Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 3 Complete Hausa Novel

A guje Muslim yai kan Abdul da shima firgicin maganar da su ka ji ta saka shi kudindi newa akan gado

Wani razanannan ihun suka saki a kusan tare, 

Muslim da ya fi Abdul ruɗewa faɗi yake

“Innalillahi wa’innailaihirraji’un!!!!! wallahi tallahi ban san da gaske yake ba, amma yanzu na tabbatar akwai ku

dan son ku da manzon Allah kuyi haƙuri shi kaɗai ne abin burgewa, ni da nake fama da uban ranƙwalelen kai bani da abun burgewa ko kaɗan”

Ruɗu iya ruɗu sun shige shi, duk ayar da muslim ya ɗakko be ƙarasa ta se ya kamo wata, 

Gaba ɗaya ya gama fitsare wandon jeans ɗin dake jikin shi 

da farko kusan a tare suka shiga ruɗun shi da Abdul, amma tun da Abdul ya fara jin sarewar nan na tashi a hankali ya manta da duk wani tashin hankalin da yake a ciki, 

se ma lumshe idanu da yai ya koma ya kwanta yana ƙara shiga wani shauƙi me wahalar fassarawa

Muslim kaɗai ke a ƙanƙame waje ɗaya yana sambatun tsoro.

Abdul ya ɗauki wajen minti goma yana jin sarewar nan, kafin daga bisani yaji ta ɗauke ɗif

A hankali cikin kwanciyar rai Abdul ya buɗe idon shi 

Karaf idanun nashi suka sauka akan muslim dake manne da jikin fridge ɗin ɗakin 

Ya haɗa uban zufa sharkaf anjikin shi, ga hawaye ga majina ga kuma fitsari da ya jiƙa mishi jiki sharkaf.

Da sauri Abdul ya sakko daga kan gadon ya matso kusa da muslim dake raɓe kamar wanda ze shige cikin bango

Dafa shi yai, kafin Abdul yace komi muslim ya kurma ihu ya ƙara ƙanƙame jikin shi da ke rawa ta ko’ina, faɗi yake 

“Dan Allah kuyi haƙuri tsautsayi ne kawai ya kawo ni gidan nan ba wai dan nai arangama da ku ba”

Girgiza shi Abdul yayi da ƙarfi yace

“meye kake yi haka guy?, lafiyar ka kuwa? wasu irin maganganu kake yi wai”

Da sauri muslim ya ja baya har yana ƙume ƙeyar shi da bango,

 wur-wurga idanun shi yayi lungu da saƙo na ɗakin, 

Seda ya tabbatar da lallai bega komi ba se  Abdul dake tsugunne gaban shi yana kwasar dariya, Sannan ya tashi

tsiyace ya bangaje Abdul yai waje da gudu

Biyo shi Abdul yai shima, duk da dariyar dake cin Abdul hakan be hanashi bin shi ba yana ƙoƙarin riƙe shi

Kafin Abdul ya fito compound ɗin gidan muslim yayi nisa, 

ko da Abdul ya leƙa caan nesa ya hango muslim yana ta zabga uban gudu bisa hanya ko waiwaye baya yi

Tsabar ruɗu da tashin hankalin da ya shiga

Anan ya bar motar shi da duk wani abu da ya shigo da shi ɗazu.

*******

“Mama dan Allah ki bani nera hamsin in siyo masu madara, kar yunwa ta hallaka min su”

Banza mamar tayi da zainab taci gaba da kaye-kayen kwanukan wanke-wanken da zainab ɗin ta gama ba ta kwashe ba

Matsowa zainab tayi kusa da maman sosai  ta ƙara saukar da muryar ta ƙasa tace

“Mama, yarda fa nake ƴar gidan nan suma fa haka suke, tunda Allah yasa an haifo su anan haƙuri zaki ki tallafa mana daga ni har su hajiya mama ta”

Banza mamar ta ƙara yi da ita, tai gaba abun ta

Zainab bata haƙura ba, haka ta ƙara bin mama har cikin ɗaki ta marairaice fuska tace

“Dan darajar annabi muhammadu mama ki bani”

A ƙule Mama tace

“Ni bazan ɓata kuɗi na ba na gaya miki, tun farko seda nace miki ki amshi muzuru ba mage ba, amma kikai kunnen uwar shegu da ni kika karɓi mace, 

To ni bazan iya dashin da ba kwasa zan rinƙa yi ba

Kuma nonon dake jikin ita magen miye amfanin su?”

