Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 24 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                          TWENTY-FOUR📍

     Da sauri fatima zainab tayi kanshi tana kokarin shako wuyarsa kozata samu ta kasheshi ta wuta, kamar ana zugata so take kawai taga baya numfashi….. 

Fuzgota yayi da karfi yana damke hannayenta da suke kokarin shakesa, hugging dinta yayi sosai yana mannata da bangon kofar…..

Fizge fizge tashigayi tana neman kwace kanta yasa mata karfi sosai ya matseta sannan yayi bismillah ya fara karanto suratul mulk kamar haka;

    “Tabaarakal lazee biyadihil mulku wa huwa ‘alaa kulli shai-in qadeer

Allazee khalaqal mawta walhayaata liyabluwakum ayyukum ahsanu ‘amalaa; wa huwal ‘azeezul ghafoor

Allazee khalaqa sab’a samaawaatin tibaaqam maa taraa fee khalqir rahmaani min tafaawut farji’il basara hal taraa min futoor

Summar ji’il basara karrataini yanqalib ilaikal basaru khaasi’anw wa huwa haseer

Wa laqad zaiyannas samaaa’ad dunyaa bimasaa beeha wa ja’alnaahaa rujoomal lish shayaateeni wa a’tadnaa lahum ‘azaabas sa’eer

Wa lillazeena kafaroo bi rabbihim ‘azaabu jahannama wa bi’sal maseer

Izaaa ulqoo feehaa sami’oo lahaa shaheeqanw wa hiya tafoor

Takaadu tamayyazu minal ghaizz kullamaaa ulqiya feehaa fawjun sa alahum khazanatuhaaa alam ya’tikum nazeer

Qaaloo balaa qad jaaa’anaa nazeerun fakazzabnaa wa qulnaa maa nazzalal laahu min shai in in antum illaa fee dalaalin kabeer

Wa qaaloo law kunnaa nasma’u awna’qilu maa kunnaa feee as haabis sa’eer”………

Ihu tashigayi cikin wata iriyar murya mara dadin sauraro tace;

     “Wayyoooooo, dan Allah kayi hakuri”….

Gyaran murya yayi yace;

     “Da wani shaidanin nake magana tukunna”….

Cikin wata kalan murya tace;

      “Ni ba shaidani bane, ni musulmi ne, ka fita sabgarmu”….

      “Bazan fita ba! Waye kai!”…

    “Yusuf ne”…….

 “Menene matsalarka da ita da kake takurawa rayuwarta haka?!”…..

   “Matata ce!”….

Hannu ya daga ze wanka masa mari dan ya shiga saitinsa, sai kawai ya naushi bango tuno da cewa ita zataji a jikinta ba dan iskan ba….

    “Matarka a gidan ubanwa? Wani mahaukacin ne ya daura muku auren?”….

    “Babana ne ya daura mana, aurenmu yau shekara uku, yayanmu biyu”….,

    “Oh yanzu nagane, kaine wahalallen da nacewa ka fita sabgarta dazu ko, amma baka daddara ba kazo ka biyomu harda hada munafurci ko, toh zakaci ubanka yau”….

Cikin shesshekan kuka tace;

    “Ka bani matata kawai mutafi, ni babu ruwana dakai”….

     “Wallahi ka sake kiranta matarka saina kona duka danginku banza mugu kawai, in banda mugunta ta ina aljani zeyi tarayya da mutum?”…

  Deen ya fada a zuciye yana kara mata rikon tsauri tsabar yanda ranshi ya baci, kai dole ma taji a jikinta daga baya…..

      “Eh mu munayi, dan Allah kayi hakuri ka kyaleni”…,

    “Kai har kasan wani Allah dan uwarka, idan kanaso na kyaleka toh akwai sharuda”…

      “Zan bi, zan bi”…

Ta fada da sauri….

     “Kafinnan kai kake sata take rashin kunya da rashin ganin girman nagaba da ita?”….

     “Aa bani bane ba, wallahi bani bane”..

  “Karya kake, aiba gaskiya ne daku ba!”…

 “Wallahi bani bane, bani bane ka yarda dani”…

     “Hmmm naji, sharadun farko ka saketa daga gantalallan aurenku da kake fada, sannan kuma ka fita daga jikinta ka rabu da ita na har abada”…..

     “Gsky bazan iya ba saboda ina sonta sosai, auren zobe mukayi ba rabuwa ba saki, inaji da ita sosai dan tana da kyau, tafi duka matan garin mu kyau”…..

      “Shikenan dan mutum yanada kyau sai ku takura masa saboda kagu mayu?”….

