MATAR MAKAHO
Chapter 13
Inna Talatu ce tsaye, sai huci take cikin masifa, Wallahi indo in baki fita harkar yaron nan ba, saina saba miki mena fad’a miki akan sa?
Don Allah inna kiyi hakuri, bazan kara ba, tace tana mikewa tsaye.
Uban me kike mika masa a laida?
Inna aikana yayi fa.
Shige nace, tayi maganar tana hankad’a indo cikin gida.
Al’ameen kam da ido ya bisu, watoh a rayuwa koh baka ma mutum kome ba, in kaje waje sai kaga masoyi da makiyi, zaka ga ka burge wani, wani kuma haushi kake basa.
Tsoho kai kad’ai kake zaune ne?gidado daya fitoh gida yace.
Eh gidado, yace yana matsama gidadon ya zauna.
Gobe fa babu zuwa kiwo.
Meyasa?
Akwai shadi ne.
Ina da yamma ne,?muhammad ya tambaya.
Au harma kana da labari kenan?
Eh indoce take sanar dani wai bazata tallah ba.
Eh gaskiya gobe za’ayi wasa da yamma.
Chap sai kuma ya hanaka kiwo?basai muje mu dawo da wuri ba, itama indo taje tallan tah ta dawo da wuri ba.
Gaskiya ne, Amma mudai anan in za’ayi shadi duka yan kauye basa zuwa koh ina a ranan.
Ok kana nufin kaima kafun kayi aure saida aka farfasa maka baya? kamar yanda nake jin Labari, don mu an daina a garin mu.
Eh nima kafun na aure matata, duka akamin Hamsin, yace yana cire rigansa ya nunawa muhammad bayansa.
Zare ido Al’ameen yayi ganin wasu bulalu kwance a bayansa rututu duk da sun warke amma tabon su na nan, yanzun kana ji kana gani gidado aka maka wannan?
Eh yanzun kai yanda kake kaunar sumayya bazaka iyya tsayawa a bulale ka, don ka mallake ta ba?
Zan iyya harma yafi wannan, indai akan tane.
Toh baka gani ba, nima zan iyya jurewa.
Gaskiya ne Allah yabar kauna, Al’ameen yayi maganar yana kallon gidado.
Haka rayuwa yake tafiya, A hankali A hankali har muhammad ya saba da rugar su gidado, yanzun ya waye a kiwo, wata rana har raba shanu suke da gidado, kowa ya kama hanyar sa, tsakanin sa da yan gidan akwai mutun tawa da ganin darajan juna, duk yanda inna ke nuna masa kyama da masifa, bai taba koh d’aga ido ya kalle taba saboda darajan gidado da bappa.
Jikinsa Alhamdulilah shi karan kansa yaji sanji a jikin sa, ba kamar da ba, haka tsakanin sa da indo akwai mutunci, duk da ba shiga tsafgarta yake ba, amma makale masa data ke, yasa yakan d’an rage mata wani abin.
A sannu sannu gashi yanzun Muhammad na neman wata biyu, a ruga kuma yana cigaba da maganin sa.
**********************
Sumayya ma tana nan da halinta nacin masara, sosai ta maida masara da kunun aya abinci, duk lokacin da Ammar zaizo dubata duk da ba shiga cikin gidan yake ba , a waje yake tsayuwa, saiya kawo mata masara koh kunu, sosai take ganin darajan sa kamar d’an uwan ta na jini, tunanin muhammad kam har gobe bata daina ba, saidai ta rage, Ashe haka b’atan d’a da miji yake? har gwara mutuwa wannan ka gama tabbatar wa kanka ya tafi kenan.
Yau asabar babu makaranta, khadija ce ke wanke kayan ta a kofar sumayya, yayinda sumayya ke zaune a gefe tana latsa system nata, hannun ta rike da masara
Assalamu Alaikum,wani yarone yayi sallama a bakin shashen su sumayya.
Wa’alaikumu salam ta Amsa masa tana mikewa zaune, shigowa yayi da kwano a hannun sa ya mikawa sumayya, wai inji goggo Amina.
Amsa sumayya tayi tace, yacewa goggo ta gode, budewa tayi gwaten shuwaka ne, yaji kyad’a da tsaki sosai, yawunta ya tsinke da sauri tamike ta d’auko shukali, ta faraci, “khadija ga gwate”
Ah ah aunty kici nagode
Kala sumayya batace ba, cigaba tayi dacin abinta, harta cinye tass, sai kuma taji bata son shan kunu aya sam, ruwa tasha sai kuma taji yawo ya cika mata baki.
Haka sumayya ta wuni tana zubar da yawo, gashi ba yawo kad’an ba, karshe dai kunun nan rabawa yara tayi.
Tun daga Ranan sumayya ta maida gwaten shuwaka da macikan zogale, sune abincin ta sai goruba haka ta maidasu abinci, masara duk sun zama tsohon yayi, haka Ammar ma ya maida ganye abin kawowar sa, sam baya gajiya da hidimar sumayya.
Yau wata biyu kenan da batar Al’ameen, haka kawai taji a daren tana son cin tsire mai yajin bakuru, da cabbage, haka tasa khadija a gaba suka fita wajen mai nama tsallake sukaje suka saya, sunzo zasu tsallake titi kawai sukaga wani MAKAHO da d’an jagoran sa, zasu tsallake titi alamu dai dare ne ya musu wajen bara.
Sosai sumayya tabisu da kallo hawaye na cika mata ido”ina suka kaimin mijina”?
Don Allah aunty kiyi hakuri, kinga mun samu kin samu lafiya karki sake jajibo ma kanki ciwo don Allah.
Shuru sumayya tayi suka tsallake titi, suna zuwa gida bayan sunci namar ta kwanta akan gado , khadija na kujera,Har khadija tayi bacci itakam ta kasa, , haka ta raba dare idanun ta biyu tunanin Rayuwar da mijinta ya shigane ya dameta.
Da asuba da mugun ciwon kai ta tashi da zazzabi, khadija taso suje asibiti Amma haka ta ki zuwa, kafun azahar sosai cikin yayi tsamari
Cikin ikon Allah Saiga Ammar yazo, shiya kaisu asibiti, bayan sunga likita ya mata tambayoyi, yace nurse ta bata roba tayi fitsari akai lab.
Tunda sumayya taji haka, sam bata damu ba don ita ta d’auka koh ahone ire iren da aka mata, lokacin da hawan jini ya kwantar da ita.
Bayan wasu hours, nurse ce ta dawo da result a hannun ta, mikawa likita tayi ta juya ta fita.
a hankali likitar ya kalli Ammar ya kalli sumayya, harga Allah ya d’auka ma’aurata ne, Congratulation Aboki na matar ka na d’auke da cikin wata biyu da sati d’aya.
Ammar kallon sumayya yayi, daidai lokacin itama ta kallesa sai kuma suka sake kallon likita har suna had’a baki, “ciki”??
Eh ciki wani abune, ya tambaya da mamaki ganinsu haka.
