Uncategorized

Kadan daga cikin shirin Labarina Season 4 Episode 11

 Haƙiƙa mutane da dama sun zaƙu kuma sun ƙagu suga abinda zai faru a cikin shirin Labarina abubuwa biyu ne zuwa uku ne mutane suke son a cikin shirin:

Na farko shine dawowar prisdor daga kasar Egypt inda har muka ga yana daukar  alwashin aikata wani laifi da zai sa a mayar da su gida tari, domin ya samu damar kashe Baba ɗan Audu.

Za Ku Iya Karanta 

✓ Maryam Yahaya bata jin magana wallahi – Datti Assalafy

✓ Allah Ya yi wa Sani Garba SK, Baya jinyar mako Biyar

Na biyu haduwar yaro da mai tsohon mai gidansa wato haɗuwar Baba ɗan Audu da Baba Rabi’u a gidan yari, shin me zai faru da prisdor idan ya shigo cikin gidan yarin, za dai a sha cakwakiya a nan tabbas!

Na uku shine kiran da masu kidnapping suka yi wa mahaifiyar Sumayya, shin idan suka ƙara kira me za su ce? 

Ga dai kaɗan daga cikin shirin Labarina Season 4 Episode 11 Wanda za’a saki cikakken Film din a ranar juma’a idan Allah Ya kai mu.

Back to top button