Uncategorized

Macijine Shi Page 21-22 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 21/22

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

_______________Wata leda Baffa ya ɗauko  ,ledar da ɗan nauyi ,alamun wani abune acikin ta .sannan ya ɗauki wannan rigar ta fattu ya cusa acikin ledar,safin yayi waje ,Abeed ya rufa masa baya.

Ahankali baffa ke takawa Abeed na biye dashi,saɓe da fattu akafaɗarsa,wacce ke cikin matsanancin hali na zazzaɓi,da damuwa.

Tafiya suke cikin sauri bayan sun bar gidan ,cikin ikon Allah basu haɗu da kowa ba ,har sukayi nisa da garin sosai,saida baffa ya fitar dasu kan kwalta kafin ya tsaya .

Har zuwa wannan lokacin fattu na saɓe akan kafaɗar Abeed ,duk da irin uban nisan dake tsakanin rugar da kwalta.

Ahankali Abeed ya sauƙe fattu ya ɗan jingina ta da jikinsa,dan yaga bazata iya tsayuwa ba .

“Malam Abeed karɓi wannan wasu yan kudadene da nake tarawa saboda irin wannan ranar,nasan zasu toshe muku wata kafar,dan Allah ka riƙe min alƙawari, ka kulamin da fattuna,karka bari wani ko wata ya cutar da ita,sannan kayi iyakar ƙoƙarin ka wajen sadata da  magaifanta.

Kaima zaka sami lada”baffa ya faɗa yana kallon bayansa ,hanyar da suka baro ,dan tsoro yake kar yaje ko anbiyosu,dan yasan zuwa yanzu labari ya isa kunnen lamiɗo,tunda gari yayi haske an kusan shiga sallah.

“In Sha Allahu Abba zan kula da amanar ka,na gode da taimakon da kukayimin, sannan zan dawo gareka very soon”Abeed ya faɗa cikin nutsuwarsa da rashin son magana,akwai abubuwan da yake son faɗa amma tsabar rashin son maganarsa bazai iya ba dan haka yayi shiru daga wannan maganar.

Hannun fattu baffa ya kama yariƙe gam-gam cikin nashi,kallon ta yayi yayinda itama take kallonsa cikin kuka wanda muryarta ko fita batayi sosai, shima baffa tuni zuciyarsa ta karaya ,sai hawaye sharrrr!!

“Allah ya shiga lamarin ki fattu, Allah ya karemin ke ka yasa damu da alkairi,ki kula da kanki,ki kama mutuncinsu.Allah yayi miki albarka”baffa ya faɗa cikin kuka sosai,abin tausayi.

“Baffa bana son tafiya ,dan Allah kace na zauna ,Ni nafison zama da kai akan iyayena ma asali,baffa karka tafi ka barni “Fattu ta faɗa cikin kuka harda shashsheka kamar zata shiɗe. Kafin baffa yayi magana saiga wata mota zata wuce ,da alama daga cikin Jos take .

Da sauri baffa yayi musu hannu alamun su tsaya.tambayarsu yayi ina suka nufa ,mai motar yace Kano.

Kallon Adeeb baffa yayi yace “duk da bansan inane Kanon ba amma Gara kubi wannan motar kafin tawagar mai gari su fito nemanku.

Kai kawai Abeed ya ɗada,tare da kamo hannun fattu suka nufi motar,hannunsa ɗaya riƙe da ledar da baffa ya basu.

Kuka fattu take harda ihu tana faɗin”wayyo baffana ,banason tafiya,dan Allah baffa kace na dawo wayyo baffa am wayyo Allah na ,wayyo rayuwata “

Baffa kam ko magana ya kasa tsabar kuka sai daga musu hannu kawai yake yana juya kai.

Abeed ne ya sanyata cikin motar tare da riƙe ta ,ɗan sai ƙoƙarin  fitowa take ,haka mai motar nan yaja motarsa yayi gaba,dan kaya zaije ɗaukowa.

