Ruwan Zuma Page 26 Hausa Novel
(26) “Shikenan zan koma.�? Fad’in Haydar yana zungurin goshinta a hankali, dad’i da farin cikin da yake ciki shi kanshi bazai iya fasaltawa ba. Itama Laila dad’in taji a ranta domin har ga Allah bata so ya sake wannan aikin nashi. A yanda samun aiki ke da wahala a wannan zamanin ina d’an talaka zai samu? “Nagode Haydar. Baka San farincikin da naji ba game da hakan. Ya ka samu Ammi?�? “Tana lafiya tace a gaishe da amarya.�? “Ina amsawa, nasan yanzu tana can tana kewarka.�? Ta fad’i hakan zata matsa daga jikinshi ya hanata motsi. A hankali ya matso da kanshi fuskarta kana ya d’aura lips d’inshi kan nata, sakan biyar da haka ya d’age yana murmusawa. “Tell me about yourself Haydar. A ina kuka zauna before ku zo nan Kano?�? “Ruwan zuman fa? Ko har kin daina kirana dashi?�? Ya fad’i hakan yana mata cakulkuli tana zillewa. “Wallahi ba’a mini cakulkuli. Ka bari kar in suma.�? Ta fad’i hakan cikin dariya da kuma k’arancin numfashi. Barinta yayi ta matsa daga jikinshi tana haki tana danna mishi harara. Shi kuma bakinshi a washe domin hakan kad’ai da yayi ya samu ya kashe k’ishin ruwa na son ta6a jikinta. Sai da ta dawo hayyacinta sannan yace, “Zan fad’a miki amma sai lokacin da kika shirya kar6an aurenmu.�? Ya dubeta cikin nitsuwa yana murmushi. Ta gane me yake nufi don haka ta kad’a kai tana sauk’e idanunta k’asa tace, “Amma ina fatan zaka yafe mini ka mini uzuri domin nasan hakan da nake yi zunubi nake kwasawa kaina.�? Kamo yatsun hannunta yayi yana mata kwas kwas yace, “Na yafe miki Laila, I know to back off when a lady says No. Amma make it fast domin ina gudun kar na rasa hankalina. Ina buk’atar matata.�? Gyad’a kai tayi kana ta kamo nashi yatsun tana mishi abunda ya gama mata. “You know what?�? Ta tambayeshi. Girgiza kai yayi tace, “I’m glad I meet you. Sannan ina godewa Allah da yasa ka zama mijina ba wani ba. Anya kana sona kamar yanda nake sonka?�? Jawota yayi ta dawo kanshi yayi caging d’inta da k’afafunshi domin ya lura tana son zillewa ne. “Haydar ka sauk’eni, ina da nauyi fa.�? “Baki da nauyi Laila, asalima in banda wannan….�? ya ta6a bayanta. �?…babu wani abu mai nauyi a jikinki. Wai meyasa baki yi k’iba irin na manyan matan nan bane?�? “Kana son mace mai k’iba ne?�? Ta kwantar da kanta kan k’irjinshi domin ta gaji da resisting feelings d’inta domin shi d’in mijinta ne halalinta. “No, nafi son mace daidai ke. You are perfect.�? Murmusawa suka yi kana suka yi shiru na wani lokaci, can yace, “I love you Laila.�? “I love you too.�? Tayi kissing k’irjinshi ta mayar da kanta ta kwanta tana jin tsantsan farin ciki a tattare da ita. “Fad’a mini abubuwan da kike so da wanda bakya so.�? A haka suka raya daren suna fad’awa juna hakan and their favorites. Ranar monday Haydar ya shirya zuwa gurin aiki, Laila ce ta kaishi da motarta akan in ya tashi zata biyo ta d’aukeshi su koma gida. Yana shiga ma’aikatar ya lura da kallon da colleagues nashi suke masa, yasan dalili ko basu fad’a ba. Sai dai su ba damuwarsa bane saboda yayi hitting jackpot Maigidansu ya kasa. Kanshi a sama ya isa office d’insu wanda yake sharing da mutane uku suka gaisa ya fara aikin daya kawoshi. A daa ya fara sabawa dasu har suna tad’i amma wannan karon sun yi shiru sun k’i masa magana bayan gaisawan da suka yi. Yana tashi daga aiki Laila tazo ta d’aukeshi suka koma gida, a nan yake bata labarin abunda ya faru a office d’in. “A yanzu ne suke maka haka amma ka basu kwanaki kad’an zasu sake ku dawo yanda kuke daa.