Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 72 Complete Novel

*ASM 072*

 

 

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

 

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

…….Ranar Laraba bayan su Fatuu sun tashi Mino ta tafi ta kwashe kayan shimfid’ar da tayi masu don yanzu da tsiya sun koma kwanan Falo don duk dare nan Farha ke zuwa ta kwana kuma duk abun nan Hajiya bata sani ba don ita a tunanin ta a d’akin da ta sauka take kwana dama bari take sai ta tabbatar Hajiya tayi bacci sannan ta taho, haka take ta faman yi masu cin kashi iri iri Harda ce ma Fatuu mayya ta lik’e tak’i tafiya gidan su, ita dae duk abunda zata mata bata biye ta, bayan ta maida kayan Farhar na kwance kan gado tana bacci, toilet ta wuce don tayi wanka, lokacin data fito cikin sauri ta fara shiryawa don yau test biyu gare su d’aya da safen nan za’ai masu d’ayar kuma sai After break so take taje da wuri don su k’ara yin karatu, bayan ta gama shiryawa ko tunanin tsayawa yin breakfast bata yi ba ta d’auki jakarta ta nufi k’opa zata fita, tana kama handle taji Muryar Farha tana mata magana hakan yasa ta dakata ta juya, tana kwance saman gadon ta d’an d’ago da kai tace mata wai taje tayi mata Breakfast, wani kallo Fatuu ta bita dashi kafin tace mata ai a part d’in Hajiya ake yi don haka taje can taci, yar tsawa ta kwatsa mata tace ita zata bata Umarni ta k’i yi mata to miye amfaninta dama in ba hakan ba miji bai son ta ya tafi ya barta yana can wurin wadda yake so suna shan soyayya amman ita da yake mayya ce ta lik’e to yau anan take son yin breakfast d’in, sosae Maganar ta daki zuciyar Fatuu har idanun ta sun fara tara k’walla amman sai tayi saurin maida su tace mata Aunty Saude zata kawo nata sai taci a fusace tace bazata ci shi ba ita take so ta dafa mata, d’an jimm Fatuu tayi sai kuma ta d’ago hannu ta duba agogon hannunta ganin da d’an sauran lokaci yasa ta juyo ta aje jakarta ta fita, bada jimawa ba ta dafo mata indomie ta kawo mata har lokacin tana a kwance, a saman bedside drawer ta aje mata tace gashi nan, tasowa Farhar tayi har Fatuu zata juya ta tsaidata ta juya tana yatsina tace mata ba ita take so ba Chips zata had’o mata, wani kallo Fatuu ta bita da shi kafin tace mata gaskiya bata da lokacin yi mata wannan School zata tafi tana da test kuma lokaci ya k’ure, tana gama fad’in hakan ta juya Farhar na mata magana cikin tsawa tay banza da ita ta tafi,

 

