Novel Document

Bintu Diyar Bayi Book 1 Complete Hausa Novel

Bintu Ɗiyar Bayi Ce Book 1

©Khadija Sidi…..✍🏼

0⃣1⃣

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI✍🏼

SHIMFID’A 🌍

NIAMEY

Niamey shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar, wanda shi ne birni mafi girma a kasar, dake da girman murabba’in kilo mita (239.30) Tun a karni na 18 ne aka kirkiro Niamey, sai dai a wancan lokacin ba’a dauke shi da wani muhimmanci ba har sai bayan da Faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarun (1890). A shekarar (1926) ya zamo babbar birnin kasar ta Nijar. Sannu a hankali yawan jama’ar yankin ya yi ta karuwa daga (3,000) a shekarar (1930) zuwa kimanin (30,000) a shekarar (1960). Yawan jama’ar Niamey ya kai (250,000) a (1980), a shekara ta (2000) kuma (800,000). Babban musabbabin karuwar jama’a a Niamey shi ne na yawan kaurar jama’a a lokutan fari.

A matsayinsa na babban birnin Jamhuriyar Nijar, akwai wuraren tarihi da suka hada da gidan tarihi na kasa da gidan zoo, akwai kuma cibiyoyin nuna al’adun gargajiya na Amurka da Faransa da Nijar. Hakanan kuma akwai manyan kasuwanni bakwai a birnin. Kashi (90)cikin dari na jama’ar Niamey Musulmai ne, anan ne kuma ake da hedkwatar mabiya darikar kirista ta Roman Katolika.

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete

SA’AYRASA

MASARAUTAR SA’AYRASA yana bangaren kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba’in kilo mita (156,906). Masarautar Sa’ayrasa na iyaka da Masarautar Fabarusa, ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi. Masarautar Sa’ayrasa ta kasance d’aya daga cikin masarautar da ba su da yawan jama’a, wanda kidayar shekara ta (2001), ta nuna yawan mutanen masarautar ya kusa dubu dari hudu. Jama’ar Masarautar Sa’ayrasa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa. Tattalin arzikin masarautar ya ta’allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina. Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono. Sai dai kuma duk da noman da ake yi a masarautar, masarautar ta kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda fari.

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

 

FABARUSA

MASARAUTAR FABARUSA shi ne ya fi kowanne yanki girma a masarautar Nijar, wanda girmansa ya kai murabba’in kilo mita (634,209), watau kwatankwacin kashi hamsin da biyu cikin dari na girman Nijar baki daya. Masarautar Fabarusa ta had’a da Hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama’ar Masarautar buzaye ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana’ar jamaar masarautar ta asali itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun (1990), harkar bude ido ta zama wata babbar sana’ar yankin, hakanan karfen Uranium da ake samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi (20)cikin dari na kudin shigar da take samu.

 

NIAMEY 1/01/2000

Tafe su ke cikin mota,tin da suka baro masarautar su wato Sa’ayara ta tsunduma cikin kogin tunani, ba ta gushe ba har su ka shigo Niamey, in da makarantar su wato SOVEREING GIRLS SECONDRY SCHOOL ta ke. Wato ‘ya’yan manya da sarakuna na sassa,masarauta da yankunan jamhuriyyar Nijar waannan makarantar su ke. Ajiyar zuci ta saki ganin sun doshi kofar makarantar, yayin da motoci biyu da ke gaban ta su su faka, ta su wacce ta ke ta uku ita ma ta faka. Waigawa ta yi dan ganin ko d’ayar da ke tafe bayan ta su ta sami isowa,ile kuwa sai gasu sun karaso a hankali su ka faka bayan ta su. Hankalin ta ta mayar kan kofar makarantar ta su. Motoci huɗu ne jere reres su ka taho kawo Gimbya Binta yar sarkin Sa’ayrasa makaranta. Ta fari ɗauke da dogarawa guda biyu da direba, ta biyu bayi ne mata su huɗu, sai kuma wacce Gimbiyar ‘yar sarki mai dole ke zaune gidan baya, ta yi ɗai-ɗai ta na shan kamshi, tare da ita baiwar ta ce Bintu zaune gaban mota da kuma direba,sai cikon na hud’un dogarawa ne su huɗu zaune, biyu gaba biyu baya.