Ah ah ba kome likita, Ammar yace yana kallon sumayya data d’aura hannu akan cikin ta, tanna hawaye na farin cikine?koh name oho baigane ba.
Am bayan wannan akwai wani abin, ya kamata aboki kana kwantar mata da hankali a matsayin ta na iyalinka, ya kamata ka bata kulawa yanda ya kamata, yanzun juna biyu gareta Amma yanda take saka tunani a ranta, zaku iyya rasa baby ku, ciwon kannan nata tunani ne ya jaza mata, bp nata yahau, kuma bama son haka, a halinda take ciki yanzun nan.
Insha Allah doctor za’a kiyaye, Ammar ya Amsa kawai, yana karban takardar magani da likita ya rubuta musu.
Fita sukayi xuwa pharmacy, magani ya saya mata suka shiga mota, har lokacin hawaye sumayya take abin gwanin tausayi.
Kinga sumayya yanzun fa Dr yaja miki kunne akan damuwar da kike sakawa kanki, waike wace irin mutunce? kukar ne zai dawo dashi kome?
” na daina”kawai tace tana share hawayen ta.
Me zan sai miki?
Girgiza masa kai kawai tayi, Alamu batason kome.
Tsayawa yayi a bakin asibiti yasai mata Alale, ya dawo motar ya mika mata
Ba musu sumayya ta karba, ta rasa me yasa duk Abinda Ammar ya bata sai taji tanason ci.
a haka Rayuwa yake ta tafiya yau farin ciki gobe akatsensa yanzun cikin sumayya nada wata uku cip, bata laulayi haka cikin yazo mata, kamar babyn yasan babu Dad a kusa, saici yanzun kam kome ta samu ci take kamar me, koh zabe batayi.
Babu abinda ta nema ta rasa, Ammar na mata goma sha, shagari shike cefenen gidan ogansa, da duk abinda zata bukata shike bayar da kudi,asai mata, maganar lalle ma yanzun batayi sai make-up kawai shima Amare take ma, duk maiso tazo gida, a hakan take ta tara yan kud’aden ta, yanzun sunyi yawa a Account in khadija.
Yau dai tunda ta tashi da safe takejin wani irin nishad’i wanda batasan dalili ba, tana tashi da safe dayake yanzun sam batason saka riga,don rigunan sun mata kad’an, sosai nonuwan ta suka cicciko, have vest da zani ta maida su kayan sawan ta, ko mai bata shafawa saboda wari yake mata, haka turare ma koh wani iri bata Amfani dasu.
Zaune take a taburma ita kad’ai ta mimike kafa, don khadija ta tafi kasuwa, babu school yanzun suna hutun first time, kosai ne a gaban ta da kunun kyad’a tanaci, sosai sumayya tayi jiki tayi kiba, wuyanta har guru guru yayi, hips natan nan sun kara buduwa haka ma breast nata, daman akwaisu bare yanzun da dalili.
Sallama akayi a tsakar gidan, na muryoyin mutane abin ya bata mamaki jin kamar muryar sani, bata gama shan mamaki ba saida taji suna gaisawa da y’an gidan Adara dake tsakar gida, suna tambayar su kofar sumayya.
Mikewa tayi tsaye koh d’an kwali babu tsaban mamaki daga ita sai zani a kwankwaso da have vest, jin sun nufo kofar ta, kamar a mafarki Amma dai bara ta tsaya taga ikon Allah, bude kofar shashin ta akayi, da sallama
Suman wucen gadi tayi, wallahi ita harta manta da wasu shugaba family, sai sa’i da lokaci take tunasu, cigaba tayi da tsayuwa tanabin wa’inda suka shigo da kallo.
Dada ce a gaba sai matan uncles nata da yaransu harta surkunayen su momy ce kawai babu, ko wance cikin shiga ta Alfarma kana ganin su kaga inda naira ta samu matsunguni, murmushin yakene koh wance a fuskar ta, da kunya suma tsayen suke suna bin sumayya da kallo, kamar yanda itama ke binsu da kallo.
Mamakine ya kamasu ganin yanda sumayya ta koma, sam bazaka taba cewa auren talaka take ba, sumayyar suce ta zama buhu haka?
Takwarata bazaki bawa tsohowa wajen zama bane?gidan ki guda fa nazo, dada tace tana kara bin sumayya da kallon mamaki yar jikanta gabaki d’aya ta canja.
“Ga taburma bismillan ku”tace tana shiga d’aki hijab ta saka ta d’auko babban dardumar ta, ta kara shimfid’awa a gefe, ganin taburmar bazai d’auke suba, dardumar ma bai gama d’aukar suba wasu a bakin dakali suka zazzauna.
Zama sumayya tayi akan kujera tsugunu bayan ta d’auko sa a kitchen” ina kwanan ku”?
Lafiya sumayya, ya maigidan naki?
“Lafiya” kawai sumayya ta amsa kamar irin bata ganesu innan ba.
Yar nan kice kika dawo haka gaskiya aure ya karbeki sosai wallahi, Hajjo matar babuji tace
“Umm ikon Allah kenan ai hajiya, sai ya baka abinda wasu basu so ba”amsar da sumayya ta bata kenan tana cigaba dacin kosanta kamar irin taga sabbin fuskar nan.
Jikin dada yayi sanyi, ganin halin koh in kula da sumayya ta nuna musu, da ace dane koh makaranta sumayya ta dawo inta ganta saita mata oyoyo ta rungume ta, suna wasa da tsokanar juna irin na jika da kaka, amma yau kallon banza sumayya ta mata, kawalli yaufa wuni muka zo miki, gabaki d’ayan mun nan munyi kewar ki yar mu.
“eh dole kuzo mini jaje ai, tunda kunsace mijin hankalin ku ya kwanta, abinda ake so a gani dai insha Allah baza’a gansa ba, koh xaku mutu haka zaku ganni ku barni, don Mu Allah muka rike” tana magana tana shan kunun ta kamar ba ita ke magana va
Miemie ce ta mike, habba sumayya wannan wani irin banzar magana ne, ya zaki bude baki kina fad’awa hajjo da dada irin wannan magana?
“Keee mimi, ban kasa dake ba karki kuskura ki kwasa, dasu nake babu ruwan ki a maganar nan, kona karta miki layin rashin mutunci”
Eyeeee lallai sumayya, yaushe kika koma mara kunya haka?
“Kubra kenan rashin kunya ai dole na koya, koh kin manta gidan da nake ciki ne”?sumayya ta bata Amsa
Habba sumayya wannan ba halinki bane, don Allah kiyi hakuri mu da kika gan munnan bamuzo don kara bata miki rai bane, munzo gyara abinda muka bata ne, aunty husna surkuwar uncle Abubukar tace.
“Keee Husna karki kuskura kisa baki a maganar nan, ina ganin mutuncin ki, sannan kina maganar ku gyara abinda kuka bata, wani abin kuka bata da har xaku gyara?aini koh sanin ku banyi ba”
Mamakine ya cikasu sumayya ta zama yar tasha, sun shiga uku, yarinyar da koh zagin yara bata iyya ba yau harda zagen manya haka.
