Zakuna Biyar Page 10 By Princess Teema
Bamar zata yi kuka ta amsa da. “To ai ni na sanka in kai baka sanni ba, kuma dama kai na zo gani”……. Ɗan waro eyes ɗinsa kaɗan ya yi, sai kuma ya yi saurin ɗauke kallonsa daga kanta. Ita kuma kara ja da baya ta yi tana turo baki…………. “Your lion voice is so sweet that touch and melting my heart!”. Ta faɗa cikin sigar tsantsar so! Tana magana kuma tana kara ja da baya wai dan ma kada ta ɓata mashi rai ya damketa.Shiru bai yi magana ba, yana dai satar kallonta ta ƙasan ido…….. “Baka son ka yi magana dani ne? Aunty ta ce in kula da kai fa”……. Still dai bai yi magana ba kuma bai ɗago ya sake kallonta ba. A daidai lokacin Angelina ta iso wajen tana faɗin. “V ki yi sauri, daddy yana jiranmu a motar zai mayar damu gida”. A ruɗe take maganar, dan idan GAT ya gane V bata wajen sun shiga uku, kun san kuma doka ce ya kafa masu cewa babu ruwansu da sojojin barrack ɗinnan, and bugu da kari manyan sojoji basa aurar da ƴaƴansu ga sojiji ƴan uwansu sai in ALLAH ya tsaga da rabo, amma basa taɓa yarda, shiyasa zakuga ga mata kyawawa a cikin barrack amma sojiji zasu fita waje neman aure, kowa baya son ƴarsa ta yi takaba, sojoji a kowani lokaci suna iya rasa ransu ko da sabbin aure ne! Angelina na zuwa ta ja hannunta, da sauri suka wuce tana waigosa hankalinsu a tashe. Da sauri Noor ya ɗago yana kallonsu, ya yi mamakin ganin tsananin kamannin dake tsakanin yaran, zuba masu idanu ya yi har suka kurewa ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai bar wajen, a nan ya lura da wayarta dake hannunsa. Da sauri ya bi bayansu, sai dai ko da ya je bai gansu ba, daddynsu ya ɗaukesu. Zubawa wayar ido na ɗan lokaci ya yi kafin ya kunna light ɗin screen, hotonta ne a gaban screen ɗin, ga wayar babu password, dan haka sai ya ɗan shiga cikinta. Videos na soyayya kawai ya fara cin karo da shi, fita ya yi ya kashe wutar screen ɗin, cike da tinanin ina zai sake ganinta ya bata wayarta ya nufi wajensu Leo. A ɗayan side na hall ɗin ya isko Leo tsaye da Big Bro ɗinsa suna magana, Leo ya ce yayan nasa ya bari sai gobe su wuce Us, shi kuma yayan nasa ya so su wuce yau ne, amma Leo yaki fir, wai akwai aikin da bai kammala ba, akwai sauran shirye-shirye da yake yi.Baki a ɗauke da excuse Noor ya iso wajen. Zayra’an yana tsaye tsayuwar jarumai Noor ya ɗaga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Shiru tamkar ba zai amsa ba, sai kuma can har sun fidda rana zai yi magana ya amsa a kalma ɗaya watau lafiya. Daga haka ya wuce ya nufi gidan da ya kasance yanzu mallakin su Leo. Bayan passing out ɗinsu sun baro yankin barrack kai tsaye, an basu gida cikin layin gidajen senior staff, gida mai shegen kyau, bene ne, mai ɗauke da ɗakuna 6, uku a ƙasa da parlo sai uku a sama shi ma da parlo, kitchen ɗaya da harabar gida, toilet a kowani room, tsarin ginin ya yi kyau matuƙa, dikka jami’ai 12 da zasu tafi mission ɗin nan a wannan gida zasu zauna kafin tafiyar tasu! Su 12 ɗakuna 6, kowani ɗaki mutane biyu kenan, saɓanin mutane 4 a lokacin da suke horo bar one!. Kallon tsab Leo ya yi wa Noor kafin in a cool way ya ce. “Wannan wayar fa?”. Kallon wayar Noor ya yi kan ya amsa da. “Na wata ce da ban santa ba, yanzu ma nemanta nike yi in bata”…….. Wani irin kallon tuhuma Leo ya jefa mashi wanda bai san lokacin da ya ce. “Bro da gaske ban santa ba, kawai ina tsaye ta zo ta sameni, ka yarda dani”.Zura hannayensa a cikin aljuhu Leo ya yi, ya ɗan taka baya step biyu gaba kafin ya ce. “Ya da saurin tsarguwa boy? Ko ka ji na ce wani abin ne?”……. “Naga kana bina da kallon tuhuma ne”. Ya faɗa yana tura wayar a aljihunsa!. “Uhm”. Leo ya faɗa tare da juyawa zai bar wajen.Da sauri Noor ya bisa yana faɗin. “Bro, believe me, I don’t know this girl shaaa”. Cigaba da tafiya Leo ya yi, har suka kusa shiga cikin gidan nasu kafin can ƙasa a natse ya ce. “Ita ce ta mafarkin da aka damemu da yinsa tsawon shekaru biyu kenan ko?”