Mutumin da al’amura sukayi masa tsanani, rayuwa tayi masa wuya kuma ya shiga cikin tashin hankali. Kai ko dama macece mai juna biyu ta shiga cikin tsoro da firgici, koda takai ace za’a yimata aikine wato CS, ta gigice hankalinta ya tashi. In har zata rinka karanta wannan addu’ar Insha Allah komai zai zo mata cikin sauki da yardar Allah.
Karanta>>> Ladubban Karbar Addu’a Guda 25 Daga Malam Aminu Daurawa
Ibn Hajar ya ruwaito daga Hassan Ibn Ahmad Ibn Said yace; Babarsa tanada juna biyu sai ta shiga damuwa, kuma macece mai tsoron Allah da taqawa. Wata rana ta kwanta bacci sai ta roki Allah daya kawo mata sauki tattare da cikin da take dauke dashi, kuma ta sauka lafiya sannan Allah SWT ya yaye mata duk abinda ke damunta. Ta kwanta bacci sai tayi mafarkin Annabi SAW yace; “Ya Ummu Habib, karanta wannan addu’ar;
“يَا مُسَيَّرَ الشَّدِيدَ وَيَا مُلِيَنِ الْحَدِيدَ وَيَا مُنْجِزَ الْوَعِيدَ وَيَامَنْ هُوَ كُلَّ يَوْمٍ فِي أَمْرٍ جَدِيدٍ أَخْرِجْنِي مِنْ خِلْقِ الْمَضِيقِ إِلَى أَوْسَعِ الطَّرِيقِ بِكَ أَدْفَعُ مَالَا أَطِيقُ وَلَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ الْعَلِيَّ الْعَظِيمِ”
“Ya musairul shadid, wa ya mulinul hadid, wa ya munjizul wa’id, wa ya man huwa kulli yaumin fi amrin jadid, akhrijni min khalqil madiq ila awsa’id dariqi bika adfa’u mala adeequ wala haula wala quwwata illa billahil aliyul azeem”.
Karanta>>> Ma’anar Mafarki A Mahangar Addinin Musulunci
ADDUAR YAYE BAKIN CIKI DA DAMUWA DA KUNCI RAYUWA DAGA BAKIN MANZON ALLAH ﷺ
Rokon Allah da dogaro ga Allah da yarda da Qaddara mai kyau ko marar kyau,yana daga cikin mafi girma hanyar samun waraka da damuwa da bakin ciki da yake damun bawa.
Manzon Allah ﷺ ya koyar da mu addu’oin da yakamata mu yawaita karantawa dan samun waraka daga dukkan wani bakin cikin da damuwa da kuncin rayuwa nan duniya da lahira da yardar Allah.
1-ADDU’AR SAMUN YAYE DA MUWA DA BAKIN CIKI
Manzon Allah ﷺ ya kasance idan damuwa ko bakin ciki ya sameshi yana cewa:
@صحيح البخاري الصفحة أو الرقم: 7426
Karanta>>> Fassarar Mafarkin Koren Macij
2-ADDU’AR SAMUN YAYE DAMUWA
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Adduar zinnun lokacin da ya roki Allah yana cikin kifi:
“لا إلهَ إلَّا أنتَ سبحانَك إنِّي كنتُ من الظالمينَ”
“LÃ ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ ZALIMIN”. Babu wani mutum da zai shiga cikin damuwa kuma ya roki Allah da wannan adduar,face sai Allah ya fitar da shi daga wannan damuwar)
@الألباني صحيح الترمذي
الصفحة أو الرقم: 3505
خلاصة حكم المحدث : صحيح
Karanta>>> Fassarar Mafarkin Tashi Sama Kamar Tsuntsu
3-ADDUAR FITA DAGA KUNCIN RAYUWA DA SAMUN WALWALA DA JIN DADIN RAYUWA
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Adduar fita daga kuncin rayuwa)
{اللهُمَّ رحمتَكَ أرجُو ، فلَا تكلْنِي إلى نفسِي طرْفَةَ عيْنٍ ، و أصلِحْ لِي شأنِي كلَّهُ ، لا إلهَ إلَّا أنتَ}
“ALLAHUMMA RAHMATAKA ARJU,FALA TAKILNI ILA NAFSI DHARFATA AININ,WA ASLIH LI SHA’ANI KULLAHU,LÃ ILAHA ILLA ANTA”
الألباني صحيح الجامع
الصفحة أو الرقم: 3388
خلاصة حكم المحدث : حسن
Karanta>>> Fassarar Mafarkin Ruwan Sama
4-MAGANIN DUKKAN WATA DAMUWA DA BAKIN CIKI
Manzon Allah ﷺ yana cewa:
(Babu wani Mutum da zai sami kansa a cikin damuwa da bakin ciki. sai Yace:
{اللهمَّ إني عبدُك ، و ابنُ عبدِك ، و ابنُ أَمَتِك ، ناصيتي بيدِك ، ماضٍ فيَّ حكمُك ، عدلٌ فيَّ قضاؤُك ، أسألُك بكلِّ اسمٍ هو لك سميتَ به نفسَك ، أو علَّمتَه أحدًا من خلقِك ، أو أنزلتَه في كتابِك ، أو استأثرتَ به في علمِ الغيبِ عندَك ، أن تجعلَ القرآنَ ربيعَ قلبي ، و نورَ صدري ، و جلاءَ حزني ، و ذَهابَ همِّي}
(face sai Allah ya yaye masa wannan damuwar da bakin cikin,kuma ya maye masa su da farin ciki da walwala) sai Sahabbai R.A suka ce:
“Ya Manzon Allah,shin bazamu koyawa yan uwanmu ba saboda mahimmanci wannan adduara ba??” Sai yace:
(Eh dukkan wanda yaji wanda adduar to yana da kyau ya koyar da wanda bai sani ba)
@الألباني السلسلة الصحيحة
الصفحة أو الرقم: 199
خلاصة حكم المحدث : صحيح
Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam
5-Adduar samun fita da kuncin rayuwa
Manzon Allah ﷺ ya cewa Asma’u bntu Umais R.A
(Shin bazan koya maki ba wata addua da zaki karantata alokacin damuwa da bakin ciki,ko lokacin kuncin rayuwa??)
Kice:
{اللَّهُ اللَّهُ ربِّي لا أشرِكُ بِهِ شيئًا}
“ALLAHU ALLAHU RABBI LÃ USHRIKU BIHI SHAI’AN”
الألباني صحيح أبي داود
الصفحة أو الرقم: 1525
خلاصة حكم المحدث : صحيح
ALLAH NE MAFI SANI
ALLAH KA YAYE MANA DUKKAN KUNCI DA DAMUWA DA BAKIN CIKI DA MATSALAR RAYUWAR DUNIYA DA LAHIRA.
Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.