Ruwan Zuma Page 53 Hausa Novel
(53) Haydar gidan yayanshi Alhaji Abdul ya isa aka bud’e mishi gate ya shiga wanda zai iya cewa wannan ne zuwan shi na hud’u gidan tun bayan da suka shirya. A lambun gidan ya samu yayan nashi da wani Ustaz yana koya mishi karatun addini, sai da ya bari suka gama sannan ya iso gurinsu ya gaisa da su kana Ustaz d’in ya tafi. “Na ga kayi nisa a karatunka.” Fad’in Haydar yana kallon littafin dake hannun Alhaji Abdul yana murmushi. Alhaji Abdul tattara littafan yayi guri d’aya shima yana murmusawa ya ce, “Har yanzu kan nawa yana ja, idan na d’auki shafi d’aya kafin gobe zan haddace matuk’ar aiki bai mini yawa ba. Ina d’ana? Na dad’e ban ganshi ba.” “Yana gida, baka da mata ne da na kawo maka shi ya yini.” “About that…” Alhaji Abdul ya tafa hannayensa wanda yana yawan yin hakan ya cigaba da magana, “Dama nima ina nemanka zamu yi shawara. Amma kafin nan wani taimako kake nema?” Ajiyar zuciya Haydar yayi kana ya fad’awa Alhaji Abdul niyyarsa ta d’aukowa Abul laptop d’in sa a gidan Senator Gambo Umar, ya karishe maganan da cewa, “Allah yasa kana da wani connection da zai iya kaimu gidan har mu kar6o.” “Ni ban sanshi personally ba amma ina ga kwanaki can da yake rik’e da kujerar Senator sun ta6a wani kasuwanci tare da Baba ya sayar masa da wata kwangila. In ka shirya mu tafi Abuja gobe, idan mun dawo kuma zaka je nema mini aure.” “A ina ka samu matar?” Haydar ya fad’a cikin farin ciki domin har cikin ranshi yake son yayan nashi yayi aure ya daina zama haka. “Yarinyar da ke hannun Ammi ce, naga ka san mahaifinta shine nake so kai ka fara nema mini izinin magana da ita. Amma kana ganin zan samu aurenta kuwa?” Haydar shiru yayi yana tunani idanunshi kyar a kan yayan nashi, ya san Meenat nitsatstsiyar yarinya ce in ka cire son da ta mishi har ta kasa 6oyewa kowa ya sani. Alhaji Abdul kuma a da yayi bidirinsa da duniya sai yanzu Allah ya shiryeshi ya samu ya nitsu a yanzu da yake da shekara arba’in da bakwai, shin had’uwarsu zai yi kyau kuwa domin shi yana tsoron cutar da d’aya daga cikinsu domin ita Meenat ta zama tamkar ‘ya a gurin Amminshi don yanzu ma haka tana Abuja a gurinsu, ta d’ayan gefen kuwa Alhaji Abdul yayansa ne jininsa kwalli d’aya rak a duniya, basu da kowa sai junansu. “Ta yi k’arama ko? Ammi ta fad’a mini shekarunta ashirin ne ciff, ban san ma meyasa nayi tunanin aurenta ba me zata yi da tsoho irina.” Ya fad’a cikin karayar zuciya annurin fuskarsa na raguwa. “Ni ban ce ba, ai age is just a number. Idan kuma nace banbancin shekaru zai hana aure to na zama munafuki. Idan har kana sonta tsakani da Allah kuma zaka rik’eta da amana ni zan nema maka aurenta da yardar Allah.” Haydar yayi saurin katseshi ganin ya karaya nan take. “Zan rik’eta tsakani da Allah Haydar ba zan cuceta ba.” “Allah ya baka iko. Zan mana booking d’in jirgin safe Insha Allah.” “Shikenan.” Haydar bai bar gidan Alhaji Abdul ba sai k’arfe tara na dare, dalilin magana da suka yi a kan kasuwancinsu. A can side d’insa ya samu Laila har ta kwanta ga can Mas’ud J ma yayi bacci, “Har kin kwanta?” Ya tambayeta yana rage kayan jikinsa. “Eh, Sannu da dawowa. Yau ka yi dare.” “Na je gidan Alhaji Abdul ne. Ya samu mata zamu je nema mishi aurenta.” Har cikin ranta Laila ta ji dad’in wannan magana domin ta san Alhaji Abdul ya so ta har son ya koma obsession, an ce wanda ya nuna maka so ya kamata ka mishi fatan alkhairi ko baka mayar da son ta yake maka ba. Lokaci kuma yayi da ya kamata ya yi aure domin