stop it!”….

Deen da yaji abin na neman fin karfinsa ya rike hannunta yana rokonta tabari dan yana gab da losing kansa….. 

      “I will not stop!”…..

    “Dan Allah kiyi hakuri, muje in baki kudin toh”…

Sai a lokacin tajanye hannunta zuciyarta fess kwalliya ta biya kudin sabulu dukda idan aka tambayeta meya faru bazata ce gashi ba…..

Tafiya yake kamar bayasan taka kasa tana biye dashi a baya, shi kadai yasan irin yakin dayayi da shedan dabe biye mata ba, har mamaki yake yanda be gaggaura mata mari ba saima lallabata dayake yana bata hakuri kamar wacce ya hana yin aikin Allah, baze manta encounter dinsa da wata staff dinshi ba wani lokaci, ta dade tana nuna masa wasu signs yanayi kamar be gane abinda take nufi ba, ranar yasata ta kawo masa coffee, fortunately sai yaji ya fita ransa ya zubar dashi, sai yasa a kirata tazo ta dauke tray din, tana na zuwa ta fara tabashi harda fadin ‘I know you need me sir’, nan ya zare belt dinsa ya hau jibgarta har saida ta fadamasa abinda tasa a ciki, duk da haka be hakura ba saida ya sumar da ita sannan yasa aka fitar da ita tare da sack letter dinta…… 

Amma in this case sai yakejin kamar be kyautawa fatima zainab ba, what if she really needed it? Karfa tashiga wani hali dan shi ya dauka dagaske take, juyowa yayi sauran kadan suyi karo dan tana dab dashi yayi saurin mannata da jikin bango yana dan maintaining distance a tsakaninsu…….. 

Kai fuskarsa yayi daidai kunnenta yayi lowering voice dinsa yace;

     “Do you really need it?”……

Yayi mata whispering kamar yana tsoron aji su…..

     “Yes, I so much need it”…..

Ta fada duk tinaninta maganar codeine yake……

    “Ohk, I’m all yours toninght, just don’t regret later,  in taimaka miki ko in kyaleki kiyi abinki?”…..

    “Ka taimaka min kaban kudin”…….

    “Ohh wai kudin kike nufi dama”…….

Ya fada yana shafa gemunsa ganin ya zama bad one din yanzu…..

    “Yes, shi nakeso”…..

Janyewa yayi ya fara tafiya yana fadin;

    “Toh muje in baki”….

Guri ya nuna mata a parlourn yace ta zauna ta jira shi ya dauko kudin……

Tana zaune ya fito ya sameta, zama yayi a kusa da ita ya zira hannu a aljihu kamar ze dauko kudin…..

      “Rufe idonki ki miko hannunki”……

Ba musu ta rufe tana jiran yasa mata kudin a hannu….

Sai ji tayi an tsira mata wani abu kamar allura a hannu, bude ido tayi da sauri zata janye ya rike hannun, be saketa ba saida ya juye mata ruwan allurar tass…..

     “Sorry, tashi muje musiyo”…..

   “Bazan tashi ba, why did you inject me when I’m not sick?”….

    “Kince kan ki na ciwo shine na miki allura, muje musiyo kinji koh?”…..

     “Ok!”….

Fitowa sukayi tana jin yanda wani bacci yake fuzgartarta ta daure, har sunkusa gate yace mata yayi mantuwa ta rakashi part din mami su dauko, batace komai ba suka juya suka tafi….. 

Kamar gaske yace ta zauna bari ya dauko abu, gurin dining ya tafi ya gama zagayen shi ya dawo, kallonta yayi yaga ta fara gyangyadi daga zaune……

     “Tashi muje musiyo”…

Firgit ta farka, cikin muryar bacci tace;

      “Kasiyomin pls, bacci nakeji yanzu”…..

    “Jeki kwanta toh, zan siyo miki”…..

     “Ok”….