�? Ta kwantar mishi da hankali tana turashi band’aki zai yi wanka. “Ki mini wankan.�? “Baka da kunya ko?�? Tace dashi tana barin gurin. Da yamma Haydar ya tuk’asu zuwa gidan Ammi bayan Laila ta nemi zuwa ganinta. Murnan da Ammi tayi har ba’a magana, sai nan da nan take yi da Laila ta kasa nitsuwa. “Dama d’azu da rana muke magana da ‘yan unguwa kan ranar jumma’a zamu je mu ga gidan naku.�? Fad’in Ammi ga Laila. Haydar dake zaune a gefenta ya dubeta cikin mamaki yace, “Ammi me zasu je su yi? Nifa bana son yawan gulma.�? “Ji mini Ali da maganar banza, don mutane zasu je su gidanka shine ya zama gulma? Hajiya kina mishi fad’a kuwa?�? Ta dubi Laila kamar itace tayi laifin. Dariya kawai tayi ta sunkuyar da kanta k’asa domin tasan Haydar ya wuce fad’a a gurinta sai dai lallashi. “Ammi kenan, bari in bar muku gidan ku ji dad’in maganata da kyau.�? Ya tashi ya fice daga gidan. A nan Ammi ke fad’awa Laila irin dad’in da taji da aka yi aurensu. Laila kuma kunya take ji sanin Ammi ta zama surkuwarta a yanzu. Daga gidan Ammi gidan Mas’ud suka je, bayan gaishe-gaishe suka yi hira kad’an suka koma gida. Duk wannan yawo da suka yi Haydar da Laila tad’insu suke yi gwanin ban sha’awa. Suna dawowa gida suka samu Abul a falonsu yana tsaye yana tangad’i ga kayan Haydar a watse a k’asa. Yana ganinsu ya fara zage-zage yana nuna Haydar da yatsa, “Munafuki mai kwad’ayin banza kawai. Uwarka tayi asarar haihuwa mara asali kawai.�? Ya fad’i hakan cikin tangad’i irinta mashaya. Tuni Laila ta fara kuka ta yiwo kanshi ya d’aga mata hannu sama har yana yin baya tamkar zai fad’i. “Uwar me zaki zo kiyi a gurina? Me zaki fad’a mini? Ni zaki nunawa iyeyi? Ba kwanciya da yaron kike yi ba kin manta damu bakya sonmu.�? “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Abul kayan maye ka fara sha? Abul me kake son ka mayar da kanka?�? Ta isa gurinshi ta kamo hannunshi ya fisge ya cigaba da tangad’i a falon yana magana wanda kwata-kwata basa ma gane me yake fad’a. Haydar da tun shigowansu bai yi magana ba yace, “Ki kira Mas’ud ya zo, ina ga ba haka banza yake wannan abun ba.�? Tana kuka ta ciro wayarta a cikin jakarta ta fad’a masa halin da ake ciki. Minti hud’u da haka ya bayyana a gidan hankalinshi a tashe ya shigo falon. Kai tsaye yayi kan Abul ya jawoshi yana kiran sunansa. Wani wari ya shak’a wanda ya gane na giya ne, cikin takaici da bakin ciki yace, “Bayan wiwin da kasha yanzu kuma giya ka fara sha?�? “Dama ya ta6a shan abun maye ne ban sani ba? Yaushe Abul yasha wiwi?�? Wannan karon cikin k’araji Laila tayi tambayan ga Mas’ud tana juyo dashi ya fuskanceta. Cikin rashin gaskiya ya bata labarin yanda aka yi Abul yasha wiwi aka masa duka har Alhaji Abdul yazo ya d’aukesa ya kaishi gidansa. “Don meyasa zaku mini k’arya ku 6oye mini ainihin abunda ya faru da d’ana? Meyasa za’a had’a baki da kai Mas’ud a munafurceni? Wallahi baka kyauta mini ba, daa nasan Abul yasha wiwi da ban d’auko maganar yin aure ba. Kaico, wai d’ana na cikina ne ke shan wiwi da giya?