Halysaah Page 205 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 205….Khaleesat ta mike daga kan darduma bayan ta idar da sallan Magrib ta cire hijab din Safiyyah dake jikinta ta linke ta ajiye kan kujera, ta nufi gun handbag dinta ta dau veil dinta da wayarta, Safiyyah dake zaune gefen gado tana shan pepper soup din da Khaleesat tayi mata daxu ta bi ta da ido ganin ta yafa gyalenta tace “Ina kuma za ki?” Khaleesat ta juya ta kalleta tace “Mijina na jirana a waje mana, baki ji wayana na vibrate ina sallah ba, nasan yana kofar gida yanxu haka” Safiyyah ta ajiye bowl din Hannunta ta marairaice tace “Dama ba kwana za ki yi ba Khaleesat?” Khaleesat ta rike haɓa tace “Wa yace maki ana kwana gidan amarya da ango” Safiyyah tace “Stop it pls, don Allah kar ki ce zaki tafi, Wallahi na zata kwana za ki yi, kar ki min haka plss” ta kare maganar hawaye na taruwa idonta, Khaleesat tace “Sai in bar ma wa mijina? Tun safe fa nake gidan nan, ban ma san ko ya ci abinci ba tunda Hadiyah ma bata nan, a gabanki muka yi waya da ita tace zata kwana gidan Aunt dinta” Safiyyah tace “To ki ba me delivery ya kai masa wanda kika dafa daxu pls, Wallahi nasan Ya Junaid bazai ki barin ki min kwana biyu ba, ni sanda naje maki sai da nayi kwana uku fa a Bauchi, sai ni ce baza ki kwana ba” Khaleesat tayi dariya tace “Ikon Allah, ai ni ba daga aure kika zo min ba ko kin manta ne, haka kawai inyi inconveniencing Ya musty” Wani shegen kallo Safiyyah ta jefa mata, aka yi Knocking din kofar dakin duk suka juya, Mustapha ya bude kofar da sallama ya tsaya nan bakin kofar, Safiyyah ta kauda kai ta hade rai, yana kallon Khaleesat yace “Khaleesat, Yarima yana kofar gida tun daxu, ya kira ki baki yi picking ba” Tace “Sallah nake yi ne, zan fito yanxu” Juyawa yayi ya fita daga dakin, Khaleesat na kallon Safiyyah tana murmushi tace “Tohm kin dai ji my husband is outside waiting for me, kar ki wani damuwa ina nan Kano for now” Hawaye suka ciko idon Safiyyah, dariya sosai ta ba Khaleesat, ta karasa kusa da ita tace “Don Allah ni dai ki dena ban kunya Sophie, Ina fa Kanon ko gobe ma zaki iya ganina na dawo gidan nan, to meye abun kuka banda ma kin ki sakin jikin ki ai Ya musty ba baren ki bane, kar ki wani damu ko gobe zaki iya ganin na dawo” a sanyaye Safiyyah tace “Da gaske?” Khaleesat tace “Kema kinsan Ya Junaid bazai hanani ba, yanxun ma don ban ce masa zan kwana bane, kuma babu abinci a gida, kin san he doesn’t like eating outside, da nayi masa girki ba abinda zai hanani kwana gidan nan” Safiyyah tace “Don Allah ki zo goben, gashi cousins dina za su zo dukkansu gobe, bana son su zo su sameni a haka dariya za su min wallahi” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace “Toh meye abun dariya, kawai ki yi yanda nace kiyi before tomorrow you will be fine baza su gane komai ba, kafin midnight ki shiga ruwan zafi sau biyu….” Safiyyah dai taki cewa komai, Khaleesat na murmushi tace “Ke naki me sauki ne ma, kuma har da gardaman ki ya ja maki, ni fa har stitches sai da aka min” Safiyyah ta gwalo ido tana kallon Khaleesat, Khaleesat tace “Uhmm, a sannan ma kin zo Bauchi, but kin tafi Gombe, you remember sanda kika dawo daga Gombe kika gan ni part din Hajja bani da lafiya?” Da sauri Khaleesat ta dau handbag dinta bayan