Fentin Zina Page 5 Hausa Novel
Bacci yadan soma fisganta ta farka tana mai jin babu dadi sakamakon karar wayar Abdul daya cika kunnenta da alamu shi har yayi nisa a baccinsa, ta mika hannu da nufin daukar wayar ta sakata a silent daidai wani kiran ya shigo ta dauki wayar tana kallon screen din da mamaki da al’ajabi ‘my world’ taga an rubuta akan number nan take zuciyarta ta bada wani irin sauti dummm.Bisa tsautsayi yatsarta ta taba finger print din wayar sai tayi received domin ya saita ta a hakan ne, daga cikin wayar maryam ce take cewa “amma dai kasan baka mun adalci ba ko? Kayi mun alkawarin kirana idan ka huta sai kuma ka barni da damuwar rashin jin halin da mijina yake ciki wannan ba daidai bane” jin ba’ayi magana ba sai take ta cewa “hello! Hello!!” Daga bisani ta kashe wayar.Ameena dake kwance ta mike zaune cikin wani irin halin da batasan ya zata fassarashi ba, hakika zuciyarta ta shiga rudani da kuma firgici sannan bata son bawa kanta damar zargin mijinta toh amma ya zatayi, a hankali ta soma magana da kanta tana cewa, “wannan wacece take kokarin shiga cikin rayuwata ta mun illah, ya Allah ka kare ni daga sharrinta ka kuma nesantata daga mijina”.Kamar a mafarki abdul yake jin maganganunta har dai ya tabbatar da zahirine ba mafarki kawai ba, ya bude idanunsa duka akanta ya ganta zaune, yace cikin muryar bacci “meya faru dake kike zaune? Akwai abunda ke damunki ne?” Ta girgiza kai “a’a babu komai yanzu dama zan kwanta ne” bata bari ya sake cewa komai ba ta kwanta ta juya baya tana mai jin wani irin tukuki a cikin ranta.Shima bai sake cewa komai ba saima gyara kwanciya da yayi ya ci gaba da baccin sa hankali kwance.Ameena kuwa bata yi wani baccin kirki ba a wannan daren, sai yau ta kara sanin girman lamarin kishi lallai ta kara tabbatarwa Abdul na sonta kuma yayi mugun kokari sosai na kokarin faranta mata a yau abunda ya faru kadai take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta huta sai ta danganta hakan ga Abdul, dole zaiji fiye da haka a ranshi dole ya kasa sarrafa kanshi a duk lokacin da wani abun ya shiga tsakaninsu daya danganci kishi, na miji koda aure kikayi kika fito idan bai danne zuciyar shiba zaiyita samun matsala da matar bare kuma ace ta haihu ba tare da aure ba wani can ya fara saninta a matsayinta na diya mace kafin shi daya kasance mijinta, a daren tayi kuka sosai tayi dana sanin abubuwa da yawa ta nemi tuba a gurin ubangiji yafi a kirga karshenta kin karasa kwana tayi a dakin ta koma nata dakin tayi alwala ta jera nafilfili tana kai kukanta ga Allah madaukakin sarki.Washe gari data tashi idanunta sunyi suntum sakamakon kuka da rashin bacci, tayi dukkan aikace aikacenta data saba, lokacin ya fito harya kammala shiri don tun da ta tasheshi yayi wanka ta fiddo mai kayan dazai saka tace tana dining idan ya gama tayi waje, zama sukayi suka ci abincin saida suka kammala sannan ta dubeshi cikin natsuwa da kwantar da murya dontana son masa magana akan jiya ta kasa hadiye maganar a ranta, “ruhul jasad jiya da kana bacci wata ta kira wayarka”.Daga inda yake zaune yaji wani abu mai kamar tafiyar mashi yazo ya dake shi tun daga tafin kafar shi har zuwa kanshi, bai dago ba kuma baiyi magana ba domin koya bude baki baisan me zai fada ya kare kanshi ba.Ta dan numfasa sannan ta cigaba da fadin “naga ka rubuta my world a sunanta dan Allah inaso so ka fada mun gaskiya game da ita kada ka fada mun sabanin abunda kasan ba gaskiya bane, zai mun ciwo ka boye mun gaskiya fiyeda abunda zanji na gaskiyar”.Shiru yayi sai can kamar ya tuna wani abu yace yana kallonta “ba wata mummunar alaqa ce a tsakanina da ita