Baffa yana tsaye har saida yaga ɓacewar motar ,sannan ya sauke wani kwauron numfashi yana mai share hawayen idanunsa,”Allah ga amanar ƴata nan  na miƙa lamarin ta ahannunka ,ya ubangiji kazama majiɓancin al’amarinta “baffa ya faɗa yana mai juya dan koma gida ayi wacce za’ayi.

Aikuwa tun kafin ya ƙarasa cikin garin ,ya hango cincirindon mutane aƙofar gidansa,jinjina kai yayi,dan dama yayi tsammanin hakan .

Suna hangoshi sukayo kan suna wllh koya fito da ƴar Shegiyar daya ɗauka matsayin ƴarsa ,da kwarton ta da suka ajiye agida,ko kuma su kashe shi yanzun nan.

Kallonsu yayi cikin kamala da dattako yace “ikon Allah me kuma mukayi dazaku kashemu?wace yarinyar kuke nema?bayan wacce mai gari ya riƙe agurinsa?baffa ya faɗa kai tsaye ba nuna alamun tsoro.

Nan wani lawwali yace masa”ai jiya yarinyar nan saida ta bari dare ya raba sannan ta sami lamiɗo tayi masa jina jina,gaba ɗaya ƙafafunsa sun ƙarye,ga hannun damanshi ma ya ɓalle baral, sannan ta gudu,kuma munsan tabbas tana gidan nan,dan kuwa hansai ta kai labari,

Kuma ta fayyace mana komai game da yarinyar ,ashe Shegiya ce ka tsinto ka kawo gidanka,sannan ka ajiye mata wani gardin suke lalata dashi,dan haka gaba ɗayanku yau sai hukunci ya hau kanku,dan lamiɗo yana nan banda ihu ba abinda yake yana kiran maciji zai kashe shi,fattu ce tayi masa ture.sannan arɗo ma yana can hannunsa guda ya shanye ya zama kamar sillan kara ,kuma duk aikin fattu ne ,dan haka yau wllh saimun kashe fattu”lawwali ya ƙare zancensa yana mai ɗaga sandarsa sama.

“Toh me yasa baku shiga kun duba fattun ba ?idan nan ta dawo,ita wacce ta kai muku rahoton saita faɗa muku inda fattun take”baffa ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa gida.

 

“Ƙarya yake wllh, saidai in ya boyesu ,ko kuma sun gudu ,dama naji yana cewa su gudu dan haka karku taga masa ” na tsinkayo muryar gwogwgo hansai na faɗin haka ,dan taji mugun haushi da ba’a sami su fattu cikin gidan ba.

Aikuwa baffa yana tsaye 

Ba zato ba tsammani yaji sun rufeshi da duka ta ko ina.

Har saida suka kaishi ƙasa.sannan suka taitayeshi sai gurin. Mai gari.suna zuwa suka tarar ana yiwa mai gari ɗori sai ihu yake yana kuka.dan haka can ɗakin hukunci suka jefa baffa,wanda yayi kaishi sosai dan ya daku.

Allah Sarki baffa ,Allah ya saka maka.

Fattu kuwa tsabar kuka har muryarta ta dashe,can jikin ƙarshen motar ta koma tare da haɗe kai da gwuiwa tana kuka marar sauti ,jikinta sai rawa yake ,fuska ta kumbura suntum tayi jajur ,abinka da farar fata.

Abeed yana daga gefe yana kallonta ,sosai yake jin kukanta har cikin ransa,haƙiƙa yarinyar tana fuskantar ƙalubalen rayuwa and she’s to Young to handle the situation.amma ya zatayi?dole ta ɗauki ƙaddara yadda yazo mata.

Kallonta yayi yadda jikinta ke ta rawa tana shashsheƙar kuka,yaso ace ya iya rarrashi, daya rarrasheta ,koba komai itaɗin yanzu amanarsace,amma Gara tayi kuka ,koba komai zata rage jin raɗaɗin da taleji cikin zuciyarta.

Tafiya suke sosai ,Dan drivern gudu yake tsulawa,kasancewar safiya ce hanyar ba motoci sosai,sai jifa-jifa suke cin karo da motocin.