Yana tsaye a gurin harta shige dakin mami, ajiyar zuciya ya sauke me karfi yana fadin ‘nasha da kyar’…. Sannan ya kwanta a parlourn kamar yanda yayi last time data kwana a gidan…..

      “Yanzu abinda yarannan yayi ya kyauta kenan? Ya mayar dani kamar wani sa’ansa? Ince karya kara barin garinman sai yayi tafiyarsa? I’ll make sure ya gane shayi ruwa ne this time around”….

       “Allah ya wuci zuciyarka alhajina, nima Deen ya bani mamaki, tiryan tiryan fa mukayi magana dashi akan yarinyarnan har cemin yayi zeje ya ganta sai gashi yayi tafiyarsa, amma gsky Deen ba haka yake ba kila akwai me zugasa”….

     “Waye ze zigasa banda uwarsa? I’m very sure abuja ya sake komawa tinda yanzu maganarta kawai yakeji”….. 

     “Gsky be kyauta ba, amma ga shawara alhaji”….

      “Ina jinki samira”…

    “Why not a daura auren 

 inyaso sai ka fada mishi an daura daga baya, kaga duk abinda ke kansa dole yayi hakuri ya zauna da ita”…….

     “Yes! Kin kawo shawara me kyau, dole in miki kyauta”…… 

    “Anything for you yallabai”…..

   “Thank you, gobe zan kira mahaifin Hamida yazo kawai a daura auren, shikuma idan yagama borin da zeyi dole yazo gareta!”…….

     “Insha Allah ba zaa sha wahala ba zasu daidaita kansu”…

    “Allah ya yadda, mu kwanta koh?”……..

     “Uhmm okay”……..

         “Allah ya bada saa”……

Umm da mami suka hada baki wajan fada suna dagawa fatima zainab dake gaban mota hannu….

Jan motar Deen yayi har lokacin fuskarta a hade yake, haushin shi takeji dan tinda safe yasata a gaba wai sai tayi karatu batasan ya akayi yayi finding out tanada exam 11 na safe ba, haka ya isheta da tambayoyi akan course din tayi banza dashi, karshe ya fara mata masifa wai she’s not serious sai taje ta kwaso carry over, ce masa tayi ko tazama serious saita kwaso course din daya yaga mata paper besan tanajin haushin abun ba haryanzu, dariya abun ya bashi sosai yace mata indai zatana jin maganarsa toh batada case da course din ko A takeso ze bata, amma kememe taki yarda suyi karatun, sai hakura yayi ya kyaleta, haka da sukazo tafiya ya dinga bata wahala dan yafi so hudu yana cewa taje a sake mata kaya, a na biyar dinne mami ta biyota tace be isa ba, tuburewa yayi wai saidai tasa hijabi har kasa, haka mami tace tayi hakuri tasa su tafi kartayi latti dan tasan Deen da kafiya, hakan be ishe shi ba wai sai tasa nikab, wai ai tasaba sawa, Umm ce ta raba wannan fadan tace toh ta saka nose mask su tafi kar lokaci ya kure…….

       “Hey baby girl?”……

Deen yayi magana kamar ba yanzu suka gama fada ba……

     “Wai fushi kike haryanzu?”……

   “Bazaki kulani ba?”….

   “Allah ya baki hakuri toh”…..

Harya hakura ya kyaleta sai kuma yaji baze iya shareta ba……

      “Talk to me baby girl”…..

    “Ka kyaleni!”…,,

   “Atleast kinyi magana, dama haka kike?”…..

      “Da nayi meh?”…..

    “Yesterday! You almost raped me! Allah ne ya kwaceni”……

Bude manyan idanuwanta da suke a lumshe koda yaushe tayi, ta zaro ido tace;

      “What?!!!”…..

   “Eh mana, ni dena zaro min idanuwannan naki kamar ta Allah, zakice bakiyi attempting yimin fyade ba last night?”……. 

