Description/Story:
A’Indo Tantagaryar Yar Aiki! Complete Hausa Novel Document Written By Maimuna Matar Abdul
Description
*A’INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
on-2477871259112678/
*Page 1_2*
*__________* Tinkim wani kauye ne dake wajen jihar Zinder ,a kasar Niger ,kauye ne wanda kusan zan iya cewa tsaka tsakiya yake tsakanin Nijeria da Niger.
Kauyen yanada kyau da dadin zama,mutanen garin akoy karamci da son bako,gidan Ado Mai saida kifi kowa yasan sa a kauyen,tunda ya taso yake sana’a saida kifi,har ya zama samari ,ya hadu da kuluwa mai bakin masifa,kowa yasan kuluwa da masifar ta,hakan yasa duk wanda yake son ta da aure yanzu ne zakaji an zuge shi.ace Masa ai batada da’a bata san darajan yan Adam ba,masifafa ce,sai kaji an fasa auren. kauyen auren wuri ake ma yarinya daga kin kai shekaru sha uku sha hudu yanzu za’a aurar dake,yayyin da kuluwa saida takai shekaru goma sha takwas kafin Ado mai saida kifi ya gani yace yana so kuma yana iyawa Saida akasha duru kafin a bari ya aureta.
Bayan anyi Aure kuluwa tana masa ladabi da biyaya da duk wani abinda ya danganci sauke hakki ne na mijin ta ,saide fa ko kadan batada hakuri ,idan ya mata abinda bashi ba,yanzu ne zata juye masa buhun bala’i…..
A haka suke zaune,yau dadi gobe ba dadi,Ado yanada daidai abin rufin asirin sa,domin dai abinci bai gagaresa ba,sanan sutura batafi k’arfin su ba,da sauran abinda ba’a rasa ba,saida sukayi shekara daya kafin Allah ya Albarkace su da samun yan tagwaye duka mata,masu matukar kama da juna,kyawawa dasu bazaka taba gane su ba,ranar suna za’a sa musu sunan su na hassana da husseina anma Kuluwa ta zuba masifa dole fa sai ansa ma daya sunan mahaifiyar ta da ta rasu,Allah ya jikan Mahaifiyar ta itama masifafa ce ta bugawa a jarida,dan kuluwa dai gado tayi……
ba yanda Ado ya iya yace”tayi hakuri asa musu hassana da husseina sai a dinga Kiran Hassanar da sunan A’indo ,anan kawai ta yarda,aiko akasa ma hassana sunan A’indo.
Tunda suka taso halinsu yadan banbanta,a halayen su kadai zaka iya banbanta su,dan ko mahaifin su saide ya Kira da sunan su tukon yake ganewa, mahaifiyar su kadai take ganesu,watarana, anma ranar da suke jin iskancin sai suyi kicin kicin ko kai waye bazaka ganesu ba.
,,,,,,,,,, Husseina mafadaciya ce ta gidan gaske,yanzu ne ta zage ku danbata da ita,bata wargi kai ko fada taga anayi idan taga ba’a danbata ba yanzu zata saye fadan ayi da ita,gata tantiriya .yayyin da Hassana A’indo ta hada kusan duka A’indo dai itama tana masifar ,saide akway ta da wauwta irin ta yan fari,ga tsiwa,ga karambani,kome ita ta iya,ga karambani yi ba’a sa ta ba,ga keta,uwa uba kauyenci saide matsoraciya ce ta gidan gaba, tunda suka taso kowace da burin ta ,A’indo batada buri sai taje birni aikatau,ita duk yanda take ganin yan mata daidai ita na kauyen in sunje aikatau wasu har a wuleliyar mota ake kawo su,to sai ta d’auki wanan tasa a ranta cewar Yar aiki baban matsayi ne da ita ,wanda ko a birinin da wuya a samu mai matsayin Yar aiki.
