Job

Yadda Zaka Cike Aikin Jami’in Tsaro Ta Kasa, Wato Nigerian Army Defence

Hukumar Jami’an Tsaro Na Kasa Wato NIGERIAN ARMY DEFENCE tana sanar da masu sha’awar shiga aiki Sojin kasa cewa ta bude Portal domin dauka rukuni na 86 tun ranar 25 ga watan Satunba 2023 ga masu sha’awar aiki.

ABUBUWAN DA AKE BUKATA YAYIN YAYI APPLY

1) Dole ne ka zama baka da aure, sannan kuma dan Najeriya cikakke mai katin shaidan zama dan Najeriya (NIN).

2) Dole ne ka zama a lafiyayye a jiki da kuma ƙwaƙwalwa sannan kuma mai kuzari kamar yadda Nigeria Army take bukata.

3) Dole ka zama baka da wani record na criminal daga Kotun shari’a.

4) Dole mai nema ya zama yana da katin shaidan haihuwa (Birth Certificate or Declaration Of Age) daga sananiyar Asibiti ko Ƙaramar Hukuma ko kuma Kotu.

5) Dole ne mai nema ya zamana yana da katin shaidan zama dan Karamar Hukumar (Indigine).

6) Dole ne mai nema ya kadda ya gaza tsayin 1.68 namiji, Mace kuma kadda ta gaza 1.65.

7) Dole ne mai neman Non Trades Mace ko Namiji kadda su gaza shekara sha takwas (18years) kuma kadda su wuce shekara ashirin da biyu (22years) daga 18 December, 2023.

8) Masu Regista Nurse da Midwives kadda su wuce shekara talatin lokacin apply.

9) Dukkanin masu nema dole ne ya zamana sunyi nasaran samun Credit 4 a takardun su na WASSCE/GCE/NECO/NABTEB kuma kadda ya wuce zama biyu.

10) Karin haske na gaba shine wayanda sukayi apply Tradesman/Tradeswomen dole ya zamana suna da (Trade Test ko City Guild Certificate)

11) Duk wanda yayi nasarar tsallake matakin farko zuwa Screening zaiyi Screening ne Jihar daya nemi aikin, sannan za’a fara tantancewar ne ranar 6 zuwa 19 na wata shadaya 2023 (1-19 November, 2023).

*FA’IDODIN HIDIMAR A SOJOJIN NAJERIYA*

(1) Damar Aiki/Sana’a.

(2) Ingantattun biyan / alawus-alawus.

(3) Damar kara ilimi.

(4) Haɗin kai tare da mutane daga kabilu/addini daban-daban.

(5) Ingantattun Ayyukan jindadi/Inshora.

(6) Damar duk sojoji sun mallaki gidaje a wuraren da aka zaba a fadin Najeriya.

(7) Fansho da Kyauta.

 

Danna Wannan Link 👇👇

 

Click Here Now 

 

Masu buƙata ayi musu apply 08131301639

Back to top button