Hausa novels

Halysaah Page 89 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 89…Khaleesat ta kallesa ta langwabar da kai tace “I don’t have the number, ban san waye ba….” Jay yace “Let me see it” Daukar wayar tayi ta mika masa ya amsa yana kallon screen din, after some seconds ya mayar mata da wayar ta karba tace “Kilan ‘yan can unguwan mu Mariri ne, daxu ma wata ta kirani za su zo nan wai Aunty Sha’awa ta bata number na” Jay yace “Ohk, but ya kamata a samu Gate Man for security” Khaleesat tayi murmushi kamar zata ce masa ai Nenne ce ke ajiye kujera ta zauna baƙin gate din tun sassafe amma kawai ta fasa, Jay ya shafa kansa yace “I will take my leave now Halysaah, ki ce ma su Kaka na tafi….” Khaleesat tace “Za ku yi celebrating birthday din Ya Junaid ne? Ko ba ya celebrating?” Jay ya ɗan kalleta yace “Ai ban san ko yace maki yana Celebrating ba” Khaleesat tayi dariya tace “A’a ni ban ma yi wishing dinsa Happy Birthday din ba ai, ko nayi bazai kulani ba ma nasani, kai yaushe ne naka Birthday din?” calmly yace “Rana daya da na Halysaah” Tayi murmushi tace “Uhmm… ai shikenan tunda baza ka gaya min ba” Shi ma murmushin yayi yace “Lokaci na wucewa bari in tafi” Tayi kasa da murya tace “Kasan me?” Yana kallonta yace “A’a sai kin fada” Tace “Promise me you will listen to me” Shiru yayi yana kallonta, can yace “To me zai hana Halysaah?” Tace “A’a ni dai kayi alkawarin zaka zauna kaji duk abinda zan ce har karshe” Cikin few seconds ya fara nazarin meye zata fada masa haka amma ya kasa ganowa, Yana kallonta with much interest yace “Ina jin ki Halysaah, meye kike tunanin zaki gaya min da bazan tsaya in saurare ki ba?” Sauke idonta tayi a hankali tace “I just want to solemnly appreciate you for everything you’ve done to me and my parent so far, I know words will never be enough to express all my gratitude… Words will definitely fail me but I believe you are a God sent angel to I and my family and I appreciate the very day I met you in my life….” Tun da ta fara yake wani kallonta, cikin sanyin murya tace “And I also want to appreciate Ya Junaid too, duk da nasan he won’t give me a listening ear, Amma Nagode da duk abubuwan da yayi min shi ma, Allah ya saka masa da alkhairi…” Mikewa Jay yayi, Khaleesat ta kallesa ta hade rai tace “You promise to listen till the end fa” Ya ɗan yi murmushi yace “You are wasting my time Halysaah, ta shi ki rakani, keep ur words for another day” Ta ɓata fuska ta mike tana kallonsa, A hankali yace “To yi hakuri, za mu ci gaba ta waya” Ita dai tayi shiru bata ce komai, ya fara tafiya yace “Ko in tafi baza ki rakani ba” Tana tafiya a hankali ta bi bayansa, suna isowa gate ta zaro ido tace “Nayi mantuwa, i am coming plss” Daga haka ta juya da sauri ta koma cikin gidan, shi dai ya fita daga gate din ya karasa gun motarsu ya samu Ajay zaune yana jiransa a gaban motar, front seat din ya bude Ajay ya hade rai yace “Thanks for wasting my time” Jay ya ciro wayarsa a aljihu jin ana kiransa, yana dubawa yaga Mami ce, daxu ma ta kirasa bai samu ya daga ba, komawa bayan motar yayi ya jingina jiki yayi picking call dinta ya kai wayar kunne, Khaleesat ta fito daga gate din gidan ta nufi gun motar ganin Ajay kadai zaune a front seat ta fara dube duben inda zata ga Jay, can ta hangosa tsaye yana waya, kallon Ajay tayi taga far end of the street yake kallo kamar ma bai san tana tsaye wajen ba, abinda ke hannunta ta ajiye masa a gefensa tace “I got you this for ur