Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 85 Complete Novel

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Wuraren ƙarfe 3:00 na dare,Jahad tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci zata gyara kwanciyarta,aikuwa taji an ƙanƙameta sosai an matse ta,numfashinta har wani kokawar ɗaukewa yake yi,ƙoƙarin janye jikinta ta shiga yi amman hakan ya faskara,saboda ruƙon da akayi mata bana wasa bane,cikin baccin ta dinga faɗin”Sehrish!ki sake Ni!kin matseni,numfashi na zai ɗauke” daƙyar sound ɗin ke fita saboda throat ɗinta da ke abushe,saboda thirsty da take ji,tun tana ambaton hakan ƙasa kasa har takai ga ɗaga muryarta “Sehrish!!dan Allah ki sake ni,baki ji nace kin matse ni ba? Shiru babu mai bata amsa domin kuwa duk bacci suke yi,

Jahad kuwa tuni ta gama galabaita hakan yasa ta tattare iya ƙarfinta na ƙarshe ta ingije junaid daga jikinta,ya ɗan yi baya,hakan yasa ta samu sarari,hannu tasa tare da zame bargon ta fiddo da kanta,tana faman sauke ajiyar zuciya,zufa duk ta wanke mata jikinta duk da weather ɗin nasu akwai sanyi,matsuwar da tayi ne yasa ta zubda gumi,juyawa ta ɗan yi tare da kallon gefen hannun hagunta,kasancewar akwai hasken electric bulbs ɗin da suka gauraye gidan daga waje da kuma na corridor ɗinsu gana main palour,Sune suka ɗan bama ɗakinsu haske,duk da an kashe Globe ɗin ɗakin nasu,dama kuma Sehrish ta lalata bedside lamp ɗin ɗakin,lokacin baya data kwala ma Haroon a goshinsa,

Ƙura ido jahad tayi tana ƙare masu kallo,gani take tamkar idonta ba dai dai suke nuna mata ba kamar mutun biyu ne kwance a gefen hagunta,hannunta ta miƙe tare da yaye masu Sehrish bargon da suka rufa dashi,gabanta ne ya faɗi rass!ganin Sehrish ga kuma hosana baje suna ta sharar bacci,nan take hankalinta yayi mugun tashi,wani irin tsoro ne ya lullu6eta,tabbas akwai mutun ɗaya 6angaren damanta,wanda suka kwana rungume da juna a ƙanƙame,wanda yayi silar taushe numfashinta,tashin hankali! kasa juyawa tayi don taga wanene saboda tsabar tsoro,sae dai ta zura hannayenta dake ta faman kerma ta laluba don taji in da gaske wani ne kwance a wurin,Sumar kan junaid ta shafo da hannunta,a razane ta zame hannunta,la66anta na kerma ta shiga furta”La’Ila ha’illah Anta subhanaka,Inni kuntu minazzalumin,”daga bisani ta shiga faɗin”innalillahi wa’inna ilaihirraji’Un!!,

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

Muryarta na kerma ta shiga kwalama su sehrish kira kaɗan kaɗan don kada aljanin ya farka,”Hosana!Sehrish!!dan Allah ku tashi!Mutum mutumi acikin ɗakinmu saman gadonmu!ina tunanin Aljani ne ya faɗo ɗakinmu don ya cutar damu,Wayyo Allah na” babban tashin hankalinta aljanin na akusa da ita,in ma cutar dasu yazo yayi toh ta kanta zai fara tunda itace a kusa dashi,

Tuni zufa ta gama wanko mata a fuskarta,numfashi kanshi daƙyar take fitar dashi don kada aljanin yaji yasan cewar idonta biyu,
“Sehrish!Sehrish!!hosana!wai ba zaku tashi ba?dan Allah ku tashi kuga abunda na gani,asaman gadon mu,”tana magana hawaye na sauka daga idonta,don ita ta riga ta sallamawa kanta cewar ajalinta ne yazo,

Duk wannan surutan da Jahad ke yi kaf a kunnan Sehrish,wadda ke lamo tayi nisa cikin zurfin tunanin da take yi,Duk a tunaninta Jahad mafarki takeyi shiyasa take sambatu,wannan dalilin ne yasa bata motsa ba,kuma bata tanka mata ba,idanunta ne kawae ke arufe amma idonta biyu,likimo kawai tayi,

Jahad na cikin wannan yanayin taji an aza mata hannu asaman waist ɗinta,a wani irin Firgice ta fashe da wata irin gigitacciyar ƙara,wadda tayi silar tashin hosana daga bacci,hatta sehrish sai da ta razana,a tare suka tashi zaune ita da hosana suna kallon Jahad dake ta ihun neman agaji,ai koda Hosana da sehrish suka ga hannun mutum a saman qugun jahad,a gigice suka duro daga saman gadon da gudun gaske har suna tuntu6e wurin tunkarar ƙopar ɗakin don su buɗe ta su gudu,jahad kuwa sam taƙi motsawa,sai ihu take tana kuka,waɗanda take tunanin cewa zasu taimaketa sun gudu sun barta asaman gadon ita kaɗai,jikinsu sae faman kerma yakeyi burinsu su buɗe ƙopar su gudu amma taƙi buɗuwa,hakan yasa Sehrish watsawa da gudu,ta shige toilet taja ƙopar ta rufe,ganin haka yasa hosana tunkarar wardrobe ɗinsu,ta buɗe gidan ƙasa da babu kaya sosai acikinsa sae bedsheets,Ta faɗa ciki tare da jan murfin wardrobe ɗin ta rufe shi,kowa yayi ta kansa kenan,duk wannan budurin da akeyi Junaid bai sani ba,domin kuwa ba ƙaramin abune ke iya tashinshi daga bacci ba,irin mutanen nan ne masu nauyin baccin tsiya,

Jahad na cikin wannan halin na firgici,taji an aza mata ƙafa asaman jikinta,firgitar da tayi ne yasa tayi wurgi da junaid gaba ɗaya,ya tafi dama yana dab da bakin gadon,aikuwa ji kake timmmm!ya ƙundumo ƙasa kanshi ya bugu sosai saman tiles,
raɗaɗin da yaji ne yasa shi farkawa daga baccin,ya fashe da matsanancin kuka,