Sumayya dafa iyayen ki maza muka zo gidan nan suna waje.
Kallon mammu sumayya tayi, jin abinda tace”meya kawo ku gida na kuma gayya guda haka”?
Munzo ne akan auren ki da yaron nan MAKAHO, tundadaman baso kike ba mumuka miki dole, sam yanzun bamu lamunce ba takardan ki xai baki baziki zauna da misk……………..
*************
Muhammad dai yau shida indo , zasu cikin camaroon tallan nono, ta uzzura masa yau saiya rakata, dayake shima yana son zuwa cikin birni yasa sa binta, yau gidado ne kawai yaje kiwo, bappa da matar gidado wance cikin ta ya tsofa haihuwa yau koh gobe.
Cikin Cameroon suka shiga, indo na tallan nono shikam sai kallon gari yake abinsa, basu dawo da wuri ba sai yamma lilis suka dawo.
Bappa ne xaune a bakin masallaci yayi tagumi, su Al’ameen suka same sa, gaidashi sukayi suka wuce cikin gida.
Da dare bayan isha’i Bappane da iyalansa zaune a tsakar gida harda Muhammad, hira ake sosai, tunda muhammad yazo gidan baitaba ganin sun zauna haka ana hira ba, harda inna da matar gidado lantana,
Bappa bakajin dadi ne?
Gidado lafiya ta klau, bansan meke faruwa ba tunda na tashi yau nakejin babu dadi a jikina.
Toh Allah ya kyauta bappa, inna tace tana kallon sa don tun safe itama ta lura akwai abinda ke damun sa.
Ameen Talatu.
Amma bappa wani irin abune yake damunka haka?
Gidado mubar zancen nan kawai bashi da Amfani.
Kamo wani tadin akayi, sai hira ake muhammad nad’an saka baki kad’an kad’an in aka sakosa a zancen.
Sosai yau gidan bappa aka sha hira sai chan dare, muhammad ya musu sallama, kwanciya yayi bayan yayi Alwala yayi addu’ar bacci, haka kawai yake jin kirjinsa na bugawa, kwanciya yayi, yayi likimo a gado,har bacci ya d’auke sa.
Ta bangaren su bappa, sallama sukayi da juna bayan wucewar muhammad don shiya fara tashi, kowa yaje ya kwanta, Amma dai jikin su a sanyaye, yau dai indo taki kwana ita kadai a dakin ta, tace da innar ta zata kwana, dole tasa inna komawa d’akin indo tabar bappa a dakin sa.
Da misalin karfe 1:14am agogon cameroon, Al’ameeen ya farka da salati jin ihu tako ta ina da salati, gari ya kaceme da hayaniya, karan yara da matane kota ina, ga ruwan bindigogi dake tashi, da sauri ya dirka daga kan gadon jin inna na salati da karfi tana wuta wuta jama’a cikin yaren fulatanci
Fita yayi a d’akin da gudu yayi waje, jikinsa rawa ya soma ganin An cinnawa gidan bappa wuta, ga sauran gidaje duk wuta ke tashi da karan mutane da guje guje.
Gidado ne ya fitoh d’aki rike da matar sa, da tashin hankali yasa ta nakuda, ya kalli bappa dake xaune shuru, babu alamun tashin hankali a fuskar sa hakama babu alamun kwanciyar hankali.
Inna ce ta mike da sauri ta isa garesa, hannun lantana ta kama wance ke kokarin faduwa,gaskiya haihuwace gadan gadan fa bappan gidado musan abinyi.
Hanyar wajen gidado ya nufa hannunsa d’auke da wuka sharbebiya.
Kai gidado ina zaka?koh bakajin abinda ke gudana a waje ne?muhammad yace cikin tsananin tashin hankali.
Kaga ku zauna a ciki bara na fita, mu munfi karfin ana kashemu, muna buya sai dai a fito a gwabza, yana magana yana kokarin barin gidan.
Kaiiii gidado, fitar da zakayi ba shine mafita ba, kanada tabbacin inka fita zaka dawo ka samemu a raye?wuta fa aka kunna wa gidan nan, mafita zamu nemawa kan mu, na fita a garin gabaki d’aya.
Allah ya sauwaka, mugudu mubar mahaifan mu, da Arzikin mu.
Gidado kabi abinda yaron nan ya fad’a, don yafika gaskiya nakuda matar ka take, kamata yayi ka fitar da ita, ga indo can sumar ta biyu,inna tace tana nuna indo dake zaune a gefe kamar ruwa ya cita.
Shuru gidado yayi ya tsaya sosai jikinsa ke rawa , kowa yasan yanda ran fulani yake baci in an tabo musu dukiya ba sauki, gaskiya inna saidai kuzo kutafi da ita kaima muhammad ka bisu, mukam zamu kare shanukan mu, yayi maganar yana tsinka zanar bayan gidansu wanda wuta bai iso gunba.
Soyayyar da ka iyya jure shadi akanta, da soyayyar tsakanin uwa da d’a, bazaka iyya sadaukar da arzkinka ba, gidado ku rayu tare?
Mikewa inne tayi, gidado ya ciccibi matarsa da tiyo ya fashe ruwa yana zuba, da gudu indo ta rike hannun inna, muhammad ma binsu yayi a baya, har sun shiga bandaki kafun suka tuna da bappa yana bayansu, juyawa dukansu sukayi suna kallon sa har lokacin bai motsa ba.
Inna ce ta dubesa, Bappan gidado yakana zaune kazo mu tafi baka ga halin da yarinyar nan take ciki bane?
Kuje kawai Allah ya tsare hanya, ni bazan iyya gudu a rugan mu ba.
Habba bappa yanzun kafison ka zauna azo a kashe ka, hakan bai dace ba koh a addinan ce, kana da damar kare kanka, ka bari a kashika, muhammad ya karasa maganar yana karasowa kusa da bappa.
Don Allah bappa y’an dillo, indo tace tana kuka.
Girgiza kai bappa yayi, kuyi hakuri bazan iyya zuwa ba.
Muhammad ne ya dube gidado, kaga gidado ku tafi da inna, lantana da indo , ka fara fitar dasu, muna zuwa da bappa.
Sanin taurin kai da kafiya irin na bappa, yasa gidado da inna suka fita ta zanan bayan gida, harda lantana data gama galabaita da indo.
Zama muhammad yayi kusa da bappa sosai zuciyar sa ta tsinke, ganin yanda wuta yaci rabin gidan yanzun ma wani irin turiri da rad’adi yakeji a jikinsa ga hayaki, bappa don Allah badon niba kazo mu tafi a rugan nan, rayuwar ka tana da matukar Amfani wa Ahlinka, kasan wani irin hali zasu shiga in aka waye gari baka?akan iyya rasa dukiya, wata rana su dawo, Amma ba’a taba rasa uba wani ya maye gurbinsa har Abada, kama iyalinka adalci ka rayu dasu koh ba kome zasu walwala koh ba shanukai, akansu rayu bakai ba dukiya.
