Halysaah Page 191 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 191…A hankali Ajay ya koma gefe yana kallonta da rinannun idonsa yana sauke numfashi, Khaleesat taki yarda su hada ido tana cusa kanta cikin pillow, zata jawo duvet ta rufe jikinta ya rike duvet din ya koma kusa da ita murya can kasa yace “Why didn’t you tell me you are on ur period?” Ta rufe fuskarta jikinsa a hankali tace “Na manta….” Rufa masu duvet din yayi ya rungumota ta kara shigewa jikinsa ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe takwas saura Khaleesat ta farka daga baccin da take, mikewa zaune tayi tana kallonsa yana bacci, ta kai hannu jikinsa taji temperature dinsa is a little high, ta sauka daga kan gadon a hankali don kar ta tashesa, bandaki ta shiga tayi wanka ta fito, har zata fita zuwa dakinta don yawanci kayanta suna can dakin, sai kuma ta dawo ta dau hijab dinta har kasa ta saka sannan ta fita, tana isa corridor din dakunan ta hango Jay zaune Main parlor yana shan fruit yana kallon TV, sai dai ya rage muryar Tv din ta yanda shi kadai zai dinga jin kayansa, ya daga kai ya kalleta, karasawa cikin parlon tayi ta tsaya bayan kujera tace “Ina kwana Ya Jawwad” Yace “Lafiya lau Halysaah, is he still sleeping?” Ta gyada masa kai tace “Bai tashi ba” Bude kofar parlon aka yi Hadiyah ta shigo rike da tray din breakfast a hannunta, Jay ya juya ya kalleta, Mai aikin Mami na biye da ita a baya da flask, Hadiyah ta sauke idonta ganin Jay a parlon taki karasawa ciki tana kallon Khaleesat tace “An tashi lafiya Halysaah” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Good morning” Hadiyah tace “Ya jikin Yaya?” Khaleesat tace “Da sauki” Mai aikin Mami ta duka kasa da ladabi ta gaida Jay ya amsa yana cin strawberry din gabansa, Mai aikin ta kalli Khaleesat ita ma ta gaisheta, Khaleesat tace “Lafiya lau” Hadiyah na kallon Khaleesat tace “Breakfast Mami ta bada a kawo, ina zan ajiye maku? Ko in kai kitchen?” Khaleesat tace “Tohm kai kitchen din, thank you….” Hanyar kitchen Hadiyah ta nufa, Jay na kallon Mai aikin yace “Zaki iya tafiya” Ajiye flask din tayi ta mike ta fita daga parlon, Khaleesat ta juya ta tafi dakinta zata shirya, Hadiyah na fitowa kitchen ta ga Jay tsaye kusa da corridor ta inda zata bi ta wuce, hakan yasa taki karasawa wajen, tana ganin ya nufo corridor din tayi maza ta bude kofar dakin Khaleesat ta shige ta rufe da sauri, Khaleesat dake zaune gaban mirror tana shafa cream dinta bayan ta ciro kayan da zata saka ta juya tana kallonta, Hadiyah ta ɗan sosa kai tace “Ohh sorry, na kai abincin kitchen….” Khaleesat dai kallonta kawai take, can tayi murmushi tace “You are running away from Ya Jawwad ko” Hadiyah ta tafi gefen gado ta zauna bata dai ce komai ba, Khaleesat bata daina kallonta ba tace “Toh saboda me?” Hadiyah ta juya ta kalleta tace “A’a saboda me dai zai dinga bi na, naga ai babu komai tsakanina da shi yanxu” Khaleesat tace “To kilan magana yake son ku yi” Hadiyah ta taɓe baki tace “Ba wani magana fa da zai min, in da zai yi maganar ai da yayi, amma babu abinda yake cewa….” Khaleesat na ci gaba da shafa cream dinta tace “But you know you wronged him Hadiyah, bai kamata ma ki dinga ignoring dinsa ba yanxu” Hadiyah bata ce komai ba, after some seconds ta juya ta kalli Khaleesat tace “I wronged Mami not him, kuma na bata hakuri na ce ta yafe min ta kuma hakura tun da dadewa, sannan ai ba magana yayi min nayi ignoring dinsa