Hausa novels

Matar Hariji Page 11 Romantic Hausa Novel

Bata ida fadin abinda ke bakinta ba taji yayi sama da ita bai direta ko inaba sai kitchen din dake cikin parlourn saman yace “shirmenki yayi yawa Hauwah yunwa nakeji me zamuci?” Turo baki tayi tace “nan kuma dakin wayene?” Janyota yayi jikinsa yace “kitchen ne anan akeyin girkin duk abinda zaaci” Dariya tayi sosai tace “amma Kado kai dan rainin hankali ne yanzu nan duk jeran nan kana nufin madafi ne to inma banda ka rainani Ina zaa girka murhu?” Haɗiye dariyarsa yayi yace “aiga murhun nan zo kiga inda ake kunnawa” matsawa tayi ya dauki abin kunna gass ya danna ta saki qara tare da cewa “wayyohh kunne na wayyohh zai qonani!” dariya sosai yace “zo kiyi mana girkin abinda zamuci yunwa nakeji” Turo baki tayi tace “chabdi nidai aa bazan iya girki ba ni ko kunu ban taba damawa ba balle wannan jagwalgwalon naku na yan birni” murmushi yayi ya dauko tukunya sabuwa dal a cikin kitchen cabinet ya zuba ruwa ya dora ya goge hannunsa ya jata suka fito yace.“Zauna Ina zuwa” baijira cewarta ba ya nufi downstairs din ya sauka ya nufi matattakalar da zata kaishi part din Mubaraka ya haura ya tarar da ita a tsaye da waya a hannunta tana yafa mayafi yace “ina Zaki?” Cikin kallo irin na tsantsar tuhuma tace.“Zanje na tambayi tsohuwarka ne da saninta ka kawomin wannan kucakar karuwar taka gidana har kayi Mata bangare a cikinsa ka shige daki da ita sama da awa guda” Murmushinsa ya fadada yace “Abinne yazo a bazata wlh shiyasa ban sanar dake ba kiyi hqr nasan nayi miki laifi duk da qila kinsamu lbrn dama Ina neman aure, Mmn Fadwah wannan yarinyar da kike gani matatace ta sunnah da aure yabani matsayinku daya a gurina babu wacce tafi wata sai wacce tafi kwantarmin da hankali”Numfashi yaja yaci gaba da cewa “Mubaraka Hauwah yarinya ce qarama qanwar bayanki ta qarshe gaba daya bazata wucce saar Zainab qanwarki ta hudu ba, haka Allah ya nufa kuma ya qaddara batasan komai ba dani dake mune zamu sanar da ita idan mukayi Mata mugun karatu dashi zata tashi idan muka bata sahihin karatu da babu mugunta ko sonkai a cikinsa to shine zaita zagawa tsakaninmu alkhairi zai wanzu cikin zamantakewarmu ya bamu kyakkyawar alaqa da fahimtar juna wanda hakan zaiyi tasirin bibiyarmu har qarshen rayuwarmu…..”Daga masa hannu tayi tace “kayyy dakata munafukin Allah ta’ala kana nufin wadannan matsiyatan kalaman naka sune zasuyi tasiri a kaina? Hmmm wai qanwa wlh kayi tsararo Allah ya kiyasheni tabewa yin qanwa da wannan bagidajiyar yarinyar kaidai daka kwaso ta kware maka can Amma badani ba” Yanda take mgnr tana nufoshi kamar zata dakeshi yasashi sakin baki yana kallon ikon Allah har ta iso gabanshi tace “wannan itace sakayyar halaccin da nayi maka ko Lameer kaje ka ajiye karuwa a Lagos sannan ka tashi dawowa ka dawomin da kishiya kishiyar ma wannan qazamar kucakar yarinyar da bazata taba wayewa ba a rayuwarta, to wlh saidai ka zaba koni ko ita nikam bazan taba zama da ita a matsayin kishiya ba Wai muna amsa suna daya gurin mijinmu.Ka cuceni a abubuwa da yawa Lameer baka damu da saukemin haqqina ba wata da watanni kana qwarata kana barina da damuwar da banida me yimin maganinta saikai sannan yanzu ace kayi aure wannan ma ai cin fuskane da wulaqanci da wanne kuzarin zaka riqemu mu biyu har ka biyawa kowa buqatarta?”Shafa sumarsa yayi yace “duk wannan ba damuwarki bace