Harijin Sarki Page 33 Romantic Hausa Novel
A daren da Samha ta haihu masarautar Zirkan ta canza tamkar ba ita ba Haske ya lulluɓe sarautar gaba ɗaya fitilun da suka daɗe suna yin rauni sun ƙara ƙarfi, kuma rana ta fito da safe ba kamar kowace rana ba tana ɗauke da wani irin haske mai sanyi. Mutanen gari suka taru suna kallon sama, suna mamakin wannan sabon yanayi.Wasu suka ce,An haifi mai alheri.”Wasu kuma suka ce,“Wani abu ya dawo duniya da bai kamata ya dawo ba” A ɗakin Samha kuwa, duk sanda ka kalli fuskar jaririn zaka ga annuri Rashid yana tsaye yana kallonsa cikin hawaye zuciyarsa tana cike da tsoro da farin ciki a lokaci guda, kallon yaron yake sosai yace “Wannan jaririn ba kawai jariri ne kamar kowa ba Samha” murmusawa tayi cikin rauni tana girgiza kai tace “Na sani, Rashid. Amma duk kuwa da haka, shi ɗanmu ne. Kuma zan kare shi da addu’a, ba da takobi ba”A ɓangaren Granny tana karanta addu’o’i cikin nutsuwa A lokacin da ta ɗaga kai, idanuwanta suka cika da haske tamkar ta ga abin da wasu ba sa iya gani.“Na ga wani abu a bayan wannan yaro,” ta furta cikin rawar murya, “Hasken da zai rushe duhu amma kuma zai fuskanci jarabawa mafi tsanani kafin ya kai ga wannan nasarar” Rashid ya matsa kusa:“Kina nufin…?”Granny ta ce cikin natsuwa:“Wannan haihuwa ta haifar da sabuwar ƙaddara. Ameer bai mutu ba, amma ikon da ya riƙe ya raunana. Yaron nan ne zai zama ginshiƙin da zai karya sirrin da sarauta ta jingina da shi tun ƙarni da suka shuɗe.”Samha ta lumshe ido tana shafa fuskar ɗanta “To in haka ne, sai mu tashi tun yanzu wajen tsarkake fadar nan da addu’a. Ba zan bari a sake shigar da duhu cikin rayuwarsa ba Sultan dole ɗayan biyu zata faru ko dai ka zubar da duk wani abu daya shafi tsafi ka ɗayanta Allah guda ɗayane ka amince shine me nasarar da yake bawa mushrikai nasara suke ganin kamar ƙarfinsu ne ko kuma ka barni Ni da ɗana mu nisanta gareka mu nemi tsarki gurin me tsarkin da yake tsarkake kowa” Kallonta Sultan Rashid yakeyi yana fahimtarta amma kuma zuciyarsa ta cika da rauni ya amince zaiyi komai kuma zai bar komai akan Matarsa da ɗansa har sarauta zai bari matuƙar zai rayu da Samha da ɗansu, a sanyaye yace “Na rantse da Allah ɗaya wanda na amince babu wani iko saman nashi nabar tsafi da duk wani abu daya shafi tsafi zan rayu da ɗayantacciyar taƙawa da imanin Allah shine komai”*************A can cikin zurfin duhu, a wani ɗaki mai kama da ramin wuta, Ameer ya buɗe idonsa.Numfashinsa yana fita da wahala, hannayensa suna ƙonewa da alamun hasken da ya taɓa shi a lokacin haihuwar jaririnne yake ƙonashi.Ya haɗiye jini yana murmushi Na yarda, yaron nan da gaske ne… Amma da na rayu, zan jira sa.”Sai ya janyo zoben da yake a ƙafarsa, ya furta cikin sanyi:“Shekaru bakwai… daga yau, ni Ameer zan dawo. Kuma lokacin da wannan yaron ya fara tafiya, shine lokacin da ni zan fara bin sawunsa sarauta bazata dawwama a sashen Rashid ba dole ta dawo gareni nine jinin duhu kuma dole duhun da aka gadar ya murki Zirkan”Wata iska mai duhu ta shafi fuskar sa, ta ɗauke shi daga gurin, ta bar ƙasan duniya cikin shiru.A fadar Zirkan, Samha ta ɗaga ɗanta zuwa sama tana cewa cikin muryar da ta