Harijin Sarki Page 28 Romantic Hausa Novel
*Duhu da Gaskiyar Ruhi*Ranar ta waye da iska mai sanyi. Gajimare suka lullube sararin Fes, kamar rana ma ta ƙi haskakawa saboda irin damuwar da ke tsakanin Samha da Sarki Rashid.Tun daga safiya, Sultan ya kasa zama. Kowane numfashi da yake ja, yana jin kamar an ɗaura masa kaya mai nauyi a zuciya.Ya zauna a ofishinsa, idonsa a kan takardu, amma zuciyarsa tana kiran suna ɗaya: Samha.“Me yasa kike guduna, Samha? Me yasa kina neman nisantar wutar da ke zafin da ni kaɗai zan iya jurewa?”A lokacin da yake cikin wannan tunanin, Al-Azraq, babban mai tsaron sarautarsa kuma amintacce a cikin al’amuran sirri, ya shigo.“Mai Martaba, alamar hatimi ta fara motsi jiya da daddare,” ya faɗa da muryar da ke ɗauke da tsoro.“Hasken ja ya bayyana a cikin hasumiyar gabas, kuma ma’abota tsafin tsofaffi suna tambayar me yake faruwa.”Sultan Rashid ya ɗaga kai a hankali, idanunsa suka yi ja kamar wanda baiyi bacci ba.“Ba su bukatar sani. Wannan al’amari na zuciya ne, ba na sarauta ba.”Sai dai a zuciyarsa ya san duk lokacin da soyayyarsa da Samha ta rikice, hatimin sarauta yana motsi.Soyayyarsu bata tsaya ga zuciya ba tana haɗe da asalin jinin da yake ɗauke da ikon masarauta.gefe guda, Samha tana zaune a dakin Granny. Fuskar ta rame, amma idanunta sun cika da natsuwa ta daban irin ta mace da ta yanke hukunci take jiran rabuwa da tsammani.“Granny” ta ce da muryar da ke cike da tsoro amma da karsashi “zuciyata ba ta samun natsuwa muddin ina kusa da shi. Duk lokacin da ya kusanto, jikina yana amsa kamar wani abu na neman tashi a cikina. Wannan ba soyayya bace tsafi ne na gani a cikin baccina kamar yanda Mahaifiyata take burin sarrafa ruhina da ƙarfin sihiri shima yana ƙoƙarin hakan meye yasa yake ɓoyemin abinda ya shafi rayuwata kuma kike tayashi?” Granny ta kama hannunta.“To idan haka ne, me kike shirin yi?” kawar da kanta tayi tace “Zan fuskance shi. Zan gaya masa gaskiya da bakina. Idan kuwa hakan zai haifar da sabani, to zan yarda. Amma bana son ci gaba da zama cikin duhu” Da yamma Rana ta fara faɗuwa, launin ƙasa ya gauraya da launin ja.A wannan lokacin ne Rashid ya dawo gidan da zuciyarsa ta ɗauki alƙawari ɗaya zai nemi ta har sai ta fahimci cewa soyayyarsu ta fi duhu ƙarfi.Yana shiga gidan, iska ta buso mai ɗauke da ƙamshin za’afaran da yake da alaƙa da ita.Ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya shiga ɗakinta Ta ji motsin ƙafafunsa ta juyo, amma bata yi magana ba.Shi ma bai ce komai ba, sai ya tsaya yana kallonta Wani lokaci mai tsawo ya shuɗe kafin ya yi magana cikin muryar da ta yi rauni:“Kin tsane ni, Samha?”Ta ɗago idanunta, ta kalle shi kai tsaye tace “A’a, ban tsaneka ba. Amma ina tsoronka. Ina tsoron abin da ke tare da kai.”Wani irin sanyi ya ratsa jikin Rashid yace “Abin da ke tare da ni?” ya maimaita cikin mamakiTa matso kaɗan, tana kallonsa kai tsaye.“Na san kai sarki ne, amma na kuma san cewa ba dukkan ikonka daga Allah yake ba. Akwai wani abu da ke ƙarƙashin wannan sarauta, wanda kake ɓoyewa.” Shiru ya biyo bayan kalamanta.Rashid ya juya ya nufi gefen taga, ya rike labulen yana kallon waje.“Kin san me yasa babu sarki da ya rayu a cikin wannan sarauta sama da shekaru sittin?” ya tambaye ta a hankali. Sannan ya ɗora da cewa“Saboda hatimin nan da kike gani a ƙirjina. Shi ne wutar masarauta. Kuma wutar nan ba ta yin aiki sai idan zuciyar sarki ta shiga soyayya ta gaskiya.”Ya juyo, idanunsa suka haɗu da nata.“A lokacin da na fara ganinki, hatimin nan ya motsa. Kece kika kunna wutar. Ke ce ginshiƙin rayuwata.”Ta girgiza kai, idonta cike da hawaye.“To me yasa kake amfani da tsafi? Me yasa baka bar ikon Allah shi kaɗai ba?”Rashid ya ɗan lumshe ido “Ba ni ne na zaɓa ba. Tsafin nan ba ikon son zuciyata ba ne. Ya gaji jinin masarauta. A duk lokacin da aka haifi sarkin Zirkan, ana ɗaura masa alaka da duhu domin ya kare masarautarsa. Amma tun da ke kika shiga rayuwata, wannan duhu ya fara lalacewa” Ta tsaya, zuciyarta na bugawa. “To me yasa baka bari ya lalace gaba ɗaya ba?”Ya matso kusa, idanunsa sun ɗauki wani irin haske haɗin zafi, tausayi, da iko.“Saboda idan wutar nan ta mutu gaba ɗaya, ni ma zan mutu da ita.”Hawayenta suka zubo, amma ta kasa magana.Ya matso ya kama hannunta, ya ɗora bisa kirjinsa.“Kina ji? Wannan wutar da ke bugu a jikina ke ce kike rayar da ita. Ke ce haske, Samha.”Ta ɗago idanunta da suka cika da hawaye tace “Idan kuwa ni ce haske, to bari in ƙone duhun da ke tare da kai”Rashid ya lumshe ido, ya saki hannunta a hankali. A lokacin da ya buɗe idanunsa, hasken hatimi cikinsa ya fara walƙiya da launin red da goldA wajen iska ta tashi da ƙarfi, fitilu suka fara karyewa ɗaya bayan ɗaya alamar cewa duhu da haske sun fara haɗuwa a karo na farko” Bayani ya zauna yi mata da ita da kanta ta fahimci tabbas rabuwa da Sultan bazai zama maslahar rayuwarsu ba, ƙaddara tariga tayi musu maɗauri guda wanda faɗan raba ƙaddara yafi yaƙi da ƙarfin ikon tsafi, da wannan ta dafa cikinta ɗan dake cikinta me watanni huɗu kenan idan tabar Mahaifinsa zai taso tsakanin duhu da haske kenan, zai tashi a makamciyar rayuwarta, da wannan taji ya ɗora bakinsa bisa wuyanta cikin kasalar firuci yace “kiji tausayina ke ɗin haske ce ga rayuwata don Allah Samha kowa ta bar miki gidanki dani dake kaɗai zamu rayuwa”……..