ba” Khaleesat tace “If you did wrong to Mami ai shi ma you wronged him kenan tunda Mahaifiyarsa ce Mami, da kika ba Mami hakuri shi ma da sai ki basa ai” Hadiyah ta ɗan yi murmushi kamar dai bazata ce komai ba, sai kuma tace “Kin san sau nawa na basa hakuri Halysaah? Did you know how many times I text and call him? Hajja ta basa hakuri on my behalf, Mai martaba ma yayi haka, Hajja har sai da ta sa Ummina ta ba Mami hakuri, amma shi yaki hakura, kin san wahalan da ya bani a lokacin ne, at the end he blocked me both on Whatsapp and phone call, duk sauran kayana dake part dinsa ya sa masu aiki suka kai bangaren Hajja da daddare wajen karfe daya, that was almost 7 months ago…..” Khaleesat dai kallon Hadiyah kawai take, can ta sauke ajiyar zuciya tace “Hadiyah…. may be yaji ya huce ne yanxu komai ya wuce a wajensa, shi yasa yake bibiyanki yanxu, pls ki basa listening ears ki ji abinda zai ce maki” Hadiyah tace “Sau nawa din muke haduwa baya cewa komai ba, idan mun hadu ba sai yayi maganar da zai yi ba, meye sai ya wani matso kusa da ni bayan babu abinda zai ce” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, Hadiyah tace “Beside i have moved on, ni ina da wanda nake so yanxu, dama Mami ne nayi ma laifi kuma na bata hakuri, and I am glad ta yafe min….” Khaleesat tace “A’a, shi ma kin masa, ki dai tuna” Hadiyah tayi shiru bata ce komai ba, Khaleesat tace “Pls kiyi hakuri ki basa second chance Hadiyah, I know you still love him kawai haushin yanda yaki hakura ne yasa baki son ki kulasa yanxu, forget everything and listen to him pls” Hadiyah ta wani zaro ido tace “Bayan nace maki nayi move on, nan ba da dadewa ba fa parent din Khalil za su zo gidan nan, yanxun ma ai ba wai ignoring dinsa nake ba kawai abinda yake yi ne bana so…” Bude kofar dakin aka yi Khaleesat ta daga kai da sauri, Ajay ne tsaye bakin kofar, Hadiyah tace “Ina kwana Yaya” Yana kallonta yace “Lafiya lau” Tace “Ya jikin?” Yace “Alhamdulillah” Khaleesat dai kallonsa kawai take har ya bar bakin kofar, Hadiyah ta kalleta tace “Ki je ki ji ko yana son wani abu ne, naga kamar he is not fine” Mikewa Khaleesat tayi ta dau hijab dinta ta saka ta nufi kofa ta fita, har ya bude kofar Main parlor zai fita ta gansa, yana jin ta fito ya juya yana kallonta ta karasa ita ma tana kallonsa tace “Ina za ka?” Jingina yayi jikin kofar parlon, ta kai hannu jikinsa taji da zafi, da damuwa tace “Your temperature is high….” A hankali yace “Zan je wajen Jay ne” Tace “Ko in kira maka shi?” Yace “A’a zan je part din sa” Tace “To in kai maka breakfast din can?” Ya gyada mata kai kawai don har ya gaji da tsayuwa ya fara jin jiri, tace “To bari in shirya sai in taho maka da shi” Nan ma ya gyada mata kai, sannan ya fita daga parlon walking slowly, da ido ta bi sa har ta dena hangosa sannan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta. Bayan Khaleesat ta gama shiryawa ta dau farfesun kifin da Mami tayi masa da safen nan, ta debar masa doya da kwai ta hada masa shayi sannan ta nufi part din Jay da shi, ita kuma Hadiyah ta tafi bangaren Hajja, sallama Khaleesat tayi bakin kofar parlon Jay, after some minutes Jay ya bude kofar, ta sauke idonta tace “Breakfast na kawo masa” Jay yace “Ohk, ki kai masa yana daki” Yana fadin haka ya nuna mata hanyar dakin, ta karasa har kofar dakin tayi sallama sannan ta shiga ciki, kusan komai na dakin irin na Ajay ne, ta karasa ciki ta ajiye tray din hannunta tana