Gaban jahad ne ya faɗi rass!!jin sautin kukan Junaid,rarrafowa tayi ta dawo gefen gadon tare da ɗan leƙawa don ta tabbatar ma kanta abunda kunnuwanta ke ji,Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonshi,yadda kasan wani jinjiri ya 6are baki sai kuka yake yi,da ƙarfi ta ambaci sunanshi”JUNAID”dakatawa yayi daga yin kukan da yakeyi jin an ambaci sunanshi,wurga idanunshi yayi akan jahad,yayi mata wuri wuri da ido yana kallonta,
Muryarta na rawa tace”juj..junaid!dama kai Ne?me kake yi acikin ɗakin mu?
cikin shessheƙar kuka yace”Nifa Zuwa kawai nayi don in taya ku kwana,”
…zuba mashi ido kawai tayi tana  kallon fuskarshi don abun ya fi ƙarfinta,
Daga cikin toilet ta jiyo Muryar Sehrish tana ce wa”Jahad wai dagaske junaid ne?Naji kin ambaci sunanshi”?
A ƙule jahad tace”Bansani ba,ku fito ku gane ma idonku,kunaji ina kukan neman taimako amma duk kuka watsa a guje kuka barni,yanzu da wani mugun abunne ba junaid ba,da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya,”
buɗe ƙopar sehrish tayi tare da fitowa daga cikin toilet ɗin,hosana ma ta buɗe wardrobe ɗin tare da fitowa daga ciki,suka tunkari inda junaid yake kwance yana faman sauke ajiyar zuciya,sae faman lumshe ido yakeyi,saboda baccin dake a idanunshi,
“Junaid!” sehrish ce ta kira sunanshi,ware idanunshi yayi akanta yana kallonta,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

..”junaid me kake yi a ɗakin mu?waya kawo ka?anya baka fara shan ƙwaya ba”
Harara ya wurga mata tare da murguɗa mata baki yace”bansani ba,duk kun bi kun takura rayuwata,hakanan kawai ina baccina kun tashe ni,laifi ne in na kwana aɗakinku,ni ba ɗan uwanku bane”? Sakin baki sukayi suna kallonshi,hosana tace”wlh saina faɗa ma Daddy da Ya Omar,ince ka shigo ɗakinmu ka kwanta mana asaman gadonmu,ƙato dakai,”tana kai ƙarshen maganarta,junaid yace”idan kin tashi ki faɗama Kaka ƙarewar daddyn,mai kan kurciya kawai” wannan maganar ba ƙaramin fusata hosana tayi ba,jikinta har rawa yakeyi wurin dauko pillow daga saman gadonsu,ta buga mashi asaman fuskarshi,koda ganin hakan,sehrish ma ta ɗauko pillow ta shiga taya hosana,jahad tace”wlh nima bazan ƙyale ka ba,junaid saboda ka bani tsoro,kuma babu kyau ma tsoratar da musulmi,”tasa hannu ta ɗauko pillow itama,nan fa suka tasa junaid kamar sun samu jaki,suka dingi jibgarshi da pillows,tun yana yi masu magiyar su daina har ya sake fashe masu da kuka yana bubbuga ƙafafunshi,suna cikin bugun nan nashi,suka ji tsit junaid ya daina motsi,cikin sauri Jahad ta kalli jikin pillown hannunta,Ɗigon jini ta gani,ɗagowa tayi da nufin ta nuna ma su Sehrish aikuwa karaf idonta ya sauka akan pillown dake hannun sehrish da hosana,duk ɗigon jini ne ajikin pillown hannunsu,Tashin Hankali!
Gaba ɗayansu ba ƙaramin kiɗima suka yi ba,ƴan hanjin cikinsu suka kaɗa,zagaye shi su kayi a zuƙunne suna kallon fuskarshi,
Fashewa hosana tayi da kuka tana faɗin”Wlh babu ruwa na!bani na kashe junaid ba!”maganar da tayi ba ƙaramin tsoratar dasu tayi ba,tuni ido ya raina fata,daga wasa!?
Jijjigashi suka shiga yi atare suna ambaton sunanshi”Junaid!junaid!!!ka tashi!dan Allah junaid ka tashi!!Wayyo Allah munshiga ukun mu!!dan Allah baby junaid ka tashi,” ko motsi wannan junaid baiyi ba,matsawa sehrish tayi tare da kanga kunnanta asaman hancinshi don taji in yana numfashi,ɗufff taji babu numfashi da sauri ta sanya tafin hannunta asaman kirjinshi saitin zuciyarshi nan ma taji zuciyar tashi tadaina bugawa,a wani irin sukwane ta ɗago da idanunta waɗanda sukayi luhu luhu cike tab da hawaye tana kallonsu Jahad da hosana,jiki a mace tace”ZUCIYAR JUNAID BATA BUGAWA HAKAN NA NUFIN MUNYI SILAR MUTUWAR JUNAID”!!!
Girgiza kai jahad ta shiga yi tana cewa”Junaid bai mutu ba,dan Allah ki daina faɗan hakan,kada ya tabbata dagaske,”tayi maganar a yayin da take kai hannu tana tatta6a fuskarshi”junaid!junaid!ka tashi dan Allah ka tashi junaid,”