Abeed yayi shiru ,tare da jingina kansa jikin kujerar da yake zaune,ba abinda ke yawo cikin zuciyarsa,sai labarin da baffa ya bashi na cewar wai shiɗin amaciji suka ganshi,to ta yaya?yaushe hakan ta faru,me yasameshi? Tabbas idan har abinda baffa ya faɗa gaskiya ne baya raba ɗayan biyu cewar sharrin Amma ne wannan ,dan ita kaɗai yake tunanin zata iya cutar dashi ,tunda afili take nuna masa ƙiyayya, amma zaibi abin ahankali harya gano mugun ƙullinta akansa kafin ya ɗauki mataki.

Ya rasa me ya tsareta Amma arayuwa sam bata ƙaunarsa ,kullum burinta ta cutar dashi,tun yana ƙarami  yake fuskantar tsangwamarta,har kawo yanzu bata fasa ba ,amma akwai lokacin da ko ance tayi masa wani abun bazata iyaba.

Juyowa yayi ya kalli inda fattu ke zaune ,har zuwa wannan lokacin kuka take ,banda rawa ba abinda jikin ta keyi.wani tausayine yaji ya kama zuciyarsa ,wannan kukan yayi yawa zai iya haifar mata da matsala.dan haka ahankali ya ɗan matsa kusa da ita ,ƙureta yayi da ido ,yana son yayi mata magana amma baisan me zaice mata ba.

Kusan minti uku yayi yana kallonta da yadda jikinta ke rawa sosai,kafin ya sanya hannunsa ahankali ya dafa kanta .

Da sauri fattu ta ɗago kanta agalabaice ,idonta ya mugun kumbura yayi jaaa!sosai lips ɗinta sai sheƙi yake .kallonsa tayi wani sabbin hawayen na kwararowa daga idanunta.

Dan yatsansa ya sanya ya share hawayen dake zuba daga idanunta,amma wasu na ƙara zubowa.

Da gyar ya buɗe bakinsa cikin hausarsa da bata fita sosai yace “menene”ya faɗa yana kallon cikin idanunta ,gabansa sai bugawa yake,ya rasa mai yasa inhar zai sanya idonsa cikin nata ,to gabansa yayi ta bugawa kenan.

Cikin dasashshiyar murya wacce  kuka ne  yasanya ta dashe fattu tace “Baffana” cikin yanayin shagwaba irin na masu kuka tayi maganar.

Wani yummmmmm!!!Adeeb yaji tun daga tsakiyar kansa har babban dan yatsan ƙafarsa.dan yanayin yadda tayi maganar sai yaji wata irin kasala ta kama shi.

Ahankali ya kumshe idanunsa yayi jimmm!kafin ya buɗe su ya ɗora akan fattu”is ok ki daina kuka”ya faɗa ahankali yana mai janyowa zuwa jikinsa ,dan shikam hakan kaɗai yake ganin zai yi mata tayi shiru.

Allah Sarki fattu kuwa tayi luƙus akan faffaɗan ƙirjinsa sai ajiyar zuciya take sauƙewa,kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta fara jin zuciyarta nayi mata sanyi, tana nan kwance ajikinsa barcin wahala yayi gaba da ita.

Shikuwa Adeeb gaba ɗaya jinsa yake wani irin,sam ya kasa samun nutsuwa jinta da yayi cikin jikinsa ,gaba ɗaya yaji yanayinsa na  sauyawa zuwa kasala da jin wani abu mai kama da feeling ,ahankali ya jingina kansa jikin kujerar ,tare da kumshe idanunsa yana mai ƙara gyara mata kwanciyarta. Tunanin  Abie ya fara yi aƙokarinsa na kawar da abinda yake ji acikin jikinsa ,dan aganinsa wannan yarinyar tayi ƙanƙantar da har zai rinƙa jin wani abu akanta,saidai sam jikin nashi yaƙi bashi haɗin kai,dan ji yayi lamarin na ƙara rikice masa,ganin ba sarki sai Allah yasashi cire ta daga jikinsa ya jingina ta da jikin kujerar da suke kai.

