Hausa novels

Gargadar So Chapter 25 By M Shakur

Batason ta shiga gidan da force, she knows Ni’ima, ba hakanan zatabada sakon nan ba, she have to respect her home, layinsu ta wuce duka zuciyanta ba dadi harzuwa gida tundaga nesa da Baba yahango motanta yamike tsaye yana murmushi hankalinshi ya bala’in kwanta, tana parking ya hade fuska kaman bashi ke murmushi ba ganin tadawo, kashe motan Hawwa tayi tafito batare data kalli inda Baba yakeba dan yanzu saidai su dinga bura’uba da Baba amman bata auren mutumin nan wlh, Booth tabude tasauko da akwatinta kasa ta goya na baya tarufe motan ta gunguro jakan daidai tazo inda Baba yake batare data kalleshi ba murya ciki ciki irin na yaron dake fushi da iyayenshi din nan tace “Assalamu Alaykum Baba ina yini” dan kyafkyafta idanu Baba yayi yace “sannu uwar zuciya ladingo mai fada da mahaifinta, sannu da zuwa jeki huta ni da kene agidan nan” wucewa tayi abinta tana shiga gidan suka hada idanu da Umma data haderai ganinta kaman bakin ciki zai kasheta tadauke kai itama haka Hawwa tawuce tabude dakinta ta shiga da komi, kayan jikinta tarage tafito tai alwala takoma daki tai salla sannan ta kwanta akasan tadauki wayanta tashiga kiran Ni’ima koma menene they need to iron it out, tabama Ni’ima sama da 15missed call babu wanda tadaga, bala’in damun Hawwa abin yake, she’s confuse ma, basu taba kalan fadan nan ba itada Ni’ima, Ni’ima bata iya gaba ba nor shariya, toh wat is happening da Ni’ima is not talking to her? Whatsapp tashiga tashiga typing.“Best enough please, talk to me Dan girman Allah, I’ve been saying sorry amman kinki kulani, daman akwai abinda zanyi da u will not understand me? Baba ne yace nabarmai gidafa, I’m sorry ban sanar dake ba naje gidan Ammi, banson kice nazo wajenki ne kuyita dawainiya dani, naje hospital yau ina shigowa garin nan bakinan nazo gidanki i learned that u don’t wanna see me, I’m very very worried, Best I’m sorry, sorry, sorry” Hawwa tashiga tura mata sorry sunfi guda dari cus ta bala’in damu sabida Ni’ima is already part of her, this few days dabasuyi magana ba ko chatting she’s feeling kaman wani part of her is gone, duk uban sorry nan amman har 8 nadare Ni’ima bata bude chats din ba, ashe harda gidan Ammi kesa abin baiwani dameta ba amman yanzu data dawo nan ita kadai sai Hawwa tashiga bala’in damuwa, sai tunane tunane take, taba cracking what could make Ni’ima this angry? Bata taba kawo Baban Yaseer ba cus tadauka Ni’ima ta turoshi yabiyota hanya, tai tunani tai tunani duka amsan da brain dinta ke bata is takama tashiga hanya da daddare batare dataje wajen Ni’iman ba abinda yasa take fushi kenan, ko abinci bata nema ba tunda tashigo garin nan cus bamata da apatite na ci haka tai bacci da yunwa.Around 5 ta farka sabida aiki wayanta tadauka ta danna abinda tafara gani is text message from Ni’ima dasauri tawani zabura ta tashi ta zauna bacci nafita daga idanunta tabude message din da sauri.“Inada magana dake Hawwa, let’s meet a Dims Eatery by 4:30 na yamma today” harwani ijiyan zuciya Hawwa ta sauke tamata reply okay good morning, saikuma ta kalli time da Ni’ima ta tura mata sakon around 2nadare, Ni’ima datasani lokacin nan bacci take Allah sa she’s fine babu wani abu dake damunta, kokuma is Ni’ima sick? Shine take boyemata cus bataso ta damu? Or is she pregnant? Dan cute murmushi Hawwa tayi kadan tace “ai kinsha miya da yawa is good kiyi ciki ama su Yaseer kanni” ta ijiye wayan dan damuwanta yaragu sosai tafito taje tai wanka tai brush da alwala tadawo daki simple riga tasa tai salla tana kan dadduma har 7 sannan ta tashi tafara shiryawa.Riga da wando tasaka, navy blue wando ne palazo da riganta shima navy blue but mai designs na flowers daya saukanmata har cinya ta makala botura rigan yamata kyau cus ita tadinga da kanta zaka dauka wasu expensive kaya ne nan ko yadi ne tasayo a wajen yan material a kasuwa tadinka abinta, sky blue veil tadauka tai rolling tai pinning tasa links na hannun rigan masu shegen kyau tashafa lip gloss lips nata na shinning sosai, hada yan abubuwan datake bukata tayi a jakanta tadauka tasa cover shoe mai dan tsini kadan mai shegen kyau na zara, tasaka agogo tafesa turare tai wani kalan calm kyau kaman ka sace tana sassanyan feminine scent, tafito ta kulle kofa tana kamshi tayi waje, Baba baya waje maybe yana masallaci har yanzu, motanta tawuce tai warming ta chanza ruwa ta maida bonnet din tarufe sannan tashiga mota tabar anguwan saida tasha mai agidan mai sannan tawuce office by 8 tana ciki.Rannan sunsha