Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 71 Complete Novel
![Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt](https://aihausanovels.com.ng/wp-content/uploads/Screenshot_20231027-164547-300x250-1.png)
* ASM 071*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………A nutse ta fara karanta sak’on wanda ke bayyana sirrin zuciyar wadda ta turo wato Zarah, bayanin tun lokacin da Allah ya jarabeta da son shi da irin wahalar da ta sha hakane ma yasa ta amince ai mata Aure Saboda ta rasa shi har Allah ya juya Al’amarin ya aureta, Hak’uri ta bashi kan zargin shi da tayi ta nuna bata san akwai Aure ba a tsakanin su kuma Saboda son da take mashi ne yasa taji zafin abun sosae hakane ma yasa data samu ciki tak’i saurarar shi harta 6arar don kuma bata son girman shi ya zube a idon mutane duk don k’aunar shi da take, a k’arshe ta nuna mashi tana cikin mawuyacin hali Saboda canza mata da yayi a yanzu da burinta ya cika ta zama Matar shi, Hak’uri ta k’ara bashi tace in don cikin da ta 6arar ne yake nuna mata halin ko in kula in sha Allah zata biya shi fin shi ma amman tana a cikin matsananciyar damuwa da har tana son shafar karatun ta………, Tun Fanan na karantawa lafiya lau har ta kai yanayin Fuskar ta ya fara sauyawa, lokacin data gama karantawa d’agowa tay da yanayin d’aurewar kai ta kallo hanyar Kitchen da Haisam ke ciki, k’ara maida idonta tayi akan Screen d’in tana sake biya sak’on lokaci guda hannuwanta suka fara yin kerma ta zuro da fararen k’afafuwan ta k’asa, Slowly ta mik’e har lokacin tana cikin k’ara karanta sak’on, saida ta karanta shi sau ukku tamkar mai yin hadda, gaba d’aya ta kasa gasgata abunda take karantawa gani take kamar ba daidai take karatun ba ko kuma ba sak’on Haisam d’in bane hakan yasa sai k’ara maida idonta take tana k’ara karantawa, zuciyar ta ce ta shiga gasgata mata sak’on shi ne in ba haka ba mizai sa ta turo mashi kuma ga alamu nan a bayyane har sunanta an ambata a ciki kan ciwon da ta yi lokacin da Fanan d’in tazo…….”Kenan Auran Zarah ya yi a 6oye???” ta fad’a acikin ran ta, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi mata ta fara numfashi da k’arfi har saida ta d’an bud’e baki jin numfashin na neman yi mata wuyar fitarwa, tana haka Haisam ya shigo cikin parlon yana sanye da wando 3 quarter da armless hannuwan shi duka biyun ruk’e da mug d’an tiriri na fitowa alamar abun ciki mai zafi ne, wani irin kallon tashin hankali ta shiga bin shi da shi hakan yasa shi dakatawa daga d’an gabanta yana kallon ta shima har saida gaban shi ya d’an fad’i ganin yanayinta da kuma wayar shi dake hannunta don yanayin kallon da take mashi na tuhuma ne, nufo shi tay a fujajen tana zuwa fuska a hautsine ta d’aga mashi wayar shi dake hannunta daidai kan sak’on a kid’ime tace “Don’t tell me dis message is for you!!!” maida idon shi yay akan Screen d’in ya gane Zarah ce ta turo saidai bai fahimci miye akace a sak’on ba, wucewa yay yaje ya aje mugs d’in akan c-table ya juyo lokacin itama ta juyo tana kallon shi, hannu ya kai ya amshi wayar ya fara karanta message d’in a nutse har ya gama, d’agowa yay ya kalleta ta kafe shi da idanunta da ta zaro Fuskarta har ta fara yin ja alamar motsuwar jini, shiru yay kawai yana kallonta yama rasa mi zai ce mata don komai sak’on ya bayyana, girgiza kai ta