Saida suka hau hanya bayan sun d’auki Mino ta kira Aunty Saude tace mata ta wuce ba sai ta kawo mata breakfast ba, tace da wuri haka ta sanar mata test gareta ne, har suka isa Makarantar tana ta tunanin irin wulakancin da Farha ke mata. Ana gab da tashi ta kira Tk tace mashi yau ya zo ya d’auketa lokacin tashi Fauzy tace mata yau bazata tsaya ba kenan tace mata eh akwae abunda zatayi sai dae gobe. Bayan ta koma gida tana shiga cikin parlon wani irin k’amshi ya bugi hancin ta, da mamaki ta shiga bin parlon da kallo tana son gane k’amshin na minene don yayi yawa kuma tasan ba haka ta bar parlon ba, hanyar corridor ta nufa tana zuwa saitin inda su Tv suke kaman ance ta waiga taga kwalaben turaren wutar ta dake jere a wurin gaba d’aya zube a k’asa sun yi kwatsa kwatsa turaren barbaje a koina, da Al’ajabi take bin su da kallo aranta ta shiga mamakin yadda akai sukai haka, ranta ne ya bata ko Farha ce tayi masu haka, da sauri ta juya ta nufi Bedroom tana tura kopar nan ma k’amshin ne ya dakar mata hanci tay tsaye tana bin kwalaben humra d’inta dake watse a k’asa da kallo gaba d’aya an fasa su harda su turaren fesawarta ga kayanta na cikin Wardrobe duk an watso su wardrobe d’in a bud’e, kai idonta tayi akan gado nan ma indomie d’in data dafo mata ce a warwatse ko ina, tsaye Fatuu tay ta kasa yin wani kwakkwaran motsi idanunta cike da k’walla take bin bedroom d’in da kallo, da k’yar taja k’afa ta idasa shiga ciki ta nufi bakin gado ta zauna a inda ba indomie d’in, kifa Fuskarta tayi cikin tafin hannunta ta fashe da kuka, tana cikin kukan ta tuno da Kitchen ta mik’e da sauri ta nufi k’opa ta bud’e, tana tura kopar kitchen d’in taja ta tsaya idanu waje take kallon cikin shi gaba d’aya duk wani abun fashewa ta fasa shi kayan Abinci ma bata k’yale su ba duka ta barbaza su harda mai duk ta zuzzubar dashi a k’asa wasu daga cikin Warmers d’in ta ma bata k’yale su ba saida tasa ta6arya ta faffasa su sosae tayi mata Asara abun ba kyan gani, wani irin 6aci ran Fatuu Yay tama kasa cigaba da yin kukan sai huci take, tana tsaye a wurin Aunty Saude ta shigo kawo mata Abinci, a kan c-table ta d’aura kayan Abincin ta nufi Bedroom a ranta tana Maganar k’amshin da take ji tayi tunanin ko turare ne ya 6are, tana shiga corridor d’in taga Fatun tsaye ta bata baya ta isa wurinta tana fad’in “Fateema an dawo yau da wuri kenan, Tk ne ya shiga d’aukar Abinci yake fad’a man kin dawo ai” jin shiru bata ce komai ba kuma bata juyo ba yasa Sauden kai hannu ta ta6o ta still bata juyo ba, matsawa tay tana fad’in Fateema lafiya mi kike kallo haka itama ta kallo cikin Kitchen d’in ba arziki ta bud’a baki tace garin Yaya haka ta faru ya akai kayan sukai haka, sai lokacin Fatuu ta juyo ta fad’a jikinta ta fashe da kuka, tambayar abunda ya Faru Sauden tay ta d’ago cikin kuka ta fara bata labari, Bedroom d’in Saude ta nufa ta shiga taga yadda shima tay mashi ta kai hannu ta ruk’e ha6a ta shiga jinjina kai, fitowa tay tazo taga na parlon ma sosae itama ranta ya 6aci don ba k’aramar asara tayi ma Fatun ba, juyowa Saude tay ta koma cikin Corridor inda Fatuu ke tsaye bakin Kitchen rai 6ace tace “Yanzu ke Fateema kin za6i ki zuba mata ido tay ta maki wannan cin kashin, nace in sanar ma Hajiya kin hana gaskiya to yanzu an zo ga6ar da dole ma in sanar mata” girgiza kai Fatuu tayi cikin kuka tace “Don Allah Aunty Saude kar ki sanar mata hakan ba k’aramar matsala zai Haifar ba….”Katseta Saude tay tace “to wai ita Mahaifiyar tasu ta isa tayi maki abunda Allah bai nufa akan ki bane” girgiza kai Fatuu ta k’ara yi “a’a Aunty Saude, nidai ki kyaleta kawai banso in shiga tsakanin su tayi ta gama ta tafi”,

 

Shiru Saude tayi tana kallon ta can tace “Shikenan indai kina son kada na fad’i mata sai kinyi abu guda in ba haka ba gaskiya bazan zuba ido ina ganin tana maki wannan iskancin ba” ce mata tay to mi zata yin,

 

