Zafafa 2023

Ajiya A Duhu Complete Novel Document

Ajiya A Duhu Complete Novel By Billyn Abdull

Description/Story:

Ajiya ADuhu! Complete Novel Document

Written By Billyn Abdull 

 

Description

…….Ƙaddarorin rayuwa tamkar TASWIRA ce dake zane a takardar lissafin rayuwar kowanne ɗan adam, duk yanda ka so gogesu ko san kauce musu ba lallai ne ka samu makaman yaƙin ba balle GARKUWAR kare kanka daga isowarsu gareka ko mai gajartar tsahon shekaru ko yawaitarsu. A wasu lokutan mukanyi kuka ne da hawaye, sai dai kukan ZUCIYA shine mafi ciwo da ɗacin kuka da yafi kassara rayuwarmu da nasarorinmu a ɓoye ko a zahirance da bama iya mantawa. Dan a wasu lokutan har tambarin tabon da zamu iya ringa tunawa a lokaci bayan lokacin yake bar mana.

A farkon haihuwar mu iyayenmu sune GARKUWARMU, dan sukan sadaukar da komai nasu ne domin lulluɓe RAYUWARMU da dukkan fatansu. Sukan rainemu da shauƙi da yaƙini har zuwa girmanmu. Hakan yake saka SOYAYYAR su bata taɓa iya goguwa a ZUKATANMU, sannan takan banbanta da irin kowacce soyayya da zata biyo bayanta. Koda hukuntamu sukai mukaji zafi mukai kuka wannan soyayyar tasu bata taɓa canja kanta a ZUKATANMU saboda su ɗin sune dai ɗaya tamkar da dubu a dukkan abubuwan dake zagaye damu na NASARA ko akasinta.

A lokacin da girmanmu ke ƙara yawaita sai TSUFA ya riskesu. Mu kuma ƘURUCIYA ta baibayemu. Sai dai me daga lokacin daka iya tantance ma’anar FARI da ƁAKI a yau ɗinka da gobenka littafin ƘADDARARKA kuma ya fara kenan da manyan zanukan layukan dake bayyana JARABAWOYINKA. Gwagwarmaya ta zama ƙawa ko abokin RAYUWARKA. Yaƙin ba yana farawa da gwagwarmayar RAYUWAR DUNIYAR kawai bane ba. Harda ta neman LAHIRA da zaɓama kai makoma ƙyaƙyƙyawa ko akasinta. Domin kuwa fara rayuwar girman na farawa ne da daidaiton mizanin ayyukan samun LADANKA da kuma ZUNUBI duk a bayyane kuma a rubuce ga wanda ya HALICCEKA. Iyayenmu kan gama gwagwarmayar ƙuruciyarmu, sannan su koma ta girmanmu babu gajiyawa saboda su ɗin na dabanne a cikin daban a garemu.

A lissafin fara fahimtar kanka da tabbatar da WANENE kai, da wahala kaga babu armashin soyayyar ƙuruciya da takanyi kutse a ƙaddararka. Ba soyayyar bace ba kawai abar kallo ko zama daban a gareka ko wanda ke tare da rayuwarka. A yaya SOYAYYAR ta FARA? Ko ta ƙare? Ko ta kasance? Ko ta cigaba da wanzuwa? Itace madubin dubawarka ko masu juriyar bibiyar labarinka.

 

★ Ƴammata ne uku sanye cikin kayan hidimar ƙasa. Tsaye suke a bakin titi kowacce hannunta riƙe da hannun trolling alamar abin hawa suke jira. Dan suna ma ta ƙoƙarin tsaida napep amma mafi yawanci sai kaga akwai wani a ciki ta yanda bazai isa su ukun duk su shiga ciki ba. Cikin ɗan damuwa da ƙosawa ta tsakkiyarsu da bata da yawan fara’ar fuska ta ɗaga kai tana kallon sararin samaniya dake haɗa hadari. Ko kaɗan bata fatan ruwan nan ya taɓa ta. Dan hakan baya zama mai sauƙi a gareta shiyyasa tafi kowa damuwa da samun abin hawan nasu, daɗin daɗawa tafiyarsu mai nisa ce. Dan kuwa jihar Kaduna suka nufa.

