Karfe A Wuta Chapter 76 By Ayshercool
*BRIGHT PENS SECOND BATCH*Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)**MUTALLAB (NIMCYLUV)*HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)**ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*Tashi ramma tayi, ta ce “Abdul, wai menene meyafaru ne?” Yayi mata shiru ya cigaba da kuka.”Dan Allah kayi magana mana, ko mutuwa aka yi muku?”Yayi mata shiru bai yi magana ba, ta kai hannu zata ɗauki wayar, amma ya janye wayar ya kashe.Kawai ya yinƙura, ya ɗauki mukullin motarsa, ramma ta miƙe ta riƙe shi ta ce “Ina zaka je ne?””Fita zan yi””A wannan yanayin da ka ke? Idan wani abu ya sameka fa, dan Allah koma menene kayi haƙuri, zuwa Allah ya kaimu gobe, dan Allah ka haƙura da fitar nan” jifa yayi da mukullin, ya koma ya zauna ya cigaba da kuka.Ta zauna a kusa da shi, cikin damuwa ta cire masa hannunsa da ya rufe idanunsa ta ce “Abdul, kalleni menene wai?”Ya sake sunkuyar da kai, kamar ita ce baya son haɗa ido da ita. A hankali ya kwanta a jikinta kamar ƙaramin yaro, ta rungume shi sosai, tana shafa kansa ta ce “Koma menen kayi ta nanata Innalillahi wa Innalillahi raji’un, zaka samu sassauci in sha Allah” wata irin ajiyar zuciya ya din ga yi, wanda sai da ya bata tsoro.”Rahama” ya kira sunanta da kyar a galabaice.”Dan Allah ko na fuskanci hukunci, kar ki manta da ni, na san koma menene zuwa ki gama karatunki, zan fito””Tom” ta faɗa a sanyaye, dan wasu lokutan har tausayi yake bata, gaba ɗaya Abdul ya saduda, duk wannan iskancin da rashin mutunci ba ya yin su.”Rahama kin ce mini kina da yaya da ƙani ko? Har su ina son in ɗauki nauyin su”Ramma ta ce “Ba na gaya maka yayana ya mutu ba, sai ƙanina sani””Da gaske ki ke fyaɗe aka yi masa ya mutu?”Ta ce “Oho ina na sani, ba ka ce mini ba a yi wa maza ba, ni kamar haka na so na ji an ce, wai za a samo masa aiki, yaje Abuja aka yi masa, amma mama ba ta taɓa zama ta gaya mini yadda abun ya faru ba, ko tunawa ba ta son yi, idan ta tuno da shi tayi ta kuka”Yayi ajiyar zuciya ya ce “Ban san me zai faru ba, amma dan Allah duk tsanani kar ki rabu da ni, ki zama mai yi mini uzuri da tausaya mini dan Allah, Allah ma baya kama wani da laifin wani”Ramma ta ce “Da bana yi maka uzuri, da bana tunanin zamanmu zai zo i yanzu, ka daina wannan kukan dan Allah kunya kake bani” tayi maganar da sigar tsokana.Ya ƙanƙameta ya cigaba da sheshsheƙar kuka.”To ɗan jariri, ya isa haka, cikin dare kawai mutum ya tashi yana kuka, ko ka je ka yi alwala kayi salla”.”Ba zan iya ba, ba zan yi karatun sallar dai-dai ba””Kaga amfanin ibada ko, idan bawa ya tuna da Allah, lokacin da yake cikin yalwa, Ubangiji yana tuna wa da shi lokacin da yake cikin ƙunci, ka cigaba da addu’a, Allah ya yaye maka damuwar ka doctor Abdul yasar” yayi lamo kamar kyanwa a jikinta, ba tare da ya kuma magana ba.****A hankali Nabila tayi juyi, tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta kawai ta ga Viper a zaune a kan kujera, yana danna waya. Ta ƙura masa ido tana kallon sa.”Wannan kallon haramun ne, ki daina yi mini wannan kallon” yayi maganar ba tare da ya kalleta ba. Ko ƙifta ido ba ta yi, ta cigaba da kallonsa.Ya waiwayo sosai yana fuskantar ta, ya ce “Ya aka yi ne? Ya jikin?”Ta ɗaga hannunta, ta kalli drip ɗin da yake shiga, ta ce “Vi””Mmm””Ina ne nan?””Wurin sayar da mutane” yayi maganar yana cigaba da danna