Fentin Zina Page 8 Hausa Novel
🙅♀️FENTIN ZIN🅰️🙆♀️🙅♀️EESHERT ADAMUPAGE 8.*******Mamakinta yakeyi meyasa take zubar da hawaye akan wannan karamin abun sai bai kulata ba ya hau ya kwanta yaja bargo ya rufe jikinshi ya juya mata baya.Kasa tsaida hawayenta tayi tana jin wani irin tsana da bata taba tsammanin zata mishi irin shi ba tana maganganu a zuciyarta tana cewa, wannan ma ai zalunci ne ta yaya yana mijinta ya kasa sauke nauyin hakkin mu’amala ta aure akanta amma idanunsa suna hango masa wata macen zuciyarsa suna kwadaita masa karin aure, ko a tsarin addini shi ba na mijin da zai iya auren mace biyu bane tunda ita kadai ma tafi karfin shi.Ta sauke ajiyar zuciya ta share hawayenta ta kira sunan shi, ruhul jasad dan Allah ka bani damar muyi magana ina so mu tattauna.Bai tashi ba sannan bai juyo ba yace ina jinki.Batayi fushi ta fasa maganar ba don tafi ganin dacewar su yita yanzu, tace da farko zan soma da baka hakuri koda na aikata wani laifi a gareka da yasa kake hukunta ni da dabi’unka ina rokon afuwa ka gafarceni sannan magana ta mu’amalar aure ita tafi damu na yanzu ka duba ka gani kai ka biya bukatar ka ni ka barni dan Allah ya kake so inyi kuma kasan cewar a tsarin halitta ni macece mai yawan sha’awa yanzu idan har kai baka biya mun bukatata ba wa kake so inje mawa wa kake so yazo ya biya mun? Ka sani mata a wannan zamanin ba kowacce keda karfin imanin zama da irin wannan lalura alhalin mijinta baya iya biya mata bukata bata fita taje ta nemawa kanta mafita ba, nayi imanin cewa bazan aikata wani abu makamancin haka ba amma ina rokonka daka duba dai da kyau gashi yanzu aure zakayi bansan kuma ya zata kaya ba dan Allah ka taimakeni wallahi marana kamar zai fashe saboda bukatuwa da bukatar in fitar da wannan abun kada ya zamemun cuta.Sauran maganar makalewa yayi sakamakon tashi dayayi da wani irin karfi ya nunata da yatsa yace kinga ki fita a idona in rufe, saboda zanyi aure duk sai kibi ki daga hankalin ki ki daga nawa? Toh da sakel bazan lamunta ba kada ki kuskura kice zaki kawo mun shirme, saboda ni lusari ne sai in tsaya inta biye miki ina karar da ruwan jikina domin kiji dadi ko? Kike fadin ina zaki kai butar ki, toh ki kai duk inda kike so daman ai kin saba don kinyi yanzu ba abun mamaki bane sai kiyi tayi na kusa maganin ki duk abunda kike takamar ji dashi.Kuka takeyi kasa-kasa ta dago jajayen idanunta ta dube shi cikin rawar murya tace, kayi hakuri ba nufina kenan ba kuma dan Allah kai miji nane ka daina jifana da mummunar kalmar zina dinnan bana jin dadi.Karya kenan nayi miki? Nace karya na miki ne? Ba kiyi zinar ba zance kinyi ne, ai ko yanzu nasan kika samu dama zaki aikata zinar tunda baki iya jure bukata.Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Allah na tuba ka yafe mun, da gudu ta bar dakin bayan ta fadi hakan.Tabe baki yayi ya koma ya kwanta yana huci yace zanyi maganin iskancin kine jarababbiyar kawai.Washe gari fateema tazo da wuri tun bakwai tayiwa inna sallama ta fito ta tari adidaita daidai kofar gidan Ameena aka ajiyeta ta biya kudi ta sauka zata shiga gidan kenan wata mota data parka a bayanta baka mai kyau kalar ta masu hannu da shuni wani saurayi ne ya fito daga cikin motar yayi sallama.Daga indatake taji shi sai ta amsa sallamar tasa kai zata shiga.Yayi saurin rufe kofar motar ya karaso kusa da ita yana cewa, haba malama kiyi hakuri ki gafarce ni bisa tsaidake da nayi ba bisa ka’ida ta shari’ah ba, zanso ki bani number wayarki saboda yanzu sauri nake asibiti ma zana je na ganki toh gudun kada ganinki ya bace mun yasa na biyo ki har nan, kiyi wa Allah kada ki hana ni.Kamar bazata ce komai ba sai kuma ta tuna idan tsautsayi ya kawo Abdul ya ganta tsaye da saurayi a kofar gidan shi Addanta ta shiga uku karshenta ma yace gurinta yazo don ba kirki ne dashi ba, don haka tace kayi hakuri dan Allah kada ka dauka na wulakanta ka ka mun uzuri sai anjima, ta shige gidan da sauri donma kada ya kara jan maganar.Baiji dadi ba kuma ba don yaso ba ya wuce ya shiga motar shi yaja ya bar gurin amma kasan zuciyar shi yasan dole zai dawo ya neme ta.Bata zauna ba data shiga bayan sun gaisa tace Adda mu fara aikin yanzu.Cikin lokaci kankani suka fito da duka kayakin dakin ya rage babu komai a ciki da yake dama kayanta ne daga gida aka mata su sai tasa fateema ta nemo mai motar da zai dauki kayan ya mayar can gidan inna a saka mata su cikin dakin da babu kowa.Haka kuwa akayi aka kwashe kayan aka mayar can ta dawo ta tayata suka kalmasa gidan ya koma kamar ba’ayi komai ba duka duka a lokacin karfe daya da rabi ne, giki Ameena ta daura kafin la’asar ta gama tuwon shinkafa