Uncategorized

Ni Na Raine Ta Complete Hausa Novel

 

Bismillahi rahamanir raheem

“Wannan kwalliyar ai dole ki kasance ke kaɗai a wajen Abba, wallahi Amma kin yi kyau” cewar Tasleem tana kashe min ido ɗaya cikin dariyar shaƙiyanci, na rarumi pillown da ke kan kujera na jefa mata cikin dariya na ce “ja’ira mara kunyar yarinya” na shige hanyar da za ta sada ni da sashen Alhaji cikin takuna ɗagwas ɗagwas kamar budurwa, bakina ɗauke da sallama na tura ƙofar ɗakinsa, ban same shi a ciki ba sai dai na ji alamar shower da ke kunne wanda hakan ya tabbatar min yana banɗaki ne. Duk da komai na ɗakin yana nan tsaf da shi bai hana ni miƙewa ba na ƙara ƙalƙale wajen tare da jona burner na ƙara turaren wuta, gudun AC na ƙara sannan na nufi gado, hannuna na miƙa na ɗauki wayarsa da ke kan gadon na latsa don duba lokaci, Alhaji da ya fito daga wanka ya yi hanzarin isowa gareni ya amshi wayarsa ya ce “wai ba ni da halin ajiye waya sai kin taɓa Hadiza?” 

Na taɓe baki na ce “lokaci na duba” ban kawo komai a raina ba duk da password ɗin da ya maƙala wa wayar tasa da bai taɓa sawa ba tsayin lokacin da muka ɗauka tare, sama da shekara ashirin a inuwar aure.

Abinci na gabatar masa marar nauyi ya tsakuri abin da zai tsakura ya miƙe yana faɗin “wallahi cikina a cunkushe yake,ɗan sa Inya ta dafa min shayi” 

“Bari na dafa maka, Inya yanzu ai ina jin karatu take yi” na ce ina miƙewa.

“A’a Hajiyata kira ta a waya ki ce ta dafa min shayi ta kawo min, ke zauna a nan na kalli wannan kwalliyar da aka yi min na more” ya ce yana ɗaga min gira. Na yi murmushi na ce “an gama ranka ya daɗe” na ɗaga waya na saka Inya ta dafa shayin ta kawo min. Na juya ga Alhaji ina jin daɗin yadda soyayyarmu har yau bayan mun hayayyafa take nan kamar ta saurayi da budurwa. Hira muka shiga yi ta abin da yake faruwa a ƙasar har Inya ta shigo, sanye da sabuwar doguwar rigar da na siya musu ɗazu ita da Tasleem, ta ɓoye dogon gashinta cikin hula sai doguwar jelar da ta kitse da ke ta reto a ƙasan wuyanta, hannunta ɗauke da tray wanda aka ɗora flask ɗin shayi ƙarami na zamani da ƴan kofuna. Ta ɗora tray ɗin kan centre table ɗin da ke ɗakin tare da cewa “ga shi nan Amma” 

Download>>> Yaro Ne Complete Document

“Na gode, Allah Ya yi miki albarka” na ce 

“Ameen, sai da safenku” ta ce da murmushi ta yi waje. 

Na dubi Alhaji da murmushi na ce “ga shayin da ka ɗauka ibada a kwanakin nan” 

Ya yi ƴar dariya ya ce “yanzu na gane masa ne”. Hira ce ta kuma ɓarkewa a tsakaninmu kafin daga bisani muka koma ɗaki don kwanciya. Bayan na idar da addu’a na shafe jikina na dubi Alhaji da ya tsiri latse-latse a waya cikin ƴan kwanakin nan, na taɓe baki na ce “wai fisabilillahi me kake yi da waya ne duk dare yanzu” 

Ya ɗago ya kalleni ya ce “Hadiza ai yanzu duk cinikayya ta koma ta yanar gizo, kuma kin ga ni ba wani samun lokaci nake da rana ba, yanzu nan muna magana ne da Basiru kan kayan da zai turo mini daga China” 