kallon Ajay dake kwance kan gadon Jay ya sa masa drip, dukawa tayi tana kallonsa ya bude idonsa a hankali ya saka hannunta cikin nasa murya can kasa yace “Jeeddah” Ta kasa cewa komai tana kallonsa a sanyaye, mikewa zaune yayi speaking slowly yace “Ke kinyi breakfast din?” Ta sauke idonta tace “Ta yaya zan yi bayan kai baka yi ba” Murmushi yayi ya nuna mata cup din shayin da Jay ya hada masa wanda ko rabi bai sha ba, cikin sanyin murya tace “To ai baka shanye ba” Yace “Zai shanye sauran, ai nace kar ya cika ya ciko min” Tace “Zaka ci doya da kwai?” Ya girgiza mata kai yace “Sai anjima” Tace “Mami tayi maka fish pepper soup da safen nan, bari in dibar maka” Bata jira cewar sa ba ta bude warmer din farfesun ta dau plate da cokali, manyan kifi ne sosai, ta dau daya ta dora masa a plate ta zuba pepper soup din a kai sannan ta zauna gefensa tana kallonsa, daukan spoon din tayi ta yanki kifin, making sure babu ƙaya jiki sannan ta kai masa baki, amsa yayi yana murmushi a hankali yace “Thanks wife” Haka ta dinga basa yana ci, duk da bai ci da yawa sosai ba yace ya koshi, ta ajiye sauran kifin ta debi ruwa a glass cup ta mika masa ya amsa ya sha ya ajiye sauran, pillow ta gyara masa ya jingina jiki cikin sanyin murya tace “Allah ya baka lafiya” Ya kamo hannunta underneath his breath yace “Ameen Mar’atussalihah….” Sauke idonta tayi, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, after some minutes tace “Zan tafi, sai na dawo anjima, let me not inconvenience Ya Jawwad” A hankali Ajay yace “Ce masa zan yi zaki dawo nan, sai ya koma can ɓangaren Mami ko ya zabi wani dakin da zai zauna a gidan, ya bar mana nan” Khaleesat tayi murmushin da bata yi niyya ba don her heart is heavy, sosai taji rashin lafiyar nasa ya tsaya mata a rai yanxu, she want him to go back to his healthy Junaid, Ya dago kanta yace “In gaya masa?” Tana murmushi tace “Ni dai ba ruwana kar kace masa haka, ai zan dinga zuwa ina duba ka har drip din ya kare” Yace “Ohk My love” Tashi tayi ta kunna burner da ta gani a dakin ta debi turaren wuta ta zuba, ta jira na few minutes sannan ta kashe bayan ɗaɗaɗɗen kamshin turare ya gauraye dakin, ta dau room freshener da ta gani ta fesa jikin curtain da labule sannan ta ajiye, juyawa tayi taga kallonta kawai yake, ta sauke idonta ta karasa kusa da shi ta duka tayi pecking lips dinsa tace “Till later” Daga haka ta dau sauran breakfast din ta nufi kofa shi dai ya bi ta da kallo har ta fita, ji yayi har zazzabin da yake ji ya sauka, ya gyara pillow ya kwanta ya lumshe ido yana kara jin wani sabon sonta a ransa, a parlor Khaleesat ta samu Jay yana breakfast, ya daga kai ya kalleta yace “Ya ci abincin?” Ta girgiza kai tace “Kawai kifi ya ci kadan, ko in dibar maka kifin?” Yace “A’a bana son karni” Ɗan murmushi tayi tace “To ai shima yanxu ya fara ci, amma ɗa baya cin kifi” Jay yace “To Halysaah me miji” Er dariya tayi tace “In dai zaka ci gwara in dibar maka kadan….” Yace “A’a ki bar masa kayansa ki dumama masa anjima, mu mun fi gane farfesun kaza, nasan duk kun cika min daki da karnin kifi yanxu haka” Khaleesat taki tankasa tana murmushi ta fita daga parlon kawai, tana komawa part dinta ta ajiye sauran breakfast din a parlor, ta zauna kan carpet ta bude warmer din doyan ta dau biyu zata ci, tana son in ta gama ci ta tafi wajen Hadiyah su karasa maganar da suke don ita dai she wish za su ci gaba da rayuwa tare da Jay, bude kofar parlon aka yi