“so nike kiyi maganinta ta daina maki wannan wulakancin, kinsan irin haka saika had’a jiki da mutum yaji a jikin shi sannan yake kiyayar ka, nasan ba fin k’arfin ki tay ba wllh kawae jikin ne ba abunda zata iya maki don haka ki dawo Fateemar ki ta da ki sameta ki lakad’a mata dukan tsiya wllh zaki ga ta shafa maki lafiya” baki adan bud’e Fatun ke kallon ta jin kalaman sak irin na Fauzy, bayan ta gama tace mata tana ganin ba matsala ita bata son Hajiya ta sani,

 

“Ba wata matsala, ai anan part d’in in tazo zaki mata hakan kuma tunda tasan ita ke bata da gaskiya bazata bari a ji ba tunda dama duk abunda take maki a 6oye take yi bata son Hajiya ta sani, shiru Fatuu tay tana nazarin Maganar, Sauden tace zata yi ko kuwa taje ta fad’i ma Hajiyar, kallonta tayi ta jinjina mata kai alamar zata yi tace to tazo taci Abincin ta k’ara samun k’arfin yin maganin mara mutunci ta kamo hannunta suka nufo cikin parlon duk fargaba ta cika Fatun don rabon data yi fad’a da wani har ta manta, da kanta ta zuba mata Abincin bayan ta cire Hijab d’inta ta aje a gefe ta fara ci, har saida taga taci ta k’oshi sannan ta bar part d’in bayan ta jaddada mata abunda take son tayi ma Farhar,

 

Saude na fitowa cikin harabar ta hango Farhar ta fito ta baya ta nufo part d’in suna had’a ido ta wurga mata uwar harara ta kauda idon ta, Sauden tay d’an murmushin yau zaki gane kuran ki, bayan Fatun ta gama toilet ta je tayo Alwala ta dawo parlon don tayi sallar anan da niyyar inta gama sai ta fara gyara inda ya 6aci, tana kokarin sanya hijab taji an turo kopar ta kai idon ta da sauri, cikin isa kaman yadda ta saba ta nufo cikin parlon tana yatsina, a gaban Fatun ta tsaya hakan yasa Fatuu dakatawa da saka hijab d’in ta bita da ido gabanta nata fad’uwa kan abunda aka ce tayi matan, ce mata tayi tana fatan taga sakamakon k’in yi mata abunda ta sakata don haka gobe ma in ta k’ara sata abu tak’i yi zata ga abunda yafi wannan kuma tunda dai ita mayyace ta lik’e bada jimawa ba zatayi maganin ta gaba d’aya, tana rufe baki ta tsitta ma Fatun miyau a fuska aikuwa hakan ba K’aramin fusatar da ita yay ba duk da fargabar da take ciki a fusace ta kai hannu ta wanka mata mari ji kake Tasss! a gigice Farha ta kai hannu ta dafe kuncinta ido waje take kallon Fatuu data d’aure Fuska tana huci, nuna kanta tayi da yatsa tace ita ta mara a fusace Fatun tace eh taje ta mara aikuwa itama ta d’aga hannu zata sharara mata Mari da sauri Fatuu ta goce kafin Farha tay wani yunkurin ta shammaceta ta turata sai gata ta fad’a saman kujera tumm da alama k’ibar biredi ce dama, kan ta yunk’ura ta taso Fatuu ta haye samanta ta fara dukanta ba ji ba gani ta shiga sauke fushin duk wani bakin ciki data cusa mata dama kuma ita a yadda ta taso bata iya fad’an cacar baki ba tafi gane ta kai bugu kawai………..