gauraye da hawaye da murmushi “Za ka rayu da haske, ba da tsafi ba. Kuma kowanne sirri da aka ɓoye, Allah zai tona shi ta hanyar ruhin gaskiya.”Rashid ya durƙusa, ya sanya hannunsa a kan jaririn yace “Wannan haihuwa ce ta ƙaddara. Amma wace ƙaddara ce zata biyo baya?”Granny ta juyo gare su ta ce da muryar da ba ta sake maimaituwa ba,“Tsanani da haske ba sa zama lafiya tare sai dai idan ruhi ya tsarkaka daga zuciya” iska mai sanyi ta busa daga waje, ta kunna fitilun turare, ta bar ɗakin cike da ƙamshi da natsuwa.Jaririn ya lumshe idonsa, kamar yana jin kowace kalma da ake furtawa.Tun bayan haihuwar yaron, dare uku kenan Samha batayi bacci me kyau ba A duk lokacin da ta lumshe ido, tana ganin haske mai kama da rana amma baya da zafi sannan a tsakiyarsa akwai wani yaro sanye da farin kaya yana tsaye yana murmushi.Sai kawai taji muryarsa tana faɗin“Ni ba kamar sauran jarirai ba ne, Ummi Sunana Rayyan, domin na fito daga ruwan da Allah Ya tsarkake kafin a halicci sarauta ki sanar da abiey sunana Rayyan nazo domin na rushe mulkin tsafi na kafa mulkin adalci nazo ne domin na tone ƙaryar da aka binne a cikin gaskiya kuma nazo ne domin cire rai ga duk jikin da ya kasance azzalumi” farkawa tayi cikin zufa Rashid yana gefenta yana kallonta da damuwa yace “Samha, wannan mafarki na yau da kuma jiya fa? Kullum kina farkawa da tsoro.”Ta juyo gare shi, idanuwanta cike da tsoron ruhi tace “Sultan na san sunan ɗanmu yanzu. Rayyan. Kuma na fahimci cewa wannan haihuwa bata zo da sauƙi ba akwai abinda yake neman sake dawowa” Rashid ya dafa kanta yace “Kada ki tsorata Mun riga mun miƙa komai ga Allah Idan wannan jariri an rubuta masa ƙaddara ta haske, to babu duhu da zai iya rufe shi”A waje kuma, Granny ta zauna a ƙarƙashin bishiyar mango tana karatun Suratul Kahf.Tun daga nesa, wani farin tsuntsu ya sauka a gabanta yana haɗa numfashi.Ta ɗaga kai, sai ga Sultan ya iso daga nesa cikin sutura ta masarauta fuska babu walwala “Granny” ya faɗa da sanyi “Na labarin haihuwar tun a baya, Amma akwai wani abu da nake ji a jikina tun ranar Haske da ciwon kai a lokaci guda. Shin kin taɓa jin abu irin haka?” Ta ɗan murmusa cikin hikima“Sultan, haske da ciwo suna zuwa tare idan ruhi na neman gyara. Ka bari zuciyarka ta tsarkaka, kar tsoron ya maye gurbin imani.”“Amma Granny ina mafarki da yaro ɗaya yana gudu a cikin masarauta yana kiran sunana ina ƙoƙarin isa wajensa kafin in iso sai rana ta ɗaukeshi kinsan fassarar mafarki ne hakan yake nufi shin meye zai faru da ɗana Rayyan?” “To kagane daga yaron nan ne hasken zai fito ya nuna wa sarauta gaskiya. Shi zai haɗa halittar mutum da aljanu cikin natsuwa domin a ƙarƙashinsa ne dukkan tsafi zai rushe ya gada daga kakansa Idris El Fahriy wanda ya bawa tsarkakkun Rauhanai ajiyar Sirrin hatimin Saiful Sihr wanda ɗiya mace bata gadon wannan tsarkakken hatimi domin tana haila tana jinin biƙi shi kuma wannan hatimin bai buƙatar yawan kusantar mara tsarki, yanzu hatimin yaƙar Tsafi a koma hannun ɗanku Rayyan shine ya gada daga abinda mahaifiyarsa ta gada daga mahaifinta wanda zai zama makamin rushe Tsafi da ɗayanta Allah a wannan birni na Amzir dama Morocco gabaɗaya”