Sun adabi mutanen gari,kowa fata yake suyi auren nesa,saboda duk kyansu ba Mai zuwa wurin su saboda masifa irin tasu da ta uwar su,a yanzu haka sunada kusan shekaru goma sha bakway anma ba mijin aure Mahaifin su har ya gaji ya zuba ma sarautar Allah ido,A’indo kuwa a kauye ba Wanda baisan sunan ta ba,da ta biyo guri kace sai kinyi A’indo sai tace Tantagariyar Yar Aiki ba.”
Ana cikin haka kanwar Mahaifin ta tazo daga birni wada take a birnin zinder tana zuwa ta samu yara ta d’auke su ta kaisu Aikatau a birini duk wata ana biyan iyayen su,itama tana samu.
A wani zuwa ne da tayi A’indo ta aza bala’i itama fa sai taje aikatau dinnan,ba yanda Mahaifin ta ya iya yace suje ,wata kila ta samu miji ita in ta fita daga kauyen tunda dai wanan kauyen ba Wanda ke son su da aure,suna kuka haka suka rabu ita da yar uwarta Husseina,tun daga lokacin da A’indo ta tafi husseina ta Kara zama masifafiya,ta adabi mutanen gari tace ai ta dalilin su yar uwarta ta tafi,saide fa tace itama dan lokaci take jira,anma in lokacin yayi duk inda yar uwarta ta tafi a birni itama sai ta bita.
Ranar da aka shigo birni da A’indo duk Wanda ke cik’in motar Saida ta cika cikin sa da dariya,ana tsakar tafiya ta fido kanta ta window mota tana ihu wai ga bishiyoyi can na gudu,akayita dariya.
kusan gidan biyar aka kaita aikatau anma duk inda taje sai tayi ta’asa,su korota.
A karo na shida ne aka kaita gidan wani dattijo Alhajin Sanmani Hamshak’kin Dan kasuwa ne Mai kudi,yayan sa biyar Mata biyu Maza uku.
Alhassan shine da na farko dan kimanin shekaru talatin da biyar a duniya (35years) Yan biyu ne yar uwar tagwaitakar sa bata zo da rai ba sai shi,a yanzu haka yana kasar waje aiki yake sodja ne baba na kasa da kasa Wanda duniya keji dashi kuma take takama dashi,saboda ilimin sa kwazo ,basirar sa,uwa uba yasan kan aikin sa .baya dariya ko kadan,babu Wanda zaice ya taba ganin dariyar sa,saide murmushi , murmushin ma iyakar sa lebo . Mai bi masa shine idrissa dan kimanin shekaru ashrin da biyar,sai khalipha dan kimanin shekaru ashrin da uku suna karatu,sai halissa Yar shekara ashrin da biyu tayi aure a Niamey shekara biyu da ta huce,sai auta khalissa, yar kimanin shekaru goma sha bakway su suna karatu ne.
Sai mahaifiyar su Hajiya saude datijuwa Yar kimanin shekaru arba’in da biyar.
Katon gida ne sosai tsarare ,Wanda aka kashe masa naira wajen tsara sa ,ginin ma ginin turai ne, yan aiki gidan kusan ma’aikata goma sha tara ne,kowace da ranar aikin ta, bayan masu gadin gidan da masu tsaron lfy masu gidan su ba’a sasu a lisafi ba,Hajiya saude duk masu gyaran falon da ake kawo mata Sam bata wani ganin kyan akin su ita tafi so in ta fito falo taga ko Ina kal kal yana walkiya,hakan yasa tasa a Nemo mata Yar aiki ta kauye a cewar ta su suka fi aiki domin basa Wasa da aiki suna sakin jikin su suyi aiki basa gajiya.
Hakance yasa Anty najin irin Yan aikin da Hajiya keso ta kawo A’INDO gidan yau ai tun a k’ofa ta tatare siket zata arta a guje Saida Antyn tata da ta gane nufin ta ta rike hanun ta kam,tayita lalaba ta sanan suka shigo..
Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:27] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A’INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
https://www.facebook.com/ANA-TARE-writers-association-2477871259112678/
*Page 5_6*
*_________* “kefa kikace shi, gashi kuma na so miki na dubu hudu da dari biyar cassss.”🙄
Cewar A’indo.
Hajiya tace uban waye yace miki kwali shine kati,Nima ai nice da shirme da na aike ki,kuma in banda hauka wa ya taba kiwo ki sayi wanan uban bubun igiyar wai Zaki fara dan tare ,dan tare saikace wata amarya,yanzu kin min asara mitssss,”dan Allah Hajiya gobe ma ki aike ni na samu canji na sayi dusa ko ta naira ashirin ce na fara dan tare,kafin nan da shekara in rago na yazo😟
Rabi’u daudu ne ya shigo falon domin shine kukun gidan,dan daudu ne in yana abu kai kace mace,yanda yake rangwada har yafi macen,lokacin da A’indo tazo baya gidan ya tafi hutu,ya iya abinci kwarare ne hakan yasa Hajiya ta kasa rabuwa dashi jiya dadare yazo ,yaji labarin A’indo kaf,ya kawo ma hajiya juis ya tarar da zancan da suke,kugu ya Kama da hanun sa daya,bayan ya aje ma Hajiya juis din,yana wani karairaya,yace”ahhh Allah daya gari banbam casss makuwa,aheee ya fada tare da tura duwawu baya,ya kada idanu tare dayin farin ya tafa hannu ya rike haba tare da cewa Hajiya me kala kala,keko hajiya me ya kaiki kwaso wanan yau Allah na tuba mutum gashinan kamar ka zuba a guje,anma kekam anyi asara ,kin bata mana sunan mata wly,kin bada mu mata,hahhh yau ni Hajiya me ya kaiki kwaso wanan jabu ki kawo mana gida,yanzu ke in banda lalaci a aike ki sanyan katin waya ki kwaso kwalin waya ki kawo,tab Hajiya sannu Ashe kina fama.”
Ya fada yana maganar mata tare da juya kugu,yayi fari sanan ya rike haba yana Kare ma A’indo kalo.”
galala A’indo tayi tana kalon sa ta Kama haba tace”tab ashe dai hajiya taron mahaukata Kika kawo a gidan nan,tab ashe ban gama kalo ba,yau Allah na tuba ya aka iya dani ma bare kuma ga wani.”
tace tare da juya kacokan hankalin ta ga Rabi’u daudu .
Yamutse fuka Rabi’u yayi,Alamun dai ransa ya bace,yace”ke bari gani na haka wly yanzu zan tube mu kwashi yan kalo ehhhe ni Zaki kira da mahaukaciya sanan ki kira ni da wani ba wata ba,yau Allah na tuba ai kece mahaukaciyar baba ma kuwa😏.”
“Kai ni karku cikani da surutun banza,ai dukan ku ragaitatu ne,ke kuma taraki nake ,Allah duk ranar da kika cikani sai kinbar gidan,haba yarinya gakinan shiriritata,ba kimtsi ,na fara yarda kinada tabin k’wak’walwa.”
“Hahhh wly Hajiya kin canka daidai ,marar hankali ce lamba daya ma kuwa,cewar A’indo tana washe baki😁.
Sakaka Rabi’u daudu yayi yana kalon A’indo yace”hahh wly Hajiya kina fama,wanan kam ta zare sai ankawo mai rukiya🤣.”
Yana gama fadar haka ya kama hanya yayi tafiyar sa, yana tafiya irin ta mata yana kada kugu,baki a sake A’indo take kalon Rabi’u daudu har yabar harabar falon,ta tuntsure da dariya ,sanan ta kara gusowa wurin Hajiya tace”Hajiya wanan anma haka haka ne ko? dan wly naga Alamun shima sha tara ne,to in ba sha tara ba wane mutum ne duba fa hajiya A’indo tace tana koyon tafiyar Rabi’u daudu Hajiya tafiyar sa wane namiji zaiyi wanan tafiyar in ba haka haka ba ,to aradu Hajiya bani kadai ke bukatar magyarin mutum ba,wly wanan ma yana bukata.”
