Halysaah Page 132 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 132…Ajay ya juyo da ita tana facing dinsa, har sannan bata fasa kokuwa da shi ba hawaye cike idonta tana cewa “Leave me alone, bana so, nace zan maka ihu idan baka kyaleni ba” Calmly yace “Shi nake jira kiyi ai” Har strength dinta ya fara karewa bata iya ta kwace kanta daga rikon da yayi mata da hannunsa daya ba, hakan yasa ta fashe da kuka a hankali tana shessheka, ya jawota kusa da shi yana kallonta har suna jiyo breathing din juna, yayi kasa da murya yace “Ba a ji sosai, increase the volume” Ta daga kai ta kallesa cikin duhun dakin har sannan tana kuka sosai, wani bakin ciki taji ya tokareta a kirji, a fusace ta fixgo hannunsa daya zata gatsa masa cizo yayi saurin warce hannun da mamaki yace “Ko dai mayya ce ke” Ko rufe baki bai yi ba ta riko dayan hannunsa da sauri shi ma zata ciza a fusace, nan ya fara turata yana komawa baya yaki yarda ta cijesa, kokuwa ta dinga yi da shi struggling to bite him, tun yana dakewa yana turata har bai san sanda ya fara dariya ba don she was very serious da gaske cizon sa zata yi, ta kara sautin kukanta jin dariyar da yake, lokaci daya ya dena dariyar after realizing he was laughing, kawai yaga ta finciko rigarsa zata gatsa masa cizon a kirji, tun bata yi hakan ba ya dauketa da hannu da ya cillar da ita saman gado yace “Sai dai ki ci kanki, ai ban san mayya bace ke” Da sauri ya bar wajen ganin ta kara saukowa daga saman gadon ta nufo sa, yayi maza ya tafi ya kunna wutan dakin, tana ganin haka ta kara rushewa da kuka ta sulale kasa tana jawo hularta da ya fadi zata saka, shi kam kallon dogon gashin nata yake, bayan ta sa hular ta mike ta tafi can karshen gadon ta kwanta ta rufa da duvet tana shesshekan kuka, a haka bacci ya dauke, can wajen karfe biyun dare ta farka saboda iskan da ake sosai yi alamar za ayi ruwa, mikewa zaune tayi tana bin dakin da kallo don ba haske ko kadan, handbag dinta ta dinga lalubawa tana dubawa har ta gani ta dauka ta ciro wayarta ta kunna Flash, haska dakin ta dinga yi gaba daya ta gansa kwance kan darduma a kasan tiles, sai kuma ta haska ledan abincin da ya ajiye mata daxu, sauka tayi daga kan gadon ta tafi ta dau ledan abincin ta bude ta fara ci, tana cikin ciki ruwa ya sauko sosai, bayan ta gama cin abincin ta tafi ta wanke bakinta a bandaki sannan ta dawo ta kwanta ta rufa da duvet ta kashe Flash din wayarta, it was raining heavily hakan yasa garin yayi sanyi sosai, bayan kusan minti goma sha biyar ta sake daukar wayarta ta kunna haske ta ajiye kan gadon, sai kuma a hankali ta koma karshen gadon ta inda yake kwance tana leka kasa taga idonsa a lumshe har sannan, duvet din saman gadon ta jawo ta rufa masa tana gyarawa taji ya fixgo hannunta saura kiris ta fado kansa tayi saurin warce hannunta tana turo baki ta koma baya, yace “Cizon nawa kika zo kiyi?” Taki ce masa komai ta koma inda take kwance ta kwanta ta rufa da hijab dinta, bata kara farkawa ba sai Asuba har sannan ba a daina yayyafi ba garin yayi sanyi ba kadan ba, ta kalli duvet din da ya rufa mata, ta sauke sannan ta mike zaune ta jawo wayarta ta duba agogo ta kunna haske, bata gansa a dakin ba duk tunanin ko masallaci ya tafi, ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki, har ta idar da sallah tayi azkar dinta ta kwanta bai shigo dakin ba, nan kuma bata san wani dakin ya fita ya sake biya ba saboda sanyin da ya damesa kwanciyar da yayi a kasa. Khaleesat na cikin shiryawa bayan tayi wanka wajen karfe goma aka yi knocking kofar dakin, kallon kofar tayi for some seconds, can ta dau hijab dinta ta saka sannan ta karasa ta bude, breakfast aka kawo mata daga hotel din, ta amsa tray din tana amsa gaisuwar ma’aikacin sannan ta juya ta koma cikin dakin, ta dade da gama breakfast tana ta zaune gefen gado tana danna wayarta Ajay ya shigo dakin, kallo daya tayi masa ta dauke kai, amma tayi mamakin ganin shima ya shirya, to ko gidansu ya tafi na nan Kano, bata dai ce komai ba ta ci gaba da danna wayarta, ya dau wayoyinsa da katin kudi sai wristwatch dinsa da makullin motar da ya amsa hannun driver, without looking at her