 

Saude na shiga parlor ta nufi Hajiya dake Zaune akan Kujera tana kallo, tana zuwa da alamun rud’ewa tace mata ga Farha can a part d’in Fateema suna fad’a tayi tayi ta raba su sun k’i rabuwa, ba shiri Hajiya ta mik’e ta d’auki sandar ta tace suje, suna kan hanya Hajiya nata faman dogara sandar tana yin sauri da alamun mamaki take tambayar abunda ya had’a su Sauden ta shiga fad’i mata asarar da tayi ma Fatun wani irin bacin rai ne ya bayyana akan fuskar ta, Har lokacin su Fatun fad’a suke sai tumurmusa suke a k’asa har ta fitar ma Farhar da jini, lokacin data ga ta fasa mata hanci da baki tsoro ya kamata ta fara k’ok’arin k’yaleta saidae ita Farhar tak’i sai k’ok’arin ganin itama ta cutar da Fatun take hakan yasa Fatun cigaba da kare kanta har jikin c-table taso bugata k’arshe ita Fatun ta buga, Saude ce ta fara shigowa sai Hajiya tana shigowa ta rafka uban salati tare da sakin sandarta ta fad’i k’asa tay k’ara aikuwa a firgice Fatuu ta k’wace ta mik’e tana ta huci, itama Farhar kokarin mikewa tay da k’yar tana ma Fatun wani kallo a fusace sai nishin wahala take tun daga k’asan hancin ta har zuwa k’asan bakin ta duk jini ne haka goshinta ma yayi jawur ita kuma ta kakkarce Fatun a wuyanta da kuma gefe gefen Fuskarta da yake k’umbuna gareta zak’o zak’o, cikin Fushi Hajiya ta kira sunan Farhar tace Saboda bata da mutunci da Matar Yayanta take fad’a haka, shiru tay sai nishi take ta kumburo baki da gani kiris take jira ta saki kuka don idanunta a cike suke taf da k’walla, kallon Fatuu data sunkuyar da kai Hajiya tayi ta tambayi miya had’a su ta d’ago cikin rawar murya ta fara fad’i mata daga breakfast da ta ce tayo mata zuwa dawowar da tayi ta iske abunda tayi mata Saude ce ta k’ara yi ma Hajiya bayani tun daga farko, sosae ran ta ya 6aci tay ma Saude nuni da ta d’ago mata sandarta, hanyar Bedroom ta nufa saida ta tsaya taga 6arnar da tayi mata a parlon sannan ta wuce ta gano sauran, bayan duk ta gani cikin parlon ta dawo Fuskarta a tamke ta tsaya daga gaban Farha rai 6ace tace “dama tunda na gan ki kinzo nayi zargin ba abun Alheri ya kawo ki ba kawae don anaso arinka kyautata zato yasa na kauda zargin hakan da tunanin mutum na canzawa, wato ke ta turo kizo kiyi mata abunda na hanata Saboda ta raina ni son d’iya yasa ta daina jin maganata, yayi kyau ai ga sakamakon ki nan kin zata don kina mata cin kashi tana k’yale ki tsoron ki take ji, uhmm baki san wacece Fateema kuwa, kin ci sa’a tayi sanyi ne da sai tayi maki fiye da hakan don har hak’oran gaban ki sai ta cire maki su, yanzu sai ki wuce muje ki tattara kayan ki kibar man gida ni ban sauke wanda ba abun Arziki ya kawo shi ba a gidana, don ma yamma tayi da wllh bazaki kwana ba amman Allah ya kaimu gobe ko ba Jirgin Lagos Kya hau na Kano daga can ki wuce, muje!” Ta daka mata tsawa ta juya tu6i tu6i ta nufi k’opa dama skin tight ne a jikinta, kallon Fatuu Hajiya tay ta bata hak’uri tace duk abunda tayi mata asarar shi za’a maida mata tace ma Saude ta taimaka mata su gyaggyra wuraren tace to daga haka ta juya itama ta nufi k’opa, bayan fitar ta hannun Fatuu dake d’an gunji da gani kukan zuci take ta kama ta zaunar da ita kan kujera, itama zama tayi ta fara lallashin ta aikuwa kaman tana jira ta saka mata kuka a cikin kukan take fad’in miyasa ta fad’o ma Hajiya ba sunyi da ita bazata fad’i mata ba Sauden tace to ba gashi ta kawo k’arshen komai ba, lallashinta ta shiga yi tana kwantar mata da hankali kan ba wani abunda zai faru in sha Allah, saida taga ta saukko tayi shiru sannan tace taje ta cire uniform sai su gyara wuraren tace to ta mik’e.