wayar.Ta lumshe idanunta ta buɗe, ta ce “Kamar bacci nake yi, kuma kamar a zahiri ne, dan Allah da gaske malam garba ya mutu?”Viper ya ce “Eh, ya mutu”Ta girgiza kai, tana kuka daga kwance ta ce “Ai shikenan, ya mutu bai shaƙi iskar ‘yanci ba, ban cika masa alƙawarin da nayi masa ba, da yaya zan kalli iyalinsa? Kullum da shi nake kwana nake tashi a zuciyata, ya mutu da mummunan tabo a zuciyarsa da rayuwarsa, ban cika masa alƙawarin da nayi masa ba, na gaza na kasa” tai maganar tana fashewa da matsanancin kuka.”Ke, wai baki da tawakalli ne? Shikenan ke ba zaki mayar da lamarinki ga Allah ba? Wani ya ce ke ki ka kashe shi ne?”Ƙara sautin kukan ta yi, ta ce “Ya ka ji da aka kashe matarka, ya zuciyarka tayi da aka ƙala maka laifin kisanta? Haka iyalan malam garba suke ji, da wannan ɗacin da baƙin cikin ya mutu, kuma ni ban yadda da wani stroke ne ya kama shi ba, wani abun suka yi masa” Viper ya janyo kujerarsa gaban gadon sosai, ya matsa daf da ita, ya ce “Ki yi haƙuri” ta kalli cikin idonsa ta ce “Kai yakamata na bawa haƙuri nayi alƙawarin saka kotu ta wanke malam garba, a gurfanar da ainihin wanda yayi laifin, amma ya rasa rayuwarsa ina kan ƙadamin aikin, na fara tsorata kamar ba zan iya ba Vi”Ya girgiza kai ya ce “Zamu cigaba da ƙoƙari, ba zamu gaza ba, ba zamu sare ba, zamu yi nasara in sha Allah, idan kina cewa kin karaya, nima karaya nake yi” ta ja wata irin ajiyar zuciya ta kalli rigar jikinsa.”Vi””Mmm””Me kake ɓoye mini ne? Ba irin wannan rigar ka yaga lokacin kana Asibiti ba, mai tambarin dragon ɗin nan ba?””Ki daina saka ido, kina ƙirga mini kaya, son rigar nake yi” hararsa tayi ta ce “Am not kid””You are” yayi maganar very serious.Wani ne ya shigo ɗakin Nabila, yana shigowa ya ce “Viperrr” ya kira sunan yana jan sunan, tare da dunƙule hannunsa, ya miƙawa Viper, Viper ya dunƙule nasa suka haɗa.Ya ce “Ya madam, ta tashi? Barrister ya ƙarfin jiki?””Ba sauƙi” ta faɗa tana tura baki.Duka suka kalleta, ya ce “Subhanallah, ba sauƙi fa, garin yaya meyafaru?”Ta nuna Viper, ta ce “Baya son na warke, bai iya jinya ba sam” dariya ya yi ya ce “Maza gumbar dutse, ina Viper zai iya jinya dama, ki manta da shi, zaki samu sauƙi in sha Allah, meyake damunki yanzu?”Ta girgiza kai ta ce “Babu komai, ƙirjina ne yake nauyi kawai””To ki cire damuwa daga ranki, zai daina in sha Allah”Ta ce “Ok sir, na gode sosai” yayi rubuce-rubuce a file ɗin hannunsa ya fita.”Vi””Mmm””Wai ina ne nan? Kuma waye wannan ɗin?””Asibiti da likita”Nabila ta ce “Ai na san asibitin ne, ina son tafiya ne, zan je na ga malam garba”Viper ya kalleta ya ce “Kina da abun gaya wa iyalinsa ne?” Jiki a sanyaye ta girgiza masa kai.”To sai ki daina maganar zuwa””To ina son na gaya wa yan gidanmu ina Asibiti, kar a neme ni””Wa zaki kira? Wanda ya ce ki bar masa gida ki je ki nemi babanki, ko kuma yayanki da yake yi miki bita da ƙulli? Ko kuma sauran yan gidan da suke yi miki kallon yar hana ruwa gudu? Ba wanda ya damu da ke, mutum ɗaya ne, kuma a halin yanzu an gurɓata masa tunani, na taɓa tsintar kaina a cikin wannan halin. Mata guba ne mai masifar dafi da saurin kashe wanda suka hara. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi gaskiya, da ya ce Bai bar wata fitina a bayansa da take cutar da maza ba a bayansa sai mata, banda haka me zai sanya mace ta raba ɗa da uba?” Yayi maganar jijiyoyin kansa na kumbura, idanunsa suka yi ja, suka ciccika da hawaye, tuna mahaifinsa da ya yi.”Ni ba guba bace ba, idan ka yi wa dukkan mata ka kira mu da guba, baka yi mana adalci ba, yakamata ko albarkacin jauhar mu ci, ka din ga kallon wasunmu ne gurɓatattu, kamar yadda kuma a jinsinku yake da akwai gurɓatattu”Yayi shiru tare da sunkuyar da kai, saboda sake soso masa wurin da yake yi masa ƙaiƙayi.****Indabo yana zauna yana karyawa, tare da matarsa, kawai Abdul ya faɗo tsakiyar wurin da suke cin abincin.”Meye haka Abdul, baka iya sallama ba baka iya gaisuwa ba”Indabo ya ce “Ko giyar ka je ka sha, ka yi shaye-shaye ne?””Na daina shan giya da miyagun ƙwayoyi, tun bayan da rahama ta shigo rayuwata, ta haskar baƙar bayahudiyar rayuwar da kuka tarbiyyantar da ni a kai, kodayeke gara ma ni shan giya ne da neman mata kawai, but am so much disappointed on you, nayi dana sanin kasancewar ka mahaifina. Dama a tsatson talakawa na taso, talakawa futuk sai ya fiye mini wannan mummunar rayuwa da iftila’in kasancewar ka mahaifina””Abdul, uban naka ka ke gaya wa haka? Duk iya ƙoƙarin da yayi na ƙarar da rayuwarsa wurin ganin ya gina ku, ka zo gabansa kana gaya masa wannan maganar?””Mummy! Wace irin gina rayuwarmu, gangar jikin da aka gina da zunzurutun haramun da jinin mutane? Haba mummy da alama mafitarki kawai ki ka nema, ya sanya ki ka auri Daddy, wallahi mu ‘ya’yanki baki yi mana adalci ba, kuma a yau ba sai gobe ba, zan bar ƙasar nan, na nesanta kaina da ku, tun kafin asirinka ya tonu a idon duniya abun da ka yi ya shafe ni, gara in kalli duniya a hukunta ni da laifin fyaɗe da nayi, da a hukunta ni da mummunan laifin da ka aikata, ga waya nan ka karɓa ka saurari saƙonka”Yayi maganar yana miƙa masa wayarsa, Indabo ya saka hannu ya karɓa, yana dubawa.Wani audio ya fara buɗewa, sai dai jin muryar wanda yayi message ɗin kawai, ya rikita masa lissafi, ya fara gumi hannunsa ya hau rawa.”Wanna saƙon ba naka bane ba, na mahaifinka ne. Duk da ina da access na yadda zan same shi, amma yafi dacewa na tura masa saƙon ta hannunka, sai yafi karɓar sa da muhimmanci. Lokaci yayi da zamu daina buga wasan ‘yar ɓuya da kai indabo, zamu yi wasa na ƙeƙe da ƙeƙe, saboda ina daf da barin ramina da nake ɓoye, na cigaba da addabar rayuwar ka ta kowane hali. Idan ka muzgunawa Nabila, tamkar jauhar ka taɓa mini, taɓa jauhar kuwa taɓa zuciyata ne kai tsaye. Dan zan yi wasa irin wanda ka ke so ayi.Ka so ta zama tarkon da zaka yi amfani da shi ka kamani, shi kuma Allah ba azzalumin sarki bane ba. Ɗanka ya yi wa rahama fyaɗe ƙanwar Nura, da ka lalatawa rayuwa ka kashe, ka ɗorawa wani daban, kuma ka bishi ka saka an kashe shi. Abun da baka sani ba shi ne, ina da cikakkiyar shaidar mummunar ɗabi’ar da ka ke aikatawa, ta lalata rayuwar matasa da sunan sama musu aikin yi. Sannan ni na saka aka kama ɗanka Jafar, a Mexico in da ya gudu neman mafaka bayan yayi kisan kai, haka zalika yanzu ma da saka hannuna a mayar da shi amurka.Yanzu haka miyagun ƙwayoyi da hodar iblis ɗin da aka loda maka a jirgin ruwa, za ayi safararsu ta ruwa, za a kama su a gaɓar tekun italy. Kamar yadda nayi maka aike na farko, ina tare da Simon kuma shi ya bani wannan saƙon naka”.Jiki na rawa ya buɗe videon, shi ne a cikin videon, yana ta kokowa da Nura guduma, wasu irin ƙarti majiya ƙarfin gaske, suka riƙe Nura, yana kururuwa yana ƙoƙarin ƙwatar kansa, amma