Marairaicewa Zainab ta ƙara yi kamar warce zata fasa ihu tace

“yanzu ita magen tana da nonon da zata shayar da su har ya ishe su mama?

guda fa biyar ta sumɓulo min”

Takaicin Zainab yasa mama ta bar mata ɗakin ta fito tsakar gida

Ba dai ta haƙura ba, ta ƙara biyo ta tana ci gaba da magiya

Da dai magiyar Zainab ta ishi mama ta ɗauki ɗari biyu ta wurga ma tace 

“in mayya ce ke kika kama mutum ya shiga uku wallahi, gashi nan ki bar ni naji iskar gari”

Da gudu zainab ta rungume mama bayan ta damƙe ɗari biyun ta tace

“Allah ya temake ki uwata maganin kuka na”

Murmushi mama tai, tana ƙara jin son ƴar’autan ta a cikin ranta

Da kanta ta ɗauki hijabin ta zuwa siyo wa magunan ta madara,

Seda ta leƙa su ta ƙara ganin lafiyar su kafin ta fita

Kamar ko yaushe, a nutse take tafiyar ta kanta a ƙasa, in kika ga fuskar ta ba zaki taɓa cewa shirmammar zainab ɗin nan bace, ta wani tsare gida irin ba wargin nan.

Da taje shagon ta samu sun kawo madara ƴar aune, aikuwa batai ƙasa a gwiwar siya ba, gaba ɗaya ta ɗari biyun ta siyo, yarda zasu kwana biyu suna sha kafin tai farautar wasu kuɗin daga wajen mama

Tunda ta siya take Allah-Allah ta koma gida ta ɗanɗana madarar, wannan karon da ɗan sauri take tafiya ba kamar ɗazu da take tafiyar ganin dama ba.

*********

Tunda Muslim ya isa gida zazzaɓi me zafin gaske ya rufe shi, gashi yaƙi kwanciya a ɗakin shi, sedai ɗakin maman shi ya tare, ko kaya da ze canza sedai ya aika su Nasma suka je ɗakin shi suka ɗakko mishi, gaba ɗaya mamar shi ta kasa gane kan shi, tambayar duniyar nan tai mishi sedai yace

“Bar maganar kawai mama, kuyi ta tofa min ayatul kursiyu, ƙila in samu nutsuwar rai”

Da sauri ɗaya daga cikin ƙannan shi ta kawo mishi wayar shi da ake ta fama kira tun ɗazu

Miƙa mishi wayar tayi, yana ƙarɓar wayar ya kalli me kiran na shi, yaga an rubuta “GURU”

A tsorace yai jifa da wayar kan gado yana zazzaro idanu waje, 

Da mamaki maman shi ke kallon shi, ba dai tace mishi komi ba ta raɓa ta gefen shi ta ɗauki wayar a dai-dai Abdul ya sake danno wani kiran

Miƙa mishi wayar ta sake yi tace “Abdul ne fa ke kiran ka, ka amsa shi ko injection ɗin zazzaɓin nan ya zo yai maka ƙila ka samu kayi bacci me daɗi ka dena wannan zabure-zaburen da kake”

Ido waje muslim ya kalli maman shi, kan kace me jikin shi ya ɗau kyarma haƙoran shi na haɗuwa da juna

Rawar sanyi sosai muslim ke yi, abun gaba ɗaya ya ɗaure ma ƴan gidan su kai,haka dai suka tsaya akan shi, ko wayar da Abdul ke ta antayo mishi sedai mama ta ɗauka sukai magana.