kullum tsufa yake k’ara yi mutuwa kuma bata sanarwa take zuwa. Sannan ya kamata ya ajiye d’an da ko bayan mutuwarsa zai mishi addu’a, wai bahaushe yace ‘ko gudu kake yi ka haifa ka jefar watarana d’an zai maka rana’. “Hamdallah Allah ya tabbatar da alkhairi yasa a yi damu.” “Baki tambayi wacece matar ba.” Haydar ya fad’a yana tu6e duk kayan jikinshi ya yi hanyar band’aki. “Wacece? Duk dama ba dole in santa ba.” “Meenat ‘yar d’akin Ammi.” “Kai wannan abun namu kamar a littafin Hausa. Shi ya so ni bai sameni ba, ita kuma ta so ka amma bata sameka ba shine suka had’e with their second choices.” Laila ta yi ‘yar dariya tana girgiza kai. “Zan fad’a mishi sak’onki.” Haydar ya fad’a yana shigewa band’aki. “Sarkin had’a fad’a.” Ta furta a hankali tana jawo wayarta gudun kar bacci ya d’auketa kafin ya fito. Minti uku da haka Haydar ya gama wanka ya bud’e band’akin yace Laila ta mik’o mishi sabon towel a cikin wardrobe. D’aukowa ta yi kana ta tako har bakin band’akin ta mik’a mishi hankalinta na kan wayarta, shi kuma zuba mata idanu yayi yana kallon surar jikinta cikin kayan baccin da ta saka wanda dashi da babu duk d’aya. Bata yi aune ba sai ji tayi ya kamo hannunta ya jawota cikin band’akin, tana tirjewa tana dariya ya rufe k’ofar ya ce, “Wanka zan miki.” Washe gari tun safe jirgin su Haydar ya tashi, har lokacin Abul bai samu ya mishi magana ba a lokacin da zasu je masallaci sallah asuba, akan cewa sai da safe in yana karyawa zai fito ya mishi wannan godiyar. Sai dai yana fitowa k’arfe bakwai da rabi ya samu Laila na tattare gurin da Haydar d’in ya ci abinci, gaisheta yayi kana ya ce, “Ina yake?” Cikin rashin fahimtan waye yake nufi Laila ta ce, “Waye?” “Umm.. Baban Mas’ud J.” “Ohh yayi tafiya, yanzun nan ya fita zasu je Abuja da yayanshi gurin Babansu. Lafiya kam?” Laila ta tambayeshi tana zama a kan kujeran dinning table d’in ganin shima ya zauna. “Lafiya kalau, kawai zan mishi godiya ne kan taimakon da ya yiwa abokina Banney. Na ji dad’in hakan domin Banney ya taimakeni a rayuwa ba kad’an ba, shi yayi jinyata har na fara takawa ina fita waje bai barni na mutu da ciwukana ba.” Ya k’arisa maganar yana tuno yanda sauran abokan shashancin nasu suka wofintar dashi lokacin da direban Sadistic Faruk ya kawoshi shagon Ima, amma shi Banney ya tsaya kai da fata yayi jinyarsa wanda har kashi Abul d’in yake yi a leda Banney na jefarwa a bola ba tare da ya nuna mishi kyama ko sau d’aya ba. Laila dubanshi ta yi a natse ta ce, “Na ce bana son a k’ara tayar da zancen amma ina son jin su waye mutanen da kake harka dasu har suke maka dariya a kan auren da nayi, ka ta6a fad’a mini cewa daga wani abu wai dark web suke wanda kuke yin abubuwa tare. Sannan ina son sanin wace irin rayuwa kayi a Abuja kafin Haydar ya sameka. Abul kar ka 6oye mini, I want to know everything.” “Baza ki so sani ba Mama.” “Tell me.” Ajiyar zuciya ya sauk’e kana ya fara magana kamar haka, “Mama sanin computer da nayi ciki da waje yasa watarana na fad’a cikin wata k’ungiya wacce ko da ka iya computer ba lallai bane ka gane k’ungiyar ta kafu ba ko kuma a yi inviting d’inka ka shiga ba. Na shiga ne ta hanyar Micheal abokina wanda shima yana cikin wannan k’ungiyar ya zama mu biyar ne kaf fad’in Kano a wannan worldwide group d’in.” “Me kuke yi a ciki?” Laila zuciyarta ce ta fara bugawa tun da taji ya ambaci k’ungiya ta yi saurin tambayarsa kwakwalwarta na kawo mata kala-kalan abubuwan da suke yi a ciki wanda kaf cikinsu babu mai kyau. Kallonta yayi