Uncategorized

Matar Makaho Part 3 Complete Hausa Novel

MATAR MAKAHO

Chapter 3

By Rukayya Ibrahim

Cikin tashin hankali ya mike ya fita Dayake shi mutum ne Mai saurin fahimta yasa dakansa ya wuce wajen biyan kudi,

Kudin 50k yaji ance Masa,

Innalilahih wainnailaihir rajuun take yaji Kamar kansa xai rabe biyu haka ya karbi takardan ya wuce zuciyansa sai rawa take, shi Ina yasan zai samu kudi gabaki daya jarinsa ma baifi dubu daya da dari biyar ba Ina zai samu dubu hamsin, Koh bashi zai karba wazai tinkara in ma an basa Ina zai samu kudin biya?

Har cikin ransa baya kaunan wani abin bukata ya Tashi ta bangarin Sumayya ya kasa Mata har sai Yan gidansu sun Mata duk da baisan dalilin da yasa duk cikin Jala Arasa mijinda zasu aura Mata sai shi suka zaba Mata Wanda har yau ya kasa samun Amsa dalilinsu,,

Kuma bayason Koh da Wasa ta Saida abinda tazo dashi daga gidansu,saboda gazawarsa wajen Bata kulawa Bai santa ba Bai ta ba ganinta ba Bai taba Jin lbrn taba Bai San ya take ba muryarta kawai ya sani Amma a D’an zaman da sukayi Yana jinta har cikin ransa,,

Ya Allah ka bani ikon kulawa da wannan Amanar da aka bani,

A hankali yake tafiya harya fita a get in hospital in da taimakon wani Almajiri ya tsallake titi 100 da ke hannunsa ya Saya Mata Ayaban 100 guda biyar aka basa ya baiwa Almajirin ayaba daya  ya sake tsallakar dashi, cikin hospital in ya shiga yanabi a hankali da sardarsa harya Isa kofar dakin da aka kwantar da ita da sallama ya shiga dakin,

“Waalaikumu salam” na amsa Masa cikin dishashesshen muryata dagaji kasan na Mara lfyne maijin jiki

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


Sannu Sumayya ya jikin ??.

“Da sauki Alhamdulillah”

Sannu ya sake cewa

**Kai kawai na iyya daga masa

Lalube ya fara Yana neman wajen zama,

“Kujiran na Gefen ka na dama”nace Masa

Laluben damansa yayi yaji kujiran plastic na roba ya matso dashi  Kusa da gadon inda yaji muryarta ya laluba ya aje kujiran kusa da gadon saitin kanta a hankali ya zauna,

Sannu Sumayya ga  ayaba na sai miki yafada yana bude laidan hade da fitar da Ayaban masu k’yau guda biyar zai bare mini,

“Ah ah ka ajiye,so nake sai nayi sallan asuba nayi brush da wanka Koh zanji dadin jikina kafun NASA Abu a bakina”

Toh bara na taimaka Miki ki shiga bandakin sai kiye wanka da brush in duk na kawo Miki harda Kaya

“Toh taimaka min na tashi “

A hankali a mike Yana lalube na harya lalubo hannuna ya Kama na mike a hankali na sauka a gadon Ina “takalmina”?

Na manta ban hada Miki ba komawa nayi na zauna a bakin gado “gaskiya ni bazan iyya taka tiles na asibiti ba takalmi  gaskiya” toh ga nawa kisa Yana fada Yana cire mini ciny’ayyen silifas  insa “ah ah innasa naka kaikuma fa”? ba damuwa Zan tafi haka

“Bazanfa saka ba sai dai ka saimin sabon silifas abakin get”

Wallahih ban fita da kudi ba sai dai in Khadija tazo taji da dauko Miki”toh” na basa amsa Ina k’wanciya a Kan gadon,

Khadija bayan fitar yayanta dakin ta fara kimtsawa ta share ta cire zanin godon ta shimfida wani  ta share baranda da kasa ta hada wanke wanke tayi kafun ta shiga kitchen,da yake akwai NEPA ruwa ta daura a hot-plate ta zuba ruwa ta rufe, ta dauko wani bojuwan daban ta daura shima ruwan ta saka ta rufe Daya ke hot-plate in Mai uku ne,