Anan mamar ke gaya ma Abdul ɗin “tun da ya dawo aiki muka kasa gane kan shi wallahi, gaba ɗaya ya rikice kamar wanda yai gamo da mummunan abu, ga jikin shi da gaba ɗaya zazzaɓin yaƙi sauka”

Shiru Abdul yayi yana sauraran maman muslim, can dai data gama magana ya nisa a hankali yace

“Bari inzo se in duba shi mama, Allah ya sawaƙe”

Koda Abdul ya isa gidan dan ya duba shi, gaba ɗaya ƙarasa rikicewa Muslim yayi, kamar wanda ze baƙunci lahira a lokacin

Seda ta kaisu ga allurar bacci sannan aka samu sauƙin tashin hankalin

Miƙa ma maman key da sauran tarkacen da  muslim ya baro a wajen shi yai, sannan yai musu sallama da niyar in ya farka a kira shi.

A ƙafa ya tako tun daga gidan su muslim, memakon ya miƙo hanyar da zata kai shi gida kai tsaye,

 waske wa yayi yabi ta layin gidan Fulani, yana tafe yana tuna dramar da aka kwasa da muslim, murmushin fuskar shi yaƙi barin shi

Wani abun gunin ban dariya, wani kuma gunin ban tausayi.

Yana tafe kanshi a ƙasa ita ma ta tawo kan ta a ƙasa, tana ta zuba uban sauri ta kai gida ta samu ta shayar da ƴan magunan ta

Ba wanda ya ankare da ɗan’uwan sa, ta tawo ya tawo, suka bangaji juna, kafaɗarta ta bangaji damtsen hannun shi, seda ya riƙe hannun yace “ouch!”

Kusan a tare suka kalli juna kowa na ja da baya, 

Ido waje Zainab ke kallon Abdul, ta kalle shi ta kalli madarar da ta faɗi daga hannunta ta fashe

Yarda take kallon shi haka shima yake kallon ta

Kan kace me idon zainab ya cika da ƙwalla har sun fara sakkowa kumatun ta

Da mamaki Abdul ke kallon fuskar ta, ƙara buɗe idon shi ya yi da kyau yana  kallon budurwa santaleliya a gaban shi kuma wai tana kuka dan tayi ɓari

Be ce uffan ba itama batace ba, kuma kowa a cikin su ya kasa tafia

Yarda ta kafe shi da idanu se ya ga kamar tana hararar shi ne ma

gefen jikin wani pole dake kusa da su ya ja ya tsaya ya jin gina da shi

Folding hannun shi yayi yana ci gaba da kallon ta

Can dai da zainab ta kasa riƙe kukan ta, tunowa da magunan ta da tayi da kuma yarda akai har aka bata ɗari biyun da kyar yasa tace

“wallahi se ka biyani madara ta, wannan ai zalinci ne”

Seda Abdul ya furta mashaAllah jin sautin muryar ta, kuma daga haka be ƙara cewa uffan ba

Kamar wanda ake ja, haka yaji an fara janshi daga inda yake a tsayen nan, be yi musu ba shima ya fara tafiya a hankali, baki sake Zainab ta bishi da ido tana kallo, be wuce taku goma Abdul yayi ba ya tsaya cak sannan ya jiyo inda take tsaye tana kallon shi

Hannun shi ya saka a aljihun shi ya ciro dubu ɗaya sabuwa dal ya miƙa mata

Ƙin ƙarɓa tayi, bata dena kallon shi ba, kuma hawayen ta basu dena zuba ba

Da dai Abdul yaji tabbas jan shi ake daka wajen ta, kuma gashi taƙi karɓan kuɗin

 matsowa yayi daf da ita, bayan ya naɗe kuɗin, se ya tura mata a cikin hijabin ta tawajen saman kanta inda hular hijabin ta ɗan ɗaga kaɗan, sannan ya juya yaci gaba da tafiya ko waiwayen ta be sake yi ba.