…….. Da sauri ya girgiza kai tare da tare gaban Leo, yana ɗan shagwaɓe fuska ya amsa da. “Bro, ka bari mana, ni fa na faɗa maka wacce nake mafarki ban taɓa ganin face ɗinta ba, sai dai kyakkyawan surar jikinta”.”Uhm”. Leo ya sake faɗa tare da sa kai zai raɓa gefensa. Sake tare gabansa Noor ya yi. “Baka yarda dani bane bro?”…… Tsayawa ya yi, suka kalli juna ido cikin ido kafin ya amsa da. “Asalin yarda kuwa, sai dai ina mamaki ne, anyway ka dai mai hankalinka a kan aiki, idan ka ce zaka biyewa mace zata shashantar da kai ne, ba zaka cinwa abin da kake so ba!”. A dake da iya gaskiyansa ya faɗa, dan shi yana ganin in dai ka haɗa hanya da mace to zaka zama ragon namiji ne, wai ba zata barka ka yi abin da yakamata ba, sai ta sa ka zama mai rauni. “For sure bro, zan yi ƙoƙarin ganin ban kauce hanya ba, kuma zan yi ƙoƙarin ganin na jajirce. But bro she’s so cutie, pretty and…….”. Sai kuma ya yi shiru………. “Ta mafarkin ko ta zahirin?”. Leo ya faɗa a taƙaice. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. “Both, amma ta zahirin karshe ce”……… “Uhm”. Leo ya sake faɗe tare da sa kai ya wuce, ya shige cikin gida, da sauri Noor ya bi bayansa, sun zo daidai tsakiyar gidan Leo ya ce. “Ba zan hanaka kula mata ba, saboda ni da kai akwai banbanci, but in ka bari ta fara ɗauke maka hankali fiye da tinani zan katse dik wata alaƙar ne”. A ɗan shagwaɓe ya ce. “Ba za ayi haka bama, aiki shi ne gaba da komai, ba zan bari ta shafi aikina ba”…… Jinjina kai Leo ya yi, a daidai lokacin suka fara tattaka staircase zasu haura sama izuwa room ɗinsu…….. “Wacece ita kuma ƴar waye?”. Leo ya faɗa can ƙasa, tamkar mai raɗa dan yana gudun yayansa ya ji suna maganar mata ya ce dama ba aiki ne a gabansu ba, yasan yayan nasa na gidan tin da ya ce bari ya zo nan ya ɗauki wayansa da agogonsa ya koma hotel da ya dauƙa.”Dik ban san waɗan nan amsoshi ba, yau na fara ganinta, amma ka bani two days zan samo maka dikkan amshoshin da kake son ji”. Cikin ɗan shagwaɓa ya faɗa………. “Hallau dai shagwaɓar”. Leo ya faɗa a lokacin da yake tura door na room ɗinsu. “Naka ne kai kaɗai ai, wa kai kawai nike yi wa, ko daddy banai wa shagwaɓa yanzu”. Ya faɗa yana nufar wajen bed. Leo kuma juyawa ya yi ya fita ganin yayansa baya ɗakin, kenan sun barosa a waje, yana son su yi sallama kafin ya tafi hotel da ya sauƙa. Shi kuwa Noor kwanciya a saman bed ya yi tare da ciro wayar V ya ajiye a gefe, sannan ya ciro tasa wayar. Lokaci guda tinaninta ya faɗo mashi a rai, yadda ta ce. “Your Lion voice is so sweet that touch and melting my heart”. Yadda ta yi maganar a shagwaɓe hakika ta taɓa zuciyansa, sai ya ji tamkar ta cigaba da yi kada ta dakata.Kawar da tinanin ya yi tare da jawo wayarta dan ya ga ko akwai wata hanya da zai bi wajen samun damar mayar mata da wayar. (Anya Noor ba neman damar sake ganinta kake yi ba kuwa? In ba haka ba me na wani damuwa da son a mayar da wayar? Naga ai zata fika buƙata, sai ta nemo kayanta!.)Yana kunna light na screen ɗinta sai ga kira ya shigo. “My life partner”. Shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin nata. Wani irin amsawa ya ji kirjinsa ta yi, sai ya fara tinanin kamar ya ɗauka kamar kuma ya bari. Can kuma ya tina ai gara ya ɗauka ya sanar masu ta bar wayar a wajensa su zo su karɓa mata. Da wannan tinani yasa wayar na gab da katsewa ya ɗaga tare da sanyata a H-free. Daga ɗayar ɓangaren aka ce. “Hello”. Ko ba’a faɗa mashi ba yasan ita ce, saboda kwarewarsu a aiki sau ɗaya suke jin sautin abu su haddace, tabbas wannan muryanta ne, kuma hakance, ita ce ta kira number tata da wayar Angelina. Dama da gangan ta bar wayar a hannunsa, dik tarko ta ɗana mashi na yadda zata samu damar yin magana da shi kenan, kunga idan wayanta na hannunsa zasu sake haɗuwa, kuma zata samu damar sake yin magana da shi, har da cewa sai bayan sati zata yarda ta karɓi wayan, wai kullum zata dinga kiran number da layin Angelina tana gaisawa da shi, sai ta ce mashi bata gari, sai sun saba ta waya sannan ta karɓo wayar, a cewarta in suka saba da kansa zai ɗauki numberta. Kai kun ji yarinya mai wayau ta kafawa Noor ɗinmu tarko! Kai yaran GAT they’re very Smart wlh.”Good evening sir”. Cikin shagwaɓa mai narka zuciya ta faɗa. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. “Evening how’s your day?”………. “Cool”. Ta amsa kafin ta sake cewa. “Na manta wayata a hannunka”. …… Jinjina kai ya yi tamkar yana a gabanta, amma bai yi magana ba. “Zaka kawo mun wayar gobe please? Ko in zo in karɓa?”…….. Shiru ya ɗan yi, can kuma ya ce. “Gobe zan bar barrack ɗin nan saboda hutunmu, faɗa mun in da kike yanzu in kawo maki”. Shiru ta ɗan yi, bata son yasan ita ƴar GAT ne, dan in ya sani ba zai sake kulata ba, ɗan damar da ta samu na magana da shi zai gudu, ga shi tana son ganinsa yanzu, so take ta shirya mashi wata dabara, in kuwa haka ne yazama dole ta fito su haɗe a waje ba a gida ba, to ya zata yi da sojojin dake gidansu har ta samu hanyar fita? Ta tambayi kanta a lokacin da yake katse mata tinani da cewa. “Baki tare dani ne?”. Da sauri ta amsa da. “Ina jinka, nima gobe zan bar barrack ɗin nan, dan haka mu haɗu a wajen itatuwan zone one in karɓi wayar”. Ta faɗa kirjinta na dukan uku-uku. Shi kuma bai kawo komai a ransa ba, sai ya ɗauka kenan ita da iyayenta suka zo wannan bikin passing out ɗin, gobe za su koma kenan, like wow, ya faɗa a ransa, bai san wannan kam uhm na dai yi shiru, amma akwai case a wannan alaƙa tasu, shin GAT zai yarda? Ita da take shalelensa ƴar autarsa ma kuna ji tsoron ya sani take yi, tana ma tsoron a san ita ƴar GAT ne kada alaƙar ta ruguje, kun kuwa san da matsala sosai.”Give me 30 mins zan zo wajen”. Ya faɗa a sanyaye yana miƙewa tsaye. Da okey ta amsa tare da miƙewa ita ma, ta sauƙo ƙasan bed ɗin, da gudu ta faɗa toilet dan yin wanka, su Arya suna can ƙasa suna faman zazzagawa masu aiki faɗa wai dan meyasa zasu yi girki dayawa a gidan, basu san cewa baki zasu yi ba, daddynsu ya ce ayi girki dayawa dan yaki yarda daddy Noor ya sauƙa a hotel, ya ce lallai ya sauƙa a gidansa, ya hakikance………. Ni kam na ce ko dan Aunty Lisa da ka sakawa ido ma ai dole ka hakikance su zo gidanka ɗan……. Bari dai na yi shiru tin da daddynmu ne, kun san ni ina bayan Arya!. A gurguje ta yi wanka, za’a haɗu da masoyi, haɗaɗun wani European wears ta sanya, wandon jeans crazy, sai kuma top mai kauri, wankan milk and maroon ta yi, ta kuwa yi kyau matuƙa, ta sanya flat shoe saboda ta ji daɗin satar hanya, ta feshe jikinta da daɗaɗan perfume na kamfanin su Noor kafin ta gyara gashin kanta, sai faman kyalli yake yi. Ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta kenan ta ji wayar Angelina na ƙara alamar shigowar kira. Da sauri ta nufi wajen bed ɗinta. New number ta gani, kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.Sanyayyan voice ɗinsa ne ya karaɗe dodan kunnenta wajen cewa. “Hello”. Wani irin daɗi ta ji na ya kirata da numbersa, ko ba komai yanzu ta samu numbersa, yana son faɗa mata yana wajen yana jiranta ta zo ta karɓi wayar, amma baya son kira da wayarta dan bashi da tabbacin tana da kati ne ko akasin haka, shi ne ya ɗauki number Angelina ɗin ya sanya a wayansa ya kira.”Sorry I’m coming now”. Ta faɗa a ɗan shagwaɓe. Kai kawai ya jinjina tare da katse kiran, yana tsaye karkashin wata bishiyar mangoro mai girma, ya yi wanka ya cire kakin dake jikinsa, yana sanye da sleeping silky pjs, dan a cewarsa yana miƙa mata wayar barci zai zo ya yi, shiyasa yai shirin kwanciya!..Fitowa ta yi daga room ɗinsu da gudu, a parlo ta haɗu da su Arya, kallon tsab suka fara yi mata kafin Arya ta ce. “Are you okey? Wannan kwalliyar fa?”…… Tsakaninsu akwai tsananin kaunar da amana sai ta faɗa masu komai dake wakana, bata ɓoye ba dan basu ɓoyewa juna komai.Siririn tsaki Arya ta ja kafin ta ce. “Soyayya yana neman sanyawa ki manta ke ƴar wacece ko? Da kika ce ya jiraki faɗa mun ta hanyar da zaki bi ki fita gidan nan?”…….. Manassa ta amsa da. “Bloody, wai meyasa kike haka ne? Ba ta ji tana son shi ba? Ku kyaleta mana, in ta ga hanyar fita to ta je, mu kuma zamu rufa mata asiri”. Angelina ta karɓe zancen da cewa. “Ban ga abin hanata yin soyayya ba, ta je mana, baby ki dawo da wuri idan kin samu hanyar fita, kuma ki tabbatar kin sace zuciyansa, ki yi mashi abin da zai kwana mafarkinki, kada ki kyale zuciyansa ya huta daga tinaninki kin ji?”