Cututtukan da suke kama Al’aurar mata, wadan da suke hana mace jin dadin saduwa, da kuma jin zafi
Cututtukan da suke kama Al’aurar mata, wadan da suke hana mace jin dadin saduwa, da kuma jin zafi.
CUTAR AL’AURAR MATA. (VAGINITIS DISEASE)
VAGINITIS : Wata cutace da mafiya yawan jama’a su na kiranta da Vaginal Infection sabida wannan matsalar ta na addabar gaban mace . Amma a Hausance a na kiranta da Ciwon Sanyin Mata.
Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah
Wannan cutar wasu kwayoyin cutar Bakteriya da Fungus da ke zaune acikin Gaban mace su su ke kawoshi.
A na Iya samun wannan ciwon a lokocin juna biyu (ciki) da shayarwa , haka kuma za a iya samun ciwon ta hanyar jima’i .
Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya
CAUSES OF VAGINITIS:
👇🏾
1- Bacteria Vaginosis : Wannan wani kwayar cutace da ke rayuwa cikin farji, ya kan haddasa matsalar Sanyin mata .
2- Candidiasis : Wannan wata kwayar cutace Wanda ta ke haddasa Sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cutar su na zama cikin farji kuma ba su cika cutarwa ba, wadannan kwayoyin cutar su na son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.
3- Trichomonas Vaginalis : Wannan ita ce wacce ta ke yaduwa ta hanyar jima’i. Ita wannan kwayar cutar parasite ce ta ke kawoshi .
4- Irritation Vaginitis : Ita wannan a na kiranta da Allergic, wassu abubuwan da jikin mutun bai daukesu ba, a na samunsa wajen amfanida kamar su condom, sabulu, ko maganin shafawa.
Karanta>>> Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Jiki Musamman Yan Mata Da Matan Aure.
SIGN AND SYMPTOMS
1- Kumburin Farji
2- Canza Launin Farji zuwa Ja.
3- Kaikayin Farji
4- Warin Farji
5- Kurajen Farji
6- Zubar da Farin ruwa a Farji.
7- Jin Zafin Lokocin Jima’i
8- Zafin Fitsari.
Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin
PREVENTION OF VAGINITIS:
👇🏾
1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akwai wassu kwayoyin bakteriya wadanda ba sa cutarwa kuma su na da amfani , amfaninsu shine su na taimakawa wajen bayar kariya ga Farji , sai ka ga wasu matan su kan wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwan da a ke amfani da su wajen wanke farji ya kan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke Farji Da Sabulu da kuma wadansu abubuwa Wanda ba mu san Kansu ba.
Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata
2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants, wasu matan su kan bar wandonsu ya yi datti, Barin datti ko amfani pant masu datti ya kan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji. A Tsaftace wanduna.
Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam
3- Cleaning Faeces : Wajen wanke bahaya mafi yawan mata su kan dauki kwayar cutar da ta ke duburarsu zuwa Farji, wanda ba sa yi wa dubura illa amma su kan yiwa Farji illah. Shawara shine a fara wanke Farji kafin a wanke dubura.
Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.
4- Sharing of Underwear: Amfani da pants na wasu , ta yiu wacce ku ke amfani da pants daya ta na da cutar Sanyi idan kin yi amfani da nata kema za ki iya dauka. Sai a kiyaye.
Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi
5- Sexual intercourse : Mutum yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji shawara itace adinga amfanida Condom lokocin saduwa.
Shawara Idan mace ta ga daya daga cikin wadannan alamomi da mu ka lissafa daga sama ta garzaya zuwa asibity domin agane me ya ke damunta kuma a bata maganin da ya dace da ita, domin wannan matsalar ba na kemis bane.
Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata
Allah ya kiyaye Allah kuma ya kara mana lafiya.