idanunsa na nuna tsantsar nadama ya ce, “Duk abun da kika sani mara kyau ana biyanmu muna yi. Muna bud’ewa mutane website da zasu d’inga Fraud dashi Mama, ana yin transactions na smuggled guns and bombs a k’ungiyar mu saboda kar Gwamnati ta biyo sahu a gane wanda suka yi, amma mu zamu iya yi sannan mu goge duk wani evidence da zai nuna an yi wannan harka a doron k’asa. A dark web ana human trafficking, child pornography, illegal Gambling, Drugs sannan muna hacking d’in phones da kuma computers d’in mutane idan buk’atar hakan ta taso. K’aramin aikin da muke yi shine tona asirin mutane idan abokan gabansu suka nemi mu yi hakan. Sau da dama mu muke watsa nudes ko maganar sirri na wani d’an siyasa, mai kud’i ko wani babban mutum da ake son a 6atashi a idon jama’a, zamu iya hakan ta hanyar hacking d’in wayarsa ko kuma computer ko kuma aika voice detector har cikin gidanshi a lokacin da muke tsammanin zai yi maganar da ake son ji. Wani lokaci kuma har Drone zamu tura ta d’auko mana pictures da videos, Mama a haka na samu video d’in Alhaji Abdul a Abuja bayan wani abokin harkana sadistic Faruk ya tura drone jikin window gidanshi.” “Duk abun da ka ambata kana yi Abul?” Laila ta fad’a hawaye na tsiyaya a idanunta tana jin kamar ta kurma ihu, ina ma bata tambayi Abul wannan tambayar ba, ina ma ta zauna cikin duhu tun da har Allah yasa ya daina ya shiryu! Sai kuma tsoron Abul d’in ya shiga zuciyarta amma bata bari ya gane hakan ba gudun kar ya fasa fad’a mata komai. “Mama zan miki rantsuwa da Allah wallahi ban ta6a yin manyan aikin ba, ban ta6a yin transactions na human trafficking, child pornography, drugs da kuma arms and ammunitions ba. Na san na ta6a creating website da ake jawo mutane masu kwad’ayi a kwashe duk abun da yake cikin bank account d’insu bayan an musu alk’awarin ninka kud’in da suke dashi, sannan na ta6a watsa nudes d’in wani Senator anonymously ba tare da an gane waye yayi hakan ba duk da cewa daga baya an yi k’ok’arin hacking d’in account d’in tare da Laptop d’ina. Mama duk sanina da computer ban yi shaharar da za’a nemeni in yi wad’ancan manyan ayyukan ba, dama kuma nima na yi alk’awarin bazan ta6a yin irinsu ba.” “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.” Fad’in Laila tana sunkuyar da kanta daga barin kallon Abul. “Mama ban d’aukeki a hoto ba, haka kuma bani na watsa hotunanki ba, sai dai nine na saka Micheal ya turo miki link na comments d’in mijinki a Twitter don ki ga ainihin k’udirinsa na auren babbar mace kuma mai kud’i, shima kenan irin mutanen nan ne da ake kira da Gigolo. Bayan an watsa hotunanku nine nayi shiga da ficena tare da Sadistic Faruk muka umurci accounts d’in da su goge wannan pictures d’in ko mu 6ata musu account d’in gabad’aya. Bayan mun nuna musu misali shine suka tsorita suka goge, duk irin haushi da takaicin aurenki da nake yi ba zan bari mutane su ci mutuncinki suna miki k’azafin zina ba.” “Ya Salam, abun ya wuce tunanina Abul. Duk wannan lokacin ni ina nake da har ka fad’a cikin k’azamar rayuwar nan ban sani ba?” Laila ta yi maganar tana tashi tsaye don ji ta yi kanta na sarawa ta kuma kasa gaskata duk abun da ke fitowa daga bakin d’an nata. Shiru Abul yayi domin babu yanda za’a yi ta san yana cikin wannan rayuwar ko da kuwa bata laptop d’in yayi ta kwana tana bincike a ciki. “Ina jinka.” Fad’in Laila tana tsayuwa a kanshi shi kuma kanshi na k’asa. “Bayan aurenki wasu mutum biyu daga cikin members d’inmu na dark web suka turo pictures