Matar Hariji Page 24 Romantic Hausa Novel
Zuciya ta aje tace “nidai ka kaini nagansu na roqi gafararsu wlh indai haka haihuwa take abban Fadwah bazan qaraba bazan sake haihuwa ba ni wannan ya isheni don Allah kada kacemin na qara haihuwa kaji?” Numfashi ya sauke yace “kin tsorata da yawa babe ki kwantar da hankalinki ke bakisha wahala bama a sadaka kika samu haihuwarki” saurin katseshi tayi da cewa “au ahakan?” Dariya ta bashi sosai yace “eh mana insha Allahu Ina dawowa zan baki wani babyn kiyi maza ke haifamin dozen guda kinji” qit ta kashe wayarta saboda kalamansa kawai bata Mata zuciya suke.Shigowa Hajiya tayi ita da Alh Alh ya dauki yaron yayi murmushi yace “masha Allahu yaro me kama da babansa Allah ya albarkaceka Muhammad Nurraddeen….” Dagowa tayi da sauri ta kalli Alh yayi murmushi yace “tun kafin Lameer ya tafi yacemin idan kin haihu nayiwa yaron huduba da sunan mahaifinki”Sunkuyar dakai tayi wasu hawayen farin ciki suka zubo Mata ta zame qasa tana hawaye cikin rawar murya tanayi musu gdy Hajiya ta dagata tace “bamu zakiyiwa gdy ba Hauwah tsakaninki da mijinki ne kunfi kusa kuma sakayyar halacci halacci insha Allahu idan ya dawo har dani zamuje mukaiki ki daidaita da mahaifanki aure dai damu da mukaqi dama wadanda sukaso babu wanda ya iya hanashi saboda Allah ya riga yayisa”Suna wannan mgnr Aunty Zulaiha da Aunty Zainab suka shigo suka zauna Suma anata hira dasu itadai bata cewa komai saboda ciwon da cikinta yake danyi Mata ciwo basu ankara ba saida sukaji ta fara kakarin amai sukayo kanta duka.Sabarta Alh yayi yasata a mota Hajiya ta shiga da jaririn sai asibiti suna zuwa sukayi Mata Allurai suka bata wasu magunguna sannan suka juyo gda, sunata zuba mata sannu suna zuwa dama isha tayi aka ciro gadon baby aka sanyashi a ciki aka kwantar dashi itama ta kwanta Hajiya me jika cewa tayi saidai su kwanta a dakinta bazaayi mata nesa da jikanta ba.Fadwah ita ke kusan yini tanawa yaron wasa wata shaquwa ta shiga tsakaninta da jaririn ba kamar Muftahu ba da basa jituwa ko kadan ita kuwa Mubaraka ta koma dangin mahaifinta Jalingo inda Alh ya shiga ya fita Muneef da Hajiya ma basu sani ba aka qullah shirin aurenta da Muneef din.Kwanan Hauwah uku da haihuwa Lameer ya diro cike da shauqi bai bari kowa ya ganshi ba ya shige dakin da lallaba ya sanya hannu zai dauke baben data rungume take feeding nashi tayi sauri qanqame abunta tare da bude idonta, murmushi yayi Mata yace “mata sunyi da rigima ta qare ohhhh Hauwah rikicin ki yawa gareshi kuka wiwi ke banasonki naqi baki baby to yaudai ga babenki dana baki a hannunki”Sunkuyar dakai tayi cike da kunya tana wasa da sumar yaron ta fulanin na gaske wacce ya debo gurin uwarsa amma komansa har fatarsa na ubansa ne hannu yasa ya daukeshi yayi masa addu’a sosai sannan ya rungumeshi a jikinsa yanajin ninkin qaunar yaron da uwarsa na mamayar zuciyarsa.Kwantar dashi yayi ya zuba masa ido kawai yana kallon buwaya ta ubangiji sumar yaronce kadai ta uwarsa amma hatta farcensa irin nasane a hankali yace “Allah daya”Kwantawa yayi a jikinta ya sanya hannunsa ya shafo nononta yace “inason taya babyna shan madara sweet abani” turo baki tayi tace “ni ka tashi ka tafi saura kadan na mutu yaseen da nasan haka haihuwa take da babu abinda zaisa nasaka kayimin ciki”Yanda take mgnr da qumajinta ya bashi nishadi yace “kuma gwarne nakeson kiyi kafin kiyi arba’in na baki wani ko?” Tureshi tayi ya koma gefe yana dariya Hajiya ta shigo yanayin data gansu ya bata kunya sosai har zatayi mgn taji tsoron amsar da lameer zai bata don yafita wauta.Miqewa yayi ya dauki Fadwah ya fita bai jima ba ya dawo dauke da wani babban akwati ya ajiye Mata a gabanta yace ki bude ki gani abinda baiyi miki ba ki ajiyeshi gobe saina canzo miki yanzu nidai kuyimin guri a dakinnan na kwanta bacci nakeji”Hajiya dake fitowa daga bathroom tace “badai dakin nan ba kaje gurin maigadi ku kwana tare tunda ka manta hanyar gdanka, sosa qeyarsa yayi yace “aa ba haka bane Hajiya kawai so nakeyi mu kwanta tare Noor dinmu a tsakiya nasan baccin zaiyimin dadi sosai…” Daquwa tayi masa tare da jifansa da pillon hannunta tace “zaka tashi ka fice mana a daki ko saina Kira Alhajinka yazo ya fitar dakai” miqewa yayi yace “ya zanyi tunda baa qaunata” sunkuyawa yayi daidai fuskar Hauwah yayi kissing nata yace “kin samu daurin gindi lkcnki ne Allah ya kaimu lkcn da Zaki shigo hannuna saina…..”Rufe masa baki tayi da sauri da nata yayi saurin tallafo kanta ita kuma tana qoqarin kwacewa Hajiya ta juyo saida gabanta ya fadi ganin yanda yake wani lumshe ido tayi saurin dauke kanta daga kansu ta fice da baya da baya.Da sauri Hauwah ta tureshi ya kamota yana wani sauke numfashi yace “kinsan Allah kisan yanda zakiyi dani nazama fitinanne nima kullum sai nayi wanka a Texas saboda tunaninki” qwalqwal tayi zatayi masa kuka tace “sai kayi duk yanda zakayi dani kama kasheni ka huta ai dama nasan basona kakeyi ba…” Rufe mata baki yayi cikin dariyarsa yace “haba yarinya nikam ai kowa ma ya shaida Ina qaunarki tun kina qwailarki lkcn da kike tsoron bindira” duka ta fara kai masa ya kauce yana dariya yace “lkcn da akeyi miki adumbuli a bayan….” Toshe kunnenta tayi tace.“Naji naji nace kaje kawai basai kayimin barbada ba” dariya yake sosai ya lakace Mata hanci yace “saida safe amarya ta ki kulamin da kanki kinji” daga masa kai tayi ya shafa kan babynsu yace “wannan shine raba gardama nasan yanzu idan kikaje garinku zasu qara yarda da cewa kowacce qwarya da abokin burminta wlh koda ban matsa nayi amfani da qarfin hukuma an bani keba idan lkcn zuwan Noor duniya yayi sai mun hadu kuma sai yazo kota wanne hali qila da sai anyi asarar rayuka ma akanshi shi daya tak sai a rasa rai sama da goma”Juyawa yayi ya fice tabisa da kallo cikin sanyi jiki tare da zubawa yaron ido ita ba komai yake bata mamaki ba girman yaron amma wai ita ta haifesa a cikinta ya rayu harna watanni tara yanzu gashi yana rayuwa a duniyar da take rayuwa to wai ma ta Ina cikin ya shiga, a Ina yake zama a cikin nata?Matsa cikinta ta farayi itadai bataji wani guri da yayi alamar wannan qaton yaron ya zauna ba, kuka ya fara ta murguda baki tace “yaro inma zakayi shiru gara kayi nagaji sai tsotse nono kakeyi bandama rainin hankali na ubanka Hajiya tace a baka madara yace aa saboda ba jikinsa kake jaba to Nima bazan bayar ba aiba dankai akayimin nonon ba lol Hauwah ananan da hali.Komawa tayi tayi kwanciyarta ta juyawa yaron baya yanata kuka yana neman abinci, Hajiyace taji kukan yayi yawa ta shigo da sauri taga yanda yaron yake neman abinci ta matsa ta daukeshi tace “ni narasa wacce irin yarinya ce ke Hauwah waike yaushe gidadanci zai barki ne yaro sai kuka yakeyi yana neman abinci amma kinajinsa”Turo baki tayi tace “toni Hajiya zafi nakeji wlh idan yanasha kamar lkcn da babansa ya farasha harma yafi haka zafi shifa jaririn nan har cizona yakeyi shikuwa Dadynsu baya cizona”Wani takaici Hajiya ta hadiya tace “to yanzu akira miki mijin naki ki bashi kenan ko?” Sai yanzu ta fahimci wautarta tace “am imm nifa ba haka nake nufi ba Hajiya kawai dai kice ya daina cizona dan yaseen ya qara cizona saina mareshi”Abin dariya yabawa Hajiya yau tana ganin ikon Allah daqyar ma aka samu ta yarda tabawa babyn nono wai ita kunya takeji yana namiji bazai gane Mata nononta ba saida taga ran Alh ya baci sannan ta karba ta bashi tana kuka wai an cuceta tasan sai babe yayi mata fada🤔Itako Hajiya dama ta zama kakarta kowanne shirme ita ake dorawa, cikin kwanaki hudun da suka rage mata tayi kyau sosai binjintar da Lameer yakeyi abin har mamaki yake bawa kowa hatta ankon suna shine yayiwa kowa hadda yan uwanta da yaje ya fada musu haihuwar sukace zasuzo suna.Bai fada Mata ba saboda sanin haukanta hana kowa sakat zatayi musamman yanzu da take a fusace saboda ance saita rinqa bawa danta nono har cewa tayi ai an tsaneta ne don anga bata da kowa.Ana gobe suna da kansa ya tura da mota cikin saa kuwa Baffa bayanan ya maqarfi yakai shanu kasuwa kuma yanayin sati bai dawo ba aikuwa su Inna Jumme su lantana da babbar yayar Hauwah ladiyo da qawarta Lahira suka dungumo suna birni.Wayyohh murna gurin Hauwah taga na gda tama manta da rakinta da takewa mutanen gidan da ance tazo parlour tayi baqi yan barka sai tace ai dinki akayi Mata tana miqewa farkewa zaiyi,Tuni ta take ta rugo a guje ta rungume Inna Jumme tanata dariya sai kuma kuka tana dube dube ganin bata hango kowa ba tace “Inna Ina Goggo da Baffa”