Kuka bappa ya fashe dashi, babana bazaka gane bane yanda abin yake, akwai zafi azo a same ka har gidan ka a kwace maka dukiya, a kwace maka muhammali, asaka gudu kamar barawo ina sukeso muje, irin wa’innan mutane, sune sukayi sanadin iyaye na, shekara talatin baya, mu kullun cikin zulumi muke bamuda sakat?
Kayi hakuri bappa, rayuwa tafi kome muhimmanci ita d’ayace, kayi hakuri mu fita anan, yana maganar yana kama hannun bappa ganin jikinsa yayi sanyi, kamasa yayi suka nufi bayan gidan, suka fita ta zanan gidan.
Da ido bappa yake bin rugansu dashi, ganin gawawwakin fulani cikin jini manya da yara, kota ina hayaki ne.
Tafiya suke kamar wasu barayi a hankali a hankali, suna bin ciyaye kamar a mafarki muhammad yaga yan ta’adan nan sanye da kakin sojoji ga bindigogi manya manya a hannunsu, kafun ma su buya tuni sun gansu, ai da gudu muhammad ya kama hannun bappa suka nausa daji, da gudun tsiya, suma suka rufa musu baya.
Gudu muhammad yake da bappa suma suna binsu a baya, bappa ne yayi tuntube ya fadi tim, da sauri muhammad ya dakata kokarin tayar da bappa yake, Amma bappa ya kasa saboda ya buga kafarsa mai ciwo a dutse, ka tafi kawai yaron nan ni inaji lokacina yayi, Allah yamaka Albarka ya sadaka da ahlinka lafiya, sai wata rana.bappa yace.
A karon farko muhammad ya sake kuka mai karfi, harga Allah a d’an zamansu da bappa jinsa yake kamar mahaifinsa, don Allah bappa karkace haka, bara na d’agaka, ciccibar bappa yayi, yana gudu kamar kiftawar walkiya yajisa a kasa dagashi har bappa, mummunan buguwa sukayi muhammad saida tsakiyar giransa ya tsage, saiga jini bappa ma gwuwarsa ta kwarzane sosai.
Kafun ma ya mike tuni yan ta’adan nan sun kewaye su, d’aya daga cikin sune ya taka kafar muhammad saida yaci ta baki, jini ya balle masa, bindiga d’ayan yasa ya buga a kan bappa, kara bappa ya sake yana dukawa hade da rike kansa da karfi yana salati, jin wani irin azaba mai tarin yawa na bazata.
Don Allah kuyi hakuri, karku cutar dashi don Allah, muhammad yana magana yana kuka.
Kai ragon maza kaika san Allah ne?wani a cikinsu yace.
Kuyi hakuri…
Bamuda imani bare hakuri.
Bappa dake duke har lokacin jikinsa sai rawa yake tsabar azaba, kamasa d’ayan yayi ya kwantar kaman rago yasa masa wuka a wuya.
Ai muhammad na ganin haka yayi wani irin mikewa da karfi, ya bangaje mutumin da ya takasa, duk wani tsoro ya fitar masa a rai ganin tabbas abu biyune zai faru rayuwa koh mutuwa, rugawa yayi da gudu ya nufi bappa, kafun ma ya iso garesa tuni mutumin ya dirza wukar jini ya fantsama.
Zuciyar muhammad ta riga ta kikashe yanzun, yaga mutuwar mahaifiyarsa, kaninsa, amma bai taba ganin mutuwar da ta mugu-mugun ratsasa ba irin wannan, sharbeben Adda dake rataye a jikin d’aya daga cikin yan Ta’adan ya zare da karfe, kafun giftawa da bismillah tuni muhammad ya shiga fad’a da mutanen nan, cikin bazata da rashin tsammani,Allah kad’ai yake kira, yakini kawai yasa a ransa koh yakashe koh a kashesa, suna da bindiga shikam wukane kawai, sosai suke..zuba alburusai yana kaucewa, cikin rashin sa’a wani yasake bullet, ya kuskure sa a hannun hagunsa, ihu yasa da karfi yayi kan mutumin, wukar hannunsa yasa ya fille masa kai,sosai jikin muhammad yake bari ganin yau da kansa ya kashe mutum shi muhammad, mutum hudu ya kwantar, daman su hudun suka bisu.
Mikewa yayi ya sabe gawan bappa, sai kuma ya rasa ina zai nufa dashi, tunda fa ya fitoh baiga su inna ba, wani shawara ne ya fado masa, aje bappa yayi ya sabi bindiga da wuka ya koma cikin rugan su gidado.
Tun daga nesa ya hango fulani da aka tara waje d’aya, cikinsu harda su gidado da wasu kattai suka danne sa, sai lantana dake kwance bata motse, sai jinjira a gefe tana cillara kara cikin jini koh cibi ba’a yanke mata ba, Alamu dai daga haihuwarta ta riski wannan masifa.
Bin jikin ciyayi muhammad yayi ya saita mutanen da suka danne gidado, su biyar gabaki d’aya ya sakar musu bullet one by one, ai take yan ta’adan nan suka fusata suna sake ruwan harsashi ta saitin muhammad, da sauri ya kwanta a kasa.
Wanna daman gidado ya samu da wasu matasan fulani suka d’auke wukake da adda aka fara aran gama.
Inna dake gefe da sauri ta rarrafa zuwa wajen jaririyar, wuka ta karba a hannun wani ta yanke mata cibi, nadeta tayi a d’an kwallinta ta kama hannun indo, tare da wasu matan suka ruga a guje, sukayi daji kowa yayi takai takai, aka bar gawan lantana a wajen, don ta rai ake.
Muhammad yau an zama zaratan maza sosai ake gomxa fad’a, duk wani tsoro nasa yau ya kau, yakini d’aya a ransa zaiyi rai koh ah ah, ganin yanda wasu dakarun barayin nan suka fara shigowa rugan, suna karuwa har sun fara ninkesu, gashi mata da yara da suka rage a raye sun dade da gudu, yasa muhammad d’aga murya da karfi, kowa yayi ta kansa karuwa suke aje-aje zasufi karfin mu.
Ai yana maganar nan da gudu ya kama hannun gidado da wani saurayi zaiyi sa’an sa suka nausa daji da gudu, haka ma sauran mazan ana harbinsu suna gudu wasu na faduwa matantu, barayin suka mara musu baya, yayinda su kuma suka raba kawunan su, kashi-kashi.