 

Suna shiga cikin parlor Hajiya ta nuna mata hanyar Bedroom tace taje ta shirya kayanta, juyawa tay ta nufi hanyar ba tare da tace komai ba don ba alamun wasa a Fuskar Hajiyar, cikin parlon Hajiya ta wuce ta zaune inda take da kafin Saude tazo, Wayarta takai hannu ta d’auka ta shiga kiran Hajiya Maryam, bayan ta d’aga ta gaishe da ita Hajiyar tay banza bata amsa ba a kausashe tace “Ga yar Aiken ki nan zata dawo gobe in Allah ya kaimu, sannan a matsayina na Mahaifiyar ki in kika k’ara yin wani yunkuri don ki raba auren Fateema ko kuma ki cutar da ita BAN YAFE MAKI BA!!!” tana gama fad’in hakan ta katse Wayar.

 

Da daddare lokacin tuni su Fatuu sun gyara ko ina bayan tayo wanka ta shirya cikin kayan bacci tana niyyar fita parlor don taci Abinci har ta kai k’opa taji wayarta na ringing ta juyo ta nufo bakin gado inda take ajiye, zama tayi ta kai hannu ta dauka tay Jim tana kallon sunan Haisam dake kan screen d’in alamar shi ke kira, Kaman bazata d’aga ba saida ta kusa yankewa sannan ta d’aga ta kaita kunne, shiru tay ko sallama bata yi mashi ba shima kuma bai ce komai ba, sai d’an bayan wani lokaci taji ya tambayi tana lafiya, sai data amsa mashi sannan ta gaida shi shima bai amsa ba ta d’an ta6e baki, tambayar ta karatun ta yay tace mashi Alhamdulillah suka d’an yi shiru taji yace sun kusa fara Exams ne a tak’aice tace mashi eh, tambayar ta yay tana karatu har saida ta curo wayar ta kalli screen d’in da alama so take ta tabbatar shi d’in ne ya kira ta, bayan ta ce mashi eh tana yi shuru suka k’ara yi daga baya yay mata saida safe ya kashe, bin wayar tay da kallo a cikin ranta ta fara kokonton kodai yaga sak’on ne wata zuciyar ta bata inda ya gani ba iya haka zai mata ba tunda dama ai duk in ya kirata yana tambayar karatun ta, tana cikin cin Abincin a parlor Mino ta shigo tana sanye da doguwar rigar material ta yafo gyale saman kanta daga baya yayi tudun kitson shukun da akai mata ta nad’e da k’aton ribbom, tun bayan zuwan Farha zuwa gidan bai mata dad’i sai jefi jefi zaka ga tazo da rana dama kuma ta fara zuwa islamiyya da daddare ne kullum sai tazo, cikin parlon ta shiga Fatuu dake kallon ta da murmushi ta nuna mata gefen ta alamar tazo ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tace mata suci suka cigaba da ci tare, bayan sun gama Minon ta kwashe kayan ta kai Kitchen ta dawo Fatuu tasa ta d’aukko masu ruwa da lemu cikin freezer d’in dining, kallo suka d’an yi daga baya Fatuu ta kalli Minon tace mata in tana jin bacci taje Bedroom ta kwanta, har saida fuskarta ta kasa 6oye mamakin Maganar data ji tace mata ba anan suke kwana ba, yar dariya Fatun tay tace yau suna da yanci a gado zasu kwana da tsananin mamaki tace mata ina ita mai idanun magen yau bazata kwana ba, dariya taba Fatuu jin sunan data kira Farha dashi dukda da gaske idanun nata kaman na magen suke, nan Fatuu ta bata labarin abunda ya faru tace mata gobe ma zata tafi, zo kaga murna a wurin Mino harda mik’ewa da yin tsalle daga baya suka je suka kwanta.