Kuma Hajiya dan Allah kice ma Alhajin gidan nan ya dinga tafiya a hankali,in ba haka ba yayi Bari dan naga cik’in sa ya kusa haihuwa,Kinga ranar ma ya Fado anma dai ya’yan basu mutum ba ko?
Da Allah Hajiya ki dinga cewa ya dinga tafiya a hankali,in zai fita gidan nan kiga Yana sauri,Kar yaje ya barar da Yan cikin,Kinga ku rasa yaran ku Dan Allah ki masa magana cewar A’indo domin itafa har ga Allah dagaske take ,dan ranar ma saida ta tambayi daya daga cik’in masu aiki cewar wai yaushe Alhaji zai haihu.
Saboda Alhaji yanada kyau saide katon ciki garesa,Wanda Yana tafiya cikin na rinjayar sa
Mugun kalo Hajiya ta jefeta dashi tace”wai A’indo yaushe zaki nutsu kiyi hankali, kuma mijin nawa kike ma haka wly ki kiyayeni zan saba miki.”
“Jiya ko shekaran jiya insha Allah,zanyi hankali hakiya.taba hajiya amsa tare da kamewa tsam.”
Kada kai Hajiya tayi ta tashi tabar mata wurin.
Ko akanta A’indo zama ma tayi a falon ta fara kalon wani American film da akasa, waro idanu tayi ganin wasu maza biyu suna fada a tv dayab ya zaune dayan yanata dukan sa,aiko me A’indo zatayi bayan aza hannu bisa kai ta kwala wata Kara da duk wani na cik’in gidan yaji,tace”Wayyo Allah dan Allah kuzo Kar ayi kisan Kai,Hajiya kuzo ku raba wly zai kashe shi,Hajiya Jin wanan ihun ta aza wasu ke fada da gudu gudu ta fito a firgice,Suma sauran jama’a gidan hakan suka garzayo a guje suna isowa falo suka iske A’indo ta aza hannu bisa kai tana sheka kuka,ganin an kashe wancan mutumin na Tv ,aiko kowa yayi cirko cirko da idanu aka zuba ma A’indo idanu cik’e da takaici,Dan sun lura da Tv ne take ,Hajiya da karasowar ta kenan tace “su waye ke fada kuma,A’indo fuska shabe shabe da hawaye,tace sai yanzu zakuzo bayan an gama yin kissa,ku yanzu gidan nan sai a kashe mutum bakuzo kun cece shi ba,ai gashinan sai kuje ku d’auki gawar kuyi mata jana’isar.”
Ni bara naje nayi Alwalla muzo muyi zaman makoki,nasan yanzu mutane zasu fara taruwa,ta fada tare da share hawayen ta tayi gaba tana cewa “Allah jikanka Hanmma.
Ahhhhh yau ni naga kala kala ni Rabi’a kekam Allah shi kwashe maki Albarka yanzu saboda Allah a TV ne ake wanan abu kika cika mana gida da kuwa,kekam anyi asara cewar Rabi’u daudu.”
ya fada tare da wani botsarewa ya turo kirji.
Cik’e da takaici Hajiya tace”A’indo bazan iya dake ba ,wly,ki tatara ki koma inda kika fito tun kafin kisa min hawan jini,in ba iskanci irin naki ba abinda ke Tv zakizo ki hana mutane kwanciyar hankali,to ni bazan iya ba tunda bazaki ki natsu ba.”
😳waro idanu A’indo tayi tace “haba hajiyata,aradu nidake mutu ka raba,kuma ai nayi haka ne dan a taimaki rai tunda naga ana gida guda.”