Fara tasowar iskar hadarin ta sata duban ƴan uwan nata idanunta na cika da ƙwalla. Sai dai kafin ta samu damar cewa wani abu wata jar mota tai parking a gabansu. Su duka idanu suka zubama motar, sai dai buɗewa da fitowar matashin saurayin dake ciki ya saka biyu a cikinsu sakin murmushi da mamaki. Yayinda ta tsakkiyar sun nan dai ta sake haɗe ƙyaƙyƙyawar fuskarta tana mai kauda kanta gefe. Shi kam saurayin nan gaba ɗaya hankalinsa na kanta. Ya ƙaraso gabansu dai-dai saitinta ya tsaya tare da faɗin, “Yanzu duk saurin da nake sai da kika nema guje min?”.

Fuska ta sake haɗewa tana ɗan matsawa baya. Kansa ya ɗan sosa yana mai sakin murmushi. Hankalinsa ya maida ga sauran biyu cikin jifansu da harar wasa ya ce, “Amana batace dai haka ba friends. Kamar ni ina daku amma a so haɗa kai da ku a gudu min”.

Dariya suka ɗanyi a lokaci ɗaya. Ta gefen damarsa mai ɗan jiki kaɗan ta bashi amsa da, “Ina ai bazamu taɓa yarda hakan ta kasance ba. Ko an gudu maka mu zamu kawoka har wajen ɓuyar RK. Amma ai mana afuwa mutuniyar taka ce ta addabemu da tafiyar sassafen nan. Kasan jiya ko barcin kirki batai ba saboda farin cikin zata koma gida taga Ammie”.

“Ko dai tana farin cikin zata gudu daga Jos ta bar ɗan nacinta ba?”. Ya faɗa idonsa a kan budurwar tsakkiyar dai. Da sauri ta gefen haggunta ta amshe da “Haba RK kaima kasan ba haka bane sam”.

“Humm Aneesa dama ai baƙya son laifinta ke tuni na fahimci haka. Duk ta inda aka ɓullo sai kin kareta. Ni dai yanzu ku shiga mota muje kunga ruwa na shirin sakkowa karya jiƙa min sarauniyata”. Kafin wani cikinsu ya bashi amsa a hankali ta fara jan akwatinta domin barin wajen. Saurin riƙo akwatin yay, hakan ya sata tsayawa cak batare da ta juyo ba. Zai yi magana Aneesa tai saurin girgiza masa kai tare da amsar akwatin. Babu musu ya sakar mata yaja da baya.

Akwatin tai ƙoƙarin ƙara ja Aneesa ta sake riƙewa. Hakan ya sata juyowa a fusace zatai magana a zatonta shine sai taga Aneesa. Idanunta tai wani irin lumshewa da cizar gefen lips ɗin ta irin na takaicin nan kawai. Hakan ya saka Aneesa sakin murmushi dan tasan ta gama ƙurewa a fusata. “Kiyi haƙuri dan ALLAH” ta faɗa da sauri, bata jira amsarta ba ta cigaba da faɗin, “Kiyi haƙuri mu bisa _Maanal_, kalla garin nan ki gani hadari ne da akoda yaushe za’a iya fara ruwa. Kinfi kowa sannin illar da hakan yake miki. Kema kin san iyakarsa yace zai kaimu tasha ne kawai. Daga yau ne fa an rabu shike nan kuma. Dan ALLAH kada ki bari kuyi irin wannan rabuwar da shi. RK bai cancanci hakan daga gareki ba. Ko bazaki taɓa amince masa ba kada ki munana masa a yau ɗin nan da zamu rabu. Yanda baki wulaƙantasa ba a baya yanzu karki aikata. A rabu lafiya daga haka kuma bashi ke nan ba tunda ko lambarki dai yanzu bai da ita ballema kice zai cigaba da takura miki, ba kuma sanin gidanku yay ba idan kika cire sunan gari”.