“To Allah Ya taimaka” na ce ina gyara kwanciya, ya jima yana latse-latsensa kafin na ji kwanciyarsa a bayana yana rungumata, na yi murmushi kan yadda Alhaji sam ba ya gajiya da abu ɗaya kullum jin sa yake kamar sabon ango, sai da na sa ma masa nutsuwa sannan muka miƙe don tsarkake jikinmu, wayarsa da ke gefen pillownsa ta kawo haske idona ya kai kan screen ɗin,ban iya karantawa ba sai kalmar ƙarshe da na gani wani abu sannan aka ƙara da baby, Alhaji ya yi saurin ɗaukar wayar ya kashe bakiɗaya, jikina ya yi wani irin sanyi ƙalau na kasa motsa wa, ya ja siririn tsaki ya ce “yaron nan Basiru sam ba shi da hankali, bai son mutum na buƙatar hutu ba, yanzu fa muka gama magana da shi amma kin ga ya sake turon wani saƙo akan kaya.” Ya wuce hanyar toilet, na bi bayansa ina ƙaryata idanuwana da suka gane mini Baby, na tilasta wa zuciyata cewar Basiru idanuna suka gani, da wannan na samu na yaƙi zargin da ya so ya ɗarsu a zuciyata.

Assalatu na farko na tashi, sai dai ko da na tashi babu Alhaji babu dalilinsa, ba ɗabi’arsa ba ce tashi da wurwuri, wani lokacin ma sai na yi da gaske yake tashi, nauyin bacci garesa. Ƙarar famfo da na ji na ta zuba babu ƙaƙƙautawa sama da minti goma ya sa na nufi banɗakin da nake kyautata zaton Alhaji ne ke amfani da shi, ina ƙoƙarin buɗewa sai na ji kamar wanda yake magana da wani a ciki, na tura ƙofar na gansa tsaye da waya a kunne alamun waya yake, cikin daburcewa ya fara inda-inda tare da sauke wayar yana washe baki da cewa “ashe kin tashi, nima yanzu na tashi ba a yi ko minti biyar ba, Sagiru ya tasheni” 

“Shi ne kake waya a banɗaki” na ce ina kallon yanayin da ya shiga na rikicewa. 

Download>>> Kwarata Complete Document

“E, ai…” Ya fara sosa ƙeya daidai lokacin aka fara kiran sallah hakan ya sa ya ratsa ta gefena ya wuce da sauri, na bi bayansa da kallo ina mamakin wannan sabon sauyin da ya shigesa. Alwala na ɗaura zuciyata cike da tunannuka na nufi dadduma, na yi sallah, da na idar sai na tsinci kaina da kwararo addu’o’i ga mijina kan Allah Ya tsare min shi daga sharrin wannan zamani, ya kauda duk wani abu da zai shigo rayuwarmu wanda ba alheri ba, bayan na shafa na jawo Qur’ani na soma karantawa, da wannan na samu nutsuwar zuciya. Bayan na idar na rufe tare da miƙewa na nufi sashen yara don na faɗi abin da za a ɗora don na san sun tashi. Tasleem sam da asuba ba ta da mamora, duk yadda ka so ta yi maka aiki ba za ta yi ba, sai ta koma wannan baccin nata na ƙa’ida yayin da Inya kuma ba ta komawa bacci kamar Ni, sai an gama gyara gidan tass yara sun tafi makaranta ta karya sannan za ta koma, da sallama na tura ƙofar ɗakinsu Bahijja da Nadiya, sanye suke cikin kayan makaranta, Bahijja na duba littafi yayin da Nadia ke kwance kan gado tana bacci, “Amma ina kwana” cewar Bahijja.

Na yi murmushi na ce “lafiya lau, har kun yi wanka” 

“E, yanzu na gama shirya Nadiya ta koma bacci” ta ce. 

“Madalla, Allah Ya yi miki albarka, bari na saka Inya ta muku break fast” na ce ina ficewa.

Tura ƙofar ɗakin na yi da sallama, kamar yadda nake zato Tasleem na kwance ta koma bacci, yayin da Inya ke linke hijabi alamun wadda ta yi salla ce, da murmushi ta ce “Amma ina kwana?” 

“Lafiya lau, kin tashi lafiya?” 

Download>>> Ingarman Namiji Complete Document

“Lafiya lau” ta ce. 

“Madalla, ki yi hanzarin ɗora doya da ƙwai don Allah kar ki bari yaran nan su makara” na ce ina ƙoƙarin fita.

“In sha Allah” ta ce. 