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Tsawar da ta ji an daka mata ya sa ta yi firgit ta dawo cikin hayyacin ta, jin an furta,
‘’idan kin gama rubuta wasikar jakin da ki ka saba sai ki fita’’.
Faɗin _(driver)_ matu’kin mota ya na mai muzurai. Hakan ya sa ta saurin fitowa daga motar dan kuwa har sun shigo farfajiyar makarantar ba ta sani ba. Tini sauran bayi yan uwanta sun yi sahu suna jiran fitowar Gimbiya Binta. Cikin su Bintu ta shige ta tsaya kan na ta sahun, yayin da dogarai su ka karaso cikin azama, su ka yi na su sahun ta ɗayan ɓangaran. Daga bayin har dogarawa kalar yadin da ke sanye jikin su ɗaya, ruwan toka ne da shuɗi. Rigar ruwan toka sai zanin shuɗi.

Kan su sunkuye babu mai motsi kai kace gumaka aka aje, matu’kin ya buɗewa Gimbiya Binta kofa. K’afafun ta fara fiddowa waje, sanye cikin takalmi fata mai dankaran tsada, sai bayan wasu yan dik’ik’a sannan ta k’arasa fitowa. Tuni suka fara ma ta kirari da faɗin,
‘’taka a hankali Gimbiya yar sarki mai dole, takawan ki lafiya sarauniyar mata’’.

Sanye ta ke cikin kayan makaranta, riga da _skert_ buje sai kuma hijabi wanda ke tsayawa iyaka kafaɗa. Alkyabba ce ta alfarma ɗaure bisa kayan makarantar. Cikin sarauta da tak’ama ta ke takawa ɗaya bayan ɗaya ta wuce, su ka rufa mata baya. Haka su ka wuce ciki zuciyar Bintu cike da tunanin halin da akwatin karfen ta zai shiga matukar ba ta dawo da wuri ba dan Ado matu’ki ba mutunci gare shi ba, dan ya koma da kayan Kuka Sheka ba k’aramin aikin sa ba ne. Hantar cikin ta tuni ta kaɗa

Motoci sai shiga da fice su ke kasancewar yau rana ce ta dawowar ɗalibai daga hutun zango na uku. Kai tsaye sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka nufa, wanda a k’a’ida kowanne ɗaki dan d’alibai biyu aka yi. A dai-dai katangar da ta raba harabar makaranta da sashen ɗakin kwanan ɗalibai su ka tsaya, dan kuwa babu damar dogarai su shiga ɗakin kwanan kasacencewar dokar makaranta ta hana maza shiga. Nan su ke jiran dogarawa masu ɗauke da akwatina su k’araso su karb’i akwatunan dan karasawa da su ciki. Ita kuwa Gimbiya Binta kai tsaye ta shige,biyu daga cikin bayim biye da ita, ya rage daga Bintu sai bayi guda biyu. Dan sauri jikin ta har ɓari yake, Allah-Allah ta ke su samu su shigar da kayan Gimbiya Binta dan ta samu damar kwaso na ta. Sai da su ka ɗauki kusan minti goma kafin su k’araso ɗauke da kaya niki-niki, wanda kuwa faɗar adadadin su aiki ne ja, wai kuma a hakan ma akwai saura cikin mota. Haka suka shiga jidar kayan su na hawa da su sama,bhar bene na uku tukanna ka isa ɗakin Gimbiya. Ta nan kishingiɗe kan gado, ɗakin yayi fes-fes dama tin ana sauran kwana uku a dawo makaranta a ke gyarawa.