. Cike da kwarara mata gwiwa ta yi maganar. Arya dai bata sake ce masu ko kala ba, dan ta lura dik suna supporting V. Da sauri V ta matso ta rungumesu kafin ta ce. “I really love you my blood”….. “Love you too baby”. Har suna haɗe baki wajen faɗa. Sakesu ta yi tare da juyawa da sauri ta nufi kofar fita cike da confidence ɗin zata iya da jami’an dake gate, tana jin zata iya raina masu hankali. Har zata fita waje muryan Angelina ya katseta da cewa. “Baby, make sure kin sace zuciyansa, kada ki bari ya tafi bai maki kallon da zai tabbatar maki da kin shiga ransa ba, ki rike mashi wuta da shagwaɓa da kalamai”……. Da okey V ta amsa kafin ta yi masu godiya, suna faɗin I love you ita tana basu amsa har ta fice.A harabar gidan ta tsaya tana kallon waɗan nan jiga-jigan sojojin dake kai komo, suna wani muzurai, to ita yanzu idan suka tambayi ina zata je ina zata ce masu? Can kuma ta tina ai ta taɓa shiga gidan MG watau Major General, ta taɓa shiga a time da matarsa ta haihu, dan haka bari ta ce masu can zata je. Nufar gate ta yi ba tare da tsoronsu ko kaɗan ba, to sun saba da su, dik muzurai da jajayen idanunsun nan su V basa tsoronsu. Tin bata iso wajen ba wasu jiga-jigan sojoji su huɗu suka miƙe tsaye suna jiran ta iso su ji dame take tafe. A daidai lokacin ana danna horn a bakin gate ta waje wanda ya ɗauke hankalin dikkan jami’an dan already an basu masaniyar zuwan baki. Da sauri suka wangale gate ɗin. Take jerin gwanon motocin daddyn Noor suka danno cikin gidan, da alama ya yarda da tayin GAT na ya zo gidansa ya kwana kenan. Lallaɓawa ta yi, ta faki idanun jami’an ta sulale ta cikin jerin gwanon motocin nan ta nufi waje. Babu wanda ya ankara da ita, da gudu ta bar arear gidan nasu. A main gate ɗinsu da ta zo fita dakewa ta yi, sojoji shidda ne ke gadin main gate na shiga Senior staff side, sai dai yanzu ɗaya ne a wajen, saura biyar dik sun tafi masallacin sallar ishai. Dan haka with her full confidence ta nufi gate ɗin, yana ganinta ya miƙe tsaye, tana karisowa fuskansa babu alamar wasa ya ce. “Where are you going by this time?”. Ya faɗa yana kallon army watch dake ɗaure a hannunsa, wajen babu haske sosai sai hasken streetlight…………. Ɗaure fuska sosai ta yi, babu alamar wasa a tattare da ita, ID card ɗinta ta ciro daga aljihun wandon jikinta, ta kunna light na wayar Angelina, ta haska mashi ID card ɗin da kyau kafin ta haska mashi fuskanta da kyau ya gani. A dake ta ce. “Wajen daddy na zan je”. Ɗan kamewa ya yi tare da shiga taitayinsa, dan matsayin biyu ta taka yanzu a gabansa, matsayin ƴa ga GAT, da kuma matsayinta a fagen aiki, ID card na aikinta ta nuna mashi, watau idan suna taƙama su jami’ai ne ita ma jami’a ce, idan suna takama da karfin dantse ita kuma jami’a ce dake taƙama da kaifin ƙwaƙwalwa, ba’a aiki sai da jami’ai irinta!…….. Da kyau, abin ya bada citta.Bata jira amsarsa ba ta nufi waje abinta, dama jami’an gate na gidansu ne take shakka, dan su ne daddynta ya baiwa cikakkiyar damar hanasu fita ba tare da babban dalili ko izininsa ba, amma jami’an dake main gate ai su dikka Senior staff side suke gadi, yaushe suke da ƴancin hana mutum fita? Su aikinsu su tsare masu shigowa su cajesu kada wata barazana ta gifta side ɗin!.Sauri sosai ta dinga yi tana addu’ar kada su haɗe da daddynta a hanya komai ya lalace. ALLAH ya taimaka har ta isa basu haɗe da shi ba. Tin daga nesa ta hango jarumin nata tsaye a ƙasan bishiya, ya juyawa hanyar da take zuwa baya, yana rungume da hannayensa a massive chest ɗinsa. Wani musulmin ajiyar zuciya ta sauke tare da yin gaggawar karisawa wajen. Excuse ta yi mashi kafin ta zago ta gabansa. Slowly ya ɗan ɗago da kallonsa a kanta, bai san time da ya waro eyes ɗinsa sosai a kanta ba! Ta yi kyau matuƙa, ga hasken streetlight dake gefe-gefensu na haskata da kyau!. Ita ma ɗan ɗauke wuta ta yi a kallonsa cikin kayan barcin, sai take jin tamkar ta rungumesa saboda haɗuwansa, amma ta daure da cewa. “Sorry sir, na barka kana ta jirana ko?”