d’inku suna mini dariya a kan cewa kin auri yaro k’arami wanda kwanaki tare dani aka yiwa wasu couples irin haka kaca-kaca a internet. Na yi mamakin yanda aka yi suka ganeni saboda muna aiki ne anonymously Micheal ne kad’ai ya sanni, sai daga baya Sadistic Faruk ya fad’a mini cewa bakinshi d’aya da su domin shi ya bayyana musu identity na. A nan suka yi alk’awarin watsa videos d’in first night d’inku wanda na san zasu iya aikata recording saboda sun fini kayan aiki da kuma kwarewa. Sadistic Faruk shi ya taimakeni ya hanasu bayan ya basu kud’i mai tsoka.” “Waye ne shi yaron nan da kake ta kiran sunansa ya taimakeka?” “Shine wanda na fara sani a dark web bayan Micheal, kuma a gidansu a Abuja na zauna bayan na gudu daga shagon Uncle Mas’ud. Sannan shi ya mini lahani ya kusa kasheni bayan na yi betraying d’insa unknowingly.” A nan ya bata labarin zamanshi a gidan Faruk da abun da ya mishi da tarihin zamanshi tare da Banney har Haydar ya sameshi ya dawo dashi gida bai 6oye mata komai ba. Laila ta kai kusan minti biyar tana kallon Abul tana share hawayenta amma wasu na zubowa, sai da ta nitsu sannan ta ce, “Abun da ya faru ya wuce ba zan maka fad’a a kai ba saboda duniya ta koya maka hankali kuma ka nitsu, sai dai ina son ka mini alk’awari da girman Allah cewa baza ka sake komawa wannan rayuwar taka ta baya ba. Ka mini alk’awarin ka bar dark web da duk mutanen cikinta har abada Abul. Wallahi tsoro ya shiga zuciyata, ni kad’ai na san me nake ji da naji wannan rikitaccen labarin naka Abul. Kai Innalillahi wa Inna ilaihir raji’un, wannan zamani da abun cikinta rashin amfaninsu yafi amfanin yawa.” “Mama na fad’a miki ne don ki gane na shiryu kuma har abada ba zan sake maimaita abun da nayi a baya ba. Da kuma zan ci gaba da bazan fara fad’a miki ba balle ki saka mini ido ko kuma ki hanani ba. I regret everything I do kuma ina rok’an Allah ya yafe mini kurakuraina da cutar da mutane da na yi.” “Abun kam babu dad’i don baka san mutane nawa aka cuta a dalilin hakan ba, sannan baka san mutane nawa ne suka kalli tsiraicin wannan Senator d’in ba. Kowanne kana da kason zunubi ba zan maka karya ba Abul, wallahi kana da kason zunubi, kawai ka cigaba da istigfari Allah kuma ya ji tausayinka ya yafe maka.” Sun dad’e suna magana sannan Laila ta jiyo kukan Mas’ud J ya farka, cikin sauri ta shiga d’akinta ta d’aukoshi domin zai iya birgima ya fad’i k’asa. A ranar daga ita har Abul haka suka yini sakaka jiki babu kuzari, hatta shago waya ta yi ta fad’a musu baza ta samu zuwa ba su kula da gurin. Sai dai yinin ranar bakinta bai daina motsi ba dalilin addu’an da take ta yi Allah ya tak’aita musu wahala da shiga jarabawar rayuwa irin haka. Haydar da Alhaji Abdul suna isa Abuja direban Baba ya zo ya d’aukesu a airport suka wuce gida. Ammi ce ta taryesu cikin farin cikin ganinsu tare kamar yanda taci buri, Haydar kuma kallonta kawai yake yi yana murmushi dalilin kyawunta da yake bayyana wanda a daa talauci da wahala ya 6oyeshi. Ya san mamanshi kyakkyawa ce amma bai ta6a tsammanin she’s that elegant ba, a yanzu tana cikin kwanciyar hankali tana kuma samun kulawa da soyayya daga Baba wanda har a yanzu bai daina kiranta da suna Lu’a ba. Sai k’arfe tara da rabi na safe Baba ya tashi daga bacci ya zauna tare da yaran nashi shima farin ciki fal a fuskarsa ganin yanda suke hira tsakaninsu kamar wata matsala bata ta6a shiga tsakaninsu ba. Babu 6ata lokaci Alhaji Abdul ya sanar dashi dalilin zuwansu Haydar ya k’arishe da cewa, “Ina