     “Aa kawai ina sonta ne sosai kuma ina kishinta”… 

Kwafa Deen yayi yace 

       “Zakaci ubanka”…

Sannan ya fara karanto suratul jinn kamar haka

     “Bismillaahir Rahmaanir Raheem 

Qul oohiya ilaiya annna hustama’a nafarum minal jinni faqaalooo innaa sami’naa quraanan ajaba

Yahdeee ilar rushdi fa aamannaa bihee wa lan nushrika bi rabbinaaa ‘ahada

Wa annahoo Ta’aalaa jaddu Rabbinaa mat’takhaza saahibatanw wa laa walada

Wa annahoo kaana yaqoolu safeehunaa ‘al allahi shatata

Wa annaa zanannaaa al lan taqoolal insu wal jinnu ‘al allahi kaziba

Wa annahoo kaana rijaalun minal insi ya’oozoona bi rijaalin minal jinni fa zaadoohum rahaqa

Wa annahum zannoo kamaa zanantum al lany yab’asal laahu ‘ahada

Wa annaa lamasnas samaaa’a fa wajadnaahaa muli’at harasan shadeedanw wa shuhuba

Wa annaa kunnaa naq’udu minhaa maqaa’ida lis’sam’i famany yastami’il ‘aana yajid lahoo shihaabar rasada

Wa annaa laa nadreee asharrun ureeda biman fil ardi ‘am ‘araada bihim rabbuhum rashada”…

        “Wayyoooooooo zan fita, zan fita zan fita, dan Allah karka konani, nace maka zan saketa”…

Be kulashi ba ya cigaba da karatu har saida yakai karshen surar lokacin harta fara wani irin kuka me ban tausayi sai ihu take tana san kwace kanta ta kasa…….

Saida ya tabbatar tayi mugun laushi ko yace yayi mugun laushi sannan yace;

      “Me kace?”…

   “Nace zan fita dagaske”….

  “Yadai fi maka, kayi alkawarin inka fita bazaka dawo ba?”…..

     “Eh bazan dawo ba”….

    “Idan ka dawo in maka me?”….

    “Duk abinda kaga dama”….

   “Yayi kyau,idan ka isa ka dawo nida kaine, yanzu ka fita ta inda kasan bazaka chutar da ita ba”…

     “Toh na fita”….

Tana fadin hakan tayi wani atishawa me karfi sai kuma ta sume a jikinsa, rungumeta yayi yana shafa bayanta cikin tsananin tausayinta, zai iya cewa betaba ganin wacce yaji yana mugun tausayinta kamar itaba, he’s just imagining what she has been going through, how he wish zatayi hira dashi kamar yanda yaji tanayi dasu Umm dayaji dadi, he had always suspect there’s something behind her ashe he was not mistaken, yanzu kuma he’s feeling like bayan wannan aljani daya ke claiming ya aureta there’s another thing, da zata fadamasa ‘WACECE ITA’ da komai yazo masa da sauki…. 

        Zaune suke su biyar a wani dakin taro gabansu dauke da lemuka da ruwa saidai babu wanda ya taba saboda tashin hankalin da suke ciki, ko wannensu kana kallon fuskarsa zagasan ba karamin tashin hankali yake ciki ba kadama daddy yaji labari da wani gumi yake keto masa kamar wanda yayi tsere….. 

     “Garin yaya kayi sake haka? Gashi yanzu komai na neman kwabe mana”…,

Cewar alhaji usman yana kallon daddy….

Gigiza kai daddy yayi yana sharce gumin dake kansa yace…..

     “Banyi sake ba wallahi, bansan ya akayi abubuwa ke neman chabewa ba”….

      “Idan bamu tashi tsaye ba akwai matsala sosai gaskiya, boss yace akwai wanda yasa mana hannu!”…

Alhaji tahir ya fadi haka yana gyara zama…

      “Dagaske? Inko hakane akwai matsala, waye shi mu kau dashi kawai mu wuce gurin”…..

Cewar daddy yana zaro ido….

     “Matsalar da ake ciki kenan boss be gano waye ba tukunna, nima haka nace muna gane waye kawai mu kau da dan banza”…..

Numfasawa alhaji lawal yayi yana kallon daddy yace;

      “Yanzu meye abunyi toh?, dole fah ka auri yarinyarnan kota halin kaka, ko mubi ta dayan hanyar kawai a wuce gurin?”………

       “Aa nafiso dai na aureta din komai zefi zuwa da sauki”…….

     “Toh shikenan, sai mu mayarda hankali akan nemota ko ina take tin kan abu ya lalace!”……

      “Wannan ba matsala bane!”…..

 “Ya kukayi da wanchan? Da fatan angama da babinsa ko?”….

Alhaji usman ya fada yana nuni da alhaji habibu….

Murmushi alhaji habibu yayi yace;

     “Wannan shi yafi komai sauki, kusa a ranku kamar labarinsa ya shude, angama da komai!”..