�? Wasu hawaye masu zafi suka sauk’o kan k’uncinta. Mas’ud shiru yayi yana damk’e da hannun Abul wanda ke fisge-fisge yana neman kwace kanshi. “Nayi hakan ne don kar in tayar miki da hankali Kalti, amma ke kinsan baza a ta6a had’a baki dani a munafurceki ba.�? “To menene amfanin 6oye mini da kayi? Yanzu ba gashi giya ma yasha ba wiwi ba? Me aka fasa Mas’ud? Ka duba yanda yaron nan yake tangad’i yana suratan banza.�? Haydar ne yayi saurin yin magana ya matso gurinsu yana cewa, “Ka sakashi a d’akinsa sai ka fitar da duk wani abun da zai iya jiwa kanshi ciwo dashi, sai a zauna ayi shawaran yanda za’a 6ullowa wannan al’amarin.�? Gyad’a kai Mas’ud yayi ita kuma Laila bak’in ciki take ji both na Abul da Mas’ud wanda ya 6oye mata wannan babban al’amarin. Zama tayi a kan kujera ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana kuka. Da taimakon Haydar suka sakashi a d’akin Sabrin domin nan ne babu tarukuce, rufeshi suka yi a ciki kana Mas’ud ya mik’awa Haydar keys d’in gidan da wanda ya cire a aljihun Abul ya damk’a mishi. Dama kowa yana da key d’in falo, wanda ko da mutum ya dawo ya samu babu kowa a gidan zai iya bud’ewa ya shiga. Shima Abul da nashi yayi amfani ya shigo musu cikin gidan har ya samu damar shiga d’akinta ya kwaso kayan Haydar ya watsar. Dukkansu zama suka yi a falon suka yi zugum-zugum suna sauraran Abul yana dukan k’ofar yana kwara ashar wai sai ya yanka Haydar. “Sai na yanka shege. Shege ne bashi da uba bashi da kowa sai karuwar uwarshi.�? Ganin abun zai yi yawa yasa Laila ta isa bakin k’ofar ta fara mishi fad’a kan yayi shiru amma kamar ma baya jinta yaci gaba da tam6elensa. Cikin bak’in ciki ta dawo ta zauna taci gaba da hawaye suna binta da kallon tausayi. “Kiyi masa addu’a Laila, Allah zai shiryeshi.�? Fad’in Haydar yana dafa kafad’arta bayan ya zauna kusa da ita. A hankali ya fara kwantar mata da hankali kan matasa da yawa irin haka sun fara shaye-shaye amma a yanzu Allah ya shiryesu sun daina gaba d’aya, kad’a kai kawai take yi tana share hawayen fuskarta cikin yarda da maganganunsa. Sai daya tabbatar hankalinta ya dawo jikinta sannan ya dubi Mas’ud yace, “Me za’ayi masa ya daina halin nan?�? Tambaya ce powerful wanda sun san dalilinsa na fara shan kayan mayen, kuma dukkansu sun san amsarta sai dai baza su ma fara d’auko wannan maganar ba.“I don’t know wallahi, ban ta6a cin karo da irin nashi ba sai wanda suka rik’a ake kaisu makarantar horo. Ya zamu yi dashi? Ba cuta bace balle a d’auki magani a bashi, sannan shi ba yaro bane balle mu kulleshi a gida mu hanashi fita ko’ina har sai ya daina marmarin abun maye. Ya zamu yi?�? Wannan magana kad’ai tasa Laila zubar da wani kwallan domin tana ganin kamar har abada Abul bazai ta6a shiryuwa ba, duk wani wanda ya fara shan kayan maye yana wuya ya daina sai dai ya rage. Ita haka k’addar rayuwarta zata kasance? ‘Yaya biyu kad’ai sai an samu bara gurbi? Ina zata saka kanta? Ya zata yi? “Ka barshi a nan d’in, idan ya dawo cikin hayyacinsa zamu yi magana a nitse ni dashi.