Uban waye yace Miki da gaske ne,wanan Tv ne wanan film ne,abinda kike gani ba dagaske bane wasan kwaykwayo ne kuma ma mu ke ganin su su basa ganin mu.
” La Hajiya yi hakuri ban sani ba anma daga yau zanyi hankali,dan Allah kiyi hakuri ,wly wanan gidan yanda kika san kanin uwata bazan iya rabuwa dashi ba.”🙄
tausayi taba hajiiya Hajiya tace “naji shikenan anma karki kara irin haka.”
Yauwa Hajiya ta wo ke wo ke,nidake mutu ka raba takalmin kaza,Yan bakin ciki saide a mutu ehehhh😏”
Ta fada tare da kalon Rabi’u daudu.”
Ahheee riiiii kom,anyi a banza wai ance da makaho ga ido yace a’a wari suke,yau Allah na tuba mai jiya taci bare yau,akace in da ranka kasha kalo,shidai dan kauye a ko ina sai ya nuna halin sa,kedai kin baro mata,gaki mace har mace anma ba gyara sai sakarci,kai wly mu mata an cuce mu.”😏
“🤔 Garjeje sangameme lukucece,tukeke,mumukeke rusheshen kato dakai kana Kai kanka jinsin mata,tab anma kam Allah dai ya shirya cewar A’indo.”
“Ke ki kiyayeni ,wly sai na tube mu ba hanmata iska dan ba ta Ido ce dani ba wly”
“Kai bana son shanshanci kuje ku bani wuri bazan iyaba Hajiya tace tare da barin gurin .”
Rabi’u saida yayima A’indo kalon sama da kasa,ya wani tabe baki irin na mata ,ya rike jalabiyar sa da hannu daya ,ya rike kugu da hannu dayan ya juya yayi tafiyar sa yana kada kugu.”
A’indo ta kece da dariya ta fita tayi ficewarta.”
Bayan kwana biyu A’indo ce zaune sai durzar kuka take baji ba gani,bini bini ta rike ciki duk Wanda ya tambaye ta lfy bata ko kula sa,Saida aka fada ma Hajiya sanan tace a Kira ta taji abinda ya faru,tana zuwa wajen Hajiya ta tsaya sai zare zaren idanu take,kamar wada tayi karya😢 Hajiya tace”A’indo me ke damun ki naji ance kinata kuka.”
Share hawaye A’indo tayi tace”yau Hajiya ba dole nayi kuka ba,ace kwana hudu mutum yana aje kahi a cik’in sa,tunda nazo banyi kahi ba,ace gaba-daya wanan katon hirgegen latsetsan gidan babu masai “A’indo ta fada tare da matse fuska😖.
“Ikon Allah to ke A’indo basu nuna Miki wajen kashin ba.”
Tab Allah ya tsari kakana habu anma wly ku yan binin nan akoi ku da Almabazaranci ,yau in banda waouwta irin taku wanan randar k’yakyawa ita za’ayi kahi wanan ai hede asha ruwa,jiya ma can ciki nasha ruwa na ,na kohi wly zar dadi🤗”
Innalillahi wa’ina illaihi Raju’un nikam Saude naga takaina A’indo a wanan farin abun Kika sha ruwa?
“Hahhh Hajiya yau ni ina ruwa na,tsab nasha kayana na kohi,yanzu dai hajiya ki taimaka min da inda zani nayi kahi dan wly tun jiya nake jin ana mun kidan danbagalaje aciki 😖 matse fuska tayi sai ji kake buuuutt ta buga tusa.
File Name | A’Indo Yar Aiki.. Hausa Novel Doc. |
Title | A’Indo Yar Aiki Complete |
Author | Maimuna Matar Abdull |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 17/07/2024 |
File Size | 433. KB |
Format Size | TXT |
Book Price | Free |
Phone No |
Download A’Indo Yar Aiki Complete Novel Document By Maimuna Matar Abdul
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.