      “Why’re you like this? Wannan wani kalan magana ne, ta ina mace ke raping namiji? And as long as I can recall nothing happen last night”……

      “Can you listen to yourself? Nothing happened for kika ce, zaki rantse da Allah you didn’t kiss me? you didn’t romance me? You were one step away nayi escaping fah! Badan tsoron Allah dayamin yawa ba da yanzu kingama dani”…….

Dan shiru tayi tana nazari abunda ya faru last night saidai she can’t recall anything, amma he sound so serious shiyasa tayi shiru…..

Shiko Deen dariya kawai yake dannewa ganin yanda tayi tsuru tsuru tana kallonsa, ya kuma fahimci duk abinda tayi jiya baa hayyacinta bane tinda ta kasa musa sharrin daya mata…..

     “Dole kiyi shiru mana tinda kinsan baki kyauta ba, ni yanzu tsoron zama inuwa daya dake nake kar kije ki lalatani”……..

     “Godddd! Why do you talk too much? Can you just keep quiet?”…….

 Sakin baki Deen yayi yana kallonta, wai shi ake cewa he talks too much? Shida magana dashi ma sai ancike form amma ita wannan complain take ya cika surutu, well dama ance duk abinda kake wani ya fika, gashi ya hadu da wacce ta fishi miskilanci, magana daya biyu tace kanta na ciwo……

Shirun yayi kamar yanda ta bukata suka cigaba da tafiya in silence har suka kai school dinsu…….. 

Fitowa yayi ya bude mata kofa ta fito, suka jera suka nufi venue din, suna zuwa lokacin har an fara exam, shiga sukayi invigilators din suka taso da sauri suka gaisa dashi, ganinta tare dashi yasa aka barta ta zauna dan a ka’ida idan aka fara exam baa bari a shiga…..

Da kanshi ya kaita chan baya dukda baa ganin fuskarta ranar dan tasa nose mask yace ta zauna anan, zama tayi ya kawo mata question paper da answer booklet da kansa sannan ya zauna a kusa da ita….. Invigilators din na kallonsa amma ba wanda ya isa yace wani abu dan yanzu sai ace maka an koreka daga sama shiyasa suke girmamasa dan bawanda besan matsayinsa dana iyayensa ba a kasar….. 

Haka students dinma sai suka hau binsu da kallo, saida ya daka musu tsawa yace ‘will you all face your exams’ sannan suka shiga taitayinsu….

Tinda ta rubuta sunanta bata kara ko a akai ba, yana kallonta ta gefen ido har akaci one hour tana a haka, ganin in ya barta a haka zaace suyi submitting batayi komai ba yasashi fadin?….. 

      “Tin dazu kinki rubuta komai, olodo kawai!”……

      “Ba ruwanka!!”…..

    “Do you know one thing about you? You do even bad things with pride!”……

    “Anyi din!”…..

    “Danma kinsamu zaa taimaka miki shine kike yiwa mutane iya shege, ni bani ingani”….

Ya fada yana janye question paper da booklet din ya hau dubawa…..

     “Olodo this is so simple!”……

   “Ai bance kamin ba! Karka kara cemin olodo kuma!”………

     “Ke kika sani, ungo zanna fadamiki amsar sai kina rubutawa”……

Karba tayi kamar gaske sannan ta cillar da pen din ta window irin zakaga wanda zeyi rubutu, sake dauka yayi yace;

     “Carry over dinki nawa? I’m sure befi course daya kika taba passing ba!”……

      “Matsalarka ko tawa?”…..

    “Shut up! Karkimin rashin kunya!”……

Shiru tayi bata kuma kulashi ba, tana kallo yasa aka kawo masa sabon pen ya mata exam din tass ko tsoro bayaji, ba ita kadai ba kowa kallonsa yake a fakaice amma ba wanda ya isa yace wani abu, mika mata yayi yana dungure mata kai yace;

     “Gashi badan halinki ba!”……

    “Ban gode ba tinda bani na saka ba!”…,,

    “Dama baso nake ki gode ba, mara mutunci kawai!”……..