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

Ganin yaƙi motsi yasa suka fidda rai da cewar junaid zai tashi,kifa kai sukayi su duka ukun suna shessheƙar kuka,ɗan ɗagowa jahad tayi tare da kai idonta kan fuskarshi,Abun mamaki sae ga murmushi ya bayyana akan fuskarshi,dimples ɗinsa guda biyu sun lotsa,Wani irin ihun farin ciki ta saki tana fadin”Bai mutu ba!junaid wasa yake yi mana,gayanan yana murmushi,’jin haka yasa su sehrish saurin ɗagowa da kawunansu suna kallonshi,sae faman wangale baki yakeyi yana dariya,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,
“Junaid”sehrish ce ta ambaci sunanshi,a hankali ya buɗe manyan idanunshi yana kallonsu one by one,sai faman 6a66aka dariya yakeyi,
Har suna haɗa baki wurin cewa”Kai junaid!meyasa zakayi mana haka?wlh ka tsoratar damu sosai,”
“Wanda yasa kuka bugeni,ko tausayina bakuji,kun wani taru akaina kuna jibgata kamar kunsamu jaki amale,shiyasa nima na rama da gangan na ɗauke numfashina don kuyi tsammanin kona mutu”yayi maganar yana murguɗa masu baki,Ajiyar zuciya suka shiga saukewa,
“Junaid dan Allah kayi haƙuri,bazan ƙara bugunka ba,kada ka faɗama kowa,”acewar hosana,
Harara ya jefa mata tare da ƙara tamke fuskarshi,
Cikin sanyin murya jahad tace”junaid baka da lafiya ne?mun ga jini ajikin pillow lokacin da muke bugunka,kuma da alama daga hancinka muka gogo shi,”
Shiru ya ɗan yi yana kallonta kafin yace”Lafiyata ƙalau Ni,nose bleeding ne ba wani abu ba dama ina yawan yinshi,yafi zuwa mun da daddare,shiyasa baku ta6a gani ba”
“Amma ka faɗama Abba ko wani game da nose bleeding din”? Girgiza kai yayi alamar a’a,da alama baison maganar,don haka yace”pls nidai mubar wannan zancen,kusan yadda za kuyi dani don Allah bazan iya komawa bedroom ɗina ba,tsoro ma nakeji,”yayi maganar ashagwa6e,
Jiki asanyaye jahad ta kalli su sehrish tace”kuje ku kwanta,bari ni na rakashi ɗakin nashi,” mikewa su kayi atare da ita da hosana suka koma kan gadon suka kwanta,tare da jan bargo suka lullu6e,
Miƙewa daga zaune junaid yayi yana cewa”Allah sai dai ki goyani,don na riga dana faɗa maki cewa ƙafafuna ciwo suke yi mun bazan iya taka stairs ba,”
Murmushi jahad tayi tare da cewa”shikenan,zan goya ka amma ka bari sai munje wurin benen tukunna in goya ka,” amsa mata yayi da toh,sannan ya mike tare da ruƙo hannunta cikin nashi yace”Tashi muje,”mikewa tayi suka fita atare,suna tafiya tana satar kallon gefen fuskarshi kamar wani zautacce sai faman sakin murmushi yake yi,hakanan ta dinga jin gabanta na faɗuwa,lamarinsa ba ƙaramin mamaki yake bata ba,kokonto ta shiga yi anya wannan ɗigon jinin da suka gani na ha6o ne? Yanayin yadda abun ya afku tamkar ba jinin ha6o bane,tabbas akwai dae wani abu dake damunshi wanda baison kowa ya sani,
Tana cikin zancen zucin nata taji yace”Mun ƙaraso wurin stairs ɗin,yanzu ki goyani,ki kaini har bedroom ɗina,kuma ki kwantar dani,”
Amsa mashi tayi da toh,sannan ta zuƙunna,ya daddage ya haye saman bayanta,tare da kwantar da kanshi luff kamar wani jinjiri,zagayo da hannayenshi yayi ta saman stomach ɗinta,hakan ba ƙaramin yanayi ya jefa ta ba,ji tayi tamkar bazata iya miƙewa tsaye ba,saitin kunnanta taji daddaɗar muryar nan tashi mai haɗe da shagwa6a”jahad ki tashi mu tafi,bacci nake ji,”

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Daƙyar ta iya mikewa tsaye goye dashi abayanta,hannu tasa ta tallaboshi sosai,sannan ta haye saman benen,tana tafiya tana tangal tangal har ta ƙaraso ɗakin nashi,hannu tasa ta ɗan tura ƙopar sannan ta shige ciki,Talal suka samu kwance yana ta sharar bacci,ƙarasawa tayi tare da sauke junaid saman gadon,ya gyara kwanciyarshi,bargo taja ta rufe mashi body ɗinsa zuwa neck ɗinsa,tana ƙoƙarin juyawa tabar wurin,taji ya ruƙo hannunta cikin nashi,jimmm tayi tana jiran jin me zaice mata,
“Jahad”ya ambaci sunanta da wata irin murya ta mai jin bacci,
“Na’am,”ta amsa mashi kiran a yayin da take juyowa” murmushi ya sakar mata tare da sanya yatsan hannunshi acikin dimple ɗin fuskarshi yace”Kiss me pls,” bakomai ya faɗo mata aranta ba,face abunda ya ta6a faruwa atsakaninsu,cikin motarshi,daga zuwa manna mashi kiss a side face ɗinsa,bakinta ya goce izuwa cikin bakinsa,a ranar zauce mata yayi,
Maƙe masa kafaɗa tayi alamar bazatayi mashi kiss ɗin ba,bubbuga ƙafarshi ya shiga yi yana yi mata shagwa6a,hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba,saboda wani irin kyau da yake bayyana akan fuskarshi aduk lokacin da yake shagwa6a,tamkar tayi hugging ɗinshi ajikinta haka ta dinga ji,
“Baza kiyi mun ba ko”?yayi maganar.yayin da idanunshi ke ƙoƙarin lumshewa,
“Shikenan,zanyi maka,amma ka rufe idanunka,” da sauri ya rufe su yana jiran jin la66anta asaman fuskarshi,tsayawa tayi asaman kanshi,tana karanto addu’o’i tana tattofa mashi akan fuskarshi,daga ƙarshe ta haɗe yatsun hannunta guda biyu na hannun damanta,a hankali ta aza yatsun nata asaman la66ansa,sannan ta furta sautin kiss ɗin da bakinta,wani irin farinciki ne ya lullu6e junaid,duk a tunaninshi bakinta ne ta aza asaman nashi,baisan cewa wayau tayi mashi ba,tasa yatsun hannunta amatsayin la66anta,
rufe mashi fuskarshi tayi da bargon,sannan ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin,
“I Love u so much jahad,” muryar junaid ce ta katse mata hanzarinta,dakatawa tayi tare da ɗan juyawa tana kallonshi,yana acikin bargon ya furta mata wannan kalmar,
“Kina sona jahad”?
Wani irin ƙayataccen murmushi ne ya sauka akan fuskarta,bata bashi amsar tambayarba,cikin sauri ta fuce daga ɗakin nashi,ta koma bedroom ɗinsu ta kwanta zuciyarta cike fal da farin ciki,ta ji daɗin kalmar da junaid ya furta mata,duk da bata da tabbacin cewar ko dagaske yake yi mata,” da wannan tunanin bacci ya ɗauketa,