�? Fad’in Laila tana mik’ewa tsaye ta shige d’akinta. Haydar ya dubi Mas’ud ya masa alama da kai suka fita can k’ofar gida wajen da Mas’ud yayi parking d’in motarsa. “We all know the solution Mas’ud. Shin zamu cigaba da wannan aure ne mu bar yaron nan ya tagayyara? Baza ta ta6a jin dad’in zaman aure dani ba matuk’ar d’anta tilo yana waje yana shaye-shaye a kan aurenta ba. Me shawararka?�? “Rabuwarku isn’t an option, koda wasa karka k’ara d’auko wannan zancen. Aure kuka d’aura wanda yake sunnar Manzon Allah (SAW) ba zaman kanku kuke yi ba. Sannan karka manta saki ba k’aramin abu bane a wajen Allah wanda idan har aka yi sai Al’arshinsa ya girgiza. Shin zaka aikata babban abu ne don wani abu k’arami da Allah zai iya canjawa a take a lokaci d’aya idan ya so? Wallahi babu wani solution da Abul yake buk’ata kamar addu’a sai kuma saka ido. Idan ta gama magana dashi zan zo na d’aukeshi ya koma gidana domin idan aka barshi a gidanku kallonka da zai yi kad’ai zai sa yaci gaba da harzuk’a yana shaye-shayen. Ka cigaba da rarrashinta domin nasan tana cikin tashin hankali. Kwanaki ya ta6a yin hakan.�? Gyad’a kai Haydar yayi domin yaji labarin d’azu da yake fad’awa Laila. “Daa kun fad’a mata tasan halin da yake ciki ta kimtsa abunta, 6oye mata da kuka yi yasa ya gane cewa bakwa son ta sani. He’s doing all this don hankalinta ya tashi Mas’ud kuma kace rabuwarmu isn’t an option.�? “Zaka iya rabuwa da ita a yanzu idan ta buk’aci hakan?�? Mas’ud yayi mishi tambayar yana hard’e hannayensa a k’irjinsa yana nazarinshi. Haydar shuru yayi na wasu sakanni kanshi a k’asa sannan ya d’ago yace, “I don’t know, but zan iya komai don ganin farin cikin Laila. Kuma nasan farin cikinta sune ‘yayanta.�? “Da kai Haydar, kune farin cikinta. Sannan kar ka k’ara kawo wannan tunanin a zuciyarka, tafi buk’atarka a yanzu sama da kowanne lokaci. Ka zama tudun dafawanta.�? “Ta yaya zan zama hakan a gareta alhali ni kaina ina neman tudun dafawan?�? Murmusawa Mas’ud yayi kana yace, “Bashi da wahala saboda a yanzu ma kana yi ba tare da ka sani ba.�? Yana fad’in hakan ya shige motarshi ya tafi ya barshi a gurin jiki a mace. Ya jima tsaye a gurin kafin ya shiga gidan ganin har magriba ta kunno kai wasu masallatan ma har sun fara kiran sallah. A kan sallaya ya samu Laila tana sallah ya wuce band’aki yayi alwala ya fito ya tafi masallaci. Bai jima ba ya dawo ya samu ta nan a kan sallayan ta jinginu da gadonta hawaye na tsiyaya a idanunta. “Taso kiji.�? Yace da ita yana kamo hannayenta. “Haydar not now please, baka san halin da nake ciki ba ko?�? “Ba abunda kike tunani bane Laila, magana zan miki.�? Yana fad’in hakan ta taso ta zauna kusa dashi a kan gadon ya rik’o hannunta. “Ban san waye ni ba Laila, na fara gane inda nake ne a lokacin ina da shekara shida, a wani tsukukun unguwa muke a Lagos wanda yawancin mazauna cikinta k’abilu ne iri daban-daban wanda suka shigo neman sana’a ko zubar da kai. Gidajen gurin ba irin na k’asa ne ko blocks ba, daga ginin har rufin duk langa-langa ne wanda a lokacin ruwa, sanyi, iska ko zafi bama ta6a jindad’insa, kenan kullum rayuwar gurin ba abun jindadi bane. Sa’i-sa’i police na shigowa cikin unguwar su jidi mutane wani lokacin har musayar bullets suke yi kafin su samu nasarar d’aukan wanda suka zo nema. Karki manta a cikin wannan musayar wutan mutane da yawa wanda basu ci ba basu sha ba zasu mutu ba tare da an kula ba. Sai dai bayan komai ya lafa za’a bi gida gida ana d’ebo gawarwaki ana bunnewa ba tare da an san ina dangin mamatan suke ba.