shiga yi tana fitar da numfashi da k’arfi cikin d’an k’araji tace “so it’s true, You married Zarah without my knowledge!” still bai ce mata komai ba aikuwa ta daka mashi tsawa a gigice tace “tell me! is she ur Wife??” d’an cize lip d’in shi yay na k’asa Slowly ya lumshe mata ido nan take ta gane mi hakan ke nufi, cikin fitar hayyaci ta fara ja da baya tana cigaba da girgiza mashi kai, bin ta ya fara yi yana ce mata “I can explain myself…” a haka har ta dangane da kujera kawai sai ta haye saman ta gudun kada ta yi ma kanta wani abu yasa shi kai hannu zai kamo ta ai kuwa ta tafi gaba d’aya ta wuntsila bayan kujerar ta fad’a saman tiles daga jin k’arar ba K’aramin bugawa tay ba, juyawa yay da sauri ya zagaya lokacin har ta mik’e tana k’ok’arin rugawa d’aki cikin zafin nama ya kamota ta fara kokowar kwacewa cikin k’araji fuskarta da idanunta sunyi jawur take fad’in “Leave me alone! Ya Haisam u’r a betrayer! u betrayed my trust, u broke the promise u have made to me! U deceived me….!” Gaba d’aya bata a cikin hayyacin ta idanunta sun jik’e da k’walla fatar k’asan idon tayi wani irin ja kamar jini, sai kiciniyar k’wace kanta take ta kansa sai rarrashinta yake yana ta tsaya zai mata bayanin yadda hakan ta faru amman ina tak’i sauraren shi fad’i take ba abunda zai fad’i mata ta san don ance tana da matsala shiyasa yayi tunanin bazata haihu ba yaje ya auri Zarah gashi nan har yayi mata ciki duk da Alk’awarin da yayi mata, abu fa ya ture gaba d’aya Fanan ta burkice mashi duk ta rud’a shi har fuskar shi ta bayyana, da dai taga ta kasa kwacewa kawae sai ta kai bakinta a jikin damtsen shi dake a bayyane ta daddage ta gartsa mashi cizo aikuwa ba Arzik’i ya saketa Saboda rad’ad’in Azabar da ya ratsa shi wurin har ya fashe nan da nan jini ya fara zubowa, ai yana sakinta ta watsa a guje hanyar Bedroom yana ganin haka shima ya bita don ya fahimci abunda take son aikatawa haka take da ranta ya 6aci sai ta ruga ta kulle kanta a cikin d’aki, ko kafin ya cimmata tuni ta shige lokacin daya kai hannu cikin zafin nama zai bud’e kopar data turo tuni har tasa Key, bugun k’opar ya fara yi da d’aga Murya yana kiran sunanta yana ta bud’e karta yi ma kanta illa, tana shiga d’akin a haukace ta nufi bango ta fara kai mashi bugu tana wani irin kuka na fitar hayyaci, har saida knuckles d’inta suka fara fitar da jini sannan ta daina ta nufi gado ta zauna dabar tana cigaba da kukan, a ranta ta fara tariyo sak’on aikuwa ta k’ara tsananta kukan ta fara sambatu tana fad’in Ya Haisam da Zarah sun ci amanarta, tunowa da Maganar ciki da ta samu tasa ta kai hannu ta fara bugun Katifar hakan bai sa ta samu sassaucin abunda take ji ba acikin zuciyarta sai ma k’ari nan fa ta mik’e ta fara wurgi da abubuwa abun har ya kai da fashe fashe, gaba d’aya hankalin Haisam ya gama tashi sai faman bugun k’opar yake da k’arfi yana kiran sunanta yana fad’in kada tayi ma kanta wani abu ta bud’e kopar, har ta kai ya fara mata Magiya ko tana jin shi ma oho ba dai alamun zata bud’e,