Ajiyar zuciya ya sauƙe yana mai kallon kyakyakywar fuskarta ,wacce ta ƙara wani jaaa!sosai ,ahankali ya sauƙe idanunsa zuwa lips ɗinta waɗanda ta ɗan turosu Baga cikin shagwaɓa  kamar kamar yadda yara keyi idan suna son yin kuka.

Haka kawai ya tsinci kansa da sakin wani murmushi mai ƙayatarwa, hannu yasa ya gyara mata hulɗar kanta,wacce ta ɗan zame  har gashinta na gaban goshi yasami damar fitowa .

Bai ankara ba yaji driver na cewa sun iso Kano,kallon garin yake ,yana tunanin inda zasu sami hotel ,dan su ɗan huta sannan ya sai kaya ya cire wannan na jikin nashi,dan sun matuƙar takura masa.

Tambayar drivern yayi nawane kuɗinsa ya faɗa masa ,bashi yayi cikin wanda baffa ya basu da zasu taho, sannan yace wa mai motar dan Allah hotel yake son zuwa .

 

Nan mai motar ya tare musu dan adaidaita yace ya kaisu hotel  mafi kusa. Ganin fattu na barci yasa Adeeb bai tashe ta ba kawai ɗauki ta yayi kamar ƴar tsana ya shiga adaidaita  ya zauna ,sannan itama ya zaunar da ita.kuma ko buɗe ido batayi ba ,dan barcin sosai ya kamata.

Bayan sunje ne ya kama musu ɗaki, sannan ya nufi ɗakin ,har lokacin kuma fattu na rike ahannunsa dan baya don tashi ta daga barci.

Da hannu ɗaya yayi amfani wajen bude dakin sannan ya shiga,kwantar da ita yayi akan gadon  ya lulluɓawa da ƙarin bargon dake kan gadon,sannan ya ɗan zauna shima yana mai lumshe idonsa ,gaba ɗaya agajiye yake  jinsa , dan bai saba irin wannan tafiyar haka ba.

Fita yayi ya siyo musu kaya a store ɗin cikin hotel ɗin sannan yayi musu odar abinci  ya dawo,fattu nata barci taji laushin gado da katifa ga ƙaton bargo .lol

Tashi yayi ya shiga bayi yayi wanka,ya faɗa sosai kafin ya fito,agurguje ya sanya kayan daya siyo ,riga da wando ne na jins  da boxers and singlet, sai turare ,sannan yayi sallar asuba.

Masha Allah duk da bayani shiri yayi ba ,amma karkuso kuga irin kyan da  Adeeb yayi ,sosai ya ƙara zama cikakken Balarabe  mai tsananin kyau,sai ƙamshi yake zubawa.

Kwankwasa ƙofar dakin  akayi,     ahankali ya tashi yaje ya buɗe ,abincin da yayi odar ne aka kawo,kaɓar yayi ya dawo ciki.

Kallonta yayi yaga bata tashi ba ,dan haka ya zauna yana cin abincinsa.kaɗan yaci ya tashi  ,da alama bashi da yawan cin abinci sosai.

Gadon da fattu ke kwance ya nufa ,ahankali ya ɗan yaye bargon daya rufa mata,hannunsa yasanya saman goshinta,har lokacin jikinta da zafi sosai.

Filin da take kai ya ɗan bubbuga sau uku, ahankali ta buɗe idonta tana mai turo baki ,sai kuma tayi saurin tashi tana ƙarewa ɗakin kallo ,wai aljanar duniya  nan ɗin shine gidansu hamma Adeeb ?lallai yan gayune su,ji laushin gado kamar auduga.fattu ta faɗa cikin zuciyarta tana mai ƙarewa dakin kallo.

 

Ji  dan Allah yadda take ta wani kallon daki kamar bata taɓa ganin daki ba “Adeeb ya faɗa cikin zuciyarsa yana ɗan kallonta.

“Go and get your shower” Adeeb ya faɗa ahankali yana mai kawar da kansa .

