Hausa novels

Halysaah Page 180 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 180…Da sallama Khaleesat ta shigo parlon Mami tare da likitan ta bayan ta idar da sallahn Magrib, tayi ma Jay dake zaune parlon kallo daya sannan ta tafi ta zauna kasan carpet, likitan tayi masa barka da zama ya gyada mata kai kawai, ta nemi waje ita ma ta zauna, Daga kitchen Mami ta fito da fruits, Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “Ina yini Mami” Mami ta karaso parlon ta ajiye ma Jay fruits din sannan ta zauna tana kallon Khaleesat tace “Lafiya lau Halysaah, ashe baki zauna gidan Hajja ba daxu da ku ka je?” Khaleesat ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba tana wasa da hijab din jikinta, Dr tace “Barka da yamma ranki shi dade” Mami tace “Yauwa Dr….” Sannan ta maida dubanta kan Khaleesat tace “Halysaah kin hada kayan naki kuwa?” Khaleesat ta kalli likitan ta, Dr din tayi murmushi tace “Ranki shi dade ai tuni ta maida su cikin wardrobe tace she doesn’t feel like going….” Mami ta ɗan yi murmushi ita ma tace “To bari in kira Ammi sai ki gaya mata haka ko? Auren Inteesar guda ki ce baza ki ba Halysaah, Ammi ai bazata ji dadi ba, ita ma Inteesar din won’t be happy, nan ta zo tayi kusan wata daya gidan nan saboda ke kwanaki….” Khaleesat tayi shiru kuma bata dago kanta ba, Mami ta dau wayarta tayi dialing din number Ammi, tana dagawa tace “To Hajiya Ammi ga er taki kuyi magana….” daga haka ta mika ma Khaleesat wayar ta amsa ta kai kunne cikin sanyin murya ta gaida Ammi, Hadiyah ce ta shigo parlon da sallama ta nufi hanyar kitchen din Mami, Jay ya bi ta da kallon gefen ido ganin dressing din da tayi sai baza kamshi take, kitchen din ta shiga ya kalli Mami dake kallon Khaleesat da suke waya da Ammi, not long after Hadiyah ta fito daga kitchen din ta ajiye tray din hannunta me dauke da drinks da bottle water biyu sai bowl din fresh fruits, tana kallon Mami tace “Mami ina snacks din fa, naga basa kitchen din” Mami tace “Ki duba wancan dakin, daxu su Kilishi suka shigo naga za su cinye maki na kai dakin na ajiye” Hadiyah ta juya ta nufi dakin, bayan ta shiga cikin dakin Jay na kallon Mami yace “What are the snacks and fruits for?” Mami ta amshi wayar da Khaleesat ke mika mata tace “Ka tambayeta mana, ba ga ka gata ba” Jay bai sake cewa komai ba, Hadiyah ta fito daga dakin da foil plate babba dauke da different snacks da aka rufe da cling film, Hadiyah ta ajiye foil plate din kan table tana kallon Khaleesat tace “To ki rakani mu je Halysaah” Mami tace “Tashi ki rakata Halysaah” Mikewa Khaleesat tayi duk da mood dinta wasn’t good saboda wayar da suka yi da Ammi, har cikin ranta ta kasa yarda Abuja kawai za su tafi bikin Inteesar, gani take gida za a maidata daga Abujan, Khaleesat ta dau plate foil din, Mami na kallon Hadiyah tace “Ina za ku zauna?” Hadiyah tace “Parlon Hajja” Mami tace “Ohk” Daga haka ta dau tray din ta nufi kofa Jay ya bi ta da kallo har ta fita, Khaleesat na tafiya a hankali ta bi bayanta ita ma ta fita daga parlon, Jay ya kalli Mami yace “Me za ayi a parlon Hajjan?” Mami tace “Kai nima ban sani ba, ba a gabanka suka fita ba me ya hanaka tambaya” Shiru yayi bai sake cewa komai ba, after some minutes ya mike ko fruits din bai sha ba ya nufi kofa, Mami ta bi sa da wani kallo har ya fita daga parlon. Kan kujera Khaleesat ta zauna a parlon Hajja tana gaida Ibrahim Khalil which was also from a Royal home, ya amsa mata da fara’a yace “Ya kwana biyu Halysaah?” Khaleesat tace “Alhamdulillah” Yace “To ya jiki?” Ta ɗan yi murmushi tana wasa da fingers dinta tace “Lafiyata qlau yanxu” Yace “Alhamdulillah, haka muke so ai” Ta juya ta kalli Hadiyah tace “Zan tafi….” Hadiyah tace “Baza ki zauna ayi hira ba” Ta girgiza kai tace “Wajen Mai martaba zan je” Hadiyah tace “To a gaishesa” Mikewa Khaleesat tayi tana kallon Khalil tace “Tohm sai anjima” Yana murmushi yace “Nagode da gaisuwa Halysaah” Kofa