sintiri ya shiga yi tsakanin Window wadda itama take a kulle da kuma kopar yana tunanin Mafita, zuciyar shi ce ta bashi ya fara bugun kopar k’ilan yaci sa’a ta bud’e duk da yasan mawuyacin abu ne don dakakkar k’opa ce, ba irin bugun da bai ma kopar ba iyakar k’arfin shi amman ba alamun zata bud’e dole ya dakata don shi kan shi ya gaji, Hajiya ce ta fad’o mashi a rai a rud’e ya nufi cikin parlon inda Fanan ta jefar da wayar ya nufa ya d’auka, tana fara yin ringing Hajiyar ta d’auka ko gaida ita bai yi ba ya shiga fad’i mata abunda ke faruwa itama rud’ewa tay ta shiga tambayar shi dama bai sanar mata ba duk da tasan inda ya sanar mata zata ji kawai ta rud’e ne, ce mata yay eh ya bari yayi 2 Months da dawowa sai ya d’auki hutun da basai an rink’a biyan shi ba su taho nan Nigeria su kwana biyu lokacin sai ya sanar mata dama irin haka yake gudu shiyasa, tambayar shi tayi to yanzu ya akai ta sanin yay d’an jimm hakanan sai yaji baison fad’i mata zancen sak’on da Zarah ta turo sai yace mata kawai a Wayar shi ta gane, ce mashi tay to yayi k’ok’ari ya 6alle kopar mana yace mata ba irin k’ok’arin da bai yi ba tak’i bud’ewa, tambayar shi tayi anan ba masu aikin 6alle k’opa ne sai lokacin ya tuna da sauri yace mata ba’a rasawa tace to yay hanzari don Allah ya kira azo a bud’e kar wani abu ya sameta ta razana ne sosae ba ta haka yakamata ta sani ba.
Bai san ina zai samo wanda zai 6alle kopar ba amman da yake yana a K’asar da aka cigaba ne komai k’ank’antar sana’ar mutum zaka samu ya d’aura a internet, yana yin searching sai gashi ya samu, kiran su yay a waya ya fad’a masu aikin da yake so ayi mashi da Address d’in gidan, bayan sun gama komawa yay wurin d’akin yana cigaba da knocking wai ko zata bud’e amman shiru abunda ma ya k’ara tayar mashi da hankali jin shiru bai jin wani motsi sa6anin da yana d’an jin k’arar abubuwan da take yi, kai da komowa ya shiga yi duk fuskarshi ta harmutse, bada jimawa ba sai ga mai 6alle kopar ya iso, ba 6ata lokaci ya 6alle Haisam har yana yin tuntu6e Saboda saurin ya shiga, a kwance ya isketa k’asa ya nufeta da sauri ya duk’a, ganin bata motsi yasa a rud’e ya kai hannu ya fara jijjigata yana kiran sunanta yana ta bud’e idonta, gaba d’aya bata numfashi ga hancin ta duk jini alamar tayi ha6o haka hannuwanta ma glass ya d’an yayyanke ta, da sauri ya mik’e ya nufi closet ya bud’e ba tare daya tsaya za6a ba ya janyo wata doguwar riga dake sagale da mayafinta ya dawo inda take ya fara k’ok’arin zura mata, kinkimar ta yayi da taimakon wanda ya balle kopar aka sakata a Mota bayan ya sallame shi ya shiga yajata da gudu ya fice ko tunanin ya canza kaya bai yi ba,
Tun bayan da Fauzy ta tura sak’on tay zaune tsuru gabanta na cigaba da fad’uwa sai fargabar abunda zai je ya dawo take a ranta ta shiga yin Addu’ar Allah yasa in yaga sak’on komai ya daidaita tsakanin su, saida aka kira sallar la’asar sannan ta tada Fatuu don tayi salla, bayan ta gama ta zuba mata Abincin ta fara ci, ta lura da yadda Fauzyn keta faman bin ta da ido hakan yasa ta tambaye ta lafiya ta d’an yi murmushi tace mata ba komai, kokonto Fauzy ta shiga yi na kodai ta fad’i mata kar daga baya ta gane taga tayi mata ba daidai ba, zuciyarta ce ta bata gara ta fad’i mata kawae in ma ta nuna bata ji dad’i ba sai ta bata hak’uri, bayan ta gama cin Abincin ne ta fara shirin tafiya, saida ta gama shiryawa ta maida Uniform d’inta sannan Fauzy tace mata tana son zasu yi magana, zama tayi a bakin gado Fauzy na facing din ta a d’ayan gadon a sanyaye tace “na maki katsalandan Zarah nasan yana iya zama laifi a wurin ki” da alamun mamaki tace laifi kuma wane irin laifi, Wayarta dake ajiye gefenta ta d’auka ta bud’o sak’on data tura ma Haisam ta mik’e ta kai mata,