Birthday, Allah ya karo shekaru masu albarka” Ya kalli package din da ta ajiye masa, sai ga Nenne ta fito daga cikin gida da sauri tana gyara yafin gyalenta, karasowa gun motar tayi cikin hanzari tana cewa “Na fito parlor naga wayam ba kowa, nace kaddai tafiya kayi yarinyar nan bata sanar mana ba, ga Parida can ta ɗora maka koren shinkafar nan da ake yi da hanta da karas, don Allah ka tsaya ka ci abinci tukun ko kuma a juye maka a Cooler ka tafi da shi” Tana ganin Ajay ta saki baki tana kallonsa, sauke kansa yayi ya sauko daga motar ya gaisheta kansa a kasa, a hankali tace “Lafiya lau ɗan nan, ashe dama tare ku ke, me ya hanaka shigowa, ko da yake naga baka da sakewa kai kamar sa, kowa da irin halittarsa dama, Malam Ali ma haka yake bai sakewa in bai saba da mutane ba” Shi dai sai murmushi yake wanda iyakarsa lips, sai ga Jay ya zagayo don saboda muryar Nenne ne ma yasa yayi ma Mami sallama har ta fara tambayarsa muryar wace tsohuwa ce take ji haka, Nenne tace “Wallahi bata ce mana zaka tafi ba Ahamad, ga kuma girki can ana maku kai da ɗan uwanka” Khaleesat ta hade rai tana kallon Nenne, can ta daga ma Jay hannu shi dai ya bi ta da ido har ta wuce cikin gidan, duk tunaninsa da ta ce masa tana zuwa kiran Nennen taje yi, sai da Nenne ta ɓata masu kusan minti goma tsaye a wajen tana zuba sannan daga karshe suka samu suka bar unguwan tana daga masu hannu… Lokaci Lokaci Ajay ke kallon abinda Khaleesat ta ajiye masa har suka isa gida, Jay ko kula da package din bai yi ba, sai bayan da yayi parking ya kashe motar yayi ido hudu da package din ya dauka yana kallo yace “Where did you get this Ajay?” Ajay dai kallonsa yake, kamar bazai ce komai ba sai kuma yace “Oho yanda ka gansa nima haka na gansa a wajen” Jay ya wani kallesa ganin raina masa hankali zai yi, bude package din that is wrapped neatly and beautifully ya fara yi, har sai da ya bude gaba daya, Ajay dai sai kallon Box din hannun Jay yake, Jay ya bude box din ya ci karo da designer perfumes biyu wanda kudinsu zai yi 200k each ko ya kusa, making almost 400k kenan, ya kalli Ajay da shima kallon turarurrukan yake, Jay ya ciro wrist watch shi ma me shegen tsada dake cikin box din, iya abinda ke cikin package din kenan sai Birthday card from a friend, ya kalli Ajay yace “Tell me how you got this? Ko dai Paul ne ya ajiye a motar daxu kafin mu fita?” Ajay ya bude hannu alamar shi ma bai sani ba, Paul worker din gidansu ne na nan kano, shi ke kula da gidan ko akwai mutane ko babu, sosai suke jin dadin mu’amala da Paul, shi ma kuma haka yake ji da su saboda kyautatawar da suke masa, ya kuma rike amana sosai ba kadan ba, Jay let out a grin yana jujjuya Birthday card din hannunsa yace “But you are his boss not his friend….” Sai kuma yayi murmushi yace “This is soo thoughtful of Paul, few months back ba ka basa kudi masu yawa ba, yana da hankali sosai ai” Gently Jay ya bude turarurrukan duk ya fesa daya bayan daya to perceive the scent, ya lumshe ido don kamshin sun tafi da shi, yace “This is waow” Lokaci daya kamshi ya cika motar gaba daya, Shi dai Ajay bai ce komai ba ya bude motar ya sauka, Jay ya maida duk gifts din cikin box sannan ya fito daga motar yana rike da su ya kulle motar, suka nufi cikin gidan…. Karfe tara saura Ajay ya dau laptop dinsa da waya zai wuce daki yana kallon Jay da Cousin Bro dinsu Mukhtar yace “Good night” Sannan ya wuce dakinsa, kulle dakin yayi da makulli ya ajiye laptop dinsa ya zauna gefen gado yayi dialing number