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

Su na hawa su na sauka har sai da su ka yi sahu uku. Bintu na Murna da sun sake komawa za su kwashe sauran kayan. Budan bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi,
‘’akwati nawa ne su ka rage?’’.
’Daya daga cikin bayin ta amsa mata da,
“huɗu ne su ka yi saura ranki shi daɗe’’.
Gimbiya ta ce,
“to! Za ku iya tafiya kubarwa ɗiyar bayi sauran ta k’arasa hawa da kayan’’.
Tuni idanun Bintu ya raina fata, ba wai wuyar hawa da kayan ba ne damuwan ta ba, a’a ita ta dan akwaitin k’arfe ta ta ke. Cikin girmamawa su ka durkusa su na mai faɗin,
“an gama ran ki shi daɗe’’,
hannu kawai ta ɗan ɗaga musu alamar sa iya tafiya. Cikin hanzari su ka daɗa rusunawa kafin su tashi su ka fice. Ai fa Bintu ba ta san san da ta arta a na kare ba, ta na ji sauran bayin suna dariya suna cewa:-
‘’Ba ke mai yiwa Gimbiya hidima a boko ba, Allah shi k’ara’’,
ɗaya ta k’ara da “ai tin da aka zab’e ta wani girman kai ya game jikin ta, ɗiyar bayi a makarantar girma’’.
Yi ta yi kamar ba ta ji su ba, ta k’arasa ta ɗauro akwati ɗaya a ka d’aya kuma ta jawo shi a hannu. Ba ta kai ga hawa bene ba ta yi kaciɓus da su, haka su ka wuce ta suna mata dariyar kyeta. Cikin himma ta haye abun ta sama, sai da ta kai ga kofar ɗakin ta tsaya dan ta ɗan sami nutsuwa dan kuwa idan Gimbiya ta gano ta lalle kashin ta ya bushe. A hankali ta tura kofar tare da sallama. Gimbiya ko ta nuna ta san ta shigo bare ma ta amsa sallamar. Cike da nutsuwa ta aje akwatinan sannan ta fito, nan ta sake zurawa a guje, ta kwaso sauran akwatinan kamar dai yanda ta yiwa biyun farko. Aje akwatinan ke da wuya ta juya da niyyar sake fita, Gimbiya ta daka mata tsawa,
“ina zaki? Nufin ki ni zan jera mi ki kayan yau kuma ɗiyar bayi?’’.
Jiki na rawa Bintu ta zube k’asa ta na mai faɗin,
“tuba na ke ranki ya daɗe ni ce zan jera dama sauri na ke dan kwaso nawa kayan kar Ado ya manta ya juya da su’’.
Shiru idan Gimbiya Binta ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka. Da shirun yayi yawa Bintu ta ɗaga kai ta kai kallon ta gare ta, sai gani ma ta yi ta runtse ido kamar mai bacci. Dole jiki ba laka Bintu ta tashi ta shiga jera akwatunan, sai da ta gama tsaf sannan ta durk’usa ta ce,
‘’ran Gimbiya ya daɗe na idda’’.

Sai da wasu dak’ikai su ka shuɗe, har Bintu ta na tunanin ko dai bacci ta ke sannan ta ji ta ce,
‘’kya iya kwaso tsummokaran na ki’’.
A wulakance ta yi furucin cike da ‘kas’kanci. Russunawa ta yi cike da girmamawa ta ce,
‘’godiya na ke ran ki shi daɗe”, ta tashi ta fice. Nan fa duk nutsuwar ta ya gushe, ta ranta a na kare, ba ta ji ba ta ba ta gani. Dalibai ma su shiga da fice cikin farfajiyar wajan faɗi su ke,
“ta fara, in dai wannan ce dama duk dawowa hutu haka ta ke”.
A guje ta fito daga harabar ɗakin kwana ta shigo sashen ajijjuwa. Ba ta ga tahowar shi ba sai ji ta yi karo da shi. Ta yi saurin yin baya saura k’iris ta faɗi ya yi saurin sa hannu biyu ya rik’o ta. Sakin baki ta yi ta na kallan sa,ta ma manta da gudun da ta ke.

Sanye ya ke cikin bakar _suite_, wankan tarwaɗa be mai dan faffaɗar kafaɗa. Ya na da dogon hanci, yayin da gashin bakin sa da ya zagaye bakin na sa ya k’ara masa kyau da k’warjini. Idanun sa rufe cikin bakin gilashi hakan ya sa ba ta sami damar ganin kwayen idanun na sa ba. Kamar daga sama muryar sa ya dakin dodon kunnan ta,jin ya ce
‘’hankali mana gudun me ki ke haka ke kuwa?’’.
Ta yi saurin ja da baya,hakan ya sa shi sakin ta.
’’Yi hakuri dan Allah Ado direba zai tafi da kaya na’’.
Bintu ta furta idanun ta na shirin kawo ruwa. Sai a sannan ya dubi kayan jikin ta ya na mai faɗin,
‘’Tabbas wannan shigar ta ki ta bayin Masarautar Sa’ayrasa ne, ina shigowa na ga motocin na su na fita, sun manta da ke ne…?’’,
ba ta bari ya karasa maganar ba bare ta bashi amsa ta sa gudu ta na mai faɗin,
“shikenan ni Bintu sun tafi da akwati na,shikenan na banu na shiga uku na lalace’’

Cikin rashin fahimta ya bita da kallo har sai da ta kure masa sannan ya d’aga kafad’a ya sauke sannan ya yi ciki abun sa.Isar ta wajan yawan motoci masu kai kawo ya k’aru,sai dai babu motocin Sa’ayrasa babu alamar su. Kwallar da ke idanun ta tuni su ka fara gangarowa bisa kuncin ta…

Domin Karanta Cikakken Littafin Sai Ku Danna Inda Aka Saka Download

 

Back to top button