.Kai ya ɗan girgiza kafin ya amsa da. “Nevermind, this is your phone”. Ya faɗa yana miƙo mata wayan. A maimakon ta karɓa sai ta ce mashi. “Tin bamu gaisa ba zaka bani wayar? Ko baka son yin hira da ni ne?”…….. Sauke eyes ɗinsa a kanta da kyau ya yi, sai da ya ji faɗuwar gaba, amma ya basar da cewa. “I’m feeling sleeping”……… Ta gamsu da hakan dan ga idanunsa nan dik sun juye, a shagwaɓe ta ce. “In zo in tayaka kwanciya ne?”…….. Lokaci guda ya ɗan saki one side smelling da bai san ya yi ba, wacce kuma ta ƙara fito da tsantsar kyansa, wai ta zo ta taya shi kwanciya, a ransa ya ce ƴar karama da ita sai iya magana da shegen shiga rai.Ganin ya ɗan yi one side smelling ne yasa ta ji wani irin Musulmin daɗi, da alama kalamanta suna huda zuciyansa, yarinyar ta iya soyayya sosai. “Baka ce komai ba! Ina auntys ɗina? Ka kira mun su mu gaisa zan faɗa masu kaki bani damar in kula da kai kamar yadda suka ce in yi”. Kafeta da ido ya yi, yana ta faman kallon ɗan bakinta, a ransa ya ce ba zaka ga baki ba sai iya magana, a fili kuma ya gagara cewa komai. Ganin yadda yake kallon ɗan bakinta ne yasa ta turo shi gaba kaɗan kafin ta ce. “Ba zaka yi magana dani bane?”……. Still dai bai motsa ba, babu ma alamar zai yi magana. Juyawa ta yi tare da taka step biyu tana faɗin. “Shikenan tin da baka son yin magana dani, bari in tafi kawai”.Sai a lokacin ya ɗan yi gyaran murya tare da ɗauke kallonsa daga kanta, ya zura hannayensa cikin aljihu, da wayar tata gabaɗaya tare da taka step uku ya dawo ta gabanta, ya zamana suna fuskantar juna. Muryansa can ƙasa ya ce. “A ina kika sanni? Wacece ke? Meyasa kike ƙoƙarin shiga rayuwata?”. Wani irin faɗuwar gaba ta ji na ganinsa a kurkusa da ita haka, da kyar ta haɗiyi yawu gwad. Muryarta ne ya fara rawa wajen cewa. “Am……. In…. Nima….. A mafarkina na sanka……”. Gagara cigaba da magana ta yi. Ganin haka yasa ya ɗan yi step ɗaya baya, dan ya lura ta tsorata da ganinsa a kusa da ita haka ne. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke ganin ya ja baya, har da ɗan dafe kirji. Intently ya ɗago da kallonsa sosai a kanta, sai haki take yi tamkar wacce ta ci gudu ya ƙoshi. Ita ma ɗago ido ta yi suka kalli juna ido cikin ido, at the same time suka ji wani irin yanayi ya ziyarci zuƙatansu. A daidai lokacin jerin gwanon motocin BGA suka danno kai kan titin zasu wuce gida. Da sauri ta mannu da jikin bishiyar. Takawa ya yi step biyu ya tsaya dab da ita dan ya kare mata motocin kada su haska su ganta a wajen, dan in suka ganta ita za’afi hukuntawa, dik da bai san wacece ita ba, amma yasan dokar AZURE, koda bakuwa ce a nan sai an ji dalilinta na biyo wani jami’i, sai an hukuntata. Shiyasa ya tare mata. Slowly ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta, while ita ma shi take kallo, kurawa juna idanu sosai suka yi, gagara rike kanta ta yi har sai da ta kwantar da kanta a saman massive chest ɗinsa, ya matsa kusa da ita ne sosai, ga kamshinsa dake ratsa hancinta, ga shi kuma abin da zuciya ta jima take begen gani ne……… Ɗan motsa eyes ɗinsa ya yi ya bi gashin kanta da kallo, wani irin yanayi ya ji na jinta a jikinsa, sai ya ji kamar komai ya tsaya mashi cak. Ita kuma wani irin daɗin da ta ji har bata san time da ta sanya hannunta dikka biyu ta rikosa ta baya ba!. A daidai lokacin motocin suka gama wucewa, ɗan ja da baya ya yi kamar yana tsoronta haka. Da sauri ta ɗago kai suka haɗa ido, sai ta tsinci kanta da jin kunyansa, hakan yasa ta juya da gudu ta bar wajen. Bayanta ya bi da kallo yadda yake gudu har ta kurewa ganinsa, tana sane sarai da bata karɓi wayarta ba, dan dama na ce maku tarko ta ɗana mashi da wayar, ta yi alƙawarin sai sun yi ta haɗuwa da sunan karɓar wayar nan, in sun zo rabuwa ta tafi ta bar mashi wayar, a haka har ya fara sonta. Da yake ya zura wayar a aljihu ɗazun ne sai ya mance da ita, dan haka yana gani har ta gudu bai tina ya bata ba. Juyawa ya yi ya koma side ɗinsu. Sai da ya koma room ɗinsa, zai hau bed kenan ya ji wayar a aljihunsa, da sauri ya cirota, mamaki ne yakama shi na yadda aka yi ya shagala ya mance bai bata wayarta ba, to me ya shagalantar da shi? Ya tambayi kansa……Ni kam na amsa mashi da kyan