Khaleesat, Khaleesat na zaune tare da Nenne a dakin da Nenne ta zabar ma kanta a gidan, Islam ta shigo da wayar Khaleesat a hannunta ta mika mata tace “Aunty ana kiran ki” Amsan wayar tayi tana duba me kiranta ganin Ajay ne ta mike don dama ta gaji da zancen da Nenne ke mata, fita tayi daga dakin tayi picking call din ta kai kunne tace “Good evening” Yace “Ke… Ni na aikeki ki siya min Birthday present? Who sent you message? A ina kika samu wannan kudin da kika siyo turaren nan?” Khaleesat dake ta sauraronsa ta kyabe baki tace “For once kayi acting like how every other person will do, kawai godiya zaka min for getting u a present and Birthday card, shikenan….” Yace “To bana so, zan kuma bada a maida maki kayanki” Ɗan murmushi tayi tace “Ka maido min da kudin dai….” Katse wayar taji yayi, ta taɓe baki, dama tasan he will never change kuma ko kadan bata ji haushin abinda yayi mata ba, in ma bai yi bane zata yi mamaki, although she sees him as the senior brother she never had, shi yasa bata jin haushinsa ko kadan, ko barin wajen da take tsaye bata yi ba sai ga Alert din 1M ya shigo wayarta, dakinta ta tafi ta zauna ta dinga dariya kamar taɓaɓɓa, wato har da riba ya kara mata a kai, kamar ta kirasa tace saura Birthday Card din yaushe za a maido mata kawai dai ta kyalesa ta bar wayar a daki ta fita parlor, yaran Mama Shatu ne zaune kasan tiles din parlon suna kallo tunda Nenne ta hanasu zama kan Carpet wai kar yayi datti, Nenne ta fito dakinta tace “Ace har karfe tara Ali yaki shigowa gidan nan, yana can zaune kofar gida kan benchi wani ba sai yace Mai gadi bane” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba don tun dawowarsu gidan har yanxu fa Babanta dari dari yake, yaki sakin jiki da gidan, in yana unguwan to a kofar gida zaka samesa zaune kan Benchi da ya sa kafinta ya buga masa, Nenne tace “Wannan ai salon ya ja mana kallon raini ne a unguwan nan, sai ya nuna ma kowa talakawa ne mu kyauta aka bamu gidan nan sannan hankalinsa zai kwanta, kwata kwata yaki sakin jiki yayi kamar shi ne Mai gidan da ya gina gidan” Khaleesat ta koma daki ta dau mayafinta ta fita compound, ita kanta she is feeling somehow yanda Babanta yaki zama comfortable a gidan, da alama babu yanda ya iya da mahaifiyarsa ne yasa ma yake gidan nan, one thing about her father is bai yarda mutum yayi maka gagarumin kyauta babu wani dalili me karfi ba, shi yasa har yau bai sake yayi na’am da gidan ba, don yace bai san dalilin siyan gidan ba, kamar kullum yana zaune kan Benchi da karamar wayarsa da yake kunna Radio yana saurare ga carbi a hannunsa yana ja, ya juya jin an bude gate, Khaleesat ta karasa ta zauna daga gefensa tana kallonsa tace “Baba bbu sauro a nan kuwa?” Malam Ali yace “Ai shi yasa na saka Safata Jiddah, sauro kam ai ba a rasa su a ko ina” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Amma Baba me yasa baka son ka dinga shiga ciki sai dai kawai ka shiga idan dare yayi sosai, da sassafe kuma ka fita kasuwa” Malam Ali yayi murmushi yace “To ai zaman gida na mata ne Jiddah, ni yaushe zan ta zama a cikin gida tare da mata” Sauke idonta tayi cikin sanyin murya tace “Baba ka kwantar da hankalinka plss, tsakaninsa da Allah ya bamu gidan nan ba don wata manufa ba, trust me pls” Malam Ali yayi wani murmushin ya jinjina kai yace “Ke yarinya ce har yanxu Jiddah, haka kawai babu wani dalilinsa bazai siya mana wannan gida me tsada da komai na more rayuwa a ciki ba, babu yanda na iya da Baabata ne