yace “We are leaving” Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, bai taɓa mata magana straightforward ba tunda ta san sa sai yau, bayan ya fita ta sauka daga kan gadon ta dau hand luggage dinta da handbag, tana tsaye ta bi dakin da kallo to be sure she is leaving nothing behind sannan ta nufi kofa ta fita, cikin mota ta samesa zaune yana jiranta don shi zai yi driving din, ta bude back seat ta saka hand luggage dinta sannan ta koma gaban motar ta bude ta shiga. Bayan sun fita daga hotel din Khaleesat ta kasa daurewa don sai fargaba take kar taga sun dau hanyar airport and this means bazata je gidansu ba kenan, ta ɗan kallesa kamar zata yi kuka tace “Bazan je gidanmu bane?” Idonsa a kan titi yace “Oh, nan kano ne ko?” Ta wani kallesa, shi dai driving dinsa kawai yake, can ta daure fuska tace “Ni dai ka kai ni gidanmu in ga Ummata da kannena da Babana” Bai tanka ta ba, hakan yasa kawai ta saka a rai bazai kai ta gidan nasu ba kenan, hawaye ya cika idonta, can ta rufe fuskarta da gyalenta ta fara shesshekan kuka, ya ɗan kalleta yana ci gaba da driving dinsa, after some minutes taji yace “Awa nawa za ki yi a gidan?” A hankali ta zame gyalenta tana kallonsa, sai kuma tace “Just 30 mins” Bai ce mata komai ba, ita kuwa ta dinga raba ido tana kallon hanya har taga gidan nasu suka nufa, she was very happy don bata san sanda tayi murmushi ba tana goge sauran hawayen idonta, bayan minti talatin yayi parking dai dai bakin gate dinsu, ko kallonsa bata yi ba ta bude motar looking so excited ta sauka ta nufi gate din gidan da gudu, ya bi ta da kallo har ta shiga gidan, Khaleesat na shiga parlonsu ko lura da Nenne da wa enda ke zaune parlon bata yi ba don hankalinta gaba daya dakin Ummanta ya tafi, Nenne ta bi ta da kallo baki bude har ta wuce su da gudu tana kiran Ummanta cikin farin ciki, can Nenne ta kalli Mama Shatu tace “Wacece wannan” Lamisah dake tsaye bakin kofar kitchen tace “Khaleesat ce fa” Nenne tace “Khaleesat kuma?” Wata makociyarsu matar Mai gadi dake parlon tace “Au… Ko ita ce ke karatu kasar waje?” Wata Agwai me kawo ma Nenne Nono tace “Ai ko ga ta tana kama da su Isilam, duk yanda aka yi ita ce yayar tasu, kuma ita ke auran ɗan sarki a garinmu Bauchi ko?” Wata makociyarsu da gidansu ke farkon shigowa layi tace “Allah sarki, ai ko kamanninta daya sak da Umma da su Islam” Mama Zubaida tun wucewar Khaleesat tayi shiru daga labarin da take bayarwa a parlon, Nenne da takaici ya isheta dai tayi shiru ta sunkuyar da kanta, yanxu duk yanda take fafa da Khaleesat a unguwan nan ko wani gida babu wanda bai san sunan Khaleesat ba da wanda take aure da kasar da take karatu shi ne zata kunyatata gaban mutane ta tsallaketa kamar wata er banzar da bata taɓa sani ba ta nufi dakin uwarta, Almajirin Nenne ya leko parlon yace “Nenne an gama ba shukokin ruwa” A fusace Nenne tace “Kai ja can ka rabu da ni, ba an baka shinkafa ba daxu” Juyawa yayi ya fita daga parlon, Ko ina yayi tsit, can dai Nenne ta mike ta nufi dakin Umma, Mama Shatu da tayi mugun jin dadin abinda Khaleesat tayi ma Nenne ta fara dariya kasa kasa tana kallon Mama Zubaida da ta sha mur, Khaleesat na kankame da Umma cike da farin cikin ganinta, ita kanta Umma was very happy to see her duk da bata nuna hakan ba, Nenne ta shigo dakin tana huci tana kallonsu tace “To sai me? Khaleesat nace sai me?? Ni dai nasan da ban haifi Alin ba ban ga ta yanda za a haifoki ba don ubanki, to meye a ciki don kin ci mutuncin uwar ubanki a gaban yan unguwa da ke ganin mutuncinta kullum sai sun shigo gaida ni, Dama ni ban sa ran ko mutuwa Ali yayi ki kula da ni ba gwara in fita danjan Kabuga inyi bara, kuma duk nasarorin da za ki yi a rayuwar nan ni ce sila ba wani shege ba, in don ta uwarki ce ai da kin zama irinta ki ci tuwo ki ja carbi” Nenne na kai wa nan ta fice daga dakin, Aunty Farida na kallon Khaleesat da mamaki tace “Wai dama baki tsaya kun gaisa da mutanen parlon da Nenne ba Khaleesat?” Khaleesat ta ɗan tura baki tace “To ni ban lura da su ba Aunty” Umma ta buge bakin nata tace “Saboda ke makauniya ce ko mahaukaciya ba? Duk yanda zaki dauko min magana dama kin iya