�? “Meyasa ka za6i wannan lokacin don ka bani labarinka.�? Laila ta tambayeshi cikin mamaki domin bata yi tsammanin hakan ba. “Saboda you deserve to know kuma ina son nuna miki wani abu a cikin labarina wanda ke da kanki nake son ki fahimta.�? Gyad’a kai tayi kana ta matsa kad’an ta kwantar da kanta kan cinyarsa shi kuma ya rik’o hannunta yana cewa, “Labarina ba mai dad’i sauraro bane Laila.�? Kana yaci gaba daga inda ya tsaya. “Ammi ce kad’ai na tashi na gani a matsayin dangi uwa da uba, a lokacin na d’auka kowa haka yake daga shi sai mamanshi ban ma san menene dangi ba. Broken English shine a bakina sai kuma hausa da Ammi ke koya mini matuk’ar babu wani mai sauraranmu, kuma ta hanani furtawa muddin ina cikin mutane. Hakan yasa kwata-kwata na tashi ban iya hausan ba sai pidgin. Kin san menene sana’ar Ammi?�? Laila ta girgiza kai yaci gaba, “Tana sayar da plantain da banana a wani k’aton tire da take d’aurawa a kanta. Kullum tare zamu fita tabi inda zata yi sarin sai ta wuce kan titi tana sayarwa tare da wasu mata ‘yan unguwarmu da muke kiran juna Squatters. A wannan rayuwar ne watarana hanya ya biyo damu cikin wata unguwa kusa damu inda naga yara da kaya iri d’aya suna shiga wani gida nake tambayar Ammi ina ne gurin, tace mini sunan gurin School kuma nan yara ke koyan karatu. Haka muka wuce gurin ina rik’e mata da gammonta muka isa gurin da zata sari plantain sannan muka nufi titi. Wallahi duk wannan tafiya da muke yi tunanina shine meyasa Ammi tak’i sakani a makaranta alhali tace yara ne ke zuwa? Muna dawowa gida tayi sallolinta wanda na lura tana yine a 6oye bata son mutanen gurin su gane ita musulma ce, kuma har lokacin bata koya mini komai na daga addinina ba. Ban san komai ba kuma ko nace ta koya mini sai tayita min fad’a watarana har da duka. Bayan ta gama sallolin ta hura huta a d’akin namu ta d’aura mana abinci wanda kullum shinkafa ce da manja. Tana gamawa ta kawo mana muci kamar yanda kullum muka saba ci tare amma na kad’a mata kai nace bazan ci ba. Ko da ta matsa mini dalili nace mata nima ina son ta sakani a school ina zuwa koyan karatu ba tare da nasan menene karatun ba. Kina jina?�? “Ina jinka.�? Laila ta amsa amma ya lura muryarta ya fara canjawa tamkar wani abu ya shak’e mata wuya. “Irin fad’an da Ammi ta mini a ranar bata ta6a mini irinshi ba tunda na taso nayi wayo, k’arshe daga ni har ita babu wanda yaci abincin haka muka kwana da yunwa da bak’in ciki. Da safe tayi sallanta ta kirani nazo take cewa; ‘Junior ba wai nak’i sakaka a school don bana son kayi karatu bane sai dai ina so ne mu 6uya daga mak’iyanmu wanda suke son ganin bayanmu. Kayi hak’uri zan koya maka duk abunda ake koyawa yaran kaji?