Ko da na tura ƙofar ɗakin Alhaji gabana ne ya yanke ya faɗi dalilin ganinsa da na yi, ya yi ruf da ciki yana waya har wani shilla ƙafa yake alamun cike yake da shauƙin wayar. 

“Da Basirun kake waya da safiyar nan?” Na ce muryata na kakkarwa. 

Ya yi wata iriyar hantsilawa ya dira kan ƙafafunsa bayan ya kashe wayar yana sosa ƙeya ya ce…

YA KUKA GA KAFCEN?

“Wani irin sa ido kika koya ne Hadiza, ba hali in yi waya ko in latsa waya sai ki sakoni a gaba,ba zan yi amfani da waya kike nufi ba kome, to da Hajiya nake magana, ba na son sa ido” ya fitittike yana faɗa sannan ya miƙe ya fice. 

Alhaji bai shigo ba sai da sha ɗaya ta gota, a gaggauce ya shirya ya ci abinci ya fice ba tare da ya ko kalli inuwata ba, wannan abu ba ƙaramin ciwo ya yi min ba, don hakan ba ta taɓa faruwa tsakaninmu ba tsawon shekarun da muka kwashe, muna samun saɓani amma duk faɗan da zamu yi wuyarta na ɓata rai, duk fushin da yake zai sauko ya shiga rarrashina ko da ni ce da laifi, bala’in sona yake, gaban kowa kuwa har da ƴaƴanmu ba ya ɓoye son da yake mini, bayan fitarsa sai na kwanta a gado cike da jimami,komai sai na ji ya fice min a rai, baccin ma na gagara komawa sai na yi ta juye-juye tunanin sauyin Alhaji na ta kai kawo a raina. Wajen sha biyu da rabi Inya ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. 

Download>>> Ana Dara Ga… Complete Document

Da murmushi ta ce “Amma yau na ji ki shiru, halan ba kya jin daɗi ne?” 

“Kaina ke ɗan sara wa, an kammala abinci ne?” Na tambaya. 

“E, dambun couscous na yi da miyar hanta.” 

“Yawwa, kira Isiya ya kai wa Alhaji abincinsa don ba wani abincin kirki ya ci ba” 

“La! Amma bari kawai na biya na kai masa, zan je saloon duk hanya ɗaya ce.” ta ce.

“To shi ke nan, sai kin dawo Allah Ya yi miki albarka, Ina Tasleem ne?” 

“Ameen. Tasleem tana kallo” 

“Aikin ke nan!” Na ce ina miƙewa yayin da Inya ta fice.

Alhaji yau kwata-kwata bai kirani ba, kira biyar na masa bai ɗaga ba. Sai gabanin magariba ya shigo gidan, duk da na ji dirar motarsa ban bi ta kansa ba don na tanada masa komai da zai buƙata na ajiye a sashensa. Bayan sallar isha’i kwalliya na ɗauka ƴar gaske kamar wata sabuwar amarya na karya ɗauri, ko kusa ban yarda na maida kaina tsohuwa ba, duk abin da zamani ya zo da shi amsa nake, ban bari an bar Ni a baya ba, fannin kwalliya da girki na zamani ƙaryar budurwa ta koya min sai dai ta koya a wajena. Na saka takalmi mai ɗan tsini na bi ko ina na jikina da turaren da suke haukata Alhaji, ko laifi na yi masa in har na yi kwalliya ta musamman shi ke nan, ya gigice a kaina ke nan, na nufi locker ta da nake ajiye kayan mata na asalin sakkwatawa masu inganci na buɗe, haɗa wannan, dama wancan na shanye tass na kwankwaɗi ruwan kwararo ni’ima, sannan na kuskure bakina na fesa mouth fresh na jefa mint a baki na fita ina takuna ɗas ɗas ɗas, a parlor na tadda yara suna kallo, nan kowa ya hau zuzuta kyawun da na yi, kullum cikin ado nake ba wai ban saba ba ne, amma adon yau ɗin na musamman ne, na yi murmushi na ce “Bahijja da Nadiya ku gaggauta tashi zuwa bacci”

Download>>> Yar Harka Complete Document

“Hooo! Amma wallahi kin wanku kamar a injin” cewar Tasleem, na girgiza kai ina dariya na dubi Inya na ce “ki saka su Bahijja su kwanta yanzu, Ni na shige, sai da safenku” 

“To Amma, wallahi kin yi kyau sosai” ta ce tana murmushi. Murmushin nima na yi na wuce su. Ina jin daɗin yadda gidan nawa yake cikin farin ciki da ƙaunar juna a kodayaushe. 