Tattasai ta dauka da dogo dogo sai albasa ta hada ta juye a blander Dayake taga yanda Sumayya tayi ranan da suka shiga kitchen kunnawa tayi ta markada she Kara Kara baiyi laushi ba dai dai irin na miyan taliya,

Sannu ishesheya munafukar yarinya uwar me kike a kofar har yanzun Naga fitar *makaho* tun dazun ya fita? Taji muryan inna asabe take fada tana shigowa kofar

Inna Aunty Sumayya ce ba lfy shine Yaya yace na musu girki,

Oh lallai ai sai ke in zai Kira don duk gidan nan ba bawan sa 

Kala Khadija batace Mata ba

Dan ubanki bara na kawo kwanona ki zubamin inkin gama saura kisamin kadan,

Kala Khadija batace ba tana cigaba da gyaran waken da ta iba cikin Kofi Daya da rabi 

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


Keee ishassheya bakiji me nace bane

Naji innah ,ta Bata amsa

Fita Inna asabe tayi sai gata ta dawo da katon kula ta ajema Khadija a gaba ta fita abinta

Ruwa na tafasa ta sauke taliya daya ta juye a tukunyan ta barbada gishiri ta rufe, dayan bujuwan wake ta wanke ta zuba ta rufe shima ta saka Masa gishiri,

Wani sabon bujuwa ta daura ta zuba Mai da albasa Yana soyuwa ta juye kayan miyarta ta soya ya soyu tukum ta saka ruwa ta bare Maggi tasa da onga classic Wanda ta gani duk a cikin kitchen in caton in kefe ta bude ta dau uku masu kyau ta aje a roba,ruwan zafi ta zuba a kettle Yana tafasa ta juye akan kefen ta barsa yadan d’auki seconds kafun ta tsame tasa a ruwan sanyi ta gyara ta juye a miyar ta rufe 

Daidai lokacin taliya ya nuna saukewa tayi ta juye a k’wando ta tsame,

Fita tayi a kitchen in ta dau omo da sabulu ta hada wankin yayanta Dana Sumayya harda zanin godo ta fitar waje ta aje ta fara iban ruwa a rijiya tana wanke kayan dashi lokaci kankani ta Gama wanke wa ta shanya a igiyar kofar shashen,

Kitchen ta shiga ta duba miyar ta nuna saukewa tayi,ta dauki wani kula a caton insa Mai azabar kyau har Yana daukar ido Mai guda hudune uku ta dauka ta wanke dayan ta zuba taliya daya Kuma Miya sauke waken tayi shima ta juye a dayan Kular,

K’wando babba na kaba Mai kyau ta  jera kulan a ciki sai lokacin ta Tuna kulan Inna asabe  zuba mata, tayi,

Ta shiga daki firij ta bude ta dauki drinks guda biyu sai ruwan gora biyu ta hada a k’wandon da plate biyu shukali biyu,..

Wanka ta shiga tana fita ta maida kayan da tazo dashi, Jin ana Kiran azahar tayi Alwala tayi sallah,

Ta dauki sallaya ta ninke tana kokarin  rufe kofar dakin  sai ga Inna asabe tana zuwa kitchen ta nufa ta bude kulanta ganin abinci a ciki Kuma Mai yawa yasata dauka tayi gaba abinta,

Rufe kofar tayi ta dauki k’wandon ta fita a shashen shima ta rufe kofar ta rike key in ta fita dashi lokacin karfe 1 na Rana hanyar FMC ta Kama da kafa,

***********Har lokacin muna zaune nida shi anzo an sake daura mini ruwa,Yana zaune cikin wani yanayi duk da na Saba ganinsa sanyi sanyi Amma nayau yafi na kullum Wanda bansan daliliba,

Jin an fara kiraye kirayen sallah yasashi tashi Yana lulube yake cemin bara yaje sallah ya dawo,da “toh” na amsa masa,

Fita yayi yaje masallaci yayi sallah ya zauna agun sai kusan 2 ya mike ya nufu Hall in emergency  har yayi nisa yaji muryan Khadija daga nesa tana k’wala Masa Kira,

Juyawa yayi saitin inda yake jiyo muryar Tata ya tsaya harta karaso Khadija kin isone?

