Gargadar So Chapter 45 By M Shakur
Ammi na zaune wuraren 11 tana duba wani littafin azkar while Hawwa na bacci sosai mai nauyin gaske taji kamshi ya daki hancinta mai dadi har saida tadago kanta ta kallo kofa Khaleel ta hango jikin kofan dago kan datayi yasa ya matsa da sauri gefe, shiru Ammi tayi saikuma ta kalli Hawwa dake bacci mai nauyi massage din yamata dadi ga drip ana samata ta lullube mata tundaga ciki har kafafu da bargo daga cikinta zuwa kai abude kanta babu dankwali tayi kyau sosai, she’s sure shine yaron jiya shine mijin Hawwa kunya yakeji ne kome? Lallai yaron kam akwai kunya yana abu saikace barawo, Ammi tayi murmushi tana tashi ta taho wajen kofan tabude tafito, Khaleel na tsaye jikin kofan yana sanye da riga da wando masu kyau milk adan hankali yace “good good morning Mom” saikuma yajuya zai tafi dasauri batare daya jira amsan Ammi ba, ahankali Ammi tace “Ibrahim” chak ya tsaya yadan juyo kanshi akasa, dan murmushi kadan tayi tace “bazaka duba matar taka ba? Dan zauna da ita nima kafafuna sunyi tsami bari nadanyi tafiya cikin asibitin kadan” kafin yayi magana ta wuce yabi Ammi da kallo saida yaga tafice sannan yajuyo ya kalli dakin kafin ahankali yabude kofan ya shiga maida kofan yayi yarufe ya tsaya jikin kofan yana kallon Hawwa dake bacci mai nauyi hakanan kawai yaji kirjinshi na bugawa sosai dum dum dum! Gently yadaga kafanshi yataka zuwa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannu a kirji yana kallonta, she looks very sick and beautiful a hospital gown din, har lokacin akwai bandage a goshinta but an cire na hannuwanta ga ciwuka a hannu, ahankali yadaga hannunshi yakai gently yadaura kan left hand dinta wani kalan shock yaji baisan sanda yarike hannun gam ba tareda sauke ijiyan zuciya sannan ahankali yakai yatsanshi yana shafa ciwon hannun wanda yasan Ni’ima ne tamata cus yana mota data tattake mata hannu haka murya chan kasa yace “why will you love a girl this much?” Yabi hannun da kallo that felts super soft kaman hannun little Noor ga nails nata so long and white and clean looks so sexy, mirginowa Hawwa tayi kanta zai fadi daga filo dasauri yakai hannunshi yatare fuskanta yafado cikin palm dinshi tana sauke ijiyan zuciya daya huro a hand nashi cikin muryan bacci tace “Ammiiii” wani irin lankwasa kai Khaleel yayi yana kallon fuskanta dake cikin hannunshiHer face is so damn soft, baitabajin wani excitement dan mace ta shiga jikinshi ba but right now he’s feeling so good, tsareta da idanu yayi yana kallonta ya duko a tsaye fuskanta na cikin hannunshi, kaman mai whispering yace “Hawwah!” Kar Hawwa tabude idanunta saida gabanshi yayi wani mummunan faduwa yanda take kallonshi da very very bright eyes saikuma tamaida idanun tashiga kullewa suna juyawa, muryan Baba yaji awaje dawani kalan sauri yazare hannunshi fuskan Hawwa ya kife anan kasan filo daidai Baba na bugo sallama yana shigowa tareda Ammi da Ramla dakuma wasu mata guda uku, biyu daga cikinsu goye da yara abaya daya babu yaro abayanta somehow somehow they look like Baba, Ammi ta wuce tana gyara fuskanta, Baba yace “Ibrahima kana nan? Ka kannin matarka Hawwa ku gaisa Khadija” Babban wacce ita kebin Aminu Khadija tace “ina yini Yaya Ibrahim” akunyace Khaleel ya gyadamata kai, Hafsa tace “ina yini Ya Ibrahim yamai jiki” Maryam tace “ina yini ya Ibrahim” Ramla itama tace “Ya Ibrahim ya jikin Ya Hawwa” kaman bai iya magana baisaba da mutane haka ba ana kiranshi Yaya Yaya yace “da…da sauki” yakalli Baba akunyace yace “Baba zan tafi zan dawo anjima” Baba yace “muje na takamaka” shida Baba suka wuce suka fita suna fita Khadija da Hafsat da Maryam da Ramla suka shiga tafi saikuma sukahau rawa, Hafsa tace “wlh mijin Ya Hawwa yahadu Wayyoo Allah na I’m so happy for Yaya Hawwa” Ammi tace “kunga karku tadamin yarinya da surutu” duk dariya sukayi sukahau hira.Around 4 DIG yazo hospital din tareda Abraham da Hayatu Baba yamusu iso suka gaisa sosai, suka ijiye kudi da basket na so many goodies sannan sukama Baba sallama suka tafi.Shima Aminu around 4 yashigo asibitin Baba yadingamai fada akanme zaibar school yazo….Wuraren 7 Khaleel yashigo asibitin Salman na binshi da shopping na kayan kwadayi daban daban yarike hannun Noor data isheshi