zuba ma Screen d’in ido Fatuu tayi tana karanta sak’on, tun kafin ta gama ta zaro ido ta kai hannun ta guda ta rufe baki alamar Al’ajabi, bayan ta gama karantawa ta d’ago tana kallon Fauzy dake tsaye gefe a rud’e tace “Fauzy miyasa kikai haka don Allah? Miyasa zaki tura mashi wannan sak’on haka?” Kamar zata yi kuka ta k’are Maganar tana yamutsa fuska idanunta har sun ciko da k’walla, zama Fauzy tay daga gefen ta cikin kwantar da murya tace “kiyi hakuri Zarah dama nasan ba lalle Kiji dad’in abunda na aikata ba, wllh tausayi kike bani ne abubuwa sun maki yawa daga wannan sai wannan ina gudun damuwar hakan tasa kizo ki fad’i Exam shiyasa nayi tunanin idan na tura mashi bayanin komai tunda shi mutum ne mai tausayi watak’il hakan yasa ya karkato da hankalin shi gare ki, nasan da kin samu kulawar shi zaki samu kwanciyar hankali” girgiza kai Fatuu tayi kwallan idonta suka fara zubowa tace ita dai da bata aikata hakan ba don hakan tamkar zubar da k’imar ta ne kuma yanzu koda bai son ta dalilin hakan zaisa ya cigaba da zama da ita Saboda tausayi ita kuma bata son hakan gara in bai sonta kawai su rabu, ganin yadda ta damu yasa Fauzy kama hannunta tace “ba wata k’imar ki da zata zube kar ki manta shi Mijin ki ne kuma dana bayyana mashi kina son shi ai kinga nace Allah ne ya jarabe ki shima yasan bake kika d’aura ma kan ki ba kuma tunda shi ba mutum bane mai wulakanci hakan bazai sa ya wulakanta ki ba sai ma kulawa dake, kuma ni nasan ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba koda kin nuna mashi ya sake ki bazai ta6a sakin ki ba domin da zaiyi hakan ai da bazai ma cigaba da zama dake ba gashi har mahaifin shi ya kar6e ki, uwa uba kuma Hajiya da take iko dasu gaba d’aya ita ta goyi bayan kuci gaba da zama tare kinga gara ya san kina son shi koda shi bai son ki in yana kula ki sai ki koya mashi son naki” a marairaice take Maganar, ita dai Fatuu sam hakan bai mata dad’i ba wllh sai yamutsa fuska take tana kwalla, k’ara duba sak’on ta shiga yi lokacin ta lura da marking d’in da yayi bai yi blue ba hakan yasa ta fara tunanin koma bai duba ba to, zuciyarta ce ta fara gasgata mata hakan ta shiga raya da ya gani tasan k’ilan ya ce wani abu don da wuya ya shareta, yin wannan tunanin yasa da sauri hannunta har yana rawa tayi delete for everyone duk Fauzy na kallon ta, wani sanyi taji a ranta fuskarta ta daidaita, ganin haka yasa Fauzy bata hak’uri tace tunda bata ji dad’i ba ta yi Addu’ar Allah yasa ba Gb WhatsApp gare shi ba Fatun tace mata ba komai tasan don Farincikin ta tayi hakan amman tafi son ya zauna da ita don yana son ta ba don tausayi ba idan ya dawo da kanta zata rok’eshi kan ya saketa, harda cewa in ma ya k’i zata ce mashi tana da wanda take so ne Fauzy tay d’an murmushi kawae a ranta ta raya fad’i kawai take tasan ba iyawa zatai ba don ba K’aramin kamu son shi yay mata ba, tare suka fito da Fauzy ta rako ta, ganin Fauzyn duk tayi sukuku yasa Fatuu bata hak’uri tace in ta 6ata mata rai Fauzyn tay murmushi tace a’a wllh ai ita zata ba hak’uri tayi mata ba daidai ba, Fatun tace itama bata d’auke shi a wani abu ba, saida ta hau Keke Napep sukai sallama tace ta gaishe mata da Mino sannan ta koma.