Eh Yaya na karaso tun dazun Amma ban gane dakin da kuke ba,

Muje toh Khadija ya fada Yana tafiya,itama binsa tayi a baya,.

Yaya ya cikin nata?

….Da sauki Khadija

Yaya Yana ganka cikin damuwa haka meke faruwa ne Koh kudin magani ne baka dashi?

Khadija Ina Zan samu kudin magani in badon Allah ya rufamin asiri ba ya hadani da wani bawan Allah ba ya biya mini kome na magani,

A Ina ka Sansa Yaya?

Bansan Saba yadaice sunansa Ammar

Toh meke damunka?

Wallahih khadija appendix ke damun Aunty ki Kuma kudin operation naira dubu hamsin shine yake dagamin hankali banda sisi Koh abinda Zan sayar na biya

Amma yaya baka ganin gara a fadawa Aunty tunda bazata rasa kudi a hannunta ba, tabiya ??

Ah ah Khadija karki fada Mata yanzun Ina son in munje ki zauna agunta ni Zan fita Koh Allah zaisa na samu bashi,

Habba Yaya wazai baka bashi tsakani da Allah fa Kaida Koh sisi baka dashi in ba mangoron da ya rage jiya ba wazai baka bashi’

Khadija kedai ki tayani da Addu’a na Allah basa karewa

Hakane kam Yaya Allah yasa ka samu 

Yauwa ameen Khadija ta

Daidai lokacin suka iso dakin, shiga sukayi Ina kwance,sauke k’wandon Khadija tayi tana gaidani Aunty Ina kwana?

“Lafiya Khadija”

Ya jikin ki Aunty?

“Da sauki Alhamdulillah”

“Khadija kiramin nurse tazo ta cire mini ruwan nan na samu nayi Sallah”

Toh Aunty tace, tana fita,sai gata da nurse sun dawo cire mini sukayi, “Khadija hau godon ki zauna ki ban takalmin ki bara na shiga toilet” toh Aunty,

*Ta kalmin nata NASA

 shi Kuma ya bawa Khadija tasa ta saka ya lalube bakin gadon ya zauna 

**Da taimakon Khadija na shiga bandaki ta koma ta dauko mini brush da maclen,da kayan da Zan saka,

***Wanka nayi da brush nayi Alwala na fitoh a hankali nake takawa Ina bin bango harna bude kofar na fitoh 

Da sauri Khadija ta tashi tazo ta taimaka mini ta shimfida mini Sallayan da tazo dashi ta shimfida mini ta Mika min hijab na saka na Tada sallah harda na asuba na biya,ina idar wa na cire hijab in,

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


 Khadija ta mikamin hula nasa, na tashi na koma Kan gadon dukansu sukaimin sannu har suna hada baki, 

Khadija takalminta ta saka Wanda na cire ta bawa Al’ameen nasa,

Abinci ta iba min a plate ta Miko mini,

“Khadija bawa yayanki abincin nan bazan iyya ci ba bakina ba Dadi Sam”

Ah ah Sumayya ki karbi abinci kici ai ba’a jinya sai da abinci” Al’ameen yace 

Gaskiya ne Aunty rabonki da abinci tun jiya fa,ta fada tana aje mini,

“Wallahih Khadija bazan iyya ci ba kidai Mika mini ayabar nan naci”

Toh Aunty, 

Ayaban ta bani na samu naci uku ta Mika mini fresh milk in da tazo dashi daga gida nasha rabi  

Plate na abincin da ta bani ta Mika Masa karba yayi Bismillah ya fara ci,

“Khadija ya Naga kin zauna ki ibi abinci kici Mana” na Bata umurni

Iba tayi ta faraci, 

Yana Gama cin abinci ruwan gora daya Khadija ta bashi yasha, Khadija ki zauna da Aunty ki bara na fita sai na dawo,ya fada Yana tashi yayi hanyar waje,

Toh yaya Allah ya bada sa’a

…… Ameen Khadija

Nidai da ido na bisa harya fita na juya Ina kallon Khadija” Khadija waya biya kudin magangunan nan Naga harda ruwa duka”?