 

Washe gari cikin nishad’i Fatuu ta tashi duk da tana d’an jin yar fargabar abun da zai iya zuwa ya dawo in Hajiya Maryam taji abunda ya faru, Bayan taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta ba kamar yadda ta saba ganinta ba da damuwa ta tambaye ta ko Ya Haisam d’in yaga sak’on sunyi Magana ne tace mata a’a itafa bata tunanin ya gani don ko jiya sunyi waya bata ga alama ba, nan ta kwashe abunda ya faru tsakaninta da Farha ta fad’i mata, cike da jin dad’i Fauzy tace amman ta burgeta wllh tuntuni abunda yakamata tayi kenan ai da duk ba’a zo nan bama. Lokacin da Fatuu ta dawo tuni Hajiya ta iza k’eyar Farha ta tafi.

 

_______________________

 

 

Ranar Asabar da wuri Mino ta tashi ta had’a Breakfast bayan ta gama ci ta tafi gida don zuwa islamiyya lokacin Fatuu nata shan bacci, sai wuraren k’arfe 10 ta tashi ba dan ta gaji da baccin ba sai don yunwa data isheta, bayan ta gama yin breakfast d’in toilet ta wuce tayo wanka tazo ta fara shiryawa, doguwar rigar material tasa ta yafa d’an gyalenta bayan ta d’auki wayarta ta nufi part d’in Hajiya, tare da ita sukai Abincin rana da Saude bayan an taso su Mino ta isketa nan, anan suka ci Abincin rana bayan sun gama suka zauna parlor harda Hajiya da Saude suna yin kallo, wuraren k’arfe ukku da rabi Mino tayi masu sallama zata je tay shirin islamiyya Fatuu ma ta mik’e tay masu sallama suka fito tare, part d’in su ta koma ta wuce toilet tayo wankan rana dama kusan kullum wanka ukku take yi k’aranci tayi biyu, bayan ta fito gaban mirror ta tsaya tana yin shafa ta k’ura ma kanta ido ita kanta tausayin kanta take game da irin rayuwar auren da take yi, bayan ta gama shafe shafen bata yi wata kwalliya ba iya powder sai lip glow ta shafa, wata fitted gown ta Atamfa ta fiddo ta saka, bayan ta gama shiryawa ta shimfid’a qq abun salla ta d’aukko Hijab ta kabbara sallar la’asar, lokacin da ta gama zaune tay a wurin ta jingina da gado tay shiru hakanan take jin ta wani iri, ta d’an d’auki lokaci a haka daga baya ta mik’e ta d’auke abun sallar ta mayar inda yake ta cire Hijab d’in itama ta linke, saman gado ta haye ta zauna ta fara latsa wayarta can ta aje wayar ta mik’e ta d’aukko jakarta ta fiddo littafi don tayi karatu, shima karatun ji tay duk bata jin dad’in shi ta maida littafin cikin jakar ta zame ta kwanta ta runtse ido tamkar mai yin bacci saidae tunane tunane kawai take, bata dad’e da kwanciya ba sosae lokacin wurin karfe biyar da rabi wayarta ta fara yin ringing, bud’e ido tay kafin ta juyo ta kai hannu gefenta ta d’auka, ganin Hajiya ce mai kiran nata yasa tay saurin tashi zaune ta jingina da headboard,picking tay tare da yin sallama on the other hand Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida ne da sauri ta amsa mata da eh tana nan, ce mata tayi tazo part d’in ta to yanzu tace to, saukkowa tayi daga saman gadon ta nufi wardrobe ta fiddo d’an madaidaicin gyale da ba zai rufe bayanta ba gaba d’aya ta yafa, a cikin Corridor ta d’aukko takalma Flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta wuce, Wata irin