son conflict d’in da yake tsakanina da yaron ya kau ko kuma ya ragu, sannan mahaifiyarshi tafi son ya koma makaranta a kan ya fara sana’a kamar yanda yace zai yi.” Gyaran murya Baba yayi kana ya ce, “Shekarun da yawa rabon da na had’u da Senator Gambo Umar amma zan nemi ganawa dashi mu gani ko za’a dace.” Bayan Haydar ya samu ke6ewa da mahaifiyarshi ya dubeta ya ce, “Ammi kin daina kewata ko?” “Me ka gani?” Ta tambayeshi tana shafa hannunsa dake cikin nata a hankali tana murmushi. “Kusan wata kenan rabonki da Kano, da kuma bakya iya yin sati biyu sai kin zo kin ganni.” “Rashin zuwan nawa ya samu asali ne kan ina son mayar da Meenat gida k’arshen watan nan, Babanta yace ya gaji da zamanta babu miji kuma ya k’i yarda a sakata a University. Yanzu maganar da nake maka cewa yayi ya sama mata miji ta koma gida su daidaita.” “To Alhaji Abdul d’in fa?” Haydar yayi saurin fad’a cikin rashin jin dad’in wannan labarin. “Na fad’a mishi ya isa gurin mahaifinta amma ya k’i don ita yarinyar ma ko maganan bai ta6a mata ba. Ban san zuciyarta ba amma idan ya zo nan tana yawan son girka mishi abun da zai burgeshi amma baya nuna ya ji dad’i ko ya yi mata magana mai nuna alamar so. Da na takurashi da zancenta cewa yayi zai maka magana idan ka yarda zaka shiga gaba wajen nema masa auren to zai yi.” Haydar girgiza kanshi yayi yana murmusawa kad’an domin yayanshi ya shiryu ba kad’an ba, yana sane da duk wani shiga da ficensa wanda baza a kirashi stalking ba sai dai kulawan d’an uwanshi. Ya daina neman mata sannan duk wata harka da zata had’ashi da mace baya shiga, in kuma ya zama dole ya shiga sai ya tabbatar akwai wani namiji tare dashi da zai tsaya tare dashi har ya gama. Wannan mataki ne da Alhaji Abdul ya d’auka don gujewa komawa ruwa. Da yamma Baba ya musu jagora zuwa gidan Senator Gambo Umar bayan ya samu ganinshi daga wani abokinsa da suke mutunci. A falonshi aka sauk’e su ya fito da kyar yana rik’e da sanda dalilin ciwon k’afa da yake fama dashi, Haydar da Alhaji Abdul da suke zaune a k’asa suka fara gaisheshi bayan ya zauna kana Baba ma ya d’aga mishi gaisuwa yana tambayar lafiyar k’afarsa. “Alhaji ka ga wannan k’afar canjata ne kawai ba’a yi ba saboda nayi yawon hospitals da dama a k’asashen duniya amma ba’a samu waraka ba, sun hanani cin jan nama tun da jimawa yanzu maganar da nake magana duk wani nama da ka sani sun hanani ci. Abubuwa da dama na nau’in abinci sai dai in gansu in kawar da kai saboda sun zama haramiyata, idan kuma na kuskura na ci to sai dai in farka a wata k’asar an kaini asibiti. Talaka yana can yana neman kud’i ya d’auka sune jindad’in duniya bai san cewa ya fi mu kwanciyar hankali da lafiya ba.” Baba ma labarin ciwon k’afarsa ya bashi yana kuma kwatanta mishi wata asibitin da ya je a India wata uku da suka wuce aka bashi magani har ya samu sauk’in k’afar ya fara taka mota. Su Haydar dai Suna zaune ba uhm ba um um suna jin labarin ciwon k’afa wanda Alhaji Abdul ya ji kamar ya tsayar dasu su yi abun da ya kawosu amma bai isa ba. “Kayi contacting asibiting tukunna a tsara komai sai ka je.” Fad’in Baba ganin Senator Gambo ya kwadaitu da zuwa asibitin. “Wannan tafiya ai kai zaka mini jagora Alhaji Sammani, in zaka iya raka tsohon abokinka kenan.” Senator Gambo ya k’arisa maganan cikin raha yana dariya. “Ai shikenan Allah ya kaimu lokacin dama matata tace k’asar na burgeta bata gaji da zagawa ba.” Fad’in Baba shima yana darawa. Maganar bata k’are ba sai da suka tsara yanda tafiyar zata