Nima ban sani ba Aunty yanzun nazo sai dai ki tambayi Yaya,

**Shuru kawai nayi na koma na kwanta

Al’ameen Bai Dade da fita ba, sai ga wani matashin saurayi baki k’yakk’yawa Mai matsakaicin tsayi da jiki ya shigo dakin mu da sallama a bakinsa 

Amsawa Khadija tayi nikam hannu nasa na dauki hijabina da na cire a jikin karfen gado nasa,

Shigowa yayi ,barka kudai ya jiki Sumayya?

Mamakine ya kamani Ina kuma wannan bawan Allah ya sanni,

“Da sauki Alhamdulillah”

Allah ya kara sauwa kewa

“Ameen” nace

Al’ameen ya fitane?

Karanta:

✓  Sabbin Hotunan Momee Gombe, Maryam Booth da Hadiza Gano.

✓  An baiwa mawaƙi Umar M. Shareef jakada a gidan television.

✓  Cikin fushi Umme Zeezee ta mayar wa da wani saurayi da martani akan cewa ita ba jaruma ba ce.

Eh wallahih yanzun ya fita baku hadu ba? Khadija ta basa amsa

Ah ah bamu hadu ba,

Koh Kaine Ammar?

Nine Hala lbrna ya baki haka kikayi saurin gane ni?

Eh yadai fadamin abin alkhari da ka Mana Allah ya kara bude,

…Ameen

Nidai shuru nayi na barsa da Khadija suna Hira Kamar Wanda suka San juna,

Khadija nikam Inaga Zan gudu fa har yanzun Al’ameen Bai dawo ba gashi Ina son muyi sallama  tafiya ne ta kamani wallahih gobe Zan wuce shiyasa naso mu hadu kafun na wuce,

Yace Yana zaro kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija ga wannan ba yawa a saiwa mara lfy lemo in yayan naki ya dawo kice Ina gaishe she ,

Mungode Allah ya saka Kuma zaiji sakon ka, 

Allah yasa yace Yana kokarin nufar kofa

“Nagode”  nace masa ba tare da na dago ba ganin irin kallona da yake tayi kamar ya samu TV tun dazun da suke hira da Khadija idonsa na kaina,

Ba kome yace yasa Kai ya fita………

Bayan fitar Ammar Khadija ta kirga kudin dubu goma ne,Mika min tayi, Aunty ga kudin

“Ajjye Khadija in yayanki yazo ki basa tunda shike fama da zirga zirgan asibiti” toh Aunty ta bani Amsa tana aje kudin a cikin ak’watin Kayana,

Al’ameen na fita daga asibiti da kafa ya koma har gida Dayake akwai sanda in Kuma yazo titi sai ya Kama yara su tsallakar dashi Yana Isa unguwan su(sintali) wajen shagunan bakin titi ta inda yake sai da mangoro a bakin su,

Shagon malam shu’aibu ya fara zuwa don shine yafi masu shagunan abin arziki sosai alayin da sallama a bakinsa ya shiga shagon,

Assalamu alaikum malam shu’aibu

Waalaikumu salam Mai mangoro ne?

Eh nine malam shu’aibu barka da jama’a

Barka dai lafiya Kam Naga yau tun safe danazo bude shago Naga hulbairon ka a rufe dazun na aiki yaron gidana ya karbo mini yako yake fadamin baka nan?

Eh wallahih malam shu’aibu iyalina ne ba lfy jiya na kaita asibiti,

Allah sarki ya jikin nata?