Muhammad gudu suke a daji koh gabansu basa gani, gudune irin na bakin Rai bakin fama, nausawa daji suke yan ta’andan nan na binsu, a hakan suka ringa gudu, (wani abu sai tashin Hankali kayi abinda koh da kudi aka had’aka bazaka iyya ba, sai kaga masifa)sosai sukayi nisan kiwo, gudu suke mutanen na binsu suna sake bullet, Allah ya tsare su, har suka isa wani baban ruwa fad’awa sukayi ciki, yaufa muhammad da kansa ya tsallake ruwa, suna tsallaka kogin har lokacin mutanen na binsu, sosai suka kara azama basu jima da gudu bayan tsallake kogi na biyu, suka hango wani kauyen, ganin Hakan ne yasa mutanen juyawa suka barsu.
Faduwa muhammad yayi dasu gidado a kasa, ganin sun shigo cikin mutane, A raye basu mutu ba, karasawa sukayi cikin gari.
Sun ma rasa ta ina zasu fara, fahimtar da sukayi garin kamar babu alamun musulunci, ganin yanda mutanen garin suke, buya Al’ameen sukayi basu bari hankalin yan kauyen ya dawo kansu ba, a hankali suke bin cikin gonaki har suka tsallake kauyen lokacin dare yayi sosai, don akiyasce zaikai 10:00 na dare, gindin wata bishiya suka samu suka zauna, kowa na maida numfashi koh bacci basuji yau, muhammad kam jingina yayi da jikin bishiyar ya lumshe idanunsa yana tunanin rayuwa, tunda ya tashi yake ganin jarabawa iri iri, Amma baitaba zata zaiga irin nayau ba, ace tun 2 na dare yana cikin tashin hankali har dare war haka, ada yayi tunanin zuwan sumayya da farin cikin da ya samu, baitaba tunanin akwai sauran wani damuwa ba, ya zauna da sumayya da zuciya d’aya, duk da an sanar dashi ita ba mutuniyar arziki bace, auren jingina za’a basa, hakan yaji A Ransa zai iyya zama da ita cikin aminci, baitaba sawa ransa, don sumayya tayi ciki zai gujeta ba.
A Ranar daya samu tabbacin farin cikin sa, sumayyar sa budurwa ce, yaji dukkan wani damuwa kunci ya yaye, a lokacin rayuwa yake tuna musu mai dadi nan gaba,don ya tabbatar auren sa da sumayya akwai dalili, bai d’auka zaiga irin masifar yau ba, shine yayi kisa?kisan ma mutum d’aya ba, ba biyu ba, atake yaji aransa tabbas yanason zama SOJA don ya bawa kasarsa gudumawa, da maganin ire iren mutanen nan, indai da rai da lafiya koh kurtune inya koma gida zai nema, tunda ba ilimi mai zurfine dashi ba, insha Allah sumayyar sa sai tabar Amsa sunan MATAR MAKAHO zuwa MATAR SOJA……..
*******************
Bazaki cigaba da zama da miskini ba yanzun sumayya, mahaifin kima yace gobe in Allah ya kaimu zaku wuce garin su mahaifiyar ki.
“Kin gama, koh baki gama ba”?
Na gama sumayya.
“Toh bara kiji, ni a haka naga mijina kuma nake son zama dashi a miskinin, banga wanda ya’inda suka isa su rabani dashi ba, wallahi sai mutuwa karyar mutum”
Sumayya Rashin kunyar da kika koya harya kai haka, bansani ba shige toh muje, su Abie na waje saikije ki kare musu tanadi bamu ba, aikoh me muka miki bamu shanshanci wannan iskancin ba.
“Inje ina? mijina bayanan kuma baibani izinin fita waje inga kowa ba” sumayya tayi maganar tana tura kosanta a baki bibbiyu ma, take turawa irin na huce haushin nan.
Innalilahi wa’inna’ilaihi raji’un na shiga uku ni sumayya,na lalace da’aka had’a baki dani aka aurar wa yan iskan Adarawan nan, yarinyar yarona ni sumayya na bonu, wi.. wi. wi dada ke kuka tana maganar nan gwanin tausayi
Mimi ce ta mike tayi waje, wajen su Abie dake zaune a cikin manyan mototi a waje na Alfarma, gabaki daya yan unguwan sun maida hankalinsu kan mototin, atunanin su koh wani masifar yan gidan suka jajibo.
Miemie na isa kuka ta fashe dashe a bakin motar da abie ke ciki.
Da sauri dukansu suka fitoh a motar , magidanta ne sun d’an manyanta, su biyar harda abie sai samari hudu da masu aure biyu, abie da sauri ya fara tambayar mimi abinda yake faruwa, ina sumayyar?gabaki d’aya inka gansa sai ya baka tausayi.
Tas mimi ta zayyana musu kwandon masifar da sumayya ta juye musu, kuma tace bazata fitoh ba mijinta bainan.
Ita sumayyar ce ta fad’a miki haka?babuji yace yana rike baki.
Eh babuji….
Ke kije cikin gidan kice ana sallama damai gidan, babuji yace wa mimi.
Juyawa tayi ta shiga gidan, daidai lokacin Ammar ma yayi packing in motarsa, suka fitoh shida khadija a ciki, rage mata hanya yayi a bakin kasuwa.
Karasowa yayi da sauri kusa da dasu, cikin sallama ganin su mutane ne ba raini, gaisawa sukayi, khadija ma ta gaidasu, tana mamakin meya kawos, don bata mantasu ba, sune iyayen sumayya, cikin gida ta shiga ta barsu a waje harda Ammar.
Bayan d’aya daga cikin mazajen gidan adara ya fitoh, gaisawa sukayi dasu babuji, sannan suka nemi izinin shiga cikin gidan zasuyi magana da yarsu in ba damuwa.
da mamaki mijin inno ke kallon su izini shi ai harma ya manta ana neman izini, kafun a shiga gidan wasu, suda gidansu ina yaga izinin shiga, amma dai ya maze yace su shigo.
Ammar fa zare ido yake, wai meke faruwa ne haka, yasa sa binsu a baya suka shiga ciki.
Sumayya na tsaka da cimar ta, taga shigowar Familin su maza, kwarjinin da suka mata yasata mikewa tsaye, haka kawai taji gwuwarta yayi sanyi, had’a ido da tayi da abienta dake binta da kallo, baitaba tsammanin xaiganta haka ba, daren jiya koh bacci baiyi ba, yana zullumin halinda xaizo ya risketa yau.
Sannu sumayya tunda baxaki fita ba, mu munshigo munsame ki, uncle gaddafi yace.
Tsunkuyar da kai, kawai sumayya tayi batace kala ba.
Shige mu tafi, in mijin naki ya dawo saiya zo muna da magana dashi, wannan auren bamu yarda dashi ba, daman kudi muka biya sulaiman akan auren.
“Kamar ya uncle bangane baku yarda da auren ba? Kuma ba wanda ya baiwa muhammad kudi, asalima cemai akai ciki ne dani”
Eh Momcy gida zamu koma gaskiya bazaki cigaba da xama a gidan nan ba,ai daman mu muka sakaki auren sa, yanzun kuma munce bazaki zauna dashi ba, uncle nata d’aya yace.