Fargaba take ji tun bayan data fito, ba yau Hajiya ta fara kiran ta ba amman wannan kiran duk sai take jin gabanta nata d’an fad’uwa, tana sanya kanta cikin parlon gabanta yay wani irin bugu mai k’arfi ba shiri taja ta tsaya, Zuba ma Mutumin da idanunta ke ganin mata ido tay wanda ko a nisan da ya ninninka wannan ta hango shi kallo d’aya zata gane shi, sosae tay Al’ajabin ganin su don bata ta6a zaton zata gan su ba, Haisam ne zaune akan 3 seater jikinshi sanye da Suit bak’ak’e saidai ya cire ta saman sai farar ciki mai santsi da dogon hannu sai bak’in wandon, daga gefen shi Fanan ce itama tana sanye da bakar doguwar riga jallabiya mai kayataccen adon stones gyalen rigar bai a saman kanta hakan ya bayyanar da brown sumar ta dake fake a tsakiya, gaba d’ayan su akan kujera d’aya suke zaune Haisam ya d’an zamo ta yadda ya jingina sosae da kujerar idon shi akan Tv ita kuma Fanan tana daga gefen shi itama ta jingina bayanta da jikin kujerar hannun ta d’aya dafe da forehead d’inta Hajiya har magana tay mata kan taje ta kwanta amman tace a’a sai an kirawo Zarah, sun d’an jima da zuwa don Fatuu bata dad’e da barin part d’in ba lokacin data koma tana toilet tana yin wanka suka iso, wani irin bugu da k’arfi da k’arfi zuciyar Fatuu ta hau yi ba kamar data ga Fanan ji tay kaman ta juya tunda ba wanda ya ganta ta koma, har zata juyan zuciyarta ta raya mata kenan k’in amsa kiran Hajiya zata yi hakan yasa ta dakata, Kamar Haisam yaji ajikin shi ana kallon shi a wani irin slow ya juyo da Fuskar shi ya kalli direction d’in da Fatun take nan take idanunsu suka shiga cikin na juna, zuba mata ido yay yana bin ta da kallo tun daga samanta har k’asa kafin ya tsaida su cikin nata, Hajiya ce ta kalle shi da niyyar yi mashi magana da yake Facing d’in su take a zaune ganin inda ya zuba ma ido yasa ta waiga ta kalli wurin, ganin Fatuu tsaye a wurin yasa ta d’an d’aga murya tace “Fateema ki shigo mana” har saida Fatun ta d’an firgita don bata san ta ganta ba, Fanan na jin Hajiya ta furta haka da wani irin sauri ta janye hannunta daga kan goshinta ta juya ta kalli inda Fatun take, gaba d’aya dabarbarcewa Fatun tay Hajiya ce ta k’ara mata magana kan ta shigo ta nufo cikin parlon idon ta a zare tana tafiya a d’arare, a bakin kujerun ta k’ara ja ta tsaya aikuwa kamar Fanan na jiran ta k’araso ta mik’e ta nufeta fuskar nan ba d’igon annuri, mik’ewar da tayi ta bayyana irin rigar jikinta mai bin shape d’in jikin mutum ce tayi kyau over, wani irin harbawa zuciyar Fatuu ke yi numfashinta ta fara kokowar fitar dashi, da za’a auna bp d’in ta a lokacin to kuwa daba makawa za’a ga ya hau, a gabanta ta tsaya daddad’an k’amshin jikin ta ya baza wurin, kyakkyawar Fuskarta a tamke take kallon fuskar Fatuun nan da nan jikinta ya hau 6ari ta hau kikkafta idanu, jin sun fara tara k’walla suna niyyar zubo mata da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa, A kausashe Fanan ta kira Sunanta “ZARAHHH!!!” murya na rawa ta amsa mata, ce mata tayi ta d’ago ta kalle ta, da k’yar ta d’ago ruwan hawaye sun lullu6e k’wayar idon ta,

 