Da sauki Daman nace bara nazo ka taimaka mini da kudi dubu hamsin za’a Mata aikine appendix ya kumbura a cikin ta don Allah ka taima kamin,

Kutt lallai ma a karnin nan da kowa ke takai takai Ina Zan iyya daukan kudi har 50k na baka da sunan bashi, bayan anyi operation in Ina zaka samu kudina ka biyani, gaskiya bazan boye maka ba ni nan Koh biyar bazan iyya baka ba banaji ance Yar masu kudi aka aura maka ba me yasa danginta bazasu Mata jinya ba tunda sunsan baka dashi Daman suka baka ita

Shikinan malam shu’aibu na gode, ya fada Yana fita ba tare da ya basa amsar tambayar Saba,

D’ayan shagon Al’ameen ya shiga  shagon gwanja bayan sun gaisa shima ya rokesa Koh zai samu bashin kudi

Amma Kai dai wallahih D’an rainin wayo ne ya Ina Saida kayan Miya zakace na baka dubu hamsin duk kayan shagon nan aka sayar Ina zaiyi dubu hamsin,

Haka yayita bin shagunan makwantansa Amma ba Wanda ya basa Koh sisi wasu kamma da bakar magana suke binsa dashi,

A haka ya iso shagon Haladu shima yace baidashi,. Wajen bairon mangoron sa yaje ya bude ya tataba mangoron rabi duk sun lalace saboda yini da sukayi a rana Kuma a rufe, zabe masu kyau yayi Yana,

D’auka yana sawa  a k’wando ya shiga shagon Haladu dashi, Yana cewa,

 don Allah Haladu Koh zaka sayar mini da mangoro na zanje na zauna a asibiti  na kwana biyu daidai Matata taji sauki 

Gaskiya bazan iyya sayar maka ba sai dai na saya kawai na sayar Nima na samu D’an riba,

Ba damuwa Al’ameen yace Masa

…..Nawane mangoron?

D’ari takwas da hansim

…..Zan baka dari biyar  don Naga wasu sunyi laushi?

Ba damuwa Allah ya saka musu albarka

……Ameen

Kudin Haladu ya basa ya karba gida ya shiga ya bude kofar,

 da yake ya karbi key a hannun Khadija wanka yayi ya saka kayansa Jin ana  Kiran la’asar yayi Alwala ya lalube takalmin Sumayya ya fita dashi a hannunsa, masallaci ya tafi yayi sallah ya wuce asibiti duk zuciyansa ba Dadi ya rasa wajen wa zai tinkara da zancen kudi,, yasan Koh mutuwa zaiyi Yan gidansu bazasu taimaka Masa ba bare Sumayya matar sa,

***Muna nan da Khadija har la’asar sallah mukayi dukan mu nurse tazo ta mayar mini da laidar ruwan a hannu na,

Na kwanta baccine ya dauken nabar Khadija na zaune,

Ya iso asibitin da sallama ya shigo dakin Khadija ta amsa masa.

Sannu yaya ka dawo?

Eh Khadija

Toh yaya ka samu kudin?

Wallahih Khadija sai addu’a naira 500 ne kadai na samu

Amma yaya ya kamata ka sanar da Aunty gaskiya don wallahih Yaya Ina Jin tsoro kaga ance appendix in ya kumbura fa tunda Allah Bai baka ikon samu ba, ka fada Mata ita sai ta biya?

Toh Khadija wallahih inajin kunya a matsayina na mijinta na kasa biya Mata kudin operation don samun lfyr ta,

Habba Yaya karfa ka manta Allah yaga zuciyar ka baka dashine Kuma ba abin kunya bane tunda itama tasan baka dashi,

Suna cikin Hira na farka a gigice Jin wani irin mahaukacin ciwon ciki ya tasarmin ” Innalilahih wainnailaihir rajuun wayyo Allah na cikina”

Subhanallah Sumayya cikin ne Al’ameen Daya Mike cikin tsananin tashin hankali yake lalubarta ,

Khadija ma da saurin ta ta iso ni,sannu Aunty take fada idon ta ya jika da hawaye