Baki sake, hanci buɗe Zainab ke kallon Abdul ko ƙyaftawa bata yi, seda ta dena hango shi tukun ta kauda idon ta daga kallon hanya ta maida a kan madarar ta da ke yashe a cikin ƙasa

Waiwaigawa Zainab tayi, seda ta tabbatar da ba kowa tukun ta tsugunna ta damƙi madarar warce bata haɗe da ƙasar ba ta hambaɗa a bakin ta, sannan ta kakkaɓe hannu da bakinta ta tashi tsaye, tace

“Ba zan iya kallon kin haɗe da ƙasa gaba ɗayan ki ba, ko banza dai na ɗanɗana”

A nan inda take a tsayen ta saka hannun ta a saman kanta ta zaro dubun da Abdul ya saka mata

Warware ta tayi tas ta zuba mata idanu tana ƙara hasko fuskar Abdul, 

A hankali ta tace

“Ƙila kurma ne”

Taɓe baki tayi ta ƙara cewa

“Allah ya temake ni ya fanshe min asarata, da duk bala’ina nasan mama ba zata ƙara min wasu kuɗin ba”

Takanas ta ƙara komawa shagon da ta siyo madarar

A memakon ta siyo ta ɗari biyun, aikuwa tace a bata na dubun gaba ɗaya

Aikuwa jim aka zubomata na iya kuɗin ta, ta kamo hanyar komawa gida

Tana tafe tana tunanin yarda zasu kwaso ta da mama in taga yawan madarar,

 a ɗaya ɓangaren kuma tana ganin ai madarar ɗari biyu ya zubar mata, kuma ga shi ya bata dubu, taɓe baki ta ƙara yi tukun tace

“yayi sadaƙa, daɗin abun ma ai ba ni zan sha ba, Allah ka bashi lada na dai-dai sauran kuɗin shi, ni ba abun nace zan aje mishi ba kuma ba lale mu sake haɗuwa ba”

Haka dai taita zancen zuci har ta kai gida

Tana shiga ƙaton soron gidan su inda anan mafi lokuta da dama Abie ke ba ɗaliban shi karatu, ta saƙe ledar madarar a cikin hijabin ta, 

Saɗaf-saɗaf ta shige cikin gidan tana baza idanu, 

Seda ta lelleƙa ta tabbatar da ba motsin  mama tukun tai wuf ta shige ɗakin ta, 

Da sauri ta samu wata ledar ta ɗibi madarar sannan ta ɗaga ƙasan kayan ta ta tura sauran a ciki, ta maida ta rufe.

Ɗakko warce ta ɗiba ɗin tayi ta fito tsakar gidan nasu bayan ta cire hijabin jikin ta,

 cikin wanke-wanken da ta yi ɗazu ta duba ta ɗauki kofi da cokali, zuba madarar tayi bayan ta afa kusan cokali biyu bakin ta, sannan ta zuba ruwa ta dama

Da ɗan kauri-kauri ta dama madarar,

Ɗakin ta tashiga inda anan ne ta aje magen da ƴaƴan ta,

Da ƙyar ta samu ta binciko inda ta ajr sirinjin ta,

ajiye me kyau,tai mishi tun ranar da ta gane magen nata na da ciki, a cewarta amfanin shi ya kusan zuwa.

Ɗaya bayan ɗaya ta shayar da magunan ta, tana yi tana musu magana kamar wasu mutane.

Kaf magunan farare ne, ɗaya ce kawai ɓaƙa, ɓaƙa wuluk kuwa

Seda Zainab ta gama shayar da fararen tas, tukun ta jawo baƙar ta fara ba, tana bata tana ƙorafi

“Ni bansan in da uwarku taje ta samo min wannan ɓaƙar ba, yanzu haka da ubanta take kama,”

Leƙowa ɗakin mama tai jin surutun zainab ita ɗaya a ɗaki, tace

“Ohh ni Binta, wai yanzu magunan kika tasa a gaba kina magana da su zainab?”

Dariya zainab tayi tace

“Dole nai magana ai mama, ni bansan inda taje ta kwaso wannan baƙar ba, duba ki ga sauran duk farare sun biyo uwarsu, shine nace kila ɓakar da babanta take kama”

Taɓe baki mama tayi, anan na gane Zainab a wajen mama ta koyi taɓe baki itama.