miyar ganye ta zubo musu suka koma dakinta suka fara ci kenan karar knocking din kofa ya iso garesu ga hayaniyar mutane daya cika harabar gidan da alama suna da yawa wadanda suka zo yin jeren.Fateema jeki bude idan sun tambayeni kice na fita domin bana so wata mu’amala ta hada mu a yanzu gaskiya.Fita tayi ta bude suka shigo suna kare ma falon kallo suna dan yatsina fuska sai guda daya daga cikinsu ce tace sannu fa mun tasoki an yini lafiya.Lafiya kalau amma ba nice matar gidan ba ta dan fita ne amma ga dakin can da zaku saka kayan nata sannan ga madafin ta ma can kusa da dakin nata.Allah sarki toh mun gode ai babu komai ma.Fateema bata kara cewa wani abuba ta wuce ta koma daki, tana shiga ta rufe tasa makulli ta zauna kusa da Ameena tace Adda Allah dai ya cece ki daga sharrin wadannan mutanen kinko gansu sam babu alamun sun san wani abu waishi tarbiyya sai guda daya ce dama dama a cikin su.Girgiza kai Ameena tayi tace Allah ya kyauta amma ba lallai ita din ta kasance haka ba kada mu yanke mata hukunci cikin rashin sani.Hum ameen dai.Haka suka gama jera kayan dayar da tayi wa fateema magana ita tazo bakin kofar ta buga lokacin da zasu tafi.Fateema ta bude ta fita tace har kun gama kenan?.Eh Mun gama sai munzo kawo amarya kuma dama zamu tafine nace barin fada miki idan mai gidan ta dawo ki fada mata mu kulle ma dakin mun tafi da makullin.Toh shikenan babu damuwa zan fada mata.Saida suka fita ta rufe falon ta koma ciki ta samu Ameena tace Adda ni kam zan tafi sai Allah ya kaimu gobe zamu dawo tare da mama idan ta iso.Toh nagode fateema Allah ya saka da alkhairi ki gaida inna da baba malam.Kai Adda banda shureim?Kinji ki kema da wata magana har dashi mana gama wannan ki kai masa duk da nasan wancan basu kare ba, ta fada tana jan drawer din mirror ta Ciro sweets da biscuits tasa a leda da dan yawa ta mika mata ta mata rakiya har gurin kofa amma bata yadda ta leka ba suka rabu a nan din.Gidan inna da fateema ta koma bayan sunyi sallar isha’i ta dubi inna tace, inna ki sa lamarin Adda na auren mijinta cikin addu’ah sosai domin addu’ahr kice zata fi yin tasiri akanta fiyeda ta kowa.Gyara zama inna tayi ta fuskanceta, hala wani abu kika ga ya faru?.A’a inna kawai mutanen da sukazo yin jere yaune kallo daya zaki musu kisan cewa gidan su babu tarbiyya sai yatsina sukeyi suna bin ko ina da kallon kaskanci ban yarda dasu ba har cikin zuciyata Allah dai ya kare ta daga duk wani abun ki.Ku kwantar da hankalinki duk mutum mai imani yasan cewa komai mukaddarine daga ubangiji Allah ya kiyaye.Daga haka sukayi shiru dukkansu.Rana Bata karya a yau aka daura auren Abdul da amaryarsa Maryam baki yaki rufuwa kamar gonar auduga.Bayan isha aka tafi dauko amarya inda saida aka dan yi hayaniya sakamakon ‘yan uwan amarya sunce sai an biya zasu saka ta a mota ‘yan uwan ango sunce basu san da wannan ba har ya jawo cece kuce sai wani daga cikin abokan shine ya zame ya kira shi ya fada mai meke faruwa yace su basu abunda suka ce kawai a wuce wajen.Sai kuwa da aka basu sannan aka sanya amarya a mota suka ja sai gidan angonta Abdul.Ameena tana jin karan motocin ta shiga bayi tayi kukanta ma ishi dakyar ta lallashi kanta tayi shiru ta wanko fuskanta ta goggoge ta fito.Mama rabi ta kalleta cike da kulawa tace kiyi hakuri Ameenatu ki bar damuwa Allah yana tare dake hakika kishi yana da zafi yana da ciwo amma kadan daga cikin mune muke iya dannewa mu kawar dashi daga wanzuwa a fuskokin mu kiyi kokarin dannewa ki daure ki ari juriya da hakuri kada ki canja daga yadda muka sanki ki lazumci karatun Qur’ani zaki samu sassaucin abunda kike ji, yanzu ki saki ranki kada ki nuna alamun kina jin babu dadi kada ki bada wata kofa da za’a yi miki ba’a idan kikayi haka ni kaina zan tafi ina mai jin natsuwa a raina bazaki sakani damuwa ba.Insha Allah mama rabi zanyi yadda kika ce.’Yan kawo amarya har aka maidasu basu kawo amarya sun bada amanarta ga uwargida ba kamar yadda wasu keyi, haka suma su mama rabi suka tattara nasu ya nasu suka mata sallama da karin nasihohi suka wuce.Can da misalin karfe sha daya ya shigo shi kadai babu rakiyar kowa don har yanzu basu shirya da Anas ba tun wancan fadan da sukayi, dakin Ameena ya fara shiga ya tarar tana bacci ya ajiye ledar daya riko guda daya ya fita da dayar.Yana fita ta bude idonta don dama ba bacci take yiba bata sone dai wata magana ta hada su.Koda ya shiga dakin Amarya wani murmushi ya buga na jin dadin cikar burin ahi ya taka ya zauna a gefen gadon ita kuma ta yaye mayafin dake rude a kanta tana jefa masa murmushi.Amarya bakya laifi koda kin kashe dan masu gida, ya fada yana washe baki.