*****Nikam.na kasa Bata amsa kuka kawai nake hankali tashe

Khadija tashi kije ki Kira doctor eiiii sauri 

Toh yaya tace tana mikewa da saurin ta

Al’ameen Kam hannun Sumayya ya Kama sai sannu yake Mata a hakan likita yazo ya sameta a halinnan

Da sauri shida nurse suka rufu a kanta tare da K’ura Khadija da Al’ameen waje,allurai sukai Mata harda na bacci lokaci daya bacci ya dauke ta,

Khadija da Al’ameen na tsaye a  bakin kofa likita ya fitoh ya kira su zuwa office,

Malam Al’ameen majinyaciyar ka tana cikin condition Mai muni ya kamata ka samo kudin aiki nan da awa uku ba wallahih kome zai iyya faruwa,

 Innalilahih wainnailaihir rajuun kawai suke fada,

Suka mike zuka fita a office in Khadija Kam kuka ta fara abin Yama Al’ameen yawa ta Ina zai fara anya zai yafewa kansa kuwa in yar mutane ta mutu ata dalilin rashin kudin aikin da Bai samo ba,

Yaya ya kamata Aunty tasan abinda ke faruwa muje ka fada mata ta Kama hannunsa sukayi dakin 

Suna shiga suka samu Sumayya na bacci ……….

Yaya Ammar innan yazo baka nan  ya bawa Aunty kudi Amma Taki karba tace na baka 

Allah sarki Ammar yazo ne?

Eh yaya kana fita Yana shiga, yace ma Wai Daman Yaso kuyi sallama tafiya ne ya kamasa, na gaggawa,

Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari Yan kiyaye sa aduk inda yake,

Ameen yaya

 Khadija Miko min kudin na hada da dari biyar in hannu na naje na Basu Koh zasu mata daidai a Nemo sauran su bimu bashi,

Uhmm lallai yaya kadai San asibiti bata ma matum aiki ba tare da kudi bak’oh?

 Khadija bara dai naje na gwada Koh Allah zaisa a dace tunda kinga hour uku aka bamu kuma yanzun bacci take, bara naje na dawo ya fada Yana karban kudin da khadijar ke mika Masa,

Yana fita yaje wajen biyan kudi, 

don Allah Dan uwa kayi hakuri ga dubu goma da dari bayar a fara mata aikin in yaso za’a cikita muku daga baya Dan Allah ku taimaka min matatace ba lfy kuma hour 3 aka bani ake son mata operation?

Amma Kai *makahon* nan Ina ga baka zuwa asibiti ne taima?

Ina zuwa ranka shi Dade sai dai ban taba kawo majinyaci irin wannan ba

Toh gaskiya ka gannin nan Koh biyar naci a cikin kudin da nake karba wallahih Sai an daure ni

Kuma anan in baka biya kudiba wallahih baza’a Mata aiki ba Koh mutuwa zatayi gwara kaje ka Nemo duk in da kudi ya shiga ya fita shawara nake baka,Amma zance a taimaka maka toh hadai asibiti ba

Shikam tsabar damuwa har jiri yakeji yana ibansa ,a rayuwar yanzun in baka dashi kana ji kana gani harka mutu indai baka da kudin jinya ba Mai taimakon ka, zama yayi a bakin barandan pharmacy in yayi shuru cikin tashin hankali da alhini,

Bayan fitar Al’ameen khadija na zaune har lokaci hawaye baibar zuba ba sai ta gogi wani ya zuba, har  hour 1 yayanta Bai dawo ba,

*** A hankali nabude idona na sauke akan Khadija dake ta hawaye ido harya kumbura abinka da farin fata fuska tayi ja” khadija lafiya kuwa meya faru Naga kina kuka”??

Babu Aunty Daman na tsorata ne danaga cikin ki ya Tashi Ashe haka kike fama da Jin jiki sannu,

Murmushi nayi “haba Khadija Menene na kuka baki ga naji dauki ba” 

Toh Aunty,

“Yauwa khadija nikam likita ya fadi abinda ke damuna ne, Koh yake sani ciwon cikin nan”?