abinda ya shafeki kuma haqqi a gareki shine na sanar dake matsayin Hauwah a gurina kuma na sanar dake ruwa nane na kusanceta kullum ruwa nane na shekara ban kusanceta ba kamar yanda nakeyi miki wannan ba matsalarka bace, amma dai ki sani kuma kisa a ranki aurena da Hauwah yin Allah ne kuma ya qullu babu wanda ya Isa ya hanashi kamar yanda mahaifinta da danginta suka qi kuma suka qyale akayishi yaka duk wani dan baqin ciki zaiyi quncinsa ya qyalemu, idan kuma mutum yana ganin bazai iya hqra ba to ya hadiyi zuciya ya mutu kowa ya huta”Wani mugun tashin hankali ta tsinci kanta a ciki da bata taba tunanin Lameer zai sata a ciki ba tunda sukayi aure tsayin shekara uku baitaba daga muryarsa sama da tata ba sai akan wata mace macen ma wannan qazamar kucakar bafulatanar dako yar cikinsa inda yayi auren wuri batakai ba, lallai da aiki ja a gabanta dole ta tashi hankalinsa dana zuri’arsa, babban tashin hankalinta yanzu cikin da take dauke dashi na watanni biyu wanda a lissafe idan zaiyi lissafi watansu hudu rabon da wani harka ta auratayya ta shiga tsakaninsu sai kwanaki takwas daya wucce ranar da tayi masa tujarar nan, yanzu ta yaya zata fara liqa masa cikin kamar yanda ta liqa masa na Fadwah?..……………Miqewa yayi yace “kewai komai ma baki iya ba bakiga toilet a bathroom ba dazu da kikayi wanka zakicemin wani kashi kikeji” sakeyin raurau da ido tayi tace “ni wlh banga juji ba” ya lura itafa komai bata ganewa sai anyi mata gwari gwari hakan yasa ya kama hannunta suka shiga bandakin ya bude seet toilet din yace “ga gurinda akeyin kashi nan idan kika gama sai ki murda wannan ki zaro tissues ki goge saiki sake danna nan ruwa zai zubo saikisa sabulu ki wanke idan kin gama kuma ki danna nan zakiga ruwa yazo yayi flurshing”Fita yayi yabarta a tsaye tana leqen cikin toilet din tana kallon ruwan ciki gare gare tace “to aini dazu a wannan randar na debi ruwan alwala”🤣Har yaja qofar yace “ehh!” Tare da zaro ido yace “kika debi ruwan alwala anan?” Daga masa kai tayi tace “eh aradun Allah kuma ruwan dumine dashi danasashi a bakina har wani zaqi yakeyi” ai baisan sanda yayi qasa ba yace “kinsha fitsarina Hauwah kewai wacce irin shashashar yarinya ce bakiga inda nayi tawa alwalar ba” turo baki tayi tace “toni Ina ruwana bakaine kace nazo nayi alwala ba”Takaici ne yasashi miqewa ya fice daga toilet din ita kuma tahau kan masan, memakon ta zauna aa saita tsuguna akai qafafunta nakan gurin zaman idan tayi kashin ya fada tsulum saita qyalqyale da dariya tace “danwake daya ya fada” haka harta gama tayi duk yanda yace.Ta wanke hannunta ta fito baya cikin dakin hakan ya bata damar yin sallar magrib da Isha ta kwanta a qasan.Ya turo qofar ya shigo ya hangeta a qasa ya matsa da sauri ya dagota yace “kekam baki gudun mgn kin mayi wanka kuwa?” Kada masa Kai tayi ya dagata yace “ok muje kiyi wankan mu kwanta gobe litinin jirgin asuba zamu bi mu wucce Lagos” itadai batace masa komai ba ya dagota suka shiga bathroom din to yanzun ma a bataso tana zillewa shine yayi mata wanka ya fito da ita shima yayi suka kwanta bayqn yayi musu addu’a.Kiran sallar farko akan kunnensa ya tashi yayi wanka ya tasheta ya fito Mata da wata doguwar rigar atamfa cikin kayan da ya bayar tunkan yatafi a dinka mata yasata ta sanya ya bata mayafi da takalmi da jaka ya koma yana kallonta tayi masifar kyau kamar ba itaba.

Back to top button