Hajjo ce ta kalli sumayya, kuma kaf mu innan babu wanda ya miki kazafin zina in karya muke a kira sulaiman in, don mu sulaiman in ma bamu sansa ba jinsa kawai muke a waliyin mijin da muka baki.
“Ai uncle bakin Alkalami ya bushe, a da kunada iko dani Amma banda yanzun, ban shirya xama karamar baxawara ba, ina son mijina.
Sumayya!! abie ya kirata da dukkan yakininsa, yau koh momcy baice ba sunan Dadansa guda ya Ambata, sumayya yau nayi miki Alkawarin cika miki burinki, zan kaiki kiga mahaifiyarki kiga danginta, zan dawo miki da aikin ki, ki Amince mu koma gida tare.
Kara khadija ta sake da karfi, hade da kuka wayyo na shiga uku don Allah kuyi hakuri, wallahi yayana na sonta babu abinda baya mata, kuma ba mutumin banza bane, don Allah karku rabasu da Aunty, wallahi nima ina son zama da ita.
“Kiyi shuru khadija koda Al’ameen bazai dawo ba, ni bazan taba barin gidan nan ba, koda na bari toh ba gidan shugaba zan koma ba, ku fita ku barmin gida banason ganin ku, nace ku fita”tayi maganar cikin karfi sai kuma ta sulale ta zube a kasa sumemmeya.
After 6 hour’s sumayya ce kwance a gado an d’aura mata ruwa a hannu, sai khadija dake gefen ta a zaune idanu jahur, sai Ammar dake gefe shima a zaune, cikin tashin hankali.
A hankali sumayya takalli ammar ” sun tafi”?
Ah ah sumayya basu tafi ba tunda aka kawoki suke zaune a asibitin nan, yanzun ma sunso shiga likitane ya hana, kamar yanda kikace saboda yanayin bp ki, sumayya duk da bansan meke faruwa ba, nasan tabbas iyayen kine su, kuma iyaye darajane dasu baikama ta ki musu abinda kikayin nan ba, sannan abinda ya tsayamin a wuya, abin mamaki daman ba auren soyayya kukayi da Al’ameen ba? Don nasan sone kawai zaisa ke dashi ku kasance a karkashin inuwa d’aya, duba da duniyar mu ayau mai kudi sai mai kudi miskini sai miskini, talaka sai talaka Amma ke kullun sai na kwana da lamarin ku keda muhammad A raina, a yanda na ganku naga tsantsan kula da juna da soyayya, gaki kyakkyawa ruwan manya, kullun saina tambaye kaina taya kika aure muhammad?Amma Amsa d’aya nake samu soyayyace , don Allah yau ki fad’amin wani abu game dake koh muhammad, koh nima zansamu na kunce kullin dake damuna akanki.
Hmm Ajiyar zuciya sumayya tayi, sannan a hankali ta bude baki”yau zan sanar dakai wacece sumayya Abdusalam Shugaba, ada kafun ta zamo MATAR
Abdul’aziz wanda aka fi sani da shugaba, haifafen mambila plateau(Gembu) ne, Ainahin su fulanin gembu ne, acan aka haifi Abdul’aziz,duk da yana kauye hakan bai hana shugaba karatu ba, yayi karatun sa na secondary kafun yayi aure, matar sa ta farko fatima wance ake kira da fa’i, ita ma yar gembu ce, auren dangi aka musu, kafun daga baya ya aure sumayya (Dada), a kauyen su yake rayuwar sa da matan sa biyu,da yaransa maza biyar, yaran fa’i uku, Abdul’aziz mai sunan babansa(babuji)sai Abubakar da gaddafi,sumayya(dada)nada maza biyu itama, Usmanu sai Abdulsalam(Abie)shine autar gidan su, akwai kyakkyawar fahimta da zaman lafiya agidan, shugaba(Abdul’aziz)hakan ya samu asaline daga zaman lafiyar da matan keyi, zamane na kwatance a kauyen su, kaf kauyen babu gidan da zaka shiga kayi mamakin zaman kishiyoyi iri na gidan shugaba, sosai abin ke bawa wasu mazan sha’awa, don shugaba adaline a gidan sa, duk da auren soyayya sukayi da sumayya hakan baisa ya nunawa fa’i banbanci ba.
bayan wasu shekaru an samu fad’an kabilanci a gembu sosai,tsakanin mambilawa da fulani wanda yazamo sanadin mutuwar fatima uwargidan shugaba, da mahaifiyar shugaba, daman mahaifinsa ya jima da rasuwa, wasu da dama a yan uwansa sun rasa ransu, a rikicin da ya afku.
Bayan kome ya daidaita, shugaba ya saida duk wani kadara nasa na kauye wanda mahaifinsa ya mutu ya bar masa, don shikad’ai babansa ya haifa namiji sauran matane kuma duk sunyi aure, ya dandanka musu nasu gadon.
Jalingo babban birnin jahar Taraba, ya tattara iyalansa suka dawo jalingo, gida madaidaici shugaba ya saya, yasa yaransa a makaranta, dada tana kula dasu kamar y’ay’anta na cikin ta, sam bata nuna musu banbanci da nata duk d’aya ta d’auke su, wannan abin shiya kara dasa soyayyar ta, a zuciyar mijinta.
Bayan wasu shekaru kudi sosai ya fara zama a Aljuhun shugaba, don business yake na manya manyan shaguna zanunuwa a kasuwa yana order daga kano, aje aje yakoma na mototi, Arziki kullum gaba gaba yake ga yaransa na makaranta, duk wanda ya gama secondary, kwasar waje yake turasa karatu.
Lokacin da yaransa suka fara nisa a boko , hakan yasa ya sakar musu wasu kud’ad’e su gwada tasu kasuwar, babuji da Abubakar sune suka fara kammala karatu, suka fad’a business abinka da yan boko, kuma kwararu a bangaren business, kankace kome kudine ya zauna company suka kafa mai zaman kansa, tare da haden gwuwar junan su, sosai arzikin su ya fantsama.
Babuji da Abubakar a rana d’aya sukayi aure , wasu yaran jalingo suka aura wa’inda suka hadu a makaranta, bayan auren su, saida suka haifi yara bibbiyu, kafun gaddafi da Usman sukayi aure.
Abdulsalam ya kammala karatunsa Amma sam yaki aure kaman yan uwansa, duk yanda iyayen sa sukaso yayi sai abin yaki, dada har magani take saka masa a abinci koh Aljanane ta aura mata yaro, Amma ina shuru abu yaki kowa aka nuna masa yace baya so, bata masa ba hardai su gaddafi suma suka hayayyafa sosai , a lokacin yaran babuji biyar, na Abubakar uku, yaran gaddafi biyu, na usman hudu.
Bayan wasu yan shekaru shugaba ya kwanta ciwo, baiyi wani dogon jinya ba Allah ya karbi rayuwansa, gadon da aka raba musu shi suka had’a suka gina katafaren gida a unguwan specialist, gabaki d’ayan su suka tattaro kan iyalansu suka dawo cikin gidan da zama, don a lokacin Babuji da Abubakar suna da company kansu har biyu, yayinda gaddafi yake aikin goverment, usmanu d’an siyasa ne, Auta Abdulsalam shi ma’aikacin Bank ne(Accounter)kasance warsu rikankun yan boko ga naira ga kyau, kowa yasan yanda fulanin gembu keda tsananin kyau.