Asibitin da take aiki ya kaita, nan da nan aka nufi Emergency da ita bayan Haisam d’in ya masu bayanin ta razana ne kuma ranta ya 6aci sosae, nan da nan likitoci suka taru kanta duk abunda ake mata Haisam d’in na gani ta faffad’an window d’in d’akin da yake gaba d’ayan shi transparent glass ne, Bayan wasu mintuna d’aya daga cikin likitocin ya fito ya sanar dashi tayi doguwar suma ne za’a bata treatment d’in daya dace zuwa kowanne lokaci zata iya farfad’owa, sai lokacin Haisam ya d’an ji hankalin shi ya kwanta da gaba d’aya jinin shi akan akaifa yake tsoron shi kar ace ta samu heart attack, daga baya bayan likitocin sun fito ya shiga cikin d’akin, a kan kujera dake a gefen gadon ya zauna yana kallon Fanan dake kwance fuskar ta sanye da Oxygen mask, a ranshi yake raya irin abunda ya guda kenan yasa bai fad’i mata ba don yasan fin hakan na iya faruwa, yana zaunen nurse ta shigo suka gaisa ta nufi gadon Fanan d’in, bayan ta gama abunda zatayi har zata fita sai kuma ta tsaya ta kalli Haisam d’in da murmushi ta nuna damtsen shi da jini mai d’an yawa ya taru tace mashi ya samu rauni ne, ce mata yay eh tace bari tayi mashi dressing d’in wurin yay mata godiyar kulawa, bayan ta gama mashi zaune yay shiru nan ya fara tunanin sak’on da Fatuu ta turo mashi, wayarshi dake ruk’e a hannun shi ya d’ago ya bud’e ya shiga cikin WhatsApp, koda ya bud’e chat d’in Fatuu sai ya ga an goge sak’on, wani kalan murmushi ya saki yay d’an jimm sai kuma ya fita daga chat d’in, Hajiya ya kirawo dama koda yana kan hanya da zai kawo Fanan d’in saida ta kira ta tambayi halin da ake ciki don ta kira bai d’auka ba hankalin ta ya k’ara tashi, fad’i mata yay an 6alle kopar da yanayin da ya iske Fanan d’in yace gashi ma a hanya zai kaita Asibiti,
Har bayan wani lokaci bata farfad’o ba k’arfe sha biyu da wasu mintuna ya bar Asibitin don su ba’a kwana wurin mara lafiya duk abunda yakamata za’ai mashi sai dae in buk’atar ganin wani nashi ta taso a kira, yana driving yana tunanin sak’on Fatuu har ya iso gida, bayan ya shiga parlor ya tsaya ya d’auke Computer d’in Fanan da wayarta dasu takardun da ke ajiye ya nufi ciki, Bedroom d’inta ya wuce ya ajiye su ya fara gyara shi, lokacin daya dawo Bedroom d’in shi toilet ya wuce yayo wanka bayan ya fito d’aure da towel ya tsaya gaban mirror yana tsane ruwan jikinshi da short towel d’in daya ruk’o, gaba d’aya Fuskar Fatuu yake ganin tana mashi gizo a cikin Madubin sai d’an sakin Murmushi yake, bayan ya gama ya nufi closet ya fiddo kayan bacci ya saka, bayan ya kwanta tunanin abu biyu ya shiga yi wato Fanan da Fatuu sak’on data turo mashi sai yawo yake mashi a rai, bazaka ta6a gane yadda ya ji ba dangane da sak’on daga yanayin Fuskar ta shi.