*Boss Bature*

🤍❤🤍
Washe Gari,

Kwance take asaman katifarsu,ta saki baki tana ta sharar baccinta,sae faman jan minshari takeyi kamar Ragon layya ga miyan bacci dake gangarowa ta cikin bakinta da ta bari a buɗe,tana cikin baccin nan taji Ringing ɗin wayarta da ƙarfin gaske har cikin dodon kunnanta,hannu tasa tare da toshe kunnanta tana faman buga tsoki,alamar an takura mata,bata ɗaga kiran ba,har ya katse kuma sai ga wani kiran ya ƙara shigowa,a hargitse Abra ta miƙe ranta a matuƙar 6ace,tasa hannu ta dauki wayar dake ajiye gefenta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta Cike da masifa tace”Wai Uban wanene ke kirana tunda sanyin safiya”?
Kafin ta rufe bakinta taji ance”Ubanki ne!” har sai da gaban abrah ya faɗi rasss,cikin sauri ta janye wayar daga kunnanta tare da kallon screen ɗin wayar don ta shaida mai kiran nata,Sunan Aunty babba ta gani,yatsina fuska tayi kafin ta mayar da wayar a kunnanta,”ina kwana aunty,an tashi lafiya”

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Rai a6ace Aunty babba tace”Ruƙe gaisuwarki,sakarya daƙiƙiya zaman uban mi kike ke da Mammy da har kuka bari AMAL ta gudo daga mai duguri tazo Abuja wurin Amani?!” jin wannan maganar yasa abrah ta zabura,don har sai da ta daki ƙirjinta da hannunta,Hankali atashe tace”Aunty laila dagaske Amal tana abuja wurin Amani!”
“Ƙarya zan maki ne?Kuna nan sake da baki har yarinya ƙarama tayi maku wayau ta gudu,Yanzu baki ga yadda Amal ta koma ba,Yarinya ta zama ƴar hutu kamar wadda ta taso a gidan naira,Tamkar bata ta6a shan wahala ba,Irin rayuwar dana so ace ke kika same ta,sae gashi ƴar kishiyar da muka tsana ita ta samu wannan damar,ina nan dake in har mu kayi sake AMAL sai ta auri ɗaya daga cikin ƴa’ƴan Alexandra,”
Saboda tsabar takaici Hannu ɗaya abra ta aza asaman kanta tana faɗin”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’Un!
Aunty babba tace”kaɗan ma kika gani!duk laifinku ne!da alama su Amani sunfi mu Jinin Nasara,shiyasa suke ta cin galaba akan mu,”
Muryar abra tamkar zatayi kuka tace”Wlh aunty laila har shawara sai da naba mammy tun kafin amal ta gudu nace mata mu 6alle ƙafarta guda ɗaya,don ta zama gurguwa kinga in mukayi hakan ba yadda za’ae ta gudu,Amma saboda shegen son kuɗi irin na mammy tace Wai mu barta da ƙafafunta,saboda tana so Amal ta auri mai kuɗi don ta rinƙa tatso mana kuɗi a wurinta,Yanzu gashi nan Mammy taja mana”
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci kafin Aunty babba tace”Abra inaso kiyi gaggawar tattara kayanki kibar gidan nan!kema ki dawo Abuja gidan surukanmu da zama!wannan kaɗae ce hanyar da zamu iya cin nasara akansu,”
“Aunty in dawo nan fa kika ce?Aunty hayaam fa?zata dawo gida ne”?
“Bazata dawo ba,zama ma yanzu ta fara shi har sai an shafa fatihar aurenta da Babban yayansu,kawai abunda nakeso dake,ki tattara kayanki ki dawo gidan da zama,saboda ni bani da tabbacin cewar zama na zaiyiyu acikinsa,atakure nake,”
Jinjina kai Abra tayi tamkar tana agabanta tace”Shikenan Aunty laila,da yaushe kikeso inzo nan ne?kuma ya zamuyi da mammy?kinsan fa bata da lafiya tana can kwance,”
Dogon tsoki Aunty babba taja tare da cewa”Wake ta wani mammy?ae kawai ki tattara kayanki yanzun nan ki biyo motar Abuja ta kawoki,Ita kuma mammy Allah ya bata lafiya shine kawai,”
Fuskar Abra ɗauke da murmushi tace”aikuwa yanzun nan zan shirya,zan ma iya sa ɗaya daga cikin samari na,ya kawoni gidan don duk suna da Mota,”
Aunty babba tace”Yawwa cikin sauƙi ma,ki kira ɗaya daga cikinsu,ya kawoki,”
“In sha Allah Auntyna,” abra ta amsa mata kafin sukayi sallama,

Duk wannan wayar da Aunty babba keyi kaf a kunnan Hafsat da hayaam dake kwance saman gado,ita kuma tana zaune asaman Stool dake agaban mirror,
“Mommy wannan abun kunyar har ina?taya zaki ce abra tadawo gidan nan da zama?bayan ga hayaam kuma!Nan fa gidan surukanku ne ba gidan ƙanin mahaifinku ba….” a fusace Aunty babba ta jefa ma hafsat wayar hannunta cikin sa’a tasamu gefen goshinta,dafe wurin hafsat tayi saboda zafin da taji,
Rai a6ace tace”Hafsat ki fita daga idona in rufe!kina yimun shisshigi acikin lamurrana,Ina ruwanki da zaman su Abra acikin gidan nan?ke zaki ciyar dasu ne?ko saman kanki zasu zauna ne”?
Shiru hafsat tayi batare da ta tanka mata ba,hayaam dae bata sanya masu baki ba,saboda gudun rashin kunyar hafsat don bata raga ma kowa acikinsu,