Maman tace “to kin basu madarar?”

“eh mama, gashi har sun koma bacci, dama ance jarirai akwai su da bacci” tai maganar ko a jikin ta

Karkaɗa kai mama tayi, tace “jariran mutane bana mage ba ko?”

Zainab tace

“ai duk ɗaya suke mama”

Maman  bata ƙara cewa komi ba ta juya ta fita a ɗakin.

Tunda Abdul ya tafi yake son ya ƙara waiwayen ta koda so ɗaya ne, 

ɗan kwatanta juyawar da yayi yaji kamar wuyan shi ze karye, haka nan ya haƙura yaci gaba da tafiyar shi ba dan ranshi ya so ba, 

yayi tsaki kamar harshen shi ze tsinke dan takaici.

Washe gari da yamma Abdul ya ƙara zuwa duba jikin Muslim da ba laifi jikin yayi mishi sauƙi

Amma in ya tuna abunda ya faru yakan shiga ɗan ruɗani, ba dai kamar na ranar ba, kuma ikon Allah ya kasa yin maganar da kowa, har sun gaji da tambaya sun haƙura.

Koda Abdul ya shiga gidan, ɗakin muslim ya fara zuwa amma ya taras da shi a rufe,

Waigawar da ze yi yaga Nasma tsaye ta na shanya,

Kamar baze kulata ba, har ya juya ze fita daga wajen, ya dai daure yace

“ehn, Muslim fa?”

Murna Nasma ta hau yi a cikin ranta, wai yau ita Abdul ke tambaya

Seda Nasma ta wani lanƙwasa murya sannan tace “yana ɗakin mama tun jiya ai”

Be sake kallon ta ba ya juya ya shiga cikin gidan

Da sauri Nasma ta ƙarasa shanyar ta, itama tai cikin gidan da sauri, a cewar ta dama ce babba ta samu na yarda zata shige ma Abdul ɗin.

Muslim najin muryar Abdul daga palour suna gaisawa da mama yai luf a gado kamar me bacci, ƙirjin shi na ta dukan uku-uku, 

gaba ɗaya muslim ya gama tsorata da lamarin Abdul.

Bayan Abdul sun gama gaisawa da mama tace “ka shiga yana nan kwance, ko palour yaƙi fitowa, amma dai jikin ba kamar jiya ba”

Murmushi Abdul yayi tukun ya nufi ɗakin da akace muslim ɗin na ciki

Ya daɗe a tsaye yana kallon muslim da ke baccin ƙarya,

Tunda Abdul yaga yarda idon muslim ɗin ke mar-mar ya gane ba bacci yake ba.

Hannu yasa ya make shi a ƙafa yace

“Guy na san idon ka biyu fa, 

naga alamun guduna kake tun jiya, ka tashi magana nazo miyi da kai”

Ba dan Muslim ya so ba ya tashi zaune yana murza idanu kanshi a ƙasa ya kasa kallon Abdul ɗin

Murya na rawa muslim ya fara magana yace “Dan Allah guru kai shiru, naji na kuma gane duk wata magana da zakayi, ni dai yanzu tsakani na da kai girmamawa ce kawai ta rage, amma ba sauran musu ko sa’insa” 

Ya ƙarashe  maganar yana haɗe hannayen sa biyu, alamun roƙo.

Sosai yarda muslim ɗin yayi yaso ba Abdul dariya, 

amma da yake yana son muslim ɗin ya saki jikin shi da shi ya daure be yi ba

Suna a haka kafin Abdul ya sake cewa komi Nasma ta shigo ɗakin ɗauke da tray ta ɗora ruwa da lemu a kai se glass cup

A yangance take tafia, kallo ɗaya Abdul ya yi mata ya ɗauke kan shi, 

kayan da ya ganta da su sanda ya shigo ba su bane yanzu a jikin ta, wasu daban ne ta saka duk dan Abdul ya yaba in ya gani