Washe gari bayan ya dawo daga sallar Asuba a Motar shi ya fito jikin shi sanye da farar jallabiya, Bedroom d’in shi ya wuce ya cire rigar ya bar short d’in jikin shi da singlet ya fito ya nufi Kitchen don had’a ma Fanan Breakfast koda zata farfad’o in yaje, Misalin k’arfe takwas na safiyar ya gama shiryawa cikin k’ananun kaya ya fito ya wuce Kitchen, bayan ya d’aukko basket d’in da ya zuba kayan breakfast d’in ya fito ya tafi, Har lokacin daya je bata farka ba ya aje basket d’in ya zauna, after some minutes ya mik’e yaje yay ma Nurse d’in dake kula da ita magana kan zaije ya dawo, bayan ya fito daga Asibitin wurin aikin shi ya wuce don yaje yay reporting kan ciwon matar ta shi. Wuraren k’arfe goma ya dawo still bata farka ba ya zauna idon shi akanta daga baya ya fara latsa wayar shi, bayan kusan awa guda da dawowar shi ta fara motsi yana ji da sauri ya kai idon shi kanta, a hankali ta fara motsa idanunta ta fara bud’e su tana yi tana lumshe su, tashi yay ya nufi gadon ya tsaya daga gefen inda kanta yake yana kallon ta, k’amshin turaren shi da ya cika mata hanci ne yasa ta bud’e idanun suka sauka a kan Face d’in shi, bin juna sukai da kallo Fuskarta har ta d’an fad’a, cikin cool voice d’in shi yace mata sannu aikuwa tamkar ya tuna mata da abunda ya faru ta kai hannu ta cire Oxygen mask d’in fuskarta, tashi tay zaune cikin fushi ta fara k’ok’arin cire cannular d’in k’arin ruwa da aka saka mata Haisam d’in na ta bari amman tamkar ma zuga ta yake, tana gama cirewa ta saukko daga saman gado ta kai hannu ta d’auki veil d’in rigar jikinta ta yafa saman kanta ganin abunda take shirin yi yasa shi zagayawa yasha gabanta ta fara k’ok’arin ture shi, ruk’e hannunta yay ya fara lallashin ta yana tayi hak’uri a gama dubata in sunje gida zai mata bayanin komai, a fusace take fad’in ya bata hanya ta wuce bin ta yay da ido sai kace ba Fanan d’in daya sani ba mai yi mashi biyayya sam bata tsallake Maganar shi, Nurse ce ta shigo ganin abunda ke faruwa yasa ta juya taje ta kira Dr, bayan ya shigo ya tambayi abunda ke faruwa Fanan d’in tace mashi gida zata tafi rarrashinta ya shiga yi shima kan ta bari ta samu sauk’i sosae ta kafe sai ta tafi fuskarta ba alamun sassauci k’arshe dole suka k’yaleta ta tafi, Haisam na niyyar bin bayanta Dr ya tsaida shi Magana yayi mashi kan halin da take ciki yace yayi k’ok’ari aga ta rage 6acin ran ko kuma ma asan yadda za’a rabata dashi don a halin da take ciki akwae yuwuwar ta iya samun heart attack saboda 6acin ran yayi yawa gashi har jininta ya hau, godiya Haisam yay mashi bayan ya gama mashi bayanin, koda ya fito harabar Asibitin bai ganta ba ya nufi inda ya parker Motar shi ya shiga, bayan ya fito daga Asibitin bai yi nisa sosae ba ya ganta a tsaye bakin titi, tsayawa yay ya sauke glass ta cikin Motar yay mata magana kan ta shigo su tafi amman ko kallon shi bata yi ba k’arshe ma sai taci gaba da tafiya gashi ba damar ya parker don ba’a parking a wurin, bin ta yaci gaba da yi da Motar har saida ta tsaida taxi ta shiga ya bi bayan su, bayan ta sun iso tana shigowa cikin gidan ta nufi Bedroom, wayar ta data hango saman