kiran Ajay ya sake shigowa wayarta tace “Sai na dawo kawata, pls ki saki ranki, Ya Junaid is calling me, bari in tafi…” Safiyyah tayi shiru bata ce komai ba don har ta fara tsoron Khaleesat ta tafi ta bar ta ita kadai da Ya Mustapha a gidan gashi dare yayi, har Khaleesat ta bude kofar dakin sai kuma ta juya tana kallonta tayi kasa da murya tace “Zan kira ki anjima in ji ko kinyi yanda nace fa” A hankali Safiyyah tace “Wayar ai yana gida” Khaleesat tace “I will try coming back tomorrow, take care” A haka Khaleesat ta fita daga dakin, Safiyyah har da hawayenta da shesshekan kuka. Khaleesat ta bude front seat ta shiga tana kallon Ajay a hankali tace “Sorry for keeping you waiting, nasan kilan ko abincin baka ci ba yau ko?” Yace “I ate cookies” Tace “To mu je gida in maka girki” Yace “So that you will sleep halfway into the cooking” Dariya tayi tace “To yau ban yi wani bacci ba in gaya maka, ai Safiyyah ma bazata bar ni in yi bacci ba” Ɗan murmushi yayi ya tada motar, Khaleesat dai sai kallonsa take, sai da suka bar unguwan a hankali tace “Na ga you are moody? What happened? Ko nayi maka wani abu ne” Ya ɗan kalleta da lumsassun idonsa yace “Ai bakya laifi Halysaah” Ta ɗan bude ido tace “Halysaah kuma yau?” Yayi murmushi yace “Ba haka naji ake kiran ki ba, Haseelah ko Haseenah….” Dariya tayi tace “A’a kawai ka bar ma Housemate dina sunan da ya sa min gashi a gidan sarki ma haka ake kirana, kasan ta yanda ya sa min sunan?” Ajay ya girgiza mata kai, tana murmushi ta gyara zama tace “Farkon da ya fara zuwa apartment dina bama shiri da shi kwata kwata, ko magana bana masa, gashi ya iya gaisuwa, ni kuma idan ya gaisheni sai in ce masa Okay, idan nayi girki in gaya maka sai ya diba ya ci without my permission, kuma ya bar min plate a parlor, ko kuma ya bar min kayan wanke wanke a kitchen, I was soo fed up with him, naji gidan ya fitar min a rai, i was desperately looking for a way out, ga shi na zo nayi misplacing key dina, shkkn ranan naje gidansu Safiyyah na dawo very late gashi babu key, shi ne na masa knocking, yaki bude min kofa wai sai na gaya masa sunana don bazai bude ma stranger kofa ba, shi ne fa nace masa sunana Khaleesat, kawai sai naji yace Halysaah, naji wani haushi, don Allah meye hadin Khaleesat da Halysaah, kawai don in ji haushi yace Halysaah, that was how he changed my name to Halysaah” Kallon Ajay ta dinga yi jin bai ce komai ba yana driving dinsa, after some seconds ya ɗan kalleta jin tayi shiru, murmushi ya sakar mata yana ci gaba da driving yace “So ta yaya ku ka fara shiri da shi?” Khaleesat tayi shiru, Ajay yace “Kin yi shiru” Tace “Ai naga kamar baka son labarin ne” Calmly yace “Ina so mana, da bana so ai bazan saurareki ba” Ta sauke idonta tace “Kawai ranan ne da na gaji da neman House key dina, gashi idan nace ya bude min kofa sai yayi ta ja min rai, sai na shiga Bedroom dinsa baya nan zan duba key dinsa in dauke, ina duba key din a aljihunsa sai gashi ya shigo dakin, shine yace dama ina shiga in masa bincike idan baya nan, ni kuma sai naji haushi na fita ina kuka, later that day I found out that my mom was very sick, shi ne na damu ina ta kuka, shi ne ya tambayeni me ya sa nake kuka shi wasa yake min he doesn’t mean it, and I told him my mom was sick, that was how