da maganan Hawwa ga teddy a hannunta looking so pretty sukai ciki, tundaga glass na kofan ya hango Hawwa zaune kan gado an ijiyemata table da abinci daban daban kekai Ammi na kaimata abinci abaki tana kaudakai tana yatsine fuska idanunta sun kumbura na kuka da bacci, ga Baba shima tsaye kansu suna fama dataci abinci murya chan kasa Khaleel yace “she’s such a child” dasauri Noor tace “Daddy mekace?” Kallon Noor yayi baiyi magana ba tace “Daddy let’s go inside I want to see FAA” dan ijiyan zuciya ya sauke yasa hannu yayi knocking tareda bude kofan Noor tasaki hannunshi tai ciki da gudu tace “My Fairy Angel Anty” Hawwa tadan bude idanu tana kallonta kawai Noor tahau gadon ta gefen Ammi ta tattaka tafada jikin Hawwa ta rungumeta tsamtsam da karfi Hawwa itama ta rungumeta yarinyar is freaking cute and adorable.Baba yace “Ibrahima shigo ga wuri” yabashi plastic chair shi Baba yakoma kan dogon kujera ya sauna su Salman suna shigo suna ijiye jakunkuna suka fice ahankali Khaleel yace “ina yini Mom” murmushi Ammi tamai tace lafiya lau Ibrahim, aran Hawwa tace “Ammi na ne Mom” da sick eyes tadan kalleshi tana rungume da Noor tana mamakin meya kawo dan iskan yaron nan asibitin nan taki gaidashi, tasowa daga jikinta Noor tayi tace “FAA ya jiki? That day of accident my Dady was taking me to school I saw wat you were doing” Noor tashiga gwadama Hawwa, tace “I told my Dady, Dady yafita yadinga bin car naki da gudu he removed you from the car you were biting my Dady hand” tanuna hannun Khaleel dake zaune da sauri yajuyar da hannunshi Baba yace “aiko naga ciwon dama Hawwa ce ta jimaka?” Kin magana Khaleel yayi, Noor tace “we brought you here FAA are you fine now? U will not fall sick again ko?” Gyadamata kai Hawwa tayi ahankali tace “yes” dasauri Noor ta rungumeta tace “I love you FAA” tashi Baba yayi cikeda hikima yace “bari na karbi sako wajen mai keke” Dasauri Ammi ta tashi tace “muje na bika nafadamai abinda zai fadama Ramla” kawai suka fice.Itama Noor dasauri tasaki Hawwa ta sauko daga gadon tai wajen Khaleel dake kallonta tace “Dady I forgot my second teddy in car I brought it for FAA” ahankali yace “meet Salman to take you” dasauri tai wajen kofa tajuyo takalli Hawwa dake binta da kallo tace “FAA I’m coming” Gyadamata kai Hawwa tayi tawuce tafita dakin yarage daga Hawwa sai shi, kafa daya yadaga yadaura kan daya yayi shiru yana kallonta, yanda Hawwa taji ajikinta ana kallonta yasa tadan juyo ta kalleshi hada ido sukayi zata ballamai harara komi daya mata nadawo mata arai, da yanda yayi attempting tabata but yanda taji shiya ceceta, plus dazu Baba nata cewa Ibrahima yakawota asibiti yabiya kudin komi da motocin data bata yasa softly da dan kyar tace “thanks” tadanyi shiru ta dai daure tasaki muryanta tace “thank you for saving my life” tasakeyin shiru ahankali tace “once nakoma aiki i will find a way to pay you back every penny daka kashe” tasakeyin shiru chan tace “all this daka kawo kasa atafi dasu banso, i hate favors barinma na mutane like you! So I will pay back everything” Murmushi kadan yayi batare dayayi magana ba wato tana sick bed still masifa take, Noor tadawo dakin ta tafi wajenta da sauri tabata teddy tace “FAA take, Dady said you will soon move to our house kikazo i will give you more and more teddy kinji” dan murmushi kadan Hawwa tamata tace “thank you beautiful Noor” tana mamaki uban me zai sake kaita gidansu dayake gayama yarsa zata” kusan 10mins yayi sannan yakalli Noor daketa zuba yace “let’s go” kiss ta manna ma Hawea tace “bye FAA” murmushi sosai Hawwa tayi tace “bye Noori” wucewa tayi wajen Khaleel yarike mata hannu sukai wajen kofa hakanan Hawwa samin kanta da kallonshi tayi, the way he walks, he way he held Noor’s hand, everything looks soo….ta tsaida tunanin, saida yakai daidai kofa ya tsaya Noor ta fita dan juyo da kanshi yayi karaf suka hada ido dasauri Hawwa ta dauke kanta, cikin dan iskan murya Khaleel yace “see you soon cry cry Kulu” dawani irin sauri Hawwa tajuyo ta kalleshi kaman zakanya, gira daya yadaga mata yace “see you very very soon Kululu” kawai yasa kai yafice daga dakin Hawwa tawani yunkuro tace “sunana Hawwa not Kulu or kulul whatever” Khaleel na jinta yayi murmushi yawuce abinsa.