Da sallama na tura ƙofar ɗakinsa, sassanyan ƙamshin da ya gauraye da sanyin Ac suka hura ni, na ɗan lumshe ido ina jin wani abu da ya taso ya tokaren zuciya yayin da na yi tozali da Alhaji yana latsa waya yana ta sakin murmushi, na daure zuciyata na shimfiɗa murmushi a leɓena, so nake yau na yi nasarar shafe koma mene yake yi a wayar nan, na farfaɗo da soyayyata da na ga tana neman disashewa, na ƙarasa wajensa cikin takun ƙaniya na zauna gefensa, ya yi hanzarin latsa wayarsa ya kashe ya ɗago yana kallona, na saki murmushin zuciyata fal takaici na yi narai-narai da idanuwana tare da kama kunnena ina aika masa kallon da na san yana gigitasa, ya kauda kansa gefe, na taushi zuciyata da ke azalzalar na tashi na ba shi wuri bai da gaskiya sam, na kwanta a kafaɗarsa na ce “karon farko tsayin zamana da kai ba ka taɓa ƙin ɗaga wayata da watsar da lamurrana ba sai a yanzu, me na aikata da zafi haka Alhajina?” 

Ya ja doguwar ajiyar zuciya tare da kamo hannuna ya riƙe yana cewa “ke ce ai Hajiyata na kasa gane miki, da na ɗauki waya sai bin diddiƙi kamar wata ƴar sanda” 

“Ni ai ba zan taɓa zama ƴar sanda ga mijina ba sai dai lauya” na ƙare ina kanne masa ido ɗaya. 

Ya saki murmushi ya ce “amma fa dole na ba da tukwicin wannan kwalliya, don an burge ni” 

Download>>> Matar Hariji Complete Document

Na yi wal da ido na ce “tukunna ma dai burgekan” 

“Allah ko, ki ce yau akwai harka” 

“Ƙwarai! sai na ga tunƙwal uwar daka” na miƙe ina dariya. Ya sa hannu ya janyoni na faɗa jikinsa ya ce “ai ba zan iya jira ba Hajiyata, yanzun nan za a fara dakan” 

Mun murji juna sosai cike da soyayya, sumbatu sosai na saka Alhaji kafin muka rankaya toilet don wanka. Daren hanasa latsar wayar na yi, a ƙirjina ya kwanta har bacci ya sure shi, na bisa da kallo ina jin ƙaunarsa da mugun kishinsa na rufeni, sai na tsinci zuciyata da addu’a Allah Ya sa ba tarkon mace ya faɗa ba, na ƙanƙame kayana ina jin wani bacci mai cike da nutsuwa na figata, na yi nisa na ji zum zum akan katifa, na buɗe idona cikin bacci na dubi gefen Alhaji da wayarsa ke haske, na janyo cike da mamakin wane zai kirasa a irin wannan lokacin. _Sweet baby_ idona ya sauka a kai wani abu ya caki zuciyata, kiran ya yanke wani ya shigo. Sosai zuciyata ke tunzura ni na ɗauka na zagi uwar wadda ke kira, jiki babu ƙwari na ɗaga tare da sallama,ba a amsa ba aka yi shiru, na ciji leɓena na ce “yanzu baiwar Allah bai yi dare a wajenki ba ki kira mutumin da kika san yana da aure, in ke ce aka yi wa haka ya za ki ji?” Tausar zuciyata kawai na yi ban cusa mata zagin kutumar kutumar ba. Katse kiran aka yi daidai lokacin da na ji kuka na ƙoƙarin kufce min, na sauke wayar ina bin fuskar Alhaji da kallo da ya tashi yanzun nan, wani mugun haushinsa ya samu gurbi a zuciyata,n cilla masa wayarsa…

WRITTEN BY:   FATIMA LAWAL SA’ID

NOVEL NAME:   NI NA RAINE TA

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         26KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      21- AUGUST -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦500 

Proceed To Download Ni Na Raine Ta Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button