he bought me a flight ticket to Nigeria, to and fro” Ajay ya gyada kai bai ce komai ba, Khaleesat ta tura baki tace “Me yasa zaka sa in baka labarin da baka so” Without looking at her yace “Ni nace maki bana so” Ganin zai yi parking gaban wani restaurant tace “Na ce zan dafa abinci idan muka koma gida fa” Yace “Bana son kina tsaka da girki ki fara bacci” Tace “Ni dai mu tafi gida kawai ai ni ce nace zan yi” Yace “Gobe kya yi, kin ga ba ingredients na girki a gida” Bata sake ce masa komai ba, ya gama parking ya bude motar ya sauka, bayan ya dawo Khaleesat dai ko kallon abinda ya siyo bata yi ba, har suka koma gida bata ce masa komai ba, shi ma haka, Ta bude motar ta sauka tayi wucewarta ciki, ya bi ta da kallo, 40 mins da dawowan su Ajay ya shiga dakinta, tayi wanka tayi sallah har ta gama shirin kwanciya, taki kallonsa ta tafi kan gado ta kwanta, yana tsaye yana kallonta, sai kuma ya karasa gun gadon ya zauna gefenta yana kallonta yace “Baki ci abincin ba” Without looking at him tace “Dama ban ce zan ci ba ai” Yayi kasa da murya yace “Zaki fara ko Jeeddah” Taki cewa komai, dagota yayi a hankali yace “To me aka maki?” Ta fashe da kuka amma ba hawaye, ya jawota jikinsa ya rungumeta murya can kasa yace “To yi hakuri….” Cikin rawan murya tace “Dama tun da ka zo daukana naga kamar anyi forcing dinka ne ka zo ka dauke ni kana ta fushi, to da ba kawai sai ka kyaleni in dawo da kaina ba a cikin adaidaita sahu” Ya ɗan yi murmushi yana shafa gashinta yace “Allah ya baki hakuri, amma ni ba fushi nake ba, kiyi hakuri ki ci abincin” Bai jira me zata ce ba ya mike ya fita ya dauko mata abincin, haka ya lallabata ta ci sannan ta shiga bandaki ta wanke bakinta, tana kwanciya bacci ya dauketa, wajen karfe sha biyu Khaleesat ta farka taga baya dakin, sauka tayi daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka ta fita daga dakin, downstairs ta gansa zaune yana kallo, ta tsaya bakin stairs taki karasawa cikin Parlon, ya daga kai yana kallonta, ya mike ya nufeta yace “You need anything dear?” Ta hade rai tace “Me yasa zaka barni ni kadai ina bacci a daki” Murmushi yayi ya koma parlor ta bi sa da kallo, taga ya kashe kayan kallon ya rage wutan parlon, sannan ya dawo inda take tsaye ya dauketa gently ya wuce sama, kwantar da ita yayi kan gado, ya kashe wutan dakin sannan ya dawo ya kwanta kusa da ita yana facing dinta murya can kasa yace “Shikenan?” Murmushi tayi ta shige jikinsa, ta fara unbuttoning din masa Pajamas din jikinsa a hankali, ya taya ta cire rigan ta kwantar da kanta saman kirjinsa kamar me rada tace “I miss you so much” Yayi kasa da murya yace “To ai kin ki bani abun, for more than a week now ke da unborn kuna ta ja min aji, sai ki ce kin gaji” Ta kara shigewa jikinsa cike da shagwaba tace “To ina so yanxu, amma bana son ka dade, zan gaji” Tana fadin haka ta fara shafasa slowly, ya kai bakinsa kunnenta yayi mata rada sannan ya fara cire mata rigar baccin jikinta. Washegari tun da Khaleesat ta koma bacci da safe bata tashi ba sai da rana, shi ma saboda ya tasheta tayi sallan azahar, bayan ta idar da sallah ta ci abinci da ya siyo mata ta sake komawa bacci, sai kusan karfe biyar suka fita zuwa tudun Yola, ta kwantar da kanta jikin kujera tana kallonsa a hankali tace “Yau ma naga you