Gargadar So Chapter 104 By M Shakur
Da gaske Khaleel yana sonta? Wait haka yakeson duka sauran matanshi? Her body is telling her yana sonta dan the way yake magana da ita you will know he meant every word but she’s curious idan haka yakeson matanshi mesa yake sakinsu to? Tana zaune awajen taji muryan Noor tana Mom FAA saitaji Mom na kiranta ta tashi ta leka taga Mom na rungumeta, koda Mom bataso tazo side nata she can’t take away the fact that Mom kam na son Noor irin mugun so din nan, cus zata fito taraka Noor har Mota sannan duk idan Noor zata dawo duk rana Mom na waje tana jiranta ashigo da ita, they share deep bond na grandmother da granddaughter, she understands cewa itama Mom na bukatan abokiyan hira and Noor akwai shiga rai, mutanen sunason yara irin sosai din nan wlh, she’s feeling bad ba’abar Noor tazo wajenta ba but kuma saitama kanta fada waye ita? She just come to the house mesa zata dauke musu jikansu su suka raini Noor din zuwa yau tunda mahaifiyarta tace daga asibiti suka karbi Noor, ijiyan zuciya ta sauke takoma ta zauna tarasa abinyi, ba hayaniya agidan babu abinyi, she’s just bored inama gobe zata koma aiki, and wlh she’s missing Khaleel sosai kaman yadaina zuwa aikin saikuma tace yadaina zuwa haka zaita cinta from safe zuwa dare, at least yanzu tana hutawa, tana wajen akai knocking ta window ta leka taga PA tareda wasu ma’aikata na saloon da uniform ajikinsu tawuce as Khaleel instructed abaya tasaka ta yafa mayafin tazo tabude kofa dukansu suka gaidata with so much respect harda PA tace “Ma Sir yace akawo su wajenki” ahankali tace “come in” shigowa tayi sunzo da komi bayin nan falo suka shiga suka wanke mata kai aka fito aka fara blow drying sannan suka fara mata kitso yan kanana around 2:30 wayanta ne yafara ringing tadauka Khaleel ne dauka tayi takai kunnenta cikeda so yace “an fara kitson?” Gyadamai kai tayi tace “uhm” ahankali yace “hannun mai kitson da zafi?” dan dariya tambayan yaso ya bata tace “a’a babu” anatse yace “i told them banson wacce hannunta ke zafi idan suka samin kan matana yayi ciwo they will have to deal with my anger, kitson yana kyau?” Wani kalan mamaki tambayan yabata tace “nima I don’t know” Dasauri yace “snap it kituramin ta watsapp lemme see” yana maganan ya katse wayan tsayawa Hawwa tayi tana kallon wayan kaman bazatayi ba saita shiga snap tama kitson dasuka just few video sannan tashiga watsapp tunawa tayi batada number shi dawowa tayi wajen calls tayi clicking number zatai saving tafara tunani wani suna zata samai sai kawai tai saving da IK Ibrahim Khaleel short form tashiga watsapp ta turamai sharp sharp yabude sai kawai taga yakirata video call kaman bazata dauka ba ta dauka tadan harareshi murmushi yamata yace “you look beautiful wowwww” yakalli jikinta ganin tasaka abaya yace “good gurl” dauke kai tayi yace “i love you My Hawwa talk to you later” ya katse wayan tayi shiru tana kallon wayan sai kawai tashiga profile picture nashi hotonshi looks so good and handsome, zuciyanta sai bugawa yake tana kallonshi fita tayi tana duba komi nashi ma watsapp taga IG nashi is link to watsapp dasauri tashiga Khaleel nada 30 something million followers ga hotunan shi a page nashi comment dubu yawanci mata daga mai cewa my crush, my dream man, my menene kawai taji kirjinta na zafi, hoton bikinsu dataga yasa yadansa taji dadi tashiga da gudu 15k comment tagani yawanci mata ke tura emoji na kuka guys kuma na dariya wasu na cewa he’s off the market finally za’aga page namu, some comment da maza keyi har suka shiga bawa Hawwa dariya dan wani harda cewa Allah ya kara, wani yace na tabbata wasu na ICU Lee yayi aure, wani yace only heir na Mangal is taken Nigerian ladies we can now bretheeeee.Hawwa tadinga dariya, saita shiga story shi taga video shi da nata ne ne yasa tana bacci ajikinshi a mota rannan da akayi dinner kunyane yakamata itafa batason PDA public display of affection saikuma ta tabe baki aranta tace abinda zai iya sakina anytime gwara ya daina nunani ma duniya thank God I’m a ghost a online saidai zuwa kallo banma cika shiga ig ba ko suna babu akan account dina same with su tiktok da snap watsapp kawai takeyi shima sabida aiki da Ni’ima ne, tuna Ni’ima yasa taji tadamu ko tafito daga prison oho ta gwada tambayan Khaleel? Saikuma tace no.Wuraren 4 aka gama everything kitson yayi kyau shade aka mata but mai style kaman wata shuwa tace “nawane” dasauri sukace no Oga yabiya komi dudda haka saida Hawwa tamusu kyautan kudi suna mata godiya sosai suka tafi ta share falon tass ta goge koina ba gashi ta kunna turare ta tafi sama tai salla tafito tadaura girki tanaso tayi