bedside ta nufa ta d’auka, gefen gado ta zauna sai nishin 6acin rai take ta shiga kiran Mom d’inta, tana d’auka ta saka mata kuka a tsananin rud’e Hajiya Maryam ta shiga tambayar ta abunda ke faruwa cikin kukan tace mata Ya Haisam yaci Amanarta ya yaudare ta duk da Alkawarin da yayi mata yaje yayi aure bada sanin ta ba, cikin 6acin rai Hajiya Maryam ta tambaye ta shine ya fad’a mata tace a’a Wadda ya auran ce ta turo mashi sak’o ta gani, nan ta shiga fad’i mata halin da ta shiga, sosae Hajiya Maryam ta razana da jin a Asibiti ta kwana ta shiga kwantar mata da hankali tace itama tasan da Maganar Hajiya ta kira su ta fad’a masu ta nuna bata amince ba yanzu haka ma tana k’ok’arin raba su ne, cikin kuka Fanan d’in tace mata ita dae gida zata taho da sauri tace mata eh ta taho harda tambayar zata iya ko tazo ta taho da ita tace a’a zata taho, k’ara lallashinta ta shiga yi sosae tana kwantar mata da Hankali tace dole ma a raba Auran tunda bada izinin su aka yi shi ba, duk Maganar da take Haisam na tsaye daga gefen gadon tasan yana a wurin jin k’amshin turaren shi kuma taga lokacin daya shigo ta wutsiyar idon ta, tana gama wayar ta ajeta saman gadon ta mik’e, wardrobe ta nufa tana zuwa ta bud’eta, kayanta ta fara kwasowa ta kawo saman gadon tana shirin juyawa ta sake d’ibowa taji ya ruk’o hannunta, cikin fushi tace ya sakar mata hannu ba tare data juya ta kalle shi ba jin bai saki ba yasa ta juya a fusace tace “I said leave my hand!” kallonta kawai yake sam bai yi mamakin yadda take mashi ba don iya fuskarta kawae ta bayyana tsananin 6acin ran da take ciki, girgiza kai ta fara yi idanun ta suka ciko da k’walla cikin karyayyar murya ta fara fad’in “I feel deeply betrayed and disappointed by ur action, you broke a promise to me and now I can’t trust you anymore….” Dakatawa tay tana fitar da numfashi da sauri kirjinta na hawa da sauka, sigh yay yana son mata magana yama rasa ta ina zai fara, k’ok’arin matso da ita yay don ya rungumeta aikuwa a fusace tace “Don’t…!!!” ganin kallon da yake bin ta dashi ne yasa ta d’an sassauta murya idanunta na cigaba da zubar da k’walla tace “I can’t believe dat you would betray my trust like this, u don’t even care weather am gonna die…..Na daina son ka Ya Haisam! na daina, our relationship will end now sai kaje ka d’aukko Zarah kici gaba da Zama da ita” k’ok’arin fuzge hannun ta fara yi aikuwa ya janyota ta fad’o jikinshi ya sa duka hannuwanshi ya rungume ta gam ta yadda ko motsin kirki bazata iya ba, Kuka ta sakar mashi tana fad’in Ya saketa, ta tsane shi bazata cigaba da zama da shi ba, ganin bazata iya kwacewa ba yasa ta kifa Fuskarta a saman faffad’an chest d’in shi ta shiga raira kuka mai cin rai, Sigh yay ya kai bakin shi saitin kunnen ta cikin Magana mai kaman rad’a yace “am deeply sorry Fanan, I know I have wronged u, amman ban ci Amanar ki ba, lokacin da nayi maki Alk’awari Already akwai aure tsakanina da Zarah, if u could remember ban so yin Alk’awarin ba a lokacin” dakatawa yay dama tamkar Maganar na mashi wuya yake furta ta, shiru tay bata ce komai ba sai sheshsheka take, Cigaba yay “Now give a chance