Rayuwa ake a cikin shugaba family house mai kyau, daban sha’awa, mazan basu bawa matansu daman da zasu kawo musu tashin hankali ba sam, koh kara kika kaiwa mijinki matar wansa ta miki kaxa, had’a meeting ake a kira kowa, ku maida maganar hakan yasa matan sam suka daina fad’awa mazajen su, saidai ayi iyya mata da mata kasa kasa.
Auren Abdulsalam ne yaxo musu da sabon salo, saboda yarinyar da ya kawo akan ita zai aura, yar maiduguri ne Amma tana karatu a TSU, tazo bank inda yake aiki cire kudi, Allah ya had’asu kanuri ce, hakan yasa dada tace ita sam bata yarda da auren nan ba, bazasu aure babarbariya ba, abinda ya xamo cecekuce a gidan kenan, duk yanda Abdulsalam yaso fahimtar da ita son da yake ma yarinyar, abu yaci tura sam taki Amince wa katafau tace bata yarda ba, shikuma Abdilsalam yace muddin ya rabu da Hafsa toh shikam bazaiyi aure ba.
Aijin haka yad’agawa dada hankali don tasan sarai halin Abdulsalam, akwai kafiya kamar me, tayaya ma aka samu ya samo hafsar kullum yace yakusa aure shuru baiyi ba, bare yanzu yace bazaiyi ba ai magana ta lalace.
Babu yanda ta iyya da banbakin su babuji ta Amince da auren hafsa, har maiduguri akaje da zancen auren.
su karan kansu iyayen ta sunso gardama amma ganin sannanen family ne, yasasu karbansu da hannu bibbiyu, tare da kafa sharadin yarsu zata cigaba da karatu insun amince, zasu basu ita?
Amincewa kam sunyi saboda kaf gidan shugaba yan boko ne, hatta matan gidan na zuwa aiki, rainon yara ma dada keyi da masu aiki.
BAYAN AURE
Hafsa fa ta fara fuskan tan banbancin launi a gidan su Abdulsalam, kasancewar ta baka kuma kanuri, sabanin yan gidan shugaba farare ne, daga matansu har maza da yara gasu fulani kyawawa, don Abdulsalam baza’ace kyaune ya rud’asa akan hafsa ba, ah ah sonta ne kawai Allah ya diga masa a zuciyar sa yaji baya ganin kyaun kowace mace sai nata, sosai ake nuna mata banbanci kuma ba wanda ya fara asasa hakan sai dada, haka zasu zauna suna hira daga sun ganta zasu koma yi da yare basa janta a jiki, inta matso garesu basa sonta rabesu sam, kansu a hade Amma ita sun ware ta.
Hakan dasuke, yama hafsa zafi, yasata watsar da kowa na gidan, ta kama karatunta daga ta dawo makaranta ta shiga kitchen tayi girkinta, zata haura upstair’s, ta shiga d’aki bata fita sai mijinta ya dawo.
Abdulsalam yasha had’a meeting da korafi akan abinda akema matar sa, duk da bata fad’a masa ba, yaga alama yayunsa mazane kad’ai ke sonta.
A haka fa abu yaki chanjawa abubuwa sai cigaba suke a haka, hafsa zaman hakuri take a gidan, babu zagi babu duka, Amma ana nuna mata mugun hali kam, a hakan cikin hukuncin Allah ta samu ciki, wanda kaf gidan babu mai farin ciki sai ita da mijin ta da yan uwan mijinta, amma babu ruwan matan dasu dada da ita, gashe cikin yazo mata da laulayi, bata iyya aikin kome, kuma babu mai taimakon ta, karshe dai Abdulsalam d’aukar hutu yayi a bank ya zauna a gida yana kula da matar sa, amma abu yaki karshe dai kiran iyayen ta yayi aka turo masa kanwar hafsa, tazo ta zauna da ita har cikin ya tsufa bata koma ba.
Wata ranan Alhamis hafsa ta tashi da nakuda tsakar dare, Abdulsalam da kanwar hafsa ne, suka kaita asibiti don baiko sanar da yan gidan tana nakuda ba, hospital aka kaita kafun asuba Ta santalo yarta kyakkaywa fara tas, jinin gembu mai tsananin kama da zuriyar gidansu, koh kama da hafsa batayi kome na babanta ne.
Sosai Abdul yayi farin cikin samun wannan baby, ga wani irin sonta daya ke sosai yaji son babyn sa, washe gari ne yan gidan suka tashi sukejin labarin haihuwar a bakin mazajen su, Dada da matan sunje asibiti bada son ransu ba, saidai ganin yanda Abdulsalam yahad’a wa kowa fuska, gaisuwa ma dada kawai ya gaishar, ya shiga yad’auko kayan baby ya fita, hakan yasan su zuwa duba baby.
Ba karamin dadi sukaji ba ganin yarinya kamar su ta biyo, bama kamar dada a murna, zama tayi a asibitin taki tafiya ita kema yarinya wanka, duk da yar uwar hafsa tazo washe gari Amma dada ta karbi kome na baby, harsuka koma gida dada fa na leke da yarinya, ranan suna yarinya taci sunan dada sumayya ana kiranta da momcy, haihuwar sumayya shine musababin zaman lafiyar hafsa, sosai taga change agun dada haka ma matan gidan, sosai suka koma damawa da ita, itama bata rikesu a rai ba, a sannu sannu har itama ta fara jin fulatanci duk ta maida martani na bata wuya, amma babu abinda zaka fad’a da fulatanci bata sani ba, dayake gidan sosai suka rike yarensu, suna hausa Amma ba sosai ba.
Sumayya(momcy) tana da shekara hudu Abie inta ya shigar da ita makaranta, lokacin hafsa(ummi)ta kammala karatunta na jami’a ta fannin koyarwa, taso kara gaba Amma abie ya hana, aiki yasama mata na koyarwa a makarantar secondary, wannan kenan.
Sumayya na cika shekara biyar kanin Dada Allah ya masa rasuwa a gembu, dukansu sukaje taziya, bayan sadakan bakwai dada ta d’auko yarsa daya haifa guda d’aya, mai suna safina(momy), bayan dawowar safina family shugaba, sai abubuwa suka fara bullowa saboda tunda safina ta shigo gidan shikenan ta fara likewa Abdulsalam(abie)duk wani iyayinta abie baya kulata, asalima sai ya daina zaman falo kwata kwata koh abinci ne saidai suci da ummi a d’aki, abin har yakai ga dada ta lura da hakan, sosai ta nuna masa bacin ranta akan yana nunawa safina mugun hali don tana zaune a gidansu.