aiki kan wasu victims da akai kidnapping sai around 4:20 sannan ta iya fitowa, salla tayi a mosque nasu da gudu gudu tawuce mota ta shiga taja tabar premises nasu tanama Ni’ima text tace “yanzu aka banni nafito I’m driving already you will see me nan da 20min” ijiye wayan tayi tana kallon hanya tana murmushi yau zasu shirya da Best, dadan holdup a hanya saida ta bata 30min around 5:00 takai resturant din tai parking, babban restaurant ne hadadde, Ni’ima na zaune asaman terrace dan wajen tabiya kudi tamusu booking, shiru tayi bata ko motsi kallon Hawwa takeyi dataga tana sauri sauri tafito daga mota sannan ta rufe kofan, kallonta Ni’ima take batako kyaftawa yau for the first time tana ganin some things da bata taba luradasu da ba, Hawwa nada kyau sosai tafita kyau sosai, bazama ka kwatanta ba, yanda take saurin nan her boobs are shaking haka jikinta ma, babu wani abu da Hawwa bata fita dashi ba, ga diri danma bata taba saka kayan da ake gane shape nata, Hawwa akwai boobs manya masu kyau a tsaye ga shape, itako nata sun soma kwantawa kai sunma kwanta yara biyu to sun sha yanbiyu wasa ne ba dole Baban Yaseer yace yanasonta ba, gata doguwa and naturally dogayen mata nada farin jini da grabbing attention da maza ko ita tana tareda Hawwa ansha complementing tsayin Hawwa maza na admiring hakan, gata da gashi ga dadin murya na fitina ga iya turenci ga iya magana ga natsuwa ga wayau with lot of maturity, bazaka taba kama Hawwa na murmushi anyhow ba ako’ina dan tafi Hawwa fara’a sosai, gata da ilimi, ga Allah yamata gata she’s so bright and she’s a lucky mutum, imagine she’s no body but Allah supported her tasa kanta a makaranta da kudin dinki, tana fara aikin police akai promoting nata sabida sunga how intelligent and smart she’s ba dole Baban Yaseer yasota ba, Hawwa tahadu in every aspect wlh boko da islamiyya ga wayau ga hankali ga jarumta ga hazaka, ga addini yawan salla da azumi kai ga komima, idan Hawwa tasami miji kowaye yanzu saita kamashi with her charming and seductive nature, kai ko ayawan addu’a da salla sai Hawwa ta kwacemata Baban Yaseer, banda haka Hawwa zatai everything possible not to live marriage idan tai aure dan tadade bataiba, how can she allow Baban Yaseer ya aureta? Bayan tasan Hawwa tafita komi cus tafi kowa sannin qualities na Hawwa, Hawwa is desperate for a Man idan tai grabbing Baban Yaseer ai tata takade, kwace mata miji zatayi ya manta dasu, gatada karfin sha’awa Aliyu yasami haka ai shikenan kuma takade tana cikin tunane tunanen nan taji ringing a wayanta firgigit ta farga daga tunanin ganin Hawwa ke kiranta yasa ta katse wayan tamata text kizo terrace ina sama.Tana zaune awajen Hawwa ta shigo bayan an bude mata kofan shigowa terrace din hada ido tayi da Ni’ima data kafeta da idanu tana zaune kan kujera tana sanye da black abaya saitaga Ni’iman ma dukta rame tai wani iri kaman mara lafiya, dawani sauri tai wajen jakanta ta ijiye kan table da wayanta kai tsaye tai hugging Ni’ima tace “Besttttt” ijiyan zuciya Hawwa ta sauke kusan 2min amman Ni’ima batasa hannunta tai hugging nata back ba, sakinta ahankali Hawwa tayi takalli fuskanta tace “are you sick? Face naki gabaki daya ya chanza, what is wrong with you?” Dan gajeren murmushi Ni’ima tamata ta nuna mata kujera tace “sit please” dan jimmm Hawwa tayi tana kallonta kafin tawuce tazauna kan kujeran, Ni’ima tadan kalleta dan hakanan bamatason tana kallon Hawwan yanzu cus is making her feel insecure and so little tace “mezakici order?” Girgiza mata kai Hawwa tayi tace “kin manta yau Monday ina azumi” gyadamata kai Ni’ima tayi batace komiba tana kallon gefe, wani iri Hawwa taji tanaji ganin yanda Ni’ima is acting wired ko kallonta ma batason yi kaman ta tsaneta, no let them iron koma menene she hates fight, ahankali tace “Ni’ima wat is wrong? Dan Allah kifadamin? Why don’t you want to look at me? Fushi kike dani”? Dago kanta Ni’ima tayi takalli Hawwa adake tace “Hauwa’u!” Faduwa gaban Hawwa yayi dan yau ne rana na farko da Ni’ima zata kira sunanta haka amman tadaure tace “na’am Best” murmushi Ni’ima tayi wanda is so obvious you can see how hurt she’s, da kyar take murmushin ma tana kallon Hawwa ido cikin ido tace “Baban Yaseer na sonki Hawwa!” Dooom!!! Haka Hawwa taji gabanta yabuga, still cikin karfin hali Ni’ima tace “nasan bai sanar dake ba saisa ni nake sanar dake, inaso na tayashi tambayanki hand naki in marriage” tai dan shiru takara murmushin da da kyar take murmusashi tace “zaki aure Baban Yaseer Hawwa!?”.

Back to top button