to explain Everything pls” shiru tay mashi saidae shesshekar da take ta ragu hakan yasa ya gane ta bashi damar, sakinta yay ya kama hannunta suka nufi bakin gado, zaunar da ita yay shima ya zauna ya juyo yana kallon ta ita kuma idonta na gefe, a nutse ya fara mata bayanin komai yadda akai Ya Auri Fatuu saida ta ji yayi shiru sannan ta juyo ta kalle shi still fuskarta a d’aure take tace mashi to miyasa ya kwanta da ita, d’an jimm yay kafin yace mata bada niyya bane shima baisan ya akai ya aikata hakan ba kuma ita kanta lokacin bata san ya aureta, shiru tay tana tunano sak’on data turo mashin a ciki ta bayyana bata san da aure a tsakanin su ba shiyasa ta zubar da cikin hakan yasa Fanan d’in gasgata Maganar ta shi wata zuciyar ta raya mata to amman miyasa zai nuna 6acin rai don ta zubar da cikin, kallon shi tay cike da tuhuma ta tambaye shi kan hakan tace kenan dae yana son Auren, nan ma saida yay d’an jimm kafin yace mata ita kanta ai tasan had’arin dake tattare da zubar da ciki hakan ne yasa bayan ta sanar dashi game da cikin tace zata zubar ya hanata gudun kada wani abu ya faru amman sai tak’i jin Maganar shi taje ta aikata sai gashi abunda ya gudan har kwanciya tayi Asibiti dalilin hakan, ji tay ta yarda da zancen shi hakan yasa ta d’an saki fuska tace mashi to tunda don taimako ya aureta ai sai ya saketa ko, ce mata yay Hajiya ta hana yanzu haka tasa an Kawo Zarah d’in part d’in shi, wani kalan d’aure Fuska tayi tace tunda shine mai zama da ita kuma bai so don me za’ai mashi dole, ce mashi tay ita gaskiya bazata zauna da Zarah matsayin kishiya ba in dai basu rabu ba to ita ta hak’ura da auren kuma yaci Amanarta, jin yayi shiru yasa tace mashi kawai ya tura mata sakin kaman yadda ta turo mashi sak’on, sai da ya nisa sannan ya d’an girgiza mata kai yace tunda Hajiya bata so bazai iya yin hakan ba tasan yadda take a wurin su, hakan ya k’ara 6ata mata rai tana d’an huci tay shiru tana d’an kallon gefe can ta jinjina kai ta kalle shi tace mashi suje Nigeria d’in tare ita zata ma Hajiya Magana shiru yay kawae yana kallonta ganin haka yasa da alamun zargi tace kodai dama shima yana son ta, d’an guntun murmushi yay yace mata kawai bai son a samu matsala ne dalilin hakan cike da tabbaci tace mashi ba wata matsalar da za’a samu tasan Hajiya zata goyi bayan abunda take so tunda dai duk basu son Auren, jinjina mata kai yay yace Shikenan ta tambayi yaushe zasu tafi yace nan da 2 weeks da sauri ta girgiza mashi kai tace mashi gaskiya yayi tsawo cikin satin nan zasu je yace Shikenan, sai gashi ta saki ranta harda d’an murmushi ta fad’a jikin shi cike da shagwaba take cewa an kusa asa zuciyarta tayi bursting yanzu haka da bai cire mata bak’in cikin da take ji ba tasan da wuya bata samu Heart attack ba, shidai murmushi kawai yake can ya d’agata yace suje tayi breakfast tace ya fara mata wanka bata jin dad’in jikinta, bayan an yo wankan ya taimaka mata ta shirya sannan suka fita don yin Breakfast, sai gashi ta sake sosae kamar ba ita ba suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba.
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.