A hankali ta buɗe idanunta da suka gama kaɗawa, ga hawaye sun cika su zubowa kawai ya rage. Lips ɗinta ta buɗe zatai magana ruwa yay wani irin kecewa lokaci guda. Gaba ɗaya ta rikice. Har bata ma san Aneesa taja hannunta ta tura cikin motar ba itama ta shiga. Sai da taji babu saukar ruwan a kanta sai ƙararsa sannan ta farga ta ɗago kanta data cusa cikin ƙafafunta da sauri. Waigowar da zatai suka haɗa ido da RK daya wani zuba mata ido kamar zai cinyeta. Nata ta janye da sauri tana mai juyawa ta kalla ƙawayen nata. Da sauri Zeezah ta nuna Aneesa alamar babu ruwanta itace. Aneesar ma saita marairaice mata fuska alamar kartace komai dan ALLAH. Harara ta sakar mata tare da ɗauke kanta, sai kawai ta juya tana goge fuskarta da ruwa ya fara taɓawa da handkhachief…..

 

Tunda motar ta fara tafiya babu wanda yay magana. Ga ruwa ana kwararawa kamar da bakin ƙwarya. Tuni wasu motocin ma sun koma gefen titin sun tsaya. Ganin sunzo sun wuce tasha yasa Zeezah yinƙurin yin magana. Da sauri RK dake kallonsu ta mirror yay mata alamar roƙon tai shiru. Haɗiye maganar tayi tana murmushi, sai kuma ta ɗan dubi Maanal da kanta ke sunkuye novel a hannunta alamar karatu takeyi, shiyyasa bata san wainar da ake toyawa ba ma.

Shima dai RK ya raba hankalinsa biyu ne. Rabi ga tuƙi rabi a kallonta. Maanal ƙyaƙyawar yarinya ce kuma nutsatstsiya. Za’a iya kiranta tsaka tsaki a tsaho, a wani gurin kuwa ma wasu kai tsaye zasu kirata doguwar duk da ba shalleliya bace, sannan bata da wani jikin kirki. A duk wanda ya santa musamman a tsukun shekarun nan zai iya sakata a jerin miskilayen mutane. Bata da yawan magana, hakama bata da fara’a ko yawan walwala sam. Dan da wahala kaga murmushi ma a fuskar Maanal balle akai ga dariya. Akoda yaushe fuskarta ciɗin-ciɗin take. Hatta da magana ma sai taso take yinta. In har ba wani abu take mai muhimmanci ba to akoda yaushe zaka samu novel a hannunta tana karantawa. Hakan na nufin ita ɗin mayyar karance-karance ce. Dan zamu iya cewa ma yawan karance-karance nata ne yasa koda yaushe zaka samu idanunta da eyeglasses fari tas da mutane da yawa basa iya ɓoye mata cewar yana mata matuƙar ƙyau. Itama kanta tasan yana mata ƙyawun, dan takai tun ma tana sakashi domin karatu, har ya zame mata jiki akoda yaushe zaka ganshi tare da ita in har ba barci take ba ko wani abinda ba’a buƙatarsa. Sai dai kuma abinda kowa bai sani ba wani dalili ne daban ya ɗabi’antata da yawan daka gilashin akoda yaushe bawai dan karance-karance kawai ba, duk da a ɓangaren karatun ma yana bata gudummawa matuƙa……..✍️

Ajiya A Duhu Complete Novel Document Txt

File Name   Ajiya A Duhu… Hausa Novel Doc. 
Title   Ajiya A Duhu Complete 
Author        Billyn Abdull
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/12/2024
File Size    50KB
Format Size    TXT
Book Price   500
Phone No  09033181070
Download Ajiya A Duhu Complete Novel Document By Billyn Abdull 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button