Ko rufe bakin ta batai ba da sallamar da tayi, aka wancakalar da tray ɗin hannun nata da duk wani abu dake kai, ita kanta kamar warce aka ɗauka akai jifa da ita, wanwar ta baje a ƙasa ƙugunta ya bugu da ƙasa sosai

Ƙarar faɗuwar Nasma da tray ɗinta ya ƙara firgita Muslim da dama a tsorace yake

Mama kam jin ƙarar faɗuwar abu da taji yasa ta taso da ɗan gudun ta, ta shigo ɗakin, tace 

“garin yaya Nasma?,

 muslim dai bece komi ba se uban idanu dake waje, Abdul ne ma yai magana yace 

“ganin ta kawai muma mu kayi a ƙasa”

Nasma dai ba baka se kunne, gaba ɗaya ta kasa kuka, raɗaɗi kawai take ji tun daga kan babban ɗan yatsar ta har zuwa kwankwason ta

Da ƙyar mama ta ɗaga ta, tana mata sannu har suka fita a ɗakin, 

Ɗaya daga cikin ƙannen muslim ɗin ce ta shigo ta tattare glass ɗin da ya fashe ɗin.

Daga Abdul har muslim ɗin shiru sukai ba wanda ya ƙara cewa komi,

Can Abdul yaji anja wata ƙwata me ƙarfi.

Haka nan Abdul yaji ranshi na ɓaci, 

Maganar da ya so suyi da Muslim ɗin ma ji yayi ya fasa, be wani jima can sosai ba ya ce ma muslim

 “bari inzo in tafi”

Kallon Abdul ɗin yayi yaga jijiyoyin kanshi sunyi ruɗu-ruɗu yace

“kan ka ke ciwo ne halan?”

Gyaɗa kanshi yayi kawai yana ƙoƙarin miƙewa

A ɗan ɗarare muslim yace “Ka rinƙa addu’a sosai abokina”

Murmushi  Abdul yayi mishi, sannan yai mishi sallama tukun ya fita

Yana fitowa daga ɗakin ya iske an kira me gyara yana gyara ma Nasma gocewar da tayi a dalilin faɗuwar da tai ɗazu

Mamar kawai ya yi ma sallama ya fice ko kallon inda Nasma ke zaune tana sharɓar kuka beyi ba.

Tunda Abdul ya shiga gida ya kulle kanshi a ɗakin shi, 

Duk uban zafin da ake zubawa hakan be hana shi kulle kanna shi ba, ya kulle windows sannan ya kashe na’urar sanyaya ɗakin, Tv kanta da take kunne itama ya kashe, har ya zauna ya tashi ya kashe wutar ɗakin sannan ya saki labule.

Zaman dirshen yayi a nan ƙasan carpet ɗin ɗakin shi ya haɗe kanshi da gwiwa ya fashe da kuka

Tun daga can ƙasan zuciyar shi kukan ke taso masa, 

kuka ne na maraici, kuka ne wanda ya jima da tara shi a cikin zuciyar shi, kuka ne na wanda ke buƙatar kafaɗar da ze jingina yayi

Sosai Abdul ke kuka, yana kukan yana cewa

“Ammah me yasa kika  tafi kika barni, bayan kin san kin fi kowa sanin damuwa ta, kin fi kowa fahimtar meke damuna koda ban buɗe baki na furta miki ba,

“Ammah, Abdul ɗin ki na kewar ki, yana maraicin ki sannan kuma yana buƙatar ki a kusa da shi, Ammah, abubuwa na neman sun caɓe min, na fara tunanin ina da matsala a ƙwaƙwalwa ta”

Kasa ƙarasa maganar Abdul yayi, sema wani sabon kukan maraici da ya ƙara fashewa da shi

Ya kai kusan awa ɗaya yana wannan kukan,

Jijiyoyin kanshi sun ƙara fitowa raɗam, fuskar nan tashi tai jajir, musamman saman hancin shi, idanun shi sun kaɗa sunyi jajir.