are moody my prince, don Allah ka gaya min menene yake damun ka” Ajay ya juya ya kalleta, sai kuma ya maida dubansa kan titi, a hankali yace “Jeeddah…. Sai yanxu abubuwa suke dawo min afresh, I am so lucky to be alive today after all what happened to me, even though I still don’t know what I went through and how I found my self in Benue, I still don’t know the story, rashin komawa ta gun saviours dina har aka dau wannan lokaci me tsawo is making me feel guilty, let me not be an ingrate…. I am alive today because they helped me, that village is supposed to be a second home to me, the people of the village are suppose to be my second family” a hankali Khaleesat tace “But ai kana da intention din zuwa ba wai baza kaje kwata kwata ba, beside we left for America for ur surgery, representative where sent to Benue after we left for America, kawai dai basu gane inda za a samu mutanen bane cause garuruwan da yawa, You are not an Ingrate my love, nasan dole zaka koma wajen su, truly they are our family too” Ajay yace “In few days time in sha Allah zan je Benue, idan ban je ba bazan samu nutsuwa ba, ni nasan inda zan samo su” Khaleesat ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, after some seconds tace “To kai kadai zaka je?” Yace “I am going with Jay, idan nace sai mun koma Bauchi za mu kara bata lokaci ne, kuma Mai martaba zai iya cewa za mu je tare da shi, Kinga sai sanda yake da lokaci ne hakan zai yiwu” Khaleesat ta gyada masa kai a hankali tace “Haka ne, but ina son zan bi ka nima” Ajay yace “The only means of transportation to the village is by water Jeeddah” Tace “Ehh ni dai ina son ka je da ni plsss” Bai ce komai ba, cause condition dinta yake dubawa, baya son wani abu ya samu karamin cikin jikinta, ta marairaice tace “Ka ji” Kawai don kar ta daga masa hankali ta daga nata hankalin yace “Na ji wife” A haka suka isa tudun Yola, Ajay yayi parking bayan wata mota dake gaban gidansu Khaleesat, Khaleesat dai sai kallon motar take wondering whose car it is, Ajay ya kalleta yace “Zaki kwana ko?” Ta langwabe kai a hankali tace “Sai yanda kace dear” Ya ɗan yi murmushi, yace “Kiyi duk kwanakin da kike son kiyi” ya fada haka ne don ya samu yaje Benue ya dawo ba tare da ta sani ba, Tace “To mu shiga sai ka gaisa da su Nenne” Yace “Ki fara shiga first….” Tana murmushi ta bude motar ta sauka tace “Bari in sanar masu zaka shigo” Gate din gidan ta nufa ya bi ta da kallo, har Khaleesat ta wuce motar dake gaban nasu sai kuma ta tsaya bayan sun hada ido da Abdul dake zaune cikin motar, don suna hada ido ya bude motarsa ya sauko, yana kallonta da murmushi fuskarsa yace “Hajajju, Barka da yamma” Tana ɗan murmushi ita ma tace “Ina yini Ya Abdul” Yace “Lafiya lau, ya kwana da yawa?” Tace “Alhamdulillah” Yace “I came to see a frnd, ya mai gidan naki? Ko tare ku ke?” Khaleesat tace “Eh tare mu ke” Abdul ya kalli motar Ajay sannan yace “Bari in je mu gaisa” Yana fadin haka ya nufi gun motar, tunda ya sauko daga motarsa dama Ajay ke kallonsa, sai da Abdul ya iso har kusa da motarsa sannan ya bude motar ya sauka, Abdul ya mika masa hannu suka gaisa, ita dai khaleesat ta nufi gate din gidansu tana kallon mutumin dake zaune bakin gate din alamar Mai gadi ne, gaishesa tayi ya mayar mata da gaisuwan da