     “Yayi na wajena, boss yace ze fadamana inda yarinyar take sannan mu tabbatar an daukota gobe!”…..

          “Karka daga hankalinka, dazu fa ina kallonka kana nemana, cikin boot na shige”….

        “Saboda baka da gaskiya ko? Meyasa ka buya toh?”….

Sameer ya fada adan tsorace dan gaskiya ya tsorata..

Dariya yayi sosai yace;

     “Yana ganka kai kadai, ina take?”……

    “Bata gidan!”…

 “Karya yake! Wallahi tananan, ka bari ya maka wayo ko?”….

     “Wani irin wayyo, dalla mallam fita min daka mota!”…..

Sameer ya fada yana samun wani courage…. 

       “Ko baka ce ba dole in fita inje in dauko ta dan bazan tafi batareda matata ba!”…..

Zaro ido sameer yayi yace;

     “Matarka???”…

   “Eh matata!”…

   “Mallam fitarmin daga mota dan magana dakai naga bata lokaci ne”…..

    “Yanzu kuwa zan fitar maka daga mota, amma kafin nan zan maka wani gargadi, ka fita daga harkar matata idan kana son kanka da rai da lafiya dan akanta babu wanda bazan iya cutarwa ba!”…….

Ya fadin haka ya fita daga motar……

Sameer ya dade a zaune yana mamakin toh waye wannan? Yana chan yana hauka besan yarinyar bata tareda Deen ba…… Koma dai menene shi yasani, tada motarsa yayi ya nufi gida dan yaje ya kara dubota, ya samu yayi dan shirye shiryenshi daze musu subar kasar shida ita……

       Daukarta yayi chak ya juyo ya kalli su Mami da har lokacin basu dawo daidai daga mamakin wannan abun al-ajabin da suka gani, su basu taba sanin aljanu na irin haka ba, sai sukaji sun kara tausayin yarinyar da wani kaunarta da Allah ya daura musu lokaci daya sannan for the first time mami taji zuciyarta ta dan nitsu da tarbiyyar Deen, she never thought ze iya handling abu irin haka koda a mafarki ne ashe ita take underestimating dinsa? Sai yau data gansa yana karatu kamar wani sheikh tasamu nitsuwa, ashe abunda take tinani ba haka bane?… Abu dayane takejin yayi ba daidai ba yanda ya rukunkume yar mutane alhalin ba muharramarsa bace, ta wani barin kuma sai taga idan shi be rike tan ba su bazasu iya ba ai…..

      “Ku sameni a waje mubar gidannan mami, it’s not safe anymore”…..

Suka jiyoshi ya fadi haka, be jira amsarsu ba ya fita da ita dauke a hannunsa…..

This time around a back sit yasata ya shiga ya gyara mata kwanciyarta, fuskarta ya shiga kallo har ya karaso kan lips dinta, be manta da abinda yaji ba a lokacin dayayi tasting dinsu, be manta da taushinsu da laushinsu da yaji ba, shifa har zaki zaki  yaji kamar yana shan sweet, and he felt tempted again, very tempted to explore more, tindaga wannan ranar yake imagining how sucking her tongue will be, shikadai yasan lots and lots of imagination da yake having, and at this very moment he felt like it’s another chance to explore more….. 

Sunkuyowa yayi ya hade fuskarsu karan hancinsu na gogan na juna, lumshe ido yayi placing his lips on hers…..

      “Kana ina ne toh”….

Ya juyo muryar mami a lokacin da yake kokarin digging into action….

 Da sauri ya janye yana kokarin saisaita kansa… 

Rufo kofar yayi da sauri sannan yayi jumping ya koma driver seat, ya lumshe idanunsa yayi yana kwantar da kansa akan steering……

     “Astagfirullah wa atubu ilahi, Ya rahman come to my rescue, wannan ba halina bane I don’t know why I’m losing myself when it comes to her, yanzu yarinyarnan idan tasan na taba kissing dinta aiba karamin hauka zatamin ba, this will be the last attempt Insha Allah”…..

Duk wannan zancen a zuci yake idanunsa a lumshe…

       “Nace ina kake ne?”…

Mami ta sake fada tana kokarin bude motar…

Bude driver seat yayi ya fito yana fadin;

      ” Na’am, gani”

 “Good, tana ina ita?”…

     “Na sata a back seat”….

     “I hope she’s comfortable?”…

   “Yes, I made sure she is”…

   “Yayi kyau! Shiga muje, prison zamu tafi!!”…

   “Prison kuma mami?!”…

  “Where do you expect dama? Dole fa ka karbi position dinka a yau dinnan ko kaki ko kaso, I’m not going back on my words!!!!”…..

~Uniqueb~

Back to top button