V da iya maganarta, ga daɗin murya da shagwaɓa, shi ya mantar da kai me ka je yi wajenta!. Kurawa wayar idanu ya yi yana ta mamaki, a daidai lokacin Leo ya shigo room ɗin bakinsa a ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa. Ajiye wayar a gefen bed ya yi tare da kwanciya yana yi wa Leo barka da dawowa! Toilet Leo ya wuce ba tare da ya amsa shi ba!. Ita kuwa kai tsaye gate na gidansu ta nufa. Tana zuwa ta hau knocking ba wani tsoro, dan dama fitar ce mai wahala, shiga kam tasan maganin jami’an, ita ma ai jami’a ce, dik wata makirci ta iya. Ɗaya daga cikin sojojin wajen ne ya buɗe mata gate ɗin. Mamakin ganinta ne ya kamasu. Ɗaure fuska ta yi tare da sanya kai zata wuce ciki, da sauri sojan da ya buɗe mata ya bata hanya ta shigo. Ɗaya daga cikin sojojin ne ya ce. “From where at this time? Kuma a yaushe kika fita gidan nan?”. Harara ta dallah mashi kafin ta ce. “Kana da business dani ne? Dik wanda ya sake mun magana a cikinku ya yi wa kansa, dan zama zan yi a nan har daddy ya dawo yasan na fita! Kun san sauran kuma idan yasan na fita, dan baku iya aikinku ba tin da zaku bari in fita ba tare da izininsa ba, ku rai nawa ne a wajen nan da har ni zan fita baku sani ba?”. A dake ta faɗa.Shiru suka yi, dan kuwa ta ɗauresu da magana, sun kuwa san idan GAT yasan ta fita sun shiga uku, ace sojoji sama da goma ke gadin gidan har V ta fita babu wanda ya sani? Ai suka yi sake GAT ya ji wannan magana sun shiga tara ne ma, dan haka suna ji suna gani ta wuce cikin gida tana hararansu, babu wanda ya sake ce mata ko ƙala. Tana shiga parlo ta daka tsalle tana faɗin. “Smart girl, wai ni ko yaushe na koyi waɗan nan wayo ne ma?”. Tana cikin surutan nata ne ta ɗago kai sai a kan su Aunty Lisa dake zaune a dining room suna dinner, da yake glass wall ne wajen dining room ɗin sai suna iya ganinta. Da gudu Angelina ta taso ta nufota, muryarta har yana rawa wajen tambayarta ya aka yi? Ta samu ganin Noor?. Bata fuskanci wata matsala ba ko?.Zazzare idanunta a kan su Aunty Lisa ta yi, cike da mamaki ta ce. “Aunty”. Suma sai kallonta suke yi, sai a yanzu suka gane gaskiya Angelina take faɗa masu na cewa ba ita ce suka haɗu da ita ɗazun ba. Kun san me yafaru ne? A lokacin da suka shigo gidan Angelina kawai suka samu a parlo, su Arya sun yi sama. Nan fa suka fara rungumar Angelie suna tambayarta dama nan ne gidansu? Ita kuma bata ganesu ba sai ta fara tambayar su waye su, nan suka zayyane mata komai, ta ce ba ita bace sai dai ko in sister ɗinta V, kuma bata nan sai ta dawo, suka kafe lallai ita ce, Aunty Lisa har da cewa ga ash hair ɗin nan nata, komai sak na wacce suka haɗu, su basu yarda ba, lallai ita ce. Ita kuwa ta kafe ba ita bace, ta ce sai dai su jira V ta dawo dan su tabbatar.Shi ne fa suka yi shiru suna ta mamaki, masu aiki suka yi masu iso kamar yadda GAT ya basu umarni, sannan suka kaisu ɗakunan da ya ce su kaisu, wanka suka yi suka shirya, sannan suka sauƙo dan yin dinner, har yansu basu ga su Arya ba, dan kun san Arya ta tsani shiga cikin mutane, bata son hayaniya, kuma idan ba dole ba bata sauƙowa ƙasa sai in daddynta ya dawo ta zo ta yi mashi oyoyo. Angelie ita ta zauna da su Lisa har yanzu da V ta dawo, Daddyn Noor kuwa yana room da aka bashi, yana jiran GAT ya dawo su ci abinci a tare.A natse V ta kariso wajensu, cikin girmamawa ta gaisa da su kafin ta zauna a kusa da aunty Lisa, nan fa suka fara nuna mata kauna tare da tambayar dama su identical twins ne bata faɗa masu ba tasa sun ruɗe! Tana murmushi ta ce a’a su identical quadruple ne ma ba twins ba! Mamaki yasa su Aunty Lisa rikicewa, suka fara lallai a nuna masu sauran, V ta ce su gama dinner zata kaisu wajensu Arya, dan tasan wlh Arya ba zata sauƙo ƙasa dan su gaisa ba, sai dai ita aje a sameta. Shiru room ɗin ya yi suka cigaba da cin abincinsu a natse, V tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda tsananin daɗi, yau ta kwanta a kirjin love ɗinta!. —————————-🔥CRYSTAL PALACE. Mu koma baya mu gani. Tin tana kuka kaɗan-kaɗan har sautinta ya daina fita, take ta ji nunfashinta ya fara sama-sama yana ƙoƙarin ɗaukewa, a zabure ta miƙe tsaye tana ta ƙoƙarin jawo numfashin, amma ina, babu iskan da zata iya ja ta shaƙa. Laluɓe ta fara yi tana ƙoƙarin kama bango ta jingina, amma ta gagara, tangaɗi ta fara yi tana kai hannu ta rike wuyanta ta fara ɓarin abubuwa, dan ji take yi tamkar an shaƙeta ne, take ta fara tari tana zazzaro idanu waje.Kafin wani ɗan lokaci ta sulale ƙasa babu numfashi a jikinta!