�? Na gyad’a mata kai ba don nayi farin ciki da hakan ba, burina shine kawai a sakani a can nima in dinga shiga school tare da yara ‘yan uwana. Duk cikin unguwar tamu mu uku ne yara kuma iyayenmu basa ta6a bari muyi wasa da juna. Na fad’a miki wannan gurin na ka zo, na zo ne kowa harkan gabanshi yake yi babu ruwanshi da makwabcinsa. Mutane sun sha mutuwa ana fitar da gawarsu in ta fara wari saboda rashin damuwa da juna. Ban san kwana nawa na d’auka ina fushi da Ammi ba, wata rana kawai naga mun shiga makarantar tare da ita, tsabar farin cikin da nake ciki yasa na sake hannunta nabi class by class ina duban yaran da ake koyawa karatu. Office d’in headmaster Ammi ta shiga dani bayan ta kamo hannuna muka samu guri muka zauna. Namiji ne wanda har in mutu bazan ta6a mantawa da fuskarsa ba mai suna Mr Eze. Bayan sun gama magana da Ammi ya fad’a mata kud’in makarantar ta ciro a jikin zaninta ta bashi muka tafi a kan cewa bayan kwana uku in an d’inka mini uniform zan fara zuwa makaranta. A ranar murnar da nayi ba’a cewa komai, itama Ammi tayani farin ciki take yi har ta saya mini biscuits da sweets. Kwana biyu da haka na fara zuwa makaranta Nursery one, na saka kayan da nake buri har da socks da sandal, sai dai duk abunda ake koya mana bana ji bana rik’ewa domin hankalina na ga window ina ganin yanda mutane ke wucewa zuwa wajen sana’arsu ina tunanin ko ina Ammina take a yanzu.�? “Har aka tashi ban san me ka koyar ba, sannan duk yaron da yaso ya mini magana bana kulashi saboda Ammi ta hanani yiwa kowanne yaro magana balle har mu saba. Kin san menene abunda take tsoro? Kar in saba da kowa har in fad’a mishi wani abu daga cikin rayuwarmu mak’iyanmu su ganmu. Ana tashi na samu Ammi a bakin makarantar tana jirana da kayan sana’arta a kanta, a gefe ta saka na cire kayana na mayar dana gida muka kama hanya zuwa gurin sana’armu. Bayan mun dawo ne take tambayata me aka koya mana nace mata babu komai. Fad’a ta mini tace idan bana maida hankalina a kan karatu zata cireni inyi ta zama haka. Jin hakan yasa na tsorita washe gari duk abunda aka koya mana nazo na fad’a mata ta saka mini albarka tana jin dad’i.�? “Ban dad’e ina zuwa makarantar ba, wata rana bayan mun dawo nake wak’an da ake koya mana na Father Mother and children, can na dubi Ammi na tambayeta waye Father? Tace mini namiji ne Baba. Na k’ara tambayarta cewa ni ina Father na? A nan ne na fara ganin tashin hankali domin rud’ewa Ammi tayi ta fara suratai tana rik’e jikinta guri d’aya tana jijjiga. Hakan da take yi ba k’aramin tayar mini da hankali yayi ba, na isa gurinta zan rik’eta ta tureni gefe na bugu da langa-langan d’akinmu, ashe buguwan da nayi na caki wani guri sai jini ya fara zuba a goshina. Kukan da nake yi yasa Ammi ta dawo cikin hayyacinta ta d’aukeni tana kuka itama ta fita dani zuwa wani chemist a can nesa damu. A nan aka wanke mini ciwon k’arshenta har da d’inki aka mini guda uku wanda har yau ina da ta6onshi.�? Laila ta mik’e zaune tana duban fuskarshi ya nuna mata gurin tasa hannunta tana shafawa a hankali idanunta na ciko da kwalla. “Haka kayi rayuwarka?�? Kad’a kai yayi cikin takaici yana cije le6e yace, “Wannan mai sauk’i ne Laila, baki ji komai ba.�? “Haydar idan hakan zai sa ka tuno wani abu da bakya son tunawa ka bar labarin haka don Allah.�? Girgiza kai yayi yace, “Tunda na fara ki barni in k’arasa Laila.