ta daga kai duk tunaninta Hadiyar ce ta shigo, zaro ido tayi ta mike ganin Safiyyah, Safiyyah ta ajiye karamin box dinta ta tafi da sauri ta rungume Khaleesat not wanting to be emotional, da kyar tayi gathering courage tace “Alhamdulillah is all I have got to say kawata, Alhamdulillah” Khaleesat ta kasa ce mata komai lokaci daya hawaye suka ciko idonta. Tun da Ajay ya kai kansa bangaren Jay, Jay yaki barinsa ya koma part dinsa don kawai ya dinga managing health dinsa har zuwa ranan da za su tafi America which is in few days time, sai dai Khaleesat ta zo part din dubasa sannan ta kawo masa abinci, amma komai Jay ne ke yi masa, Safiyyah ma part din Jay din ta zo duba Ajay, sosai Ajay ke missing Khaleesat a kusa da shi, don in har ta zo kawo masa abinci sai ya rungumota jikinsa na wasu mintuna, ko yayi kissing dinta he is missing her soo badly, ita ma kewansa take yi don sai taji kamar kar ta tafi idan ta zo, kwanan Sophie biyu gidan tace ma Khaleesat zata koma Kano, Khaleesat tayi shiru tana kallonta, can ta sauke ajiyar zuciya tace “Plss ki bari jibi mana Sophie, daxu Mami tace min gobe za a kawo Aunty Faridah….” Safiyyah ta zaro ido tace “Da gaske don Allah?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Idan sun iso gobe, mu kuma jibi za mu tafi America, kin ga kawai sai mu tafi Airport gaba daya tare dake” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Toh zan kira Momy in gaya mata, don na riga nace mata gobe zan koma gida” Khaleesat tace “Yauwa kawata, wai Ya Musty fa? Naga tun da kika zo bai kira ki kamar yanda ya saba ba” Safiyyah tayi shiru, can ta taɓe baki tace “Uhum, ya kirani yace min uwar me? kawai don kina cikin naki damuwan ne yasa bana son kara maki da tawa kawata, amma for the past 2 weeks ai ina cikin jalala ne da tashin hankalin da ba a sa masa rana” a hankali Khaleesat tace “Me ya faru kawata?” Safiyyah tace “Wallahi banda ke kanki zaki ga ban kyauta ba ban zo taya ki farin cikin dawowar mijin ki ba ai da bazan ma zo garin nan ba saboda halin da nake ciki na bakin ciki da kunci” Cike da damuwa Khaleesat tace “Subhanallahi, what’s happening ki gaya min don Allah, dama ni tun da kika zo naga you are not lively kamar yanda na san ki, kuma da na tambaye ki kika ce min you are just recovering from sickness” Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Wai ni Ya musty zai kalla saboda rashin kunya yace zai aureni, ke kiji wani tashin hankali da masifa, wallahi kwana nayi ina kuka ranan, sannan abinda ya min bakin ciki da su Daddy da Momy suka goyi bayan hakan irin kamar sun san da maganar dama, ashe shi yasa duk saurayin da nayi sanda muke Maryland sai yace ɗan iska ne, haka yayi ta kora min samarina turawa, don Allah me zan yi da ya Mustapha mijin Surayyah, ashe dama algungumi ne ya Mustapha ban sani ba” Tana kai wa nan ta fara hawaye tana gogewa da hannunta, Khaleesat na son yin dariya amma saboda halin da taga Safiyyah ke ciki yasa ta danne dariyar tayi keeping serious face tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, shi ya Mustaphan? To ke sai kika ce masa me?” A fusace Safiyyah tace “Me kuwa zan ce masa, kawai sai mu shige daki mu kulle da shi a matsayin mata da miji, ya kwanta kan gado nima in kwanta, to ayi uban me? shi bai ji kunya ba don girman Allah, ko kuma uban me zan ci da sauran Surayyah?” Khaleesat ta kasa ci gaba da danne dariyar ta, Ta tuntsire da dariyar har da kyakyatawa….