amma wannan gida ba gidan da za mu saki jiki a cikinsa bane mu zauna don komai zai iya faruwa in ma yanxu in ma nan gaba, shi yasa ma nayi amfani da wannan dama wajen fara gyaran gidanmu da muka baro a Mariri tunda babu kowa ciki, yanxu haka har an fara plaster a kasa, kuma duk za a canza zinc din gidan da Ceiling, sannan a kara girman window din dakunan, a fitar da inda ruwa zai dinga fita ya dena taruwa cikin gidan, duk abokaina na can ni bance masu gida aka siya min ba, na dai ce an bani gida in zauna har zuwa sanda zan gama gyara nawa gidan na Mariri” Khaleesat ta kasa cewa komai, amma duk jikinta yayi sanyi sosai, tasan bata da wani kalman da zata sake using wajen convincing Babanta, don his belief will be his belief, ita dai tasan daga ɓangaren Housemate dinta baza a taɓa samun matsala akan gidan nan ba balle tuni ya basu takardun gidan da komai, wasu motoci uku ne suka shigo layin a jere, Malam Ali da Khaleesat suka juya suna kallon motocin da suka dallaro masu hasken fitila, amma lokaci daya duk aka kashe fitilun motar masu haske wanda da alama saboda su aka yi hakan, haka kawai Khaleesat taji gabanta na faduwa barin da taga motocin all halted at the same time a kusa kusa da su, Malam Ali dai ya gyara zama har sannan yana kallon motocin shi ma, after almost 2 minute da tsayuwar motocin, motar dake gaba wani ya bude ya sauko daga front seat da alama dai Security ne, ya bude back seat wanda ke bayan motar ma ya sauko, Malam Ali dai sai kallonsa yake don kara tabbatar da shi din yake gani ko ba shi ba, can ya kalli Khaleesat yace “Tashi ki shiga ciki Jiddah” Gaba daya hankalin Khaleesat ya gama tashi ta girgiza kai tace “A’a baba I will remain here” Guard din mutumin na biye da shi a baya ya nufo Malam Ali da murmushi fuskarsa ya kai masa hannu yace “Assalamu alaikum Alhaji Aliyu” Malam Ali ya mike ya kai masa hannu yana mamakin me kuma ya hadasa da Deputyn garin nan, Khaleesat dai bata ma ganesa ba amma ta mance rabon da ta shiga tashin hankali irin na wannan moment din, me zai kawo su wajen Babanta da daddaren nan da motoci har uku, Deputy ya kalleta yace “Sannu yarinya” Dakewa tayi ta gaishesa ya amsa da fara’a sannan ya maida dubansa kan Malam Ali yace “Idan babu damuwa Alhaji Ali mun zo maka ne akan wani batu me muhimmanci, Allah yasa zaka bamu lokacinka ka saurare mu, in kuma lokacin da za mu dawo zaka saka mana to duk babu damuwa” Malam Ali yace “To ni dai Allah ya sa lafiya ranka shi dade” Deputy yace “Babu komai sai Alkhairi ka kwantar da hankalin ka, ni da abokina ne da sauran manyan mutane muka zo har inda kake muka same ka akan wannan batu da ke tafe da mu, amma sai dai muna baka hakuri mun maka zuwan bazata, and this could be sort of inconvenient…..” Malam Ali ya dake don zuwa yanxu kam ya gama ƙaguwan yaji me kuma ya hadasa da manyan mutane kamar yanda Deputy yace, sannan me ya kawo Deputy da kansa inda yake, a ina ma ya san sa?? Duk da yasan Deputy mutumin kirki ne kuma kowa ya shaida amma fa hankalinsa yaki kwanciya, yana gyada kai cikin karfin hali yace “A’a ba komai ranka shi dade, bari a shimfida tabarma sai mu zauna a nan tsakar gida, hakan yayi ko?” Deputy yace “To babu laifi Alhaji Ali” Malam Ali ya kalli Khaleesat yace “Shiga ciki ki shimfida mana tabarma a compound Jiddah” Mikewa Khaleesat tayi jiki a sanyaye ta shiga cikin gidan don yin abinda Babanta yace tayi….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*07087865788

Back to top button