ba, soyayyace kawai wacce muke sa ran ta kaimu ga aure”.Saukar da kai tayi daga barin kallon shi tana mai nadamar tambayar shi, hawayene suke kokarin taruwa mata a ido sai tayi kokarin maida su ta kakaro murmushi ta aza a fuskar ta tace “Allah sarki! Allah ya tabbatar da alkhairi”.”Ameen” yace yana mikewa tsaye tare da cewa “idan kina bukatar wani abu akwai kudi a drawer na ajiye, muje kimun rakiya kada in makara sannan dan Allah kada kisa tunani na daban a ranki gameda wancan yarinyar ina fatan kin fahimta”.Gyada kai tayi ta mike ta Karbi jakarshi ta rataya a kafadarta tayi murmushi tace “kada ka damu babu komai ai, ni banida ikon hanaka abunda Allah ya halasta maka sannan kuma kanada damar auro wasu har su uku idan kanada halin yin hakan”.”Naji muje kada in makara” ya fada kamar da dan hasala kadan.Tsuke bakinta tayi ta rakashi ya shiga mota ya tafi yana daga mata hannu, saida ya bar gidan gaba daya tukun ta juya ta koma falo ta zauna ta zabga tagumi tama rasa wani irin tunani ya kamata tayi, zuciyarta cike take da tarin kunci da damuwa karshe ta yanke shawarar hawa online don debe kewa, takoyi sa’a fateema tana kan WhatsApp don haka hira sukayi sosai har take ce mata jibi zata zo Ameena tayi farin ciki dajin haka koba komai ta dan rage wani abu daga cikin damuwar da take ciki.**** ***Ta bangaren Abdul yana isa office ya tarar seceteriyarsa harta riga shi zuwa, baiyi mamaki ba duba da jiya ya mata alkawari kuma bai cika ba sannan ta kira bata same shi ba.Takowa tayi ta rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya ta dago ta dube shi tace “nayi kewarka masoyi, kaki ka kirani kuma na kira ka dauka baka ce komai ba”.”Sorry nayi bacci sanda kika kira, matata ce ta dau wayar banma sani ba sai da safen nan take fada mun”.Dan bata fuska tayi tace “nima ai na kusa zama matar taka sai ka raba komai gida biyu indau rabi tadau rabi ko?”.Suka shiga office din ya sauna a kujerar shi, itama ta ajiye jakar tashi saman table taja kujera ta zauna.Ya dubeta yana cewa “yanzu muna farkon wata idan zai yiwu ina so muyi aure zuwa karshen watan nan”.Dadi yasa ta tashi ta buga tsalle kana taje ta rungume shi tana wage baki domin har cikin zuciyarta take some shi kuma ta jima tana masa tayin suyi aure yana kaucewa gashi yau yazo mata da albishir.”Dear yau ka faranta mun ka saka ni farin ciki nagode! Nagode sosai”.Murmushi yayi yace “kada ki damu kedai ki sanar da iyayenki cewar za’a taho neman aurenki gobe idan Allah ya kaimu”.”Nagode! Yanzuma zan kira mamata na fada mata nasan zatayi farin ciki”.Ki koma bakin aikin ki domin daga gobe itace ranarki ta karshe a wannan company din don bazan lamunci matar da zan aura tana sintirin zuwa aiki ba.Da haka ta koma kan aikinta tanayi tana jin dadi har aka tashi ya fito cikin shirinshi na tafiya gida ya kalleta yace “bye sai gobe ba sai kin tashi ba ina saurine”, ya fada lokacin da take kokarin mikewa daga kan kujerarta, fasa mikewar tayi ta zauna ta daga masa hannu ya tafi.Gidan iyayenshi ya nufa don so yake yaje musu da albishir din da suka jima suna jira.Mamar shi da kannen shi su biyu ya samu a falon bayan sun gaisa yake tambayar ina Abba? Mama tace “yana dawowa yanzu”. Bata gama diga aya ba Abba yayo sallama suka amsa yana fadin “Abdul ne a gidan namu yau? Anyi kusan sati rabon daka zo fa”.Sosa keya yayi yace “yi hakuri Abba lamarin aikinne idan na fita tun safe sai yamma nike komawa gida, bana samun hutu sai weekend yanzun ma wani muhimmin al’amarine ya biyo dani”.”Ayya Allah ya taimaka toh ina dai fatan lafiya?” Abba ya tambaya.Sosa keya yayi ya soma fada cikin dan kunya “Abba daman wata