Kallonsa take ƙuri tana rarraba ido,dan bata fahimci me yake cewa ba.

Jin bata tashiba yasa shi dan juyowa yana kallonta.

“Ɗan harararta yayi kafin yace ” nace kije kiyi wanka ne”ya faɗa fuskarsa aɗaure ba walwala.

Tashi fattu tayi sumi-sumi ta nufi hanyar fita ,tana zuwa bakin ƙifar taja ta tsaya tare da juyowa yana kallonsa.

Shima kallonta yake cike da jin haushi ko ina zata kuma?nace take tayi wanka.

Ganin irin kallon da yake mata ne yasa tace “bazan iya budewa ba”ahankali tayi maganar cikin dasashshiyar muryarta kanta aƙasa.

Harararta yayi cike da jin haushin wai yaje bakin ƙofar fita, kuma tana faɗin bazata iya buɗewa,sai kace nan ne toilet ɗin.

Tashi yayi ya nufi bakin ƙofar toilet ɗin ya buɗe sannan ya juyo yana kallonta.

Shiru tayi itama tana ɗan kallon nasa,dan bata gane nufinsa ba.

Wata iska ya furzar mai zafi yana lunshe idonsa,kafin yace “zo kishiga “ya faɗa yana kallonta ,fuskarsa sam ba walwala,shi wllh ya gaji da wannan shirmen nata fa.

Kanta adurƙushe tazo  ta shige toilet ɗin , kayan daya siyo mata ya ɗauki tare da ɗan kwankwasa toilet ɗin ya buɗe kadan yace “take”

Fattu kuwa da tun shigar ta toilet ɗin ta saki baki galala tana kallon ikon Allah,anya kuwa yasan inda ya buɗe mata yace tazo tayi wanka?yo wannan ai Dakin kwanan ne,kalli da harda wani ƙaton  gado mai rami,to ma ta a ina zataga ruwan bare har tayi wankan?

Juyowa tayi tana kallon farin hannunsa daya miƙo mata leda.ƙarasawa tayi kusa dashi ta karɓi ledar sannan tayi saurin cewa “inane banɗakin?

“What ” ya faɗa yana mai buɗe kofar gaba ɗaya ,sannan ya kalli fattun ko fara wankan ma batayi ba.

Cikin faɗa -faɗa  yace “do you expect me to West my time here?Ina jiranki?”ya faɗa yana zaro mata manyan fararen dara-daran idanunsa.

Nan da nan jikin fattu ya kama rawa ,tsoro ya kamata ,har kayan hannunsa saida suka faɗi  ƙasa” duk da batasan me yake cewa ba ,tabbas ta san faɗane yake mata ,cikin muryar kuka tace”dan Allah hamma kayi haƙuri bansan a inda zabga ruwan ba”ta faɗa tare da fashewa da kuka tana mai toshe bakinta.

Shiru yayi yana kallonsa,lokaci guda kuma tausayi ta ya kamashi, sai yanzu ya tuna daga inda ya taho da ita,ba abin mamaki bane idan tace bata san ya zata yi ba.dan haka cikin sanyin murya yace “is ok daina kuka “ya fadi yana mai ƙarara shigowa toilet ɗin.

Idan kina son yin  wanka nan zaki danna ruwa zai zubo, sannan idan kina biyan buƙata nan zaki zauna ,In kin gama saiki dannan nan ,wannan na wanke bakine  and ga  soso da soap kin gane “ya faɗa yana kallonta .

Kai ta ɗaga masa  alamun ta gane ,

Hanyar waje ya nufa sannan ya juyo yace mata “kiyi sauri yanzu zamu wuce”yana faɗin haka yayi waje.

Zama yayi abakin gadon yana mai dafe kansa,ciwo yaji kansa nayi , sakamakon wannan doguwar maganar da yayi, gaskiya kula da yara akwai wahala ,ji yadda tasa masa ciwon kai rana ɗaya kawai.