Zama ya fara rashin dadi lokacin da safina ta fitoh karara tace ita abie take so, sam abi yaki zancen kuma ya nuna bazaiyu ba, ummi karan kanta a lokacin ba karamin bakin ciki taji ba, don gwara tayi kishi da kowa akan safina, irin yaran nan ne shegun kauye masu shiga idon mutane, gashi batada kunya sam.
Dada fa ta tuntube abie akan zancen ya nuna bazaiyu ba, hakan yasa dada bata tilasta masa ba ta watsar da xancen, abinda ya konawa safina rai kenan, kaf gidan babu mai supporting nata, kowa ya nuna baya goyon baya akan zancen, harda matan babuji basa sonta.
Safina makaranta aka saka ta na islamiyya, don sam taki zuwa boko duk yanda akayi bazata ba islamiyyar ma daker ta fara zuwa, zuwan ta islamiyya shiya had’ata da kawa nafisat, nafisa irin yaranan ne watsansu marasa jin magana, haduwar su da safina, yasa nafisa nunawa safina abubuwa da yawa, ta kara kangarar mata da kai, bata tsoron uban kowa.
Abin yayi matukar d’agawa dada hankali duk yanda taso rabata da safina abin ya gagara, gashi a lokacin nafisa bazawarace harda y’a d’aya take dashi, hakan yasa dada mawa safina barazanan zata maidata kauye, amma safina koh a jikin ta, ta nunawa dada koh ta maidata kauye tasan hanya, duniya da fad’i.
Bayan wata uku da haduwar safina da nafisa, lokacin sumayya nada shekara 6 a duniya, hafsa ta fara ganin change a zaman su, sam yanzun zaman ba dadi tsakanin ta da mijinta, kullum cikin rikici suke wanda itama karan kanta batasan dalili ba, sosai abin ke damunta, wasu lokacin har Abdulsalam na dukanta, Amma bata taba fad’awa iyayen ta ba, koh wani nata saboda tanason mijinta, sai kawarta wance suke karantar wa a makaranta d’aya, don lokacin kanwar ta da aka kawo mata lokacin cikin sumayya tayi aure, batada wani nata kusa.
Yau an waye gari da wani masifa a gidan shugaba, amma dada satan sarkan gwal inta, sosai tayita masifa tana zagin yan aikin gidan wance ke mata gyaran d’aki kamma koranta akayi, koh sati ba’a kara ba aka sake ma hajjo(matar babuji) sata, ba’a kama barawon ba, haka aka ringa sace sace kusan wata har rashin yarda ya shiga tsakanin juna, kowa na zargin d’an uwansa, ba yan aiki kad’ai ba.
Kamar yau aka sacewa Matar abubakar agogonta na demond, yau kam masifa aka sake akan sai anbi d’aki d’aki anyi bincike, sai an fitar da barawon don kaf gidan tunda safe babu bakon daya shigo koh ya fita, kuma kowa na gida ranan don weekend ne.
Bincike aka ringayi har akazo d’akin hafsa, kamar a mafarki aka ga agogo da wasu sarkoki na dada a cikin wardrop na ummi abinda ya kawo cece kuce dacin mutuncin hafsa a gidan.
Daman mai hakuri bai iyya fushi ba don ita da iyya gaskiyar ta, bata d’auki kome ba yama za’ace a iyya tsawon zamansu bata taba sata ba? sai yau sannan ita aitafi karfin sata tunda bayar matsiyata bace ita, sosai ta fara maida martani kowa ya gaya mata bakar magan fad’a masa take ita ma, ana cikin haka abie ya dawo daidai lokacin dada ke zagin hafsa, ita kuma ta gaya mata bakar magana, daman tun asali bata son zaman ta da d’anta, shiyasa ta had’a baki aka lika mata sata.
Abie babu tambayar ba’asi yaja ummi d’aki ya rufe, duk da sumayya yarinya ce, amma a ranan tasan gidan shugaba sunyi ma mahaifiyar ta ba daidai ba, duka abie yama ummi kamar zai kasheta daker aka kwaceta.
Cikin kuka ummi ta kira kawar ta a waya don ta tsorata lokacin, ganin jini nabin kafafunta, bayan zuwan kawarta, asibiti ta kaita ashe karamin cikine da ita wanda likitoti suka tabbatar daya zube, ga rauni kota ina a jikinta, wayar hafsa kawarta ta d’auka ta kira iyayenta, ta fad’a musu duk abinda ke faruwa tun zaman hafsa a gidan, kamar yanda hafsar ta taba fad’a mata.
A ranan mutanen borno suka diro Taraba, cikin tsananin bacin rai, direct hospital suka dosa, duk da isan dare sukayi, ganin halinda hafsa take ciki abin yayi matikar musu ciwo sosai, kotu suka maka abie Amma ina abin ya gaggara saboda iko da kudi da abie suka fisu dashi a jalingo, hakan yasa shari’a taki bima hafsa hakkinta, karshe dai mahaifinta yayi rantsuwa hafsa bazata zauna da Abdul ba, saiya sakar masa da yarinyarsa, ba jinkiri agun abie ya saketa, ya basu takarda a hannu, wannan ciwon yasa mahaifin hafsa yace koh bayan ransa baiyarda hafsa ta kuskura ta sake taka gidan shugaba koh da wasa ne babu ita babu sumayya, ta manta ma ta taba haifar y’a, yajama abie kunne mundin ya taka kafa a gidansa koh sumayya , zai nuna masa ikonsu a maiduguri.
Wannan shine dalili koh ince musababin rabuwar sumayya da hafsa, su karan kansu yan gidan basuso sakin hafsa ba duk da abubuwan da ta sace musu, Amma bakin Alkalami ya bushe.
Bayan tafiyar hafsa sosai sumayya ke kewar mahaifiyarta, kullum haka zatayi ta kuka a kaita wajen ummin ta, duk yanda dada zatayi rarrashe ki take, karshe da abie yagaji bulala yake mata kafun tayi shuru, a haka haka ta fara cire abin a ranta, soyayya sosai ake gwada mata a gidan baga dada ba wanda ita ke kula da ita yanzun, d’akinsu d’aya haka matan gidan na mugun sonta da mazan, wannan karon harda safina amasu nuna mata so, ba kamar daba inta ganta kamar ta cinnnta a wuta, sosai yanzun sumayya ke wa yara lalle na wasa, daman tunda haka ta tashi da abin abien ta na kara mata karfin gwuwa, duk da kananun shekarunta don lokacin tana neman shekara 7.
A wannan lokacin ne safina ta sake yad’a manufarta nason auren abie, kamar wanshan karon ma abie yaki amince wa, amma dada ta murza ido tace bata yarda ba aure dole koh yaso koh yaki, haka abie yana ji yana gani aka D’aura masa aure da safina, batare da son ransa ba, sam sam yarinyar batayi masa ba yaji baya kaunar ta.
Tirkashi dada batasan wannan aure shine ummul’kaba’isin kome ba…………..🍀🍀🍀🍀🍀