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Wuraren ƙarfe tara,Azmee da Saude suka kammala girke girken breakfast na gidan,yanzu ta samu sauƙi wurin yin aiki don Saude ba ƙaramin taimaka mata takeyi ba,dayake itama kwararriyace wurin iya girki tana son yin girki,bayan sun kammala,Azmee ta shiga jera mata Warmers acikin tray tana kaiwa saman dining table,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala jera abincin,

ɗaya bayan ɗaya matasan gidan suka shiga fitowa daga bedroom ɗinsu,su Kanal yousouf,Irfan jabeer khaleed twins,fawan,sune waɗanda suka fara hallara daga baya,Abbansu tare da Mommynsu junaid suka fito,kafin wani lokaci kowa ya fito,hadasu Dr haris su Captain adam,najeeb talal da kuma junaid,da sauransu duka dai,Mutun ɗaya ne bai fito ba,bakowa bane fa ce Surgeon general Rafayet,

Bayan matasan sun hallara Azmee taje ɗakinsu Sehrish ta taso su daga bacci,atare suka fito bayan sunyi brush su uku kowacce sanye da hijabi ajikinta,tun ta sallar asuba ce da suka sanya ajikinsu basu cireta ba,bacci yayi awon gaba dasu,
Gaishe dasu Abba suka fara yi,fuskar kowannansu ɗauke da murmushi haka suka shiga amsa masu gaisuwar,daga bisani suka shiga gaisar da yayyensu,kowa da irin yadda yake amsa masu gaisuwar cike da zolaya,don wasu ma hada kwaikwayon Muryarsu,hakan ba ƙaramin nishaɗi ya sanyasu ba,

Komawa su kayi tare da samun wuri suka zauna a dining chairs ɗin da Abusufyan ke zaune,atare suka haɗa baki wurin cewa”Daddy ina kwana?ka tashi lafiya,”
ɗagowa yayi tare da kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya kafin yace”Lafiyalou Alhamdulillah!”

Natsuwa kowa yayi,yayin da Azmee da saude suka shiga zuzzuba masu abincin,kowa na faɗin abunda yake so yaci,
Gyaran murya Abba yayi tare da kallon azmee yace”An kai ma Ammi nata breakfast ɗin”!?
azmee tace”Eh nakai masu,a ɗakin gwaggo don acan tace mun zatayi kalacinta,ita da ƴar uwarta,”
Murmushi ya ɗan yi don ba ƙaramin daɗi yaji ba,
“Azeema fa”? Ya kuma tambayarta,
“Itama tana atare dasu,can ɗakin gwaggon,”
Jinjina kai abba yayi kafin ya kuma cewa”Aunty saratu fa?da ƴanmatan ta suma ankai masu nasu”?
Saude ce ta kar6e da cewa”Ni nakai masu a ɗakinsu,”
Abba yace”Aikin ku yayi kyau,”ya ƙarasa maganar tare da kai hannu ya ɗauki plate ɗin dake hannunsa yaci gaba da cin abincinsa da azmee ta zuba mashi,
Abbas yace”Azmee banga su Amal ba?ko ankai masu nasu ne”?yayi maganar ayayin da yake ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunshi,?
“Na kai masu a bedroom ɗinsu,” ta bashi amsa,

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Nonuwanki Lokacin Da Kike Shayarwa 

Ganin Abbas ya tambayi iyalinsa ne yasa Ishaq yin gyaran murya yace”Azmee wai ni ina ƴata hafsat ne?ko an manta dasu ne?naga ban gansu ba!?
“Ni kaina inata so in tambayesu,tun shekaran jiya rabon da in Sanya su a cikin idona,tamkar basa a cikin gidan nan”!Acewar Abbansu,
“Bari na kirasu,”Azmee ta faɗi hakan tare da juyawa ta nufi ɗakinsu laila,
abinci take ci,amma hankalinta ba akwance yake ba,Yau tunda ta tashi daga bacci gabanta ke ta faɗuwa rasss!rasss!mafi yawancin lokutta in taji gabanta na yawan faɗuwa to tabbas wani abune zai faru da ita!mai kyau ko mara kyau,sam takasa cin abincinta,sae faman jujjuya cokalin hannunta takeyi acikin plate ɗin dake agabanta,
A hankali ta ɗago da idanunta tare da azasu akan Hosana dake ta faman cunkusa Burger acikin bakinta,yadda kasan zata 6ara bakin ko gajiya da Ci ba tayi,Allah sarki rayuwa kenan,Allah mai yadda yaso,kamar basu bane waɗannan yaran ba,masu yawo babu takalmi a ƙafafunsu,kawunansu babu ɗan kwali,Kayan jikinsu duk a yayyage,babu mai son su,rayuwarsu a wulaƙance kowa gudunsu yakeyi,Amma yanzu komai ya canza!Yanzu gasu acikin danginsu,kowa sonsu yakeyi,suci mai kyau su sha mai kyau,su kwana a mai kyau,suturar sawa ma sai sun za6i wadda suke so su sanya ajikinsu,duk mai yajawo wannan, haƙuri!sun rungumi ƙaddararsu sun cinye jarabawar da Allah yayi masu,basuyi gajan haƙuri ba,kullum cikin kai kukan su wurin Allah suke,saboda sun san cewa shi kaɗai ne zai iya share masu hawayensu,duk irin ƙuncin rayuwar dasu Sehrish suka shiga,basu ta6a ƙasƙantar da kansu ba don suyi bara,ko su siyar da mutuncinsu don su samu kuɗi,kamar yadda wasu mutanen keyi,