Yana a wannan yanayin ya fara jin iska na kaɗa labulen windows ɗin ɗakin, tun iskar na kaɗawa a hankali har ta fara ƙarfi tana ɗaga labulen sosai, 

Mamaki Abdul ya shiga jin iskar 

A sanda ya shigo ɗakin be ga alamar hadari a waje ba, 

Da yake ba abinda ke gaban shi ba kenan ya maida kanshi a kan gwiwar shi yana ci gaba da kukan shi da ya fara

Ɗas-ɗas, haka wutar ɗakin ta kawo.

A firgice Abdul ya ɗaga kanshi, ido warwaje yake kallon hasken ɗakin 

Kamar a mafarki yaji an dafa kafaɗar shi ta dama, 

da siririyar murya tace

“Kukan ka na taɓa min  zuciya ta ya kai ma’abocin kyau da haiba, 

Mene damuwar ka a faɗin duniyar nan? me kake da buƙata baka samu ba da har zaka zo ka rufe min kanka a ɗaki ga zafi ga duhu?”

A zuciye kuma rai ɓace Abdul ya miƙe tsaye,

Hannun shi ya saka a kafaɗar shi ta dama ya wancakalar da hannun ta

A fusace ya waiga inda anan yake jin alamun tsayuwar ta, duk da ba ganin ta yake ba, da yatsar shi manuniya ya nuna wajen yace cikin hargowa da ƙaraji

“Kin ishe ni! ki rabu da ni bana buƙatar ki a rayuwata, na daɗe da gaya miki ki fita harka ta, amma kin ƙi ji!”

Ta ko’ina a kusurwar ɗakin ya fara jin dariyar ta, ba inda baya amsawa, dariyar ta kamar zata kashe mishi dodon kunne, seda ya saka hannun shi biyu ya toshe kunnuwan shi

Ta kai kusan minti biyar tana ɓaɓɓaka dariyar kafin ta tsagaita

Ƙwas-ƙwas-ƙwas haka yaji takun tafiyar ta na zagaya shi, 

seda ta zagaye shi kusan so uku tukun ya ji tsayuwar ta a gefen shi kuma ta ɗora hannun ta again akan kafaɗar shi. tace

“Bari in ƙara gabatar da kai na masoyi na,

Suna nan sarauniya Aziza, shekaruna da dama, sannan ina barar in zama matar ka kuma uwar ƴaƴan ka”

Wawan tsaki Abdul yaja, kamar yana ganin ta ya zazzaro mata idanun shi yace

“Banda mahaukaciya ce ke ina kika taɓa ganin hakan ta kasance?

To bari kiji, dama na taɓa faɗa miki hakan tun ban san kai na ba, yanzu ma bari in ƙara faɗa miki, “na tsane ki kuma ki fita harka ta”

Saitin kunnen shi aziza tace “ina son ka kuma bazan taɓa kyale ka ba Abdul’aziz”

Iska me ƙarfi ta fara tashi kamar sanda zata zo,

minti kaɗan yaji ɗif ta ɗauke ba kuma alamar motsin ta.

COMMENTS AND SHARE PLS

TALLAH!!

INA AMARYA, INA KUMA UWARGIDA KUZO GA SIRRIN KAMA MIJI A HANNU, SINADAREN GIRKI BA ABUN WASA BANE, KUMA NAMU BA IRIN NASU BANE.

MUNA SEDA

GINGER AND GARLIC SPICES

CURRY(AKWAI NA JELLOF RICE DA FRIED RICE) CINNAMON

THYME

TUMERIC

CHICKEN AND MEAT

DA NA PEPPER SOUP

MUNA SEDA NA SATCHETS KANANU DA MANTA SANNAN AKWAI NA ROBA, DUK AKAN FARA SHI ME SAUƘI, MUNA SEDA ƊAI-ƊAI SANNAN MUNA BADA SARI

ZAKU IYA SIYA TA WANNAN NUMBER

08137256112 KO 07046637375

SE KUN ZO, KARKU BARI A BAKU LABARI.

MRS SULAIMAN(ZAINAB FALALU)

SE YARDA HALI YAYI, ZAZZAU BA’A SAMUN WUTA

COMMENTS AND SHARE SABODA ALLAH

Back to top button