Fattu kuwa bayan ta cire kayanta na gado ,wato rigar fulaninta ƴar dingila da zanin ta ,kai tsaye  gurin soso da sabulun nan ta nufa ta ɗauka sanna tazo ta tsaya saitin gurin da akace idan ta danna ruwa zai zo ,dannawa tayi tana jiran taga ta ina ruwan zai zubo,ai ba zato ba tsammani kawai taji ruwa akanta shaaaaaa!!!

Wata zabura da fattu tayi tare da watsar da  soso da sabulun nan ta kurma uban ihu iya ƙarfinta ta nufi kofar fita ba komai ajikinta “wayyo Allah na hamma wayyo kazo ka buɗe ni na shiga uku dakin yan shan jini ka kawoni ana min ruwan jini akaina wayyo hamma am” abinda fattu ke faɗa kenan cikin rikicewar da tashin hankali gaba ɗaya jikinta rawa yake kamar ɗan mazari.

Adeeb na kwance a gefen gado yayi nisa cikin tunani kawai ya biyo ihunta  ,ai baisan lokacin daya zabura da mugun sauri yayi toilet ɗin ba,yana zuwa ya buɗe kofar da da sauri ya danna kansa ciki.

Kicibis sukayi da fattu abakin ƙofar, tayo gunsa ga gudu tana kuka.

Wani irin bugawa ƙirjin  Adeeb yayi kansa ya hau juyawa ,sakamakon ganin da yayiwa fattu haka zirr ɗin ta ba kaya.tunda yake arayuwarsa yau ya taɓa ganin mace data fara girma haka ba kaya agabansa. Cikin hanzari ya juya bayansa yana mai dafe ƙirjinsa dake barazanar fashewa.”innalillahi “ya faɗa cikin sassarfa  lokacin dayaji fattu ta kankameshi tana kuka.

“Sosai shima jikinsa ya hau rawa kamar ɗan mazari,cikin rawar murya yake faɗin”le..a…ve. me… Lea….ve… M….e” yana kasa nutsuwa yayi mata magana.

Fattu kuwa banda rawa ba abinda jikinta keyi,wannan wace irin masifa ce haka?wane irin gida ya kawota ,za’a cinyeta ya sama.

Runtse idanun Adeeb. Yayi da mugun ƙarfi yana ambaton sunan Allah ,ya ɗauki kusan minti biyu cikin halin ruɗewa da rawar jiki.gaba ɗaya jikinsa yayi wani iri,kafin yayi ƙarfin halin sanya hannunsa dake rawa ya fizgota daga bayansa tare da tureta can gefe guda,yana mai sauƙe numfashi cikin sauri ,kawar da kansa yayi daga gareta yana mai cewa”kisa zani ki rufe jikinki Please.

Fattu kuwa cikin rawar jiki ta ƙara matsowa gareshi sam tama manta da batun wasu kaya,”dan Allah ka fitar dani daga ,Ni gurin baffana zani “ta faɗa cikin kuka.

“Kisa zani nace miki”ya daka mata tsawar data ƙara hargitsata.tsugunnawa tayi tare da ƙanƙame jikinta tana kuka.

“Ni ka kaink gurin baffana dan Allah ka maidani gurin baffa “abinda take daɗi kenan cikin kuka da rawar jiki ,gaba ɗaya ta gama tsorata .

Zanin nata Adeeb yaje ya yayumo  cikin lalube,dan ko gani batayi sosai .yana zuwa ya lulluɓa mata sannan,ya fice daga bayin, da gyar ya iya ƙarasawa kan gadon yana zuwa ya faɗa kan gadon tare da duƙunƙune jikinsa yana rawar sanyi ……

Masu karatu mutara next oage.

Ina ganin comments ɗinku masoya ta ko ina ,ina matukar jin daɗi da ƙaunarku ga wannan novel ɗin .

Na gode sosai Allah ya bar ƙauna ,

And I love you  guys where ever  you are🥰🥰🥰🥰

Anty mammy ce 

Mrs babi💘💘

Domin samun littafin daga Farko sai ku taɓa bulun rubutun dake ƙasa 👇🏻👇🏻👇🏻

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/macijine-shi-complete-novel.html

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Back to top button