Kafun ta bude baki ma sai ga doctor ya shigo,Wai har yanzun baku samo kudin aikin ba Koh bakuji condition inda nace muku tana ciki ba Wai ina MAKAHON yake ne?

“Doctor ban gane mikake nufi ba” nace ina kallon sa?

Au baku fada mata bane? Yana kallon khadija alamar tambaya

Eh doctor bata sani ba khadija ta bashi Amsa,,

“Wai meke faruwa ne kun sani a duhu” waza’a ma aiki??

Kece appendix ya kumbura sosai tun jiya na sanar dasu Amma haryau shuru Basu biya kudiba yanzun haka  hour 3 na Basu su kawo kudin Dan kina bukatan aiki  gaggawa Amma an share hour 1  shuru, Banga alaman zasu biya ba

Da mamaki nake kallon khadija”yanzun khadija Ina fama da wannan babbar matsala irin wannan Amma kuke mini Wasa da rayuwa Ina da kudin da Zan iyya biya ba bandashi ba”

Kiye hakuri Aunty Daman Yaya ne yace shi yake son biya

” Koh ance lallai sai yayanki ne ya wajaba ya biya ai ni Karan kaina nasan Bai dashi don Bai biya ba ai bazai  zama wani abu na daban ba” menene riban ya fita yana neman bashi alhalin Ina da kudi”??

Kiye hakuri Aunty,ta fada jikinta a sanye ganin Raina ya baci

“Nawane akace kudin aikin”?

……50k ne

“Khadija tashi ki dauki key kije gida ki dauko mini jakana  wani yellow a cikin whtdp nawa ki dauko mini jakan akwai kudi a ciki”

Toh Aunty ta fada tana mikewa daukan key in tayi a jakan kayana ki hadamin da wayata ki dauko darduma babba da filo, ga kayan da nacire ma kikai mini gida kisa a basket in bayan kofa”

“Kihau nepep   ya kaiki kofar gida ki shiga in kin dauko kudin saiki shiga ya dawo dake ki basa 1k ya d’auki kudinsa karfa kice Zaki tafi da kafa”??

Toh Aunty ta d’auki  kayan nawa ta fita  a dakin, doctor Kam Dan kallo ya zama Daman tun da ya ganni yake ganin alamun Jin Dadi a tare Dani Amma abinda ya daure masa Kai mutanen da suka kawo ni asibitin abin yana bashi,mamaki harda Nurses Amma basuga fuskar tambaya ba

**komawa nayi na kwanta shima doctor fita yayi

Tsabar rudewa Khadija Koh yayanta Bata Lura dashi ba akan baranda ta wuce,

Shikam ganin lokaci na wucewa yasa ya Tashi ya shigo dakin,da sallama a bakin sa,

**Amsa Masa nayi Ina kallon sa yazo ya zauna a kujiran gefena,

 Sumayya,yakira sunana

Na’am” na amsa Masa 

Kiye hakuri Sumayya na kasa kula dake wallahih nayi iyya kokari na Amma ban samu kudin ba Daman appendix ne ke damunki Kuma ya kumbura, shine ake son Miki aiki kuma……..

**Da nayi niyar rufesa da matsifa Amma sai jikina yayi sanyi Jin bayanin da yake mini” ban bare ya karasa ba na katse sa”ba kome, me amfanin Ina dashi kaje kana,.. baran attaimaka maka kazo ka biya mini kudin aiki”? Karka sake mini irin wannan banaso duk abin da zai taso a waje na Koh Khadija Koh Kai, in baka dashi  karka sake zuwa gun wani da sunan ya taimaka maka indai abin baifi karfina ba pls”

Kiye hakuri insha Allah bazan sake ba,

Shuru na Masa

Jin Bata amsa ba ya sashi yin shuru

Khadija na Isa gida ta samu jama’a na cike a kofar gidan dam alamu dai wani  abinne ya furu don harda motar police ga jama’an unguwan makil……………

Back to top button