Janye idanunta tayi daga kan hosana ta mayar dasu kan jahad,wadda ke ruƙe da bread a hannunta,tana goga mashi butter,abun ya ɗaure mata kai kowa sai cin abinci yake yi hankali kwance,amma ita takasa Cin nata,to ko dai bata da lafiya ne? ta ƙarasa zancen zucin tare da juyawa,karaf idanunta suka sauka akan Fuskar Abusufyan wanda ke kallonta,har sai da ta ɗan razana kaɗan,sunanshi ta ambata abakinta a hankali”daddy,”
..murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa”Daughter,tun ɗazu ina kallonki,kin ƙi cin abincinki,kin tasa ƴan uwanki gaba kinata kallonsu ɗaya bayan ɗaya,faɗamun meke damunki ne’?
“Daddy am not feeling well,gabana sai faɗuwa yakeyi,bansan meyasa ba,shiyasa ma nagaza cin abincin”muryarta akasalance tayi maganar,
Jahad tace”Daddy,jiya ma batayi wani isasshen bacci ba,”
“Saboda me”?yayi tambayar yana kallonta,
“Nikaina bansan meyasa ba,kawai bana jin daɗi ne,”
Jinjina kai yayi tare da cewa”Kada ki damu in sha Allah wannan faɗuwar gaban da kikeji Alkhairi ne zai faru dake,”
“Allah yasa haka ne daddy” ta ƙarasa maganar tare da kai hannu ta ɗauki cup of tea ɗin dake agabanta,ta shiga kur6arsa a hankali,ba don tana jin daɗinsa ba,

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Suna cikin cin abincin nan,sae ga Azmee tare da hafsat,sun shigo dining area ɗin,Aunty babba na a bayansu ta sanya Niqab a fuskarta,hayaam dai bata fito ba,saboda gudun karsu haɗu da Sgr a wurin,da hannu Azmee tayi masu nuni da su zauna a inda su Jahad suke,saboda nan ke akwai empty chairs guda biyu da suka rage,da yake table ɗin mai mazaunin mutun Shida ne,
Tunda suka zo wurin,idon kowa ya koma akan Aunty babba dake sanye da niqabi,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,sai da suka fara gaishe dasu Abba,sannan suka samu wuri suka zauna,hankalin Aunty babba sam ba’a kwance yake ba,bata so fitowa ba,Azmee ce ta sanar da ita cewa Ishaq yace su fito dining suci abinci,tayi mata hakan ne saboda ta rama Wulaƙancin da sukayi mata,

Daƙyar ta iya gaishe da Abusufyan,batare daya ɗago ya kalleta ba ya amsa mata,hafsat tace”Uncle ina kwana,”?
“Lafiya lou hafsat,ashe kuna acikin gidan,ae nayi tunanin kun koma Kaduna ne,”
Murmushin yaƙe tayi,sae faman zazzare ido takeyi,duk sunbi sun tsargu,ita da mommynta,ita dai Sehrish ta zuba ma sarautar Allah ido,so take taga ta yadda Aunty babba zataci abinci da niqabi a fuskarta,ba ita kaɗae ba hatta jahad abunda take jira kenan,Ishaq kuwa tuni ranshi yayi mugun 6aci,sarai yasan cewa da gangan ta zura niqabi a fuskarta bayan tasan cewar abinci zata ci,alamun rashin gaskiya duk sun bayyana atattare dasu,ita da hafsat,
Serving ɗinsu Aunty azmee tayi,ta tura masu plate ɗin abincin agabansu,hafsat dai tayi kokarin cin abincin,kaɗan kaɗan take tura chips abakinta,Aunty babba kuwa kamar gunki haka ta ƙame saman kujerar taƙi motsi,fargabarta kada hosana ta gane cewa itace,
Murmushin mugunta sehrish ta saki,tare da yin gyaran Murya tace”Aunty,ki cire niqabin mana,in ba haka ba,bazaki ji daɗin cin abincin ba,gashi yana ta hucewa,bazaiyi maki daɗin ci ba inya salafce,”
Mazurai Aunty babba tashiga yi ta cikin niqabin,ƙululun baƙin ciki kamar ta shaqo sehrish ta rufe ta da bugu,ƙin magana tayi saboda gudun kar Hosana taji Muryarta,ta kara tona mata asiri,hakan yasa Jahad cewa”Na ji tayi shiru,kodai bacci ne bai isheta ba”?tayi maganar tana faman ƙumshe dariya abakinta,sehrish tace”inaji tayi bacci ne a zaune,bari na cire mata niqabin don tasha iska kada numfashinta ya sarƙe,” yunƙurawa Sehrish tayi tare da kai hannu zata zame niqabin dake a fuskar Aunty babba,ae kuwa a firgice Aunty babba ta zabura ta miƙe tsaye tana faɗin”Karki kuskura ki ta6amun niqabi na,” rai a6ace tayi maganar,aikuwa Hosana najin Muryarta,ta daddage ta fasa uwar ƙara,tare da yin wurgi da kofin dake a hannunta,a gigice ta miƙe tana ƙokarin guduwa,gaba daya hankalin kowa ya dawo kanta,Omar ne ya miƙe da sauri ya ruƙo hannunta yana tambayarta lafiya,
A tsorace tashiga fadin”Banason ta!na tsane ta!wlh ya Omar muguwace matar nan,tazo nan ne don ta kashe mu,dan Allah ku koreta daga gidan nan,wayyo Allah na…..”ta fashe da matsanancin kuka,tashin hankalin da ba’a samashi date!nan fa kowa ya miƙe tsaye yana bin Aunty babba da kallo,saboda tsabar ruɗu muryarta na kerma tashiga

