Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 34 Hausa Novel

Ta mike ta fice tsakar gidan suka gaggaisa da mutanen dake zazzaune, ta kalli wajen da su Yaya Jidda suka yi aikinsu yanda yayi kace-kace ta dauke kai. Har ta juya zata koma ciki Habib ya turo gate ya shiga, daga inda yake ya kirawo sunanta ‘Anti.’Ta tsaya ta juyo ‘Yaya Habib, ina ka shiga ne tun dazu Shukra take nemanka.’‘Ina nan Anti, wajen abokina naje. Yanzu na wallahi yunwa nake ji, abinci zaki bamu.’Tace ‘To ai Anti Jidda zaka yiwa magana ga abinci nan an dafa.’Ya shafa kai yana cewa ‘Anti ai na gaya mata, tuwo ne fa da masa Anti don Allah ni dai ki bani abinci.’Tayi dariya don ta san tabbas Habib baya cin tuwo da masa da ma abincin gargajiya da yawa, tace ‘Kaje sama wajen Anti Nabeela ta zuba maka.’Har ya wuce yace ‘Ni da abokaina Anti?’‘Eh, ka gaya mata ko ku nawa ne.’Bai jima da hayewa ba itama ta bi bayansa, kafin taje ya dauko flask Nabeela ta zuba masa shinkafa da kaza ga coleslawa da sauce din dankalin bature wanda duk a nan saman suka dafa shi tunda basu da yawa. Ya dauko kwanukan ya sauko ya fice.Haka aka yi ta hada-hada ana kaiwa da kawowa. Sai dai zuwan Hajia ya sa babu yanda Khadeeja zata yi dole ta zauna a kasa a yi da ita, don haka Yaya Mama da kuma Anti Innani suka sauko suka gaida Hajia suma suka zauna don tayata zama.Bin mutane kawai takeyi da kallo zuciyarta tana kuna; ji take a ranta kamar da za a bude zuciyarta to da za a tara tana turirisaboda zafin da take ji. Fuskokinsu take kallo daya bayan daya, musamman Hajia wadda ake ta yi mata Allah ya sanya alkhairi ana barka da arziki tana amsawa kamar wadda aka yiwa bushara da kujerar Makka. Haka tacigaba da zama a cikinsu tana jin kamar ta ruga da gudu; sai dai loakci zuwa lokaci ta kan tashi kamar mai duba wani abu ta haye sama, idan ta ja numfashi ta share kwalla sai ta dawo. Haka suka yi ta yi har gefin magriba; abokan ango suka zo da motaci suka debi yan dauko amarya sannan suka tafi dauko amarya.Hak ta yi sallar magriba zuciyarta tana dukan uku-uku; ta rsa ma abinda yake bata mata ran. Tabbas tana kishi to amma ta fi tsoron rashin adalcin da take ji a jikinta Mustapha zai shimfida; amma tana addu’a kuma za zata fasa ba don ta san tabbas Allah ne gatanta.Wajen 8:30pm aka shigo da amarya, nan da nan gida ya dau guda mata na ta shewa. A lokaci guda kuma bugun zuciyar Khadeeja ya kara gudu. Tana zaune a kan kafet kusa da Hajia; duk su Yaya Jidda suka mike suna tarbar amaya, aka budawa wadanda suka riko amarya suka karasa gaban Hajia wadda take hakimce a kan 3-seater. Aka zaunar da amarya a gaban Hajia, mata suka cigaba da zabga guda.Sai da hayaniya ta lafa sannan aka gaisa da masu kawo amarya, suka mikata hannun Hajia. Hajia tace ‘Ma sha Allah, Allah ya sa wannan aure har aljannah. Wannan ai ‘yar uwarta za a bawa ita ba ni ba, ina Khadeejan ne da fa tana nan zaune kusa da ni.’Wadda take zaune kusa da Khadeejan tace ‘Gata nan fa.’Mutane ne suka zauna a gabanta suka kareta da aka shigo da amaryar; nan da nan aka buda. Hajiya ta mika hannu yayinda Khadeejan ta matso tna cewa ‘Zo Khadeeja ga kanwarki an kawo miki.’Ta sunkuyar da kanta tana duban cinyarta domin tana tsoron kada idanuwanta su bada ita ta hanyar tunkuda awaye a daidai wannan lokacin. Hajia ta kama hannunta sanna ta kamo hannun Naja ta dora ta hada ta rike tana kallon Khadeejan tana cewa ‘Ga amanar kanwarki nan, ki riketa amana ku zauna lafiya ku samarwa da mijinku nutsuwa. Allah ya hada kayuwanku.’Mata suka kaure da amshi ‘Amin. Amin.’Wata cikin iyayen amaryar ta karbe ta cigaba ‘Eh gata nan amana, a yi hakuri uwargida sarautar mata ku zauna cikin amincin Allah domin kayan Alah na annabi ne.’Aka sake kaurewa da guda.So take ta zare hannunta amma hajia bata basu dama ba; bugun zucuyarta kara sauri yake yayinda take jin hanunta kamar ta rike wuta. Kokari take ta dafe bakinta saboda kada abinda yake zuciyarta ya fito; Amana! Ita za