ta nufa walking slowly ta fita daga parlon, Khalil ya kalli Hadiyah yace “Amma dai jikin nata da sauki yanxu?” Hadiyah ta ɗan yi murmushi tace “To Alhamdulillah za a ace, nasan bai wuce labarin mafarki zata je yi ma Mai martaba ba yanxu haka” Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace “Allah sarki, this shall pass in sha Allah, she will surely overcome it” Hadiyah tace “Hopefully” Yace “Amma kuma sai naga kamar therapy din isn’t working for her, kusan shekara biyu fa yanxu, i think it’s best a samu me irin predicament dinta a hadasu su dinga communicating sosai suna hira, let them be friends and discuss their situation together, i mean warce mijinta ita ma ya rasu, i assure you she will gradually start coming back to reality….” Hadiyah tayi shiru tana kallonsa, can tace “To zan gaya ma Mami haka” Yace “Allah Ubangiji ya yaye mata” Hadiyah tace “Ameen” Yace “To meye labari gimbiyata” Tana murmushi tace “Yana wajen ka kai da ka tafi business trip na kusan wata biyu ban gan ka ba, nayi missing dinka sosai….” Khaleesat na fita ta nufi part din Mai martaba, duk sanda take son zuwa part dinsa take zuwa kanta tsaye tunda Aunty bata kasar, he is always alone zaka samesa yanxu a part dinsa, sallama tayi ya amsa mata sannan ta shiga, yana zaune Main parlonsa ta samesa da fruits a gabansa amma ba sha yake ba don yayi nisa tunanin da yake yi, ya ɗan yi murmushi calmly yace “Jiddah, yau baki shigo da safe ba” Ta zauna inda ta saba zama ita ma tana murmushi tace “Mun je gidan Hajja ne” Yace “Ai Hajja tace kin ki zama da kuka je” Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers dinta, sai kuma ta gaishesa ya amsa yace “Ya jikin naki?” Ta daga kai ta kallesa tace “Ai naji sauki ranka shi dade, daxu ne dai yace in gaida masa kai” Sarki na gyada kai cikin sanyin murya yace “Ina amsawa Jiddah” Ta gyara zama tace “Kuma ya gaya min abinda za ayi masa idan zai dawo, kasan ya kusa dawowa…..” Mai martaba ya sauke idonsa a hankali yace “Ohk….” Cikin sanyin murya tace “To ranka shi dade baka tambayeni me yace za ayi masa ba?” Sallaman Jay yasa Sarki ya daga kai yana kallon bakin kofar sannan ya amsa masa, Jay ya shigo parlon walking slowly ya karasa ciki ya zauna sannan ya gaida Mai martaba da ladabi, Mai martaba ya amsa yace “Ya aiki Jawwad?” Jay ya sauke Idonsa yace “Alhamdulillah” Khaleesat tana kallon Sarki tace “Zan tafi ranka shi dade” Yace “To ki dawo anjima sai mu ci gaba da maganan ko?” Ɗan murmushi tayi alamar taji dadi tace “To zan dawo ranka shi dade” Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon zata tafi side din su Kilishi, Mai martaba ya kalli Jay ganin kamar da magana a bakinsa yace “Ya aka yi Jawwad?” Jay ya sauke idonsa yayi shiru, after some seconds yayi kasa da murya yace “Dama ranka shi dade na zo ne akan maganar Hadiyah” Sarki dai kallonsa kawai yake, Can yace “Ohk ina jin ka” Bai yarda ya dago kansa ba yace “I think i am now ready, zan maidata ko gobe” Mai martaba was just looking at him, don a kwanaki da aka yi masa maganar Khaleesat har ya gigice yace gwara kawai ya maida auren Hadiyah don shi babu aure tsakaninsa da matar ɗan uwansa, bayan few weeks Mai martaba yayi masa maganar Hadiyah don yana ganin idan da mace kusa da shi zai daina shan abubuwan da ya tsiri sha all of a sudden, amma Jay ya nuna bai ma san ya fada cewar zai maida wata Hadiyah ba, shi bai san sanda ya fada haka ba, ko kadan Mai martaba bai son tilastasa a lkcn shi yasa ya bar zancen bai kara tado sa ba, Hajja ma bata sake masa magana ba don ita ma duk wani abu da zai zama an turasasa Jay yanxu bata so, barin yanxu da ta rasa Ajay bata son komai ya samar mata Jay riritasa kawai take tana lallabasa kamar kwai, da kanta ma tace kar wanda ya kara yi masa maganar Hadiyah tunda baya so, Allah Ubangiji yayi ma Hadiyah zabi na alkhairi, Mami ma tayi masa magana kusan sau biyu duk yaki bata listening ears, and