shi, ta yaya parlor cike da jama’a kice baki gansu ba?” Aunty Farida was speechless tana ta kallon Khaleesat, a fusace tace “Anya zaki yi hankali a rayuwarki ta duniya kuwa Khaleesat? To maza tashi ki fita duk kije ki gaishesu kar in maki dukan tsiya a nan, wawiyar yarinya kawai” Mikewa Khaleesat tayi kamar zata yi kuka ta nufi kofa ta fita, Umma tayi tagumi tayi shiru, ai kuma shikenan ta tsokano masu Nenne sai abinda ta manta kuma, Khaleesat ta tafi parlor ta gaida Stepmom dinta da mutanen dake parlon sannan ta nufi dakin Nenne ganin bata parlon, Nenne na zaune gefen katifarta ta dafe kai abun duniya ya isheta, to ai sai su Harira matar Mai gadi da Fatu me Nono su ce ba ita ta haifi uban Khaleesat din ba ma irin wannan tozarcin da Khaleesat tayi mata a gabansu, Khaleesat na shiga dakin ta fada kan Nenne tana murmushi tun bata ce komai ba Nenne ta hankadata tace “Tafi don ubanki” Khaleesat ta fashe da dariya tace “Toh don Allah ta yaya zan gane ki kin ci kwalliya haka, ni fa na zata wata yan mata ce zaune a parlon” Nenne tace “Uwarki Zahra’u ce yan mata” Ita dai Khaleesat dariya kawai take, tasan har Grandmum dinta ma tayi missing ba Ummanta ba kadai, ta kamo hannun Nenne tace “Tare fa yace za mu koma Amurka dake kike bata rai” Nenne ta sake fuska tace “Kai, haka yace?” Khaleesat tayi dariya tace “Har an fara maki Visa, dama ai kina da passport” Nenne ta fara murmushi tana gyara zama tace “To yanxu kaya zan fara hadawa?” Khaleesat was still smiling tace “A’a sai fa mun fara zuwa Bauchi sannan in za mu koma mu biyo mu dauke ki mu tafi” Nenne tace “Toh ki ja bakin ki kiyi shiru ko uwarki kar ki gaya ma bana son tonan asiri, shi kansa Ali sai ana gobe tafiyar zan sanar masa, ai sirri na da dadi” Nenne tace “Mike tsaye in ga” Tashi tsaye Khaleesat tayi, Nenne ta dinga kallonta daga sama har kasa, can tace “Ikon Allah, har yanxu shiru Khaleesah? Anya lafiya kuwa?” Khaleesat ta turo baki ta koma ta zauna, Nenne tayi shiru ta kankance ido alamar ta shiga damuwa, can tace “Kusan wata hudu fa yanxu amma in ganki wayam ba komai, gaskiya zama bai gan ni ba kuma, haka wancan gantalallen auren naki na farko kika yi kika fito ba wani labari, yanxu kuma ga auren arziki shi ma shiru, to Allah ya kai mu gobe da asuba akwai inda zan je gaskiya” Khaleesat ta kauda zancen ta kawo mata wani labarin, ta fi 30 mins a dakin Nenne tana ta mata labari, Mama Zubaida da Mama Shatu dai sun ki barin parlon suna zaune duk sun kasa kunne, gashi sai tsegumi suke basu ga Khaleesat da komai ba na tsaraba daga ita sai ita ta shigo gidan, daga karshe Nenne ta tafi kitchen wai zata yi ma Khaleesat Farfesun kayan ciki tunda akwai kayan cikin a freezer, Khaleesat ta koma dakin Ummanta, ta tafi kusa da ita ta zauna tana murmushi tace “Umma Allah ya sa da wuri su Islam ke tashi islamiyya, nayi missing dinsu sosai wallahi” Aunty Farida tace “Ina Junaid din ya sauka?” Khaleesat ta ɗan yi shiru, can ta kalli Aunty Farida tace “Kamar yana waje fa” Bude baki Umma tayi with shock, Aunty Farida da ta bude bakin ita ma tace “Me kika ce???” Khaleesat ta mike daga kusa da Umma tace “A cikin mota na bar sa, in ce ya shigo?” Da sauri Khaleesat ta fice daga dakin da gudu ganin Aunty Farida na kokarin jawo wayar wuta, Umma ta kalli Aunty Farida da damuwa sosai tace “Anya kuwa yarinyar nan Farida? Naga ta kara tabarbarewa babu arziki, sanda take tare da Abdul kamar ta fara hankali don abubuwanta da yawa sun ragu a lokacin, ko lokacin aurenta da Junaid din ai naga da nutsuwarta, yanxu kuma naga abu ya kara lalacewa” Aunty Farida tace “To shi Abdul ba ya gina mata tsoronsa da shakkarsa a rai ba, ina taga sararin tabara, ai ubanta yake ci baya daukar duk nonsense dinta, shi yasa ta nutsu a wannan lokacin ta dawo kamar ba ita ba, kinga yanxu da ta samu waje ai ta dawo gidan jiya” Da damuwa Umma tace “To yanxu haka Junaid din ke hakuri da abubuwan nan Farida? Ta ina za mu fara wannan lamari?” Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya wai a haka bata gaya mata iskancin da Khaleesat din ke masa ba ma.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788*