yarinyace muka jima muna soyayya da ita shine na yanke shawar zan aureta tunda mun daidaita abunda yasa nazo in fada muku kenan”.Murna suka hau yi mama tana cewa “Allah yasa rabon ‘ya’yanka ke kiran ka dama tun farko ki kayi, ka nace wa zama da waccan lalatacciyar amma yanzu komai ya wuce tunda har zakayi aure nagode Allah”.Abba ya dubesu duka yaga yadda suke farin ciki kamar auren shi na farine akace zaiyi yace “ki daina irin wannan abun, ba’a hanashi yayi aure ba amma ba daidai bane ki dinda aibata matar shi domin dai kin haifa don haka ki san me zaki dinga fada akan ‘ya’yan mutane kai kuma kaji tsoron Allah kada kayi wannan auren da nufin musgunawa ga ita matar ka, idan kayi haka Allah bazai barka ba”.”Insha Allah Abba”.Ya ci abinci anan gidan nasu tunda an gama ya tashi ya musu sallama ya tafi gida.Kamar yadda aka saba ta tarbeshi babu alamun bacin rai a tare da ita ko canjin fuska, ta taimaka mishi yayi wanka ta jawoshi dining ta soma zuba danwaken data musu, yace “barshi haka domin naci abinci a gidan mama a koshe nike donma kada kiji babu dadine yasa zan dura a dole”.Murmushi tayi tace “Allah sarki ai basai ka takura kanka ba idan kanajin cin zai zamar maka matsala, ya ka same su, suna dai lafiya ko?” “Eh sunma ce a gaishe ki” ya shirga mata karya.”Ina amsawa” ta fada lokacin da take kai lomar farko bakinta, shima cin ya fara amma ya rigata koshi, saida takoshi ta tattare gurin ta kaisu kitchen lokacin ana kiran sallah, ya wuce masallaci itakuma tayi sallah a falo.Bai dawo ba saida akayi sallahr isha kafin ya dawo gida.Sun dan taba hira kadan a falon kafin ya tattara duk wasu kalaman shi ya soma magana “ina so ki saurareni da kunnen basirah ki kuma fahimceni”, tattara natsuwarta ta maida kanshi.Yaci gaba “akan maganar safe da muka fara ce gobe insha Allah za’a tambayo mun izinin auren ta a gidansu kuma auren za’a saka shi zuwa karshen watan nan, kiyi hakuri ba zanyi aure don in tozarta ki ba ko in wulakanta ki ba ki dauka cewa kaddarar muce hakan, kiyi list din abubuwan da kike bukata ko nawane zan miki sannan zan hada ku a nan gidan ne kafin zuwa gaba in canja miki gida ita ta cigaba da zama anan”.Tunda ya fara magana ta rasa a wace duniya take bata masan ya gama maganar shiba har saida ya dan taba ta kadan ta dawo hayyacinta, tayi saurin boye firgicinta tace “am Allah ya taimaka zan shiga daki indan kwanta kaina ke ciwo sai anjima zan shigo dakin ka”.”A’a ba sai kinzo ba da kaina zanzo yau a dakin naki zamu kwana”.Murmushi tayi ta mike ta shiga daki, ya bita da ido yana mai jin tausayinta a ranshi da yana da damar barin auren nan daya fasa amma zahirin gaskiya zuciyar shi a kwadaice take daya auri budurwa sabuwa dal ko zai rage radadin da yake ji game da Ameena.Ameena Koda ta shiga daki fadawa kan gado tayi ta fashe da kuka mara sauti, kuka takeyi sosai yayinda kwakwalwar ta ta shiga hasko mata lallai idan Abdul ya auri budurwa ta shiga uku dole zai fifita waccan akanta saboda ta kawo masa budurcin ta gidan shi bata watsar a titi kamar yadda ita tayi ba.Ta Kasa tabuka komai balle ta tashi tayi wanka ta sauya kayanta, a haka har ya shigo da shirin kwanciya ya sameta.Zama yayi kusada kanta yana shafa fuskarta cikin kulawa yace “sannu kinji har yanzu ciwon kan ne?” Kai ta gyada masa yace “ko muje asibiti?”.Ta girgiza kai ta mike zaune cikin son danne abunda ke bijiro mata tace “abu daya nike so ka daukar mun alkawari akan shi Abdul”.Cikin son sanin abunda zata ce ya kama hannunta ya rike.Yanzu ma aka soma, yanzune zamu fara ainahin labarin da fatan kuna tare dani. LIK£…COMM£NT..SHAR£…..FISABILILLAHI.MATAR MAJEEDADI✍️