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

cewa”wa…wallahi Billahil azimu Ni bansanta ba!bansan laifin me na aikata mata ba,yarinyar nan fa mahaukaciya ce tana da ta6in hankali,shiyasa take wannan sambatun….”tunkan ta ƙarasa maganar Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa”karki kuskura ki ƙara kiran ƴata da sunan mahaukaciya!in ba haka ba ranki zai 6aci a wurin nan ne!hosana bazata ta6a tsangwamar mutun hakanan ba batare daya aikata mata wani mugun abun ba,” ya karasa maganar tare da jan dogon tsoki,
“Ya Omar dan Allah ku sakar mata karnuka su fiddata daga cikin gidan nan,wlh babu Allah aranta!so take takashe maka hosanarka,”cikin shesshekar kuka take maganar,Marshal sai ƙokarin rufe mata bakinta yakeyi don ta daina amma ina hosana taƙi rufe bakin,don har cizon hannunshi takeyi,in yayi ƙoƙarin toshe mata baki,Aunty babba kuwa sae faman zabga salati takeyi,jikinta sae kerma yakeyi,tuni zufa ta jika ta sharkaf,ƴan hanjin cikinta kuwa sae faman kaɗawa sukeyi,hankalin General ishaq ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kada ace wani mugun abunne laila ta aikata ma yarinyar da har take tsoron ganinta,
Lalla6awa Aunty babba tayi da gudu tabar dining area ɗin ta koma cikin dakinsu,tana shiga ciki ta aza hannayenta asaman kanta tana faɗin”Na shiga uku!Na bani!na lalace!Waccen mahaukaciyar yarinyar tana son taja mun bala’e ina zaman zaman lafiyata,”tana magana tana cizon yatsan hannunta,”Aunty laila meya faru,”hayaam ce tayi mata tambayar,
“Hayaam ta faru ta ƙare!yarinyar can ta gama dani!”muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,hannu tasa tare da zame niqabin fuskarta,tayi wurgi dashi ƙasa,sannan tashiga zagaye ɗakin tana faman cizon yatsanta,

“Dan Allah kowa yayi haƙuri ya koma ya zauna,ina tunanin ciwon hosana ne ya motsa,ba wani abu ba shiyasa take ta sambatu,”Omar ne yayi maganar don ya kwantar masu da hankalinsu,
Fashewa da wani sabon kukan hosana tayi tana faɗin “Wlh ya Omar Ni da hankalina,da tunani na!nasan me nakeyi,wannan matar itace ta….”kasa ƙarasa maganar tayi saboda tsawar da Omar ya daka mata “Shut up hosana!bana son na ƙara jin maganarki a wurin nan!in ba haka ba saina sa6a maki,” tafin hannunta tasa tare da toshe bakinta,tana yin kuka ƙasa kasa,
“Ka daina yi mata tsawa Omar,tabbas akwai abunda akayi ma yarinyar nan,wanda ya ƙona mata zuciya shiyasa take wannan sambatun,ya kamata mu lallasheta,muji menene matsalarta”? Acewar Abba,
Ishaq yace”hakane,In ba damuwa Inason ganinka Omar tare kuma da yaran,”
Ya ƙarasa maganar tare da shigewa gaba,Omar yabi bayansa hannunshi ruƙe dana hosana,jahad kuma na abayansu,

Bayan tafiyarsu,kowa ya koma ya zauna,wasu suka cigaba da cin abincinsu,wasu kuma suka bar dining ɗin waɗanda suka ƙoshi da abincin kenan,wurin yayi tsit kowa da abunda yake saƙawa aranshi,

Karanta>>> Amfanin Zogale Guda 18 A Jikin Dan adam

A 6angarensu General ishaq kuwa,a farfajiyar gidan suka zauna saman wasu ƙayatattun kujeru na shakatawa,kowa ya zauna,Hosana da jahad suna fuskantar Ya Omar da kuma ya ishaq,
Gyaran murya ya ɗan yi tare da kallonsu yace”dalilin dayasa na buƙaci ganinku,saboda inason jin menene alaƙar dake atsakaninku da Laila matata?shin taya akai hosana ta santa da har take tsoran ganinta”?
Kafin su bashi amsa Omar yayi hanzarin cewa”Ae farko sun ta6a zama a wurinta,Ni na kaisu gidanka,a lokacin kayi tafiya,na damƙa amanarsu a wurin laila,saboda ina da tabbacin cewar zasu samu kyakkyawar kulawa a wurinta,tun da ita mace ce,zasu fi sakewa a wurinta,”
Tunda ishaq yaji hakan gabanshi ya fadi,saboda yasan halin laila sarai,bata da mutunci,saboda mugun halinta yasa masu aiki suke gudun gidan,duk ƴar aikin da sukayi ƙarshe guduwa takeyi daga gidan saboda masifarta,
janye idonshi yayi daga kan Omar dake magana,ya mayar dasu kansu jahad da hosana,yace”Ina sauraronku?A zaman da kukayi tare da laila me ya faru?
Jahad tace”babu komai,munyi zaman lafiya tare da ita,”tana rufe bakinta hosana tace”wlh ƙaryane!jahad ƙarya takeyi maku,batason ta faɗi gaskiya ne,”ta ƙarasa maganar tana matse kwallar data zubo mata a idanunta,
“Jahad!kinsan banason wasa!faɗamun gaskiyar abunda ya faru acikin gidan,bayan na barku,” Marshal ne yayi maganar fuskarshi a ɗaure babu alamun wasa tattare dashi,hakan ne yasa jahad ta natsu ta shiga kora masu bayani,
“Ya Omar,tun lokacin da ka tafi kabarmu a gidan,Aunty laila ta rufe mu acikin wani tsohon store,babu ci babu sha,iska kanta daƙyar muke shaƙarta saboda wurin a ƙuntace yake,babu window,ga ƙwari dake yawo acikin store ɗin,ranar acikinsa muka kwana,hosana ko bacci bata samu ba……”gaba ɗaya jahad ta kwashe duk abunda ya faru dasu agidan Aunty babba,tun daga A har Z ta sanar masu,a ƙarshe ta fashe da kuka,
Ishaq kuwa ba abunda ke fitowa daga bakinshi sai kalmar innalillahi’wa inna ilaihirraji’un,’Muryarshi har kerma takeyi wurin cewa”Omar meyasa ka kaisu gidana ne?wlh da ace ka sanar dani tunda farko,da banbari ka kaisu wurin laila ba,saboda nasan halinta,hakanan nake zaune da ita,matar nan bata da imani!muguwace!yanzu ni bansan ya zanyi ba!da wani ido zan kalli Abusufyan da sauran ƴan uwana idan sukaji wannan Zaluncin da laila ta aikata ma Yaran nan!!
Yana magana,huci na fitowa daga bakinshi,ranshi yayi mugun 6aci idanuwanshi sunyi jawur,
Marshal Omar kuwa saboda tsabar 6acin rai,ya gaza buɗe baki yayi magana,tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu saboda takaicin abunda laila ta aikata ma su jahad,yaran da ya damƙa mata amanarsu,sai yanzu ya gane dalilin da yasa duk in yaje gidan a lokacin da suke wurinta,sai yaga fuskokinsu babu walwala ashe bayin Allah azabtar dasu takeyi,
Daƙyar ya iya buɗe baki yace”Amma Laila ta cuce Ni!ban ta6a tunanin zatayi mun haka ba,Meyasa zatayi mun haka?laifin me kuka aikata mata?kawai saboda taga baku da gata ne,don nace mata marayu ne ku shine ta ƙuntata rayuwarku?Ashe itace ta sanya wannan fasiƙin mutumin ya ɗauke ku acikin motarshi don ya zubar mata daku acikin dajin,har yayi ƙoƙarin Yima hosana fyaɗe acikin gidan gonarshi…. ” sai yanzu ya gane dalilin da yasa Major yaƙi sanar dashi gaskiyar lamarin daya afku,koda ya tambayeshi a lokacin baya sai cewa yayi yalla6ai banso in shiga tsakaninka da Matar yayanka ne,Ashe mugun abu ta aikata masu,
A fusace Ishaq ya daki table ɗin dake agabansu,ya miƙe azabure yana ƙokarin zame belt ɗin wandonshi,a ƙoƙarinshi na ya shiga cikin gidan yayi ma Aunty babba bugun tsiya,
Da sauri Omar ya ruƙo hannunshi,”Ya ishaq,ba anan yakamata ka yanke mata hukunci ba,koba komai ita uwar ƴa’ƴanka ce,mutuncinta zai zube agaban kannenmu,da sauran mutanen gidan,inaso taci albarkacin wannan,”
Runtse ido ishaq yayi wani irin huci ke fita daga bakinsa,damƙar hannun Omar yayi tare da janye shi daga ruƙon da yayi mashi,ko waiwayenshi baiyi ba ya shige cikin gidan,