this was almost 5 months ago, Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace “To yanxu kun yi magana da Hadiyar ne Jawwad?” Jay ya girgiza kai yace “A’a, ba sai nayi magana da ita ba ranka shi dade” Mai martaba yace “Kana nufin kawai a maida auren without her knowledge?” Ya gyada kai, Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace “It’s not done that way Jawwad, dole sai ka sameta kun yi magana kun kara fahimtar juna da ita before the next step” Jay yayi shiru don baya jin zai iya, Mai martaba yace “Idan ku ka yi magana da ita sai ka dawo ka sanar min yanda ku ka yi, sannan sai in tuntubeta ita ma” Jay bai iya yace komai ba, after a while da kyar yayi ma Sarki sai da safe sannan ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon. That same day wajen karfe goma da rabi na dare Mami na zaune parlon Mai martaba bayan yayi kiranta, ta sauke ajiyar zuciya after listening to him attentively, cikin nutsuwa tace “Wallahi nayi farin ciki da wannan batu ranka shi dade, bazan ce i am not in support ba, kuma gaskiya bazan ce i am in support ba saboda Fulani, don kasan mu mata dole dai baza a rabamu da taya namu kishi ba, muna tare da Fulani Hafsat for more than 30 years a gidan nan da dadi babu dadi, kaga dai bazan ce lallai ayi mata haka ba, kuma bazan ce kar ayi ba…..” Tana murmushi ta kare maganar, sai kuma tace “Amma fa abu ne me matukar kyau da ace zai yiwu” Sarki dai kallonta kawai yake, can ya nisa yace “Fulani ai duk kame kame kike min a nan, you are not being straightforward, bazan ce maki na fahimci inda zancen ki ya dosa ba, da zuciyata kawai nayi wannan shawaran, sai ke yanxu da na zauna ina neman taki shawarar, ko Hajja bata san komai ba, kin ga kuwa ya kamata ace kin zama very straight, tunda ke na zaba inyi magana da before anyone” Mami dai bata fasa murmushin da take ba, ta gyara zama tace “Ranka shi dade, kamar yanda nace maka wannan batu ne me kyau wallahi, kuma nayi farin ciki da jin sa, sannan kaga zaman Khaleesat a gidan nan won’t look somehow again, don nasan ba kowa zai fahimci halin da yarinyar ke ciki idan ba zaunawa yayi da ita ba, gani kawai ake tana ta zama gidan nan tun bayan rasuwan mijinta shekara biyu kenan bata koma gaban iyayenta ba, sannan mu ma bamu ce ta koma ba alhalin ba ‘ya ya gareta tare da marigayi ba balle ace zaman da take kenan, gani za ayi abun babu tsari, and the question will be what is she still doing in the Emirate for 2 years now, don ni akwai warce ta min wannan maganar kawai dai nayi murmushi ban bata amsa ba, nan kuwa basu san taki zaman gidan nasu bane, mu kadai muka san halin da take ciki sai iyayen nata, shi yasa kwanaki nayi mata sha’awar auren Jawwad kaga da hakan ta kasance babu wanda zai yi querying zamanta a masarauta kuma, amma yanxu kaga idan akwai uwarta a gidan nan babu me cewa komai wallahi” Mai martaba ya gyada kai cikin gamsuwa yace “That is my thought too Fulani, nayi wannan tunanin few months ago, kawai dai zuciyata ce bata bani go ahead din furta batun nan ba sai a yanxu” Mami tace “Sannan bayan haka kai kanka kana bukatar kulawa yanxu ranka shi dade, bazai yiwu kana zaune for more than a year a haka kai kadai babu kowa kusa da kai even though an san lalura ne ya jawo hakan, i know you are still yet to recover fully from the death of Junaid, sannan ga zama kai kadai which is giving you enough space to think and ponder, shi yasa health dinka ke deteriorating now and then don ma kana da karfin hali, don haka nake ganin kayi abinda ya kamata kawai amma sai in Hajja ta yarje maka da yin hakan ranka shi dade” Mai martaba na jinjina kai yace “Shikenan Fulani, duk yanda ake ciki i will let you know first before anyone….” Tace “To Allah ya kara maka martaba ranka shi dade….” Sallama tayi masa daga haka ta mike ta fita daga parlon, Mai martaba ya jingina da kujeran da yake zaune yana kara nazarin maganar….

Back to top button