kasance wacce za’a yi nan da sati biyu masu zuwa. “Kace wad’annan d’in duk ‘yayanka ne Alhaji Sammani?” “Har yanzu kana mamaki ne Senator?” Baba ya kwashe da dariya yana kallon ‘yayan nashi cike da alfahari. “Kayi sa’an ‘yaya Alhaji, ni ban ga ‘yayan bama balle har in samu su rakani wani guri irin haka. Dalilin da yasa kaga na nace maka ina son tafiyar da kai saboda sun ce sun gaji da yawon asibitoci da ni ne, wai in hak’ura ciwon tsufa ne dashi zan mutu. Basu damu dani ba Alhaji, duk irin gwamutso da wahalar tara kud’in nan da nayi domin su yanzu basa gani saboda kowa yayi fiffike ya tashi zai bautawa matarsa da ‘yayansa.” “Kayya abun bai yi dad’i ba, yaran yanzu sai addu’a Senator. Allah ya karkato da hankalinsu gida yasa su gane gaskiya.” “Amin Amin.” Sai a lokacin Baba ya sanar dashi dalilin zuwansu wanda Senator yana jin cewa d’ansa Faruk ne ya kwacewa jikan Alhaji Sammani Laptop d’insa ya hau fad’a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. “Ka ji ko Alhaji? Shi yaron nan menene ban mishi ba don kawai ya dawo gida ya zauna kusa dani? Kwanaki shi ya saka na mayar da lambun gidan nan nashi shi kad’ai wai yafi son guri da babu hayaniyar mutane saboda kukan tsuntsaye yafi mishi dad’in sauraro a kan maganar mutane. To yanzu maganar da nake maka ya tafi yau wata shida kenan ban san ina yayi ba, yaran nan gaba d’aya sun lalace na rasa gane yaya aka yi hakan ya faru.” Haydar da yake jin duk abun da yake faruwa ya ce a ransa ‘dama idan aka ciyar da yaro da haram aka kuma nuna mishi so babu kwa6a dole iyayensa su yi kuka a k’arshe’. Senator Gambo shi ya kira direban Sadistic Faruk da yake shi yafi kowa sanin shiga da ficensa ya tambayeshi ko Faruk d’in ya ta6a yin bak’o wanda ya tafi bai d’auki kayansa ba. “Yalla6ai ya ta6a kawo bak’o a matsayin abokinsa amma rabuwarsu bata yi dad’i ba. Shine wanda nake baka labarin a kwanakin baya.” Dafe kai Senator Gambo yayi cikin jin kunyar wannan abun saboda shi yana da labarin duk abun da d’ansa yake yi ta hanyar Direbanshi ba tare da shi Faruk d’in yasan ana kai rahotonshi ba, sai dai duk abun da Faruk d’in yake yi Senator Gambo baya iya mishi fad’a saboda yana tsoron kar ya tafi ya barshi kamar yanda sauran ‘yayan nashi suka gujeshi. Su kuma su Baba basu da masaniyar ainihin abun da ya faru, abun da suka sani shine Laptop d’in Abul na tare da d’an Senator Gambo. “Ka je gidan nashi ka d’auko duk wani abu da ka sani na wannan yaron ne ka kawo nan.” “To Yalla6ai.” Bayan fitansa Senator Gambo yayi ta basu hak’uri musamman ga Haydar da aka fad’a masa cewa d’an matarsa ne. Minti ashirin da haka Direban ya dawo hannunsa d’auke da jakar Abul wacce ta k’unshi suturunsa da kuma laptop d’insa. Ganin magriba ta yi yasa Baba ya mishi sallama suka tafi Senator bakinshi bai daina basu hak’uri ba. Suna shiga cikin mota fuskar Baba ta murtuk’e ya dubi ‘yayan nashi ya ce, “Me kuke 6oye mini game da wannan case na Abul da Faruk? Yanda ubanshi yake ta bada hak’urin nan ba banza ba.” Alhaji Abdul ya kalli Haydar wanda shi kuma ya fad’a musu duk yanda suka yi da Abul. Kad’a kai Baba yayi ya ce, “Duk maganar su iri d’aya ne cewa sun yi rabuwar rashin dad’i amma shi Abul ya k’ara da cewa shi Faruk d’inne yayi masa lahani a k’afarsa. Ku yi booking flight d’in gobe da ni da Amminku da kuma Meenat, zamu koma Kano tare ina son jin duk abun da ya faru daga bakin yaron, idan har sun zalunceshi ni zan tsaya masa har kotun koli sai an kwato mishi hak’k’insa.”
Mum Fateey 👌