a bawa amanar matar Mustapha? Ina ruwanta da ita? Ko sunyi mantuwa ne? shi da yaga zai iya da amanar ai yayi gammo ya dauko. Don me zasu ce ita aka bawa amana? Tabbas wanna amana ce da bata karba ba kuma ba zata taba iya karba ba.Sai da aka gama addu’oi sannan Hajia ta saki hannuwansu, cikin dabara Khadeeja ta faki ido ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta.Ba dadewa kuma aka fara mikewa aka kama hannun amarya aka nufi dakinta, a haka ne Khadeeja ta samu ta sulale ta haye sama, yayinda su kuma matan suka bi bayan amarya.Haka ta koma cikin su Yaya Mama ta cigaba da dagewa, su kuma suna ta bata baki da nasiha. Wajen 9pm gayya ta fara watsewa, aka kirawota ta yi sallama da Hajia, ba dadewa kuma su Yaya Mama suma suka yi mata sallama suka barta ita da Nabeela.Tana zaune a gefen gadonta tana jiyo yara wajen 11pm suka hawo saman, gaba dayansu sai da suka leka dakinta suka yi mata sai da safe amma banda Afaf, suka wuce dakinsu inda suke kwana tare da Hafsa. Basu dade ba kuma Nabila ta fito daga dakin bakin da yake saman ta turo kofar dakin a hankali ta shiga, ta wuce Khadeejan a gefen gadon ta zagaya ta kwantar da Hammad a gafe ta lullubeshi. Ta zagayo ta zauna a kusa da Khadeejan, bata motsa ba kamar ma bata san an zauna a kusa da ita ba.Ta mika hannu ta dafa nata hannun da yake kan cinyarta tana kallon fuskarta tana cewa ‘Yaya Khadeeja ga Hammad fa na kwantar miki da shi.’Ta kalleta suka hada ido, ba tare da tace komai ba ta sake kawar da idonta saboda ta tokare hawayen da suke neman kwace mata. Nabila ta dan matsa hannunta tana cewa ‘Ya Khadeeja.’Kafin tace wani abu hawayen ya fara bin idonta, gaba daya ta sakesu saboda yanda take faman rikesu tana jin kamar an dora mata dakon wani kaya mai nauyi. Gaba daya ta fada jikin Nabeela wadda ta rungumeta gaba daya suka sa kuka. Ita Nabeela auren ma gaba daya ya kara bata tsoro’ kuma ta tabbatar ko da wanne lokaci za a iya daura nata auren; tunda da ba don Ahmad ya tafi UK karo karatu ba da tuni ta shekara a daki. Ita kuma Khadeeja gaba daya komai ma ya tsaya mata; tana dai fatan Allah ya sa Mustapha ya zama mai adalci.A hankali suka fara lafawa, Khadeeja ta zare jikinta ta kalli Nabeela. Suna hada ido suka tuntsire da dariya duk da hawayen da suke fuskokinsu. Suka rike hannun juna suna murmushi. Khadeeja ta dubeta tace ‘Sorry.’Itama murmushin tayi mata tana cewa ‘Its’s ok, you will be fine in sha allah. Komai zai wuce kamar ba ayi ba.’Murmushi ta sake mayar mata sanna tace ‘Kije ki kwanta, na san yanzu Abbansu zai shigo.’Ta sake rungumeta sannan tayi mata sallama ta fice ta rufe mata kofa.Ba tare da bata lokaci ba ta mike ta shiga bandaki inda ta yiwo wanka sannan ta fito da alwala, ta shirya ta sa kayan bacinta sannan ta kabbara sallar isha’i.A nan ya shigo ya sameta tana zaune a kan dadduma tana gyangyadi; kallo daya tayi masa taji zuciyarta ta sake komawa cikin damuwa wadda ta fi ta da. Sai wani faman yage baki yake yana muzurai a lokaci guda; a sanin da tayi masa ta san murnace da doki yakeyi na amarya kuma yana kokarin tabbatarwa ita din bata kawo masa cikas ba. Nan da nan ta danne duk wata damuwa da take ranta ta kakalo murmushi tayi masa sannu da zuwa.A tsaye ya amsa yayi mata bangajiyar biki sannan yace ‘Um ni bari naje, na ga kema bacci kike ji. In ya so da safe na shigo da kanwar taki ku gaisa.’‘To Allah ya kai mu.’Ya juya ya fice ya rufo mata kofa.Ta ji dadi sosai da ya sanar da ita ba zai shigo da atarsa a wannan daren ba, domin gaba daya a gajiye take. Ba jikinta ba har ruhinta ma ji take ya gaji, fatanta kawai wadannan kwanakin su wuce ko kuma ma ta farka taga mafarki takeyi. Taga rayuwarsu ta dawo kamar yanda take a farkon aurensu; ko da yake a farkon auren ma babu wani abun kirki da zata dorar; kamar dai gara ma tace rayuwarsu ta dawo yanda ake kafin aure.Sai da bacci ya fara dibanta sannan ta tashi ta kwanta a kan ganto ta kashe fitila.………

Back to top button