Jiki ansayaye Omar ya mayar da idanunshi kan su hosana dake tsaye,wani irin tausayinsu ne ya lullu6eshi,matsawa yayi tare da janyosu ya rungumesu ajikinshi,tamkar ya zubar masu da hawaye haka yake ji,Yayi danasanin kaisu wurin laila,bakomai ne yaja hakan ba fa ce rashin sani,cikin sanyin Murya yace”kuyi haƙuri ku yafe mun,duk laifina ne dana kaiku wurinta,wlh danasani kai tsaye Abuja na kawoku gidanmu,Ni duk atunanina zaku fi samun kulawa a wurinta,ƙaddarace kawai ta riga fata,Amma wlh da ace kun sanar dani tun lokacin da nake zuwa gidan,da saita ɗanɗani kuɗarta,” ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga nasu,
Jahad tace”Ya Omar kadaina ɗaura ma kanka laifi,dama can Allah ya ruga da ya ƙaddara faruwar hakan,kuma yanzu ae komai ya wuce,ni wlh ba don hosana ta fara tona mata asiri ba,da babu wanda zaiji wannan maganar abakina,don har gargaɗin hosana nayi akan kada ta sanarma kowa amma bataji ba,”
Murmushi Omar ya ɗan yi tare da kallon hosana dake ta faman sauke ajiyar zuciya,ruƙo hannunta yayi cikin nashi sannan yace”Hosana tayi mun dai dai jahad!idan har aka biye ta taki,bazaki ta6a bari a hukunta mara gaskiya ba,saboda tausayinki,abunda nakeso ki gane jahad,Irin waɗannan mutanen masu baƙar zuciya,idan har ba’a dinga hukunta su ba,to basu ta6a gane kuskurensu,balle har suyi nadamar abunda suke aikatawa su daina,” jinjina kai jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace”Hakane ya Omar,kayi gaskiya,Sehrish ma ta ta6a fadamun hakan,lokacin da nayi ƙokarin hukunta hosana akan tonan asirin da taso tayi ma matar Ya ishaq,’ sun jima atsaye suna magana kafin daga bisani Omar ya ruƙo hannayensu tare da shigowa dasu cikin gidan,

Hankalin aunty babba fa yaƙi kwanciya,babban abunda takeyi ma fargaba shine kada Hosana ta tona mata asiri agaban surukansu,kusan sau uku tana shiga toilet saboda cikinta daya katsa,har wurin ƙarfe 2:30,bata daina safa da marwar nan ba,acikin ɗakin,ƙafafunta har sai da suka fara yi mata raɗaɗi sannan ta samu wuri ta zauna daga gefen gadon tana faman sakin huci,shigowa hafsat tayi cikin ɗakin,fuskarta jawur sae faman kuka takeyi,aunty babba na ganinta ta miƙe hankalinta a matuƙar tashe ta shiga tambayarta Meya faru,Cikin shessheƙar kuka hafsat tace”daddy ne,Yayi mun faɗa sosai akan abunda muka aikata masu hosana,har mari na sai da yayi,kuma yace daga yanzu babu ni babu shi,In nemi wani uban,!”
Hannu aunty babba ta aza asaman kanta tana ambaton”Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un!wayyo!nashiga uku!shikenan Hosana ta gama dani ta tona mun asiri wurinsu ishaq,Wayyo Ni laila,Zawarci ba fashi,” tana magana tana cizon yatsanta,
Fitowar hayaam kenan daga cikin toilet taji suna wannan maganar,jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,babban abunda take ji ma tsoro shine Ishaq ya saki Laila,saboda tasan cewa muddin ya saki aunty babba,to zamanta a gidan ya qare!!tunda bata da wata aƙala dasu,!Tashin hankali,ishaq bai ta6a gigin ta6a jikin hafsat ba,duk irin girman laifin da take aikatawa,amma yau akansu hosana Tasha mari,idan har hakane menene hukuncin aunty babba?ita da ta ɗauki nauyin shirin gaba daya,OMG!! Rungumota hayaam tayi ajikinta tana lallashinta,daƙyar ta samu hafsat tayi shiru,

*Boss Bature*

❤🤍❤

Back to top button