NASIHA MAI RATSA ZUCIYA
Akwai ranar da zata zo, lokacin da kowa zai kalli sunanka an ma ba zaka kasance Online ba. A haka zaka kasance Offline. Masoyanka zasu yi ta jiranka dan ka yi hira dasu, an ma ba zaka sake hawa ba.
Zasu aika maka da saƙo na E-mail, Wall Post, Inbox, WhatsApp, Tictok, Text.. An ma ba zaka maida masu da amsa ba.. Zasu kasance cikin jiranka na tsawan awanni, an ma ba zaka taɓa hawa Online ba..
Matsayinka a Internet a kullum zai kasance da kalmar “Offline” a wannar ranar ka tafi babu kai.. Ba ka da halin yin “chatin”, “like” ko kuma “comment”, Ba ka da halin bada haƙuri ga waɗanda ka ɓata wa rai.
A wannan ranar ba zaka kasance tare damu ba, zaka kasance cikin ƙabari, rami mai duhu duk kai kaɗai.. Wataƙila zaka kasance mai da na sanin aikata munanan ayyukanka!
Wataƙila kuma kyawawan ayyukanka zasu zamo abokanan hirarka. Zaka tafi ka bar mu, babu abin da zai rage bayanka face dukkan abubuwan da ka rubuta a Facebook ɗinka da wanda ka rubuta wa abokanka.
Don haka ka kasance a cikin sanin cewa ba zaka bar komai ba face alkairin da ka rubuta wa kowa da wanda kai sharing a groups.
Yaya kenan idan ka zama mai sanya ko sharing hoton batsa/hoton masu tallata kansu, saƙo wanda ya saɓa wa addinka, da kalmomin da basu dace ba.
Kaga ka yaɗa alfahsha da shi za a riƙa tuna ka ana tsine maka a yayin da kake matuƙar buƙatar kyawawan addu’a!
Akwai wata rana, kowa Allah zai masa hisabi akan ayyukanshi don haka ina yiwa kai na nasiha da dukkan ƴan uwa musulmai.
________________________
Allah sa mu dace. Amin