     “Anji din”……

   “In the next ten minutes zakiyi submitting mu wuce”……

Yi tayi kamar bataji ba har wayarsa ta fara ringing babu kakkautawa, kallon screen din yayi yaga dad dinsa ke kira, saida kiran ya kusa katsewa sannan ya daga yana fita daga hall din……

Tana ganin ya fita ta tashi taje tayi submitting ta fice ta daya kofar which is the main door, tafiya tayita yi harta kusa wani isolated garden dake school din, horn taji daga bayanta ta kara speed duk a tinaninta Deen ne ya biyota, ganin bazata tsaya ba yasa khaleel saurin fitowa yabi bayanta yana kiranta…

    “Wifey! Wifey! Dan Allah ki tsaya!”….,

Da sauri ta juyo jin muryar khaleel, mutumin daya tsaya mata arai tin bayan haduwarsu a gidan daddy randa aka kusa daura auren chan..,.,,

     “Khal! Where have you been?”…..,

    “Ke zan tambaya, waya tafi dake ranar?”…..

     “Bansan shi ba!”…..

     “Alright mushiga garden din chan muyi magana, there’s something important I want us to discuss”….

       “Okay”….

Saida suka samu guri suka zauna sannan khaleel yayi gyaran murya yace;

     “I am uncertain about what the future holds for us, whether our dreams will come to pass, or how far our love will go, but I know that I love you”…….

Sosai jikinta yayi sanyi dan ita kanta tasan khaleel na sonta, and he never fails to remind her how much he loves her duk sanda suka hadu, and he so much deserve her love plus what she’s feeling idan suka hadu yanzu is something else…. Murmushi tayi tace;

      “I have failed you in many ways, but I am glad you never left me. Thank you for being my ride or die”…..

     “For real? Am your ride or die? Between you have never failed me wifey, I wish every day you could see yourself the way I see you. Because I see you as absolutely perfect, I am still leaving because my heart only beats for you!”……

     “Thank you for warming me up with your words  khal!”…….

      “It’s my pleasure, how is the exam?”…..

      “Alhamdulillah”…..

    “Wifey you’re in danger, bansan me daddy yake nufi dake ba but ba alkhairi bane and I can’t bare losing you, kizo mu gudu muje muyi aure dan Allah”…….

     “Mu gudu kuma, don’t you think of your father mom and dad?”…..

    “I don’t care so far as I’ll be with you, let’s just go far away from all the wicked people, mu gudu muje muyi aure muyi rayuwarmu mu biyu abunmu, I promise to take very good care of you, if it takes giving you the world completely I’ll do”……..

        “Na amince!”…..

Ta fada with a devilish smile saboda faduwa ce tazo daidai da zama, dama tana tinanin yanda zata gudo daga gurin mayen chan sai gashi Allah ya kawo mata, khaleel ko tasan sai yanda tayi dashi dan in tace yes ko uwarsa bata isa ta chanja ba…….

     “Wayyo am I dreaming? Naji dadi sosai wallahi, I knew we’ll someday get along that’s why I’ve always been patient”…..

Khaleel ya fada grinning from ear to ear…..

       “Yeah”…..

      “Alhamdulillah, ya Allah thank you”…..

     “Khal!”…..

Ta kirashi with a serious tone….

     “Yes my love”….

   “I don’t know how it happens but I think I’m in love with you!”…….

Kamar saukar aradu haka Deen yaji wannan kalaman nata, tun da suka fara zancen yake gefensu basu sani ba wai su masoyya, harsu zancen guduwa yanaji yace zega yanda zaayi tabi saurayi su gudu, ji yayi kamar ya shakota yanda take wani kashe masa murya, ransa in yayi dubu ya baci a inda yake a tsaye, daurewa yayi yanaso yaji inda zancen nasu ze kare sai kawai yaji wani abu kamar saukar dalma, wai she’s in love with him?!!!……

Back to top button