…….. A can cikin gida kuwa, bayan sun kulle ɗakin kai tsaye suka sauƙo ƙasa, wanka Champion ya shiga room ɗinsa ya yi, ya shirya cikin tail coat mai bala’in kyau launin ash color, still dai fuskan sanye da nose mask, ya fito ya isko scorpion a parlo. Miƙewa ya yi suka nufi hanyar fita, da alama barin gidan za su yi.Gab zasu hau elevator Champion ya tsaya, scorpion na kokarin yi mashi magana ya juya da sauri yana faɗin. “My phone, I’m coming”. Bai jira amsarsa ba ya wuce ciki da gudunsu na terrorist. Sama ya haura tare da nufar wannan ɗaki. A gaggauce ya buɗe ya shiga, kai tsaye wajen table ɗin da suka zauna ɗazun ya nufa, wayar ya ɗauko tare da nufar kofar fita. Dab zai fita ya kunna wutar wayar. Ganin jini a ƙasa yasa ya ɗan ja baya kaɗan, ya kara haska wajen da kyau. Tabbas jini ne, a ransa ya ce meyakawo blood wajen nan kuma?. ALLAH sarki jininta ne, dan a garin neman iskar shaƙa ta dinga buge-buge har bakinta ya fara jini. Ɗan bin jinin da light ya yi har izuwa wajen da take yashe a ƙasa bata ko motsi. Ɗan waro eyes ɗinsa waje ya yi, da sauri ya kai hannu ɗaya ya ɗauketa cak sai saman shoulder ɗinsa suka yo waje. Kai tsaye ya nufi kasa da ita. Sai cikin mota, kai tsaye ya ce su wuce CPH da ita, dan a bata taimakon gaggawa idan ma tana raye kenan. Kun gane ne, ɗakin binciken nasu sun yi shi ne musamman ta yadda babu wanda zai iya leƙan asirinsu, ko ka samu nasarar shiga a sace ba da saninsu ba to 30 mins ya yi maka yawa ka baƙunci lahira ba tare ma da sun taɓakaba, haɗarin dake cikin ɗakin tamkar haɗarin dake tattare da su ne! Kun gane ai?.Suna zuwa CPH aka ce ba za’a karɓeta ba sai da wannan notebook ɗin nasu na shaidar mazauna CP ne su. Champion ji ya yi tamkar ya harbe likitan dake mashi wannan jawabi, amma sai ya daure da cewa. Scorpion ya je ya ɗauko notebook ɗin a gida, a room ɗinta cikin drugs ɗinta. Da sauri ya juya ya tafi, yau ba dan Lion ɗinsu ne ya ce su kula da yarinyar kuma su bata kome take so ba da babu abin da zai hana Champion bai kasheta ya jefar da gawarta ba, dan ta cika karambani dayawa a cewansa. Haka dai ya dinga tausan kansa har aka kawo note-b ɗin, ya karɓa ya baiwa likita aka karɓeta. In takaice maku sai da ta yi kwana biyu a sume bata san in da kanta yake ba sannan ta farfaɗo da taimakon ALLAH da taimakon likitoci, sai da ta sha ruwa keda 3, kamar ma za’a kara mata jini, sai kuma aka fasa, aka haɗa mata magungunar jini kawai.After two days suka ɗauketa suka koma gida, a cikin wannan sati Champion ya nema mata boarding school, ya shirya mata komai ya ɗauketa ya jefata can ba tare da ya jira dawowar Lion ɗin nasu ba, watau ft, yana kwance a gadon asibiti bai san in da kansa yake ba, saboda raunin da ya ji, ga shi ya rasa jini sosai, sai da aka kara mashi leda biyu, har yanzu dai yana fama da jinya. To shi dai Champion ba zai iya jurar kiriniyar Seraph ba, shiyasa ya yanke nasa hukuncin, dan a kullum basa zaman lafiya a gidan, ta dinga kukar mammy ɗinta, abinci sai an mata ɗure, idan ta fito suka haɗe da zakin nan ta dinga ihu tana suma kenan, dik ta hanasu samun peace of mind a gidan, dan haka ko dan hero (zaki) da take tsoro gara a bar gidan da ita!. In kara takaice maku sai bayan zuwanta school da sati biyu Lion ya warke ya dawo, ko da ya dawo bai tambayi ina take ba, bai bi ta kanta bama, suka shiga sabon babi na aikinsu, dama gagarumin aiki ne a gabansu aka samu wancan matsala su Eagle suka farmasu, kungiyar su eagle sun basu aikin kashe wani ne suka ce ba zasu yi ba, dan su ba kowa suke yi wa aiki ba sai wanda suka yi ra’ayi, to abin da ya haɗa tsama a tsakaninsu kenan, su eagle suna ganin ai sun san sirrinsu sannan su ki yi