dasu Mom takira Baba sukai hira tanadan kunyanshi sabida karanta da Khaleel yayi tai magana da Umma umma tagayamata Miemie takoma school sannan tai sallama dasu takira Ammi tai magana dasu Ramla, takira kanninta su Hafsa tana rokanso da suzo sukace to zasuzo ranan sunday.Around to 6 yagama ganin all patients nashi Sam dayaci bacci yakoshi yakalleshi yace “let’s go” dan yatsine yayi yadauki yazare lab coat nashi daga jikinsa yace “Sam I don’t wanna go besides I’m even hungry inaso naje gida I know matana must have made me something delicious” kaman Sam zaiyi kuka yace “common Leee please I don’t want to go ni kadai babu kai banjin dadi Allah saimu tafi dawuri 8 mun tafi I promise”Shiru yayi yaki magana Sam yace “can’t you do this little thing for me just accompany me pleasseeeeee” dan lumshe idanu Khaleel yayi yace “okay but 8 nabar wajen I’m a married man now” tsalle Sam yayi yace “deal” wucewa sukayi suka fito har wajen dayayi parking ya wurgamai key yace “drive kaikabar motanka anan” karban key Sam yayi ya suka shiga yajasuInda suke party da nisa chan kaman za’abar Abuja ne, infact around 7:30 ma sukakai aka bude musu gate suka shiga ciki manya manyan security ana tsaresu dan yaran manyan mutane ne da yaran turawa masu kudi ga wasu mutane tsirara ana ganin Khaleel aka fara ihu Lee Lee Lee kaman wani celebrity yazo yayi murmushi still not feeling comfortably ga waiter yakawo musu shot daukan musu Sam yayi yabama Khaleel daya ahankali yadan yatsine fuska yace “nooooo ahhhh” Sam yace “common dalla ana kallonmu don’t embarrass me” Ahankali Khaleel ya karba yakai bakinshi wai yau shine har faduwa gabanshi keyi zaisha abu sabida Hawwa but yanda kowa ke kallonshi ana ihu ana Lee ga Sam shima yasa gently yakai bakinshi ya kurbe duka is just one shot babu abinda zaimai, aka kawo shisha Sam yabashi pipe Khaleel ya yatsine fuska Sam yace “wai Khaleel mehaka? Ba I promise you you will not get high ba bagashi nan just one shot na bari kasha ba na tequila ba, let’s smoke jor have some time for yourself today” Moh yace “dudeeeee enjoy yourself” dan karba yayi yakai shishan baki Sam ya kashe ma Moh idanu sukai murmushin mugunta dan shisha yaji hadi ko shot na tequila sun saka abu Khaleel yafara busan hayaki one two three yaki karasha yarike a hannu dai yana magana dasu..….Har magrib Khaleel bai dawoba Noor ma ba’a batta tazoba ita kadai agidan bata wani so tana kiran Khaleel but har tai Isha’i bai kirata ba gashi taci gayu gidan sai kanshi yake yau lace tasaka pink dogon riga tsayinta yafito sosai bata saka dan kwali ba sabida yaga kitsonta dayayi masifaffen kyau 8:15 daidai Hawwa tadauki wayanta ahankali kaman kartayi takasa daurewa tai dialing number shi, Khaleel na zaune yanashan shisha idanunshi sun soma juyawa yama kasa tashi wayanshi yashiga ringing dasauri yakai hannu yaciro wayan yana bude idanu da kyar yakai wayan hannunshi zai danna wayan ya dauka Moh ya kwace wayan garin kwacewa ya danna wayan ya amsa kiran bai sani ba yace “Leee common let her be! Yarinyar dazaka saka bayan ka moreta ka auri wacce is better than her kake wannan rawan jikin akanta let’s party jor, nakira strippers Babes dinchan sudanyi pleasing naka I know you’re horny already this one da you’re high, common DJ put hot beat for Lee everybody shout Lee” yanda kirjin Hawwa ke bugawa ranta na baci kaman zata haukace tana Hello Hello Hello saitaji an kashe wayan wlh wlh kaman zata kashe kanta the part dataji ana cewa mata su mene mene huuuu ta fuzar da iska saita tashi tafara zagaye dakin sai kawai tai ihu tace “I hate youuuyyy!I hate you! I hate you!” kaman zata kama da wuta zuciyanta na tafarfasa yana tuna yammata dataji ana fadi sai kawai tadauki wayan data jefar akasa direct takira number Abraham ringing daya biyu yadaga yace “Hey Miss Hawwa our Amarya” dan murmushin dole tayi tace “I will call you properly muyi magana can you track a number for me now please” dasauri Abraham yace “sure ina gaban laptop dina” number Khaleel tashiga kiramai kai tsaye ashe ta haddace number sai yanzu tasani yace “give me 2min” thanks tace ta ijiye wayan ta shiga closet nata ta fito da akwatintana gida kawai ta ciro uniform nata na yan sanda ta saka tai rolling gyale kanta tadauki bindiganta ta makala a a gun vest nata tafito bayan tasaka boot tadauki wayan taga abraham yaturo mata location din kawia ta dauki wayan Ya Allah zuciyan Hawwa yana saman kanta not kirji bamatasan metake ba key mota kawai tadauka tafito tayi wajen motocinsu ta danna taga motan dayayi kara ta shiga tai connecting location din da motan kawai taja motan aka bude mata gates tafita.