�? Kad’a kai kawai tayi kana ta gyara zamanta tana fuskantarshi yaci gaba da bata labarinshi tana saurara. “A kan hanyar mu ta dawowa wasu mutane suka tare Ammi ta rik’o hannuna gam taci gaba da tafiya cikin sauri sauri, binmu suka yi Ammi ta sa6ani a baya tana gudu, k’arshenta a haka suka cim mana suka fara kwatoni daga bayanta wanda hakan yasa ta daina gudu ta juyo tana rok’ansu su bata ni. Tsakaninsu suka dinga cillani suna ca6ewa, wani daga cikinsu ne yayi bayan d’akunanmu dani Ammi tabi bayanshi tana ihu tana neman taimako amma babu wanda ya iya fitowa a cikin unguwarmu ya zo ya taimakemu. Sai da suka yi nisa suka bar cikin mutane sannan biyu daga cikinsu suka kama Ammi d’aya kuma ya rik’eni suka fara farka mata kayan jikinta. A gaban idanuna Laila maza uku suka yiwa mahaifiyata fyad’e ba tare da nasan menene abunda suka mata ba sai daga baya da nayi hankali, but all i know is Ammi bata son abunda suke mata and that they should stop doing it.�? Hawaye ne ya gangaro kan fuskarshi yayi saurin sharewa ita kuma Laila hani’an take kuka ta rufe bakinta. “A gurin na kwana kusa da Ammi bayan sun gudu sun barmu, duk tashinta da zan yi tak’i tashi k’arshenta ni na gyara mata kayan jikinta na kwanta a kan hannunta ina kuka ga zafin rad’ad’in da ciwona yake mini.�? “Haydar.�? Laila ta kirashi tana kamo hannayensa. Girgiza mata kai yayi yaci gaba. “Ina ga sanyin asuba ne ya farkar da ita ta tashi tana kuka ta jawoni jikinta, jawoni da tayi yasa nima na tashi daga baccin da nake yi ina tambayarta meya sameta tace mini babu, da haka ta tashi muka koma gida, a d’akin namu muke wanka sai dai kuma in zamu yi bayan gari ne zamu nemi leda muyi a ciki sannan muje mu jefar a bola. Ni na rufewa Ammi kwanan da muke wanka tayi wanka sannan tayi sallah, duk wannan abun da take yi kuka take yi ni kuma har na gaji dayi nayi shiru. A ranar ban je makaranta ba kuma haka Ammi bata je sana’arta ba. Kwana uku da haka muka farka cikin tashin hankali domin gwamnati ce ta aiko motar rusau tazo zata kwashe duk gidajemu wai za’ayi titi a gurin. A lokacin zan iya cewa bakwai na safe yayi, Ammi na tonon gurin da take ajiyar kud’inta muka ji motar ta d’aye gefen d’akinmu wanda saura kad’an a had’a da Ammi wacce ke tsugunne a gurin tana tonon rami. Ganin hakan yasa naje na jawota ta k’arfi muka fito a guje ba tare da mun tsira da komai ba sai suturun jikinmu. Muna tsaye a can gefe aka wargaza gidajenmu ya zamana tamkar mutane basu ta6a zama a gurin ba. A nan ne kuma muka fara tunanin ina zamu je mu zauna. K’arshenta sauran ‘yan unguwan namu muka bi babu mai yiwa d’an uwanshi magana muka je k’ark’ashin gada muka samu guri muka zauna. Bayan kwana biyu da haka Ammi taji ana labarin za’a je unguwar squatters a tono kayayyakinmu. Tare dasu muka je kowa yayi inda yake tunanin a nan gidansa yake aka fara tone k’asa ciro kayan sakawanmu da sauransu. Burina d’aya a wannan lokacin shine a fito mini da uniform d’ina in koma makaranta. Cikin sa’a kuwa aka samu kayan nawa da sauran kayan abincinmu har da tire d’in Ammi na sana’a. Sai dai duk tonon da Ammi tayi na neman kud’inta bata samu ba, k’arshe ita da kanta ta hak’ura muka kwashi abunda muka tsira dashi muka koma k’ark’ashin gada.
Mum Fateey 👌