“Zaraah u married my Husband!” Fanan ta fad’a muryarta har wani vibration take, shiru Fatuu tayi tana gunji kiris ya rage ta saki kukan, cigaba Fanan tay “na d’auke ki matsayin my own Sister Zaraah, amman shine kikai man haka, kin san yadda nike son ki na damu dake amman duk da haka kika iya auran man Miji?” Yanayin muryar ta tamkar itama zata saka kukan idanunta har sun canza, girgiza kai Fatuu ta fara yi fuska a yamutse da k’yar ta bud’e baki cikin trembling voice tace “D…on Allah Aunty Fanan kiyi hakuri wllh nima ban san ya Aure ni ba….kin ji na rantse maki…” Kuka ne yaci k’arfinta ta sadda kanta k’asa tana cigaba da yi, d’an ta6e baki Fanan tayi tace “But u loved him Zarah, Ur Message said it all!” d’agowa Fatun tay ta kalleta ta kasa cewa komai don ta gane sun ga sak’on da Fauzy ta tura,

 

“Kinsan abunda ke tsakani na dashi tun farko amman kika fara son shi kuma kinsan ya Aure ni amman baki daina son na shi ba Saboda cin Amana!” Sautin kukan Fatun ne ya k’aru tace “Don Allah ki yi hak’uri Aunty Fanan wllh kinji na rantse maki ni bansan abunda ke tsakanin ku ba saida kika zo, bai ta6a fad’i man ke zai Aura ba kuma gashi can ki tambaye shi” yamutsa fuska tay “daga baya da kika sanin miyasa kika cigaba da son shi!” A fad’ace take Maganar, shiru tay ta maida idonta k’asa tana gunji, da d’an tsawa tace ta bata amsa miyasa ta ci gaba da son shi,

 

“Kiyi hakuri nasan nayi maki ba daidai ba amman na daina son shi” d’age gira tay tace shine kuma ta turo mashi sak’o tana bayyana mashi son da take mashi, girgiza kai Fatun tay tace “Yanzu na daina son shi wllh kin ji na rantse maki” sai lokacin Fanan d’in ta d’an saki fuska tace “Good! haka yakamata” tana furta hakan ta juya tana tafiya cike da isa ta nufi wurin Haisam da har lokacin yana zaune a yadda yake, a gaban shi ta tsaya ta mik’a mashi hannunta dake sanye da zoben diamond, still yay yana kallonta ta wani yamutsa mashi Fuska, hannu ya kai gefen shi ya d’aukko wata takarda plain sheet dake nannad’e ya mik’a mata, juyawa tay ta koma wurin Fatun, a gabanta ta tsaya yanayin Fuskarta kamar zata yi murmushi tace “am sorry Zaraah we do not welcome u in our Fam, bazan iya yin kishi dake ba, not only u, da Kowacce mace ma because yayi man Alk’awarin zamu rayu tare mu biyu until Death do us part” tunda ta fara Maganar Fatuu ke jinjina mata kai har ta gama ta mik’o mata takardar hannunta, tana amsa ta juya har cikin ranta taji dad’in hakan tana fara tafiya taji Muryar Hajiya ta kira Sunanta, juyawa tay ta kalleta da kai tay mata alamar tazo, daga gefenta ta tsaya da alamun damuwa akan Fuskarta ta fara Magana “Kiyi Hak’uri Fateema ban so hakan ta faru ba saidae gaba d’aya sun nuna basu son Auren ban so ki cutu ne shiyasa na goyi bayan ya sallame ki kawai, yanzu kije ki kai ma Dije ina nan zuwa” kai Fatun ta d’aga mata idanunta sharkaf da k’walla, har zata juya Hajiya tace mata ta bud’e ta fad’i mata saki nawa yayi mata Saboda sheda, hannunta sai kakkarwa yake ta fara warware takardar………….. ALHAMDULILLAH, Ba don na gama ba sai don nazo inda nike son in tsaya😀

 

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka Book 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 da 2 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button