masu aiki? Shi ne suka nufi kashesu, suka shirya zama da su, a wannan zaman ne Lion shi kaɗai ya yi attending har suka farmakesa, su Champion basu je ba, dan basu cika zuwa waje su ukun a tare ba. Kada ku manta suna da fuskoki da dama, su eagle ba da fuskan Iron Fist suka sansu har suka ƙulla harƙallah ba, da wani fuska ne, shi fuskan Iron Fist suna amfani da shi ne kawai idan zasu yi gagarumin kisan da zai jinjiga duniya! Fatan kun gane?.Seraph dama Jss 1 take a school, Champion yasa aka kaita Jss 2, daga nan ta cigaba. In kara takaice maku har tsawon shekara biyun nan suka wuce, Seraph ta kammala Jss 3, tana da shekaru 12 kenan yanzu, Lion bai taɓa tambayar ina take ba, da alama ma ya manta da ita a duniya, amma Champion yana zuwa wajenta a school time to time, yana kai mata kayan abinci idan ya dedeci lokacin karewarsu. Amma ku zo mu ɗan bi rayuwarta a makarantar ko kaɗan ne mu gani kafin mu yi skipping.GOLDEN ROOTS ACADEMY, shi ne sunan school da Champion ya sanyata. Boarding school ne wanda daga jss 1 ake fara kwana a makaranta zuwa Ss3.Ranar da ya kammala shirya mata komai ya ɗauketa a mota ya wuce kai tsaye da ita school ɗin. A ranar sai kuka take yi tana tambayar ina zai kaita? Kuma ina mammy ɗinta? Bai ko kalli in da take ba, yana driving cikin zafin jini abinsa. Tin da suka shararo titin da ya sadasu da school ɗin ta yi tsit tana kallon hanya har suk shiga ciki, katafaren makaranta ce na gani na faɗa, ƴaƴan manyan kai ne kawai a cikinta, shinfiɗaɗɗiyar titi ce ta ratsa ko’ina a school ɗin. Kai tsaye parking lot ɗinsu ya nufa. Yana parking ya fito tare da buɗe side ɗin da take ciki. Sanin cewa baya yi mata magana yasa ta fito da sauri, jakarta dake ciki ya ciro tare da buɗe bayar motar ya ɗauko echolac ɗinta, ba tare da ya sake kallon in da take ba ya wuce gaba abinsa. Da sauri ta rufa mashi baya suka nufi office na director.Yana zuwa ya wuce ciki kai tsaye, kafin ta karisa shigowa sai gani ta yi yana ƙoƙarin fitowa, zata bi bayansa wani kyakkyawan farin fata dake zaune a saman office chair ɗinsa ne ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Da sauri ta dakata, alama ya yi mata da hannu a kan ta zo. Ba musu ta je, tana tafiya tana waigo Champion har ya kurewa ganinta.Cikin harshen turanci director ya ce ta samu waje ta zauna bari Madam Rohisha ta zo ta ɗauketa su tafi side na ɗalibai!. Muryanta na rawa ta ce. “Uncle where is my Mammy? Do you know where she is? Will you take me to her?”. A kiɗime take magana, ya fahimci akwai firgici da tashin hankali a tattare da ita, dik tana ruɗe, ga idanunta a kumbure luhu-luhu! Lokaci guda mugun tausayin yarinyar ya kama shi, miƙewa ya yi daga kujeransa ya dawo in da take, cikin tausasawa ya fara rarrashinta har ya samu ta ɗan natsu.A daidai lokacin Madam Rohisha ta shigo bakinta a ɗauke da excuse, wata haɗaɗɗiyar mata ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, tana da ido masu zurfi da kyakkyawan dogon gashi, gata da kyan jiki, sanye take da arabian dress, ta yi rolling kanta da veil alamar musulma ce. Tana ɗaura dara-daran eyes ɗinta a kan Seraph ta ji yarinyar ta yi mugun tafiya da imaninta, gata kyakkyawar gaske. Ai cikin azama ta karisa gareta. Director ne ya miƙe ya bar wajen, ya koma saman kujeransa, ita kuma Madam ta zauna kusa da Seraph tare da riko hannunta tana ƙoƙarin tambayarta sunanta kenan director ya katseta, a natse ya fara bata bayanin wacece Seraph, watau marainiya ce da bata da uwa kuma bata da uba, dan haka ta kula da ita. Sosai Madam Rohisha ta ji kalamansa, ta kuma yi alkawarin ɗaukar Seraph a matsayin ƴar cikinta, daga nan ta kama hannunta, ta ja mata echolac ɗinta da ɗayar hannunta, sai ta ce Seraph ta ɗauki dakarta, daga nan suka fice izuwa side na mata, watau wajen kwanansu kenan!.Farko kenan a rayuwar Seraph a school, dan haka zan yi labarin ne bisa ɓangare biyu, idan na waiwayo wajen Seraph to muna baya ne in da take rayuwa a school, idan na koma wajensu Leo muna gaba ne kafin in yi skipping, kun gane ai?.
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