ladabi, ta shiga cikin gidan, bin ko ina ta dinga yi da kallo tsabar yanda gidan ya canza ya dawo kamar lokacin aka gina sa, ga flowers din gidan duk sun girma, ko ina was very neat, babu kowa a compound din gidan ta karasa har cikin parlor nan ma taga tsadaddun furnitures da aka canza a parlon har da TV da labule da carpet duk an canza, infact komai na parlon sai da aka canza, ga dinning table sabo a dinning area, bedroom din Ummanta ta nufa taga bata ciki, nan taga sabbin kayan gado masu tsada sosai a dakin, ta dawo ta tafi dakin Nenne, farin ciki gun Nenne ba a cewa komai bayan Khaleesat ta rungumeta tana mata Oyoyo, Nenne tace “Ikon Allah, saukan yaushe Khaleesat?” Khaleesat na murmushi tace “Jiya muka shigo Kano daga Abuja” Nenne sai kare mata kallo take ganin yanda take sheki, gashi duk ta cicciko, Nenne na washe baki tace “Ina mijin naki?” Khaleesat tace “Yana waje, Nenne ina mutanen gidan? Naga ba kowa” Nenne tace “Uwarki ta shiga gidan Hajiya Zaliha dubota bata ji dadi kwana biyu ba, yara kuma gaba daya sun tafi islamiyyah, Kinsan yanxu ba a wasa da karatu daga islamiyyan har boko a gidan nan, kannenki dama shirye shiryen saukan Al-qurani suke, sun haddace Al-qurani me tsarki, nasan dai uwarki ta gaya maki” Khaleesat na murmushi tace “Eh ta gaya min, to ina su Mama Zubaida?” Nenne tace “Zubaida na can bangarenta yanxu dai atamfofi yake siyarwa da leshi, Shatu kuma taje kauyensu biki ita kuma craw fish take sarowa buhu buhu tana siyarwa, duk Farida ce ta basu jari yan wahala” Khaleesat tace “To babana fa, ko yana kasuwa?” Nenne tace “Malam Ali na kasuwa, kin san yanxu shagunan sa na kayan hatsi hudu a kasuwa, sari ma yake badawa baya awo, yaran shagunansa sun fi takwas yanxu haka, bana ma da shi za ayi aikin Hajji, duk juma’a sai mun yi sadaka kwana biyar a gidan nan da rana, da safe kuma ayi sadakan koko da kosai” Khaleesat na murmushi tace “Alhamdulillah, Umma ta gaya min, yauwa Nenne naga Ya Abdul kofar gida yace min ya zo wajen wani abokinsa, waye abokinsa a layin nan?” Nenne tace “Wani aboki?? Bai da wani aboki a layin nan karya yake, wani ranan juma’a ne fa da ya zo wai gaisheni sai suka hadu da ɗan mijin Hajiya Zaliha yaro me hankali me sunan babanku ana ce masa Haiydar, shi ne fa suka gaisa suka ɗan yi hira da yaron, tun daga sannan ya fake da cewa wajen Haiydar yake zuwa a unguwan nan, kuma wallahi ni na ganosa wajen Noor yake zuwa sai yace ya zo wajen Haiydar, duk yamma haka zai zo kofar gidan nan yana jiran ta dawo islamiyyah, ni dai har yau ban yarda da Awdul ba, a tsorace nake da shi, zan ce kar ya sake zuwa Zahra’u ta hanani wai in kyalesa kawai, shi ne Haiydar ke ce min ai mahaddacin qur’ani ne ga sanin addini kaca kaca a kansa, wai idan ya fara rero karatu kai kace Shek Sudess din Saudiyya ne, to kin san Noor ita ma akwai kira’a kuma in dai ka shigo gidan nan ranan juma’a zaka sameta ne tana karatun ta, to in gaya maki kwana daddaya ne Awdul baya zuwa kofar gidan nan, ni dai har yau ban yarda da shi ba, lokaci kadan nake jira na ja masa layi da zuwa unguwan nan yana tare min jikata a bakin gate idan ta dawo islamiyyah, bai san ni bane da Sarkin Bauchi zan hadasa wallahi” Khaleesat dake ta kallon Nenne ta sauke idonta a hankali tace “Ni na yarda da shi Nenne….”