abu ya gagara, kuma ba iya fuskar Indabo ba ce a videon, har da wasu daga cikin manya a ƙasa.Da ƙyar Indabo ya iya ɗaga ido, ya kalli Abdul, ya haɗiye wani irin abu mai yaji da ɗaci, ya kasa magana. Abdul kuma ya ƙure shi da ido, yana jiran ya ji mai indabon zai ce.Mahaifiyar Abdul tayi shiru, suka yi tsuru-tsuru.”Na tabattar ba sharri aka yi maka ba, kai ne a jikin videon nan, naga baka buɗe sauran audios ɗin ba, amma ya tabattar da cewa, mutum goma ne suke da videon, muddin ka cigaba da takura musu, sai sun sake shi a duniya, kuma sai an ɗauki mummunan mataki a kanka, babban takaicina me zan cewa rahama, yarinyar da nake nema ta yafe mini, ashe akwai babban aiki a gabana jawur, kai kayi silar mutuwar ɗan uwanta, tayaya mahaifiyarta zata yafe mini ta bari na cigaba da rayuwa da ita?””Abdul ka cigaba da rayuwa da wa? Tona wa mahaifinka asiri zaka yi? Satin bikinka ya kama kana nufin zaka yi aure kuma ka ajiye karuwa?””Rahama ba karuwa ba ce, aurenta nake yi, kuma yau zan tattara na bar garin nan da ita, da wannan abun kunyar da ka aikata”Indabo ya ce “Aurenta ka ke yi kamar yaya?”SOME MONTHS BACK.Abdul ne ya shigo, ya tarar da rahama a rakuɓe, a jikin gado, idanu duk sun kumbura saboda kuka.”Wai ba zaki raba kanki da wannan kukan ba? Aikuwa kina tare da wahala, dan kuwa yanzu ki ka fara, tashi ga abinci”Ta ɗago ta kalleshi ta ce “Ba na ci, ka ƙyale ni na mutu, ai tun farko cewa kayi zaka kashe ni, menene na ajiye ni kana tozarta rayuwata, saboda kawai ina ‘yar talaka? Talauci ne ya saka na fita aikatau, da burin yin karatu, mahaifiyata ba zata iya ɗaukar ɗawainiyata ba, ban da haka killace ni zata yi a tare da ita, ba zata bari ma ka ganni ba balle ka keta mini haddi” ta yi kneel down ta ce “Dan girman Allah ka kasheni na huta””Ke naji, kin cika mini kunne da koke-koke, zan mayar da ke”Ta girgiza kai ta ce “Ko ka mayar da ni, ba zan yi daraja ba, abar ƙyama zan zama, kawai ka kashe ni, ka kaiwa mama gawata dan Allah”Abdul ya zauna a kusa da ita ya ce “Ya isa haka kukan, ki ci abinci zan san abun yi” kwanaki biyu, tana jiran ya kashe ta, ko ya mayar da ita amma shiru, gashi tun da tayi ɓarin nan, da ya zo mata zata fara kuka kamar ranta zai fita, tana yi masa magiyar ya daina wulaƙanta mata rayuwa.Cikin marairaicewa ta same shi, ta durƙusa a ƙasa ta ce “Ka ce zaka mayar da ni gida, kuma baka mayar da ni ba””Rahama ba zan iya mayar da ke ba, zan ta tunaninki ne, kawai na ji ina damuwa da ke, ki haƙura kawai” cikin kuka ta ƙare masa zagi, amma ko a jikinsa.Washegari ya ɗauki Salim, ko saifu bai gaya wa ba, suka tafi gidan su ramma.Mahaifiyar ramma na ganin Abdul, ta tashi cikin ƙarfin hali ta ce “Ina ka kai mini ‘ya ta? Ka dawo mini da ‘ya ta”Abdul ya ce “Mama masalaha na zo muyi, ɓarna an riga an yi ta, dan Allah ki yi haƙuri ki bar mini ramma, ki bani aurenta” Sai da Salim ya kalle shi, dan bai san abun da zai ce kenan ba.”Allah ya tsare, cuta ka riga ka gama cutar da mu, kai da Allah, amma ka dawo mini da ‘ya ta”Ya girgiza kai ya ce “Kar mu yi haka, a rufa wa juna asiri, kun ɗauki aure da muhimmanci sosai, ta ce babu lallai tayi daraja, ƙyamarta za a din ga yi, dan haka ki yi haƙuri dan Allah, ki aura mini ita””Wallahi ba zan taɓa aura maka ita ba, gara ayi ta tsangwamarmu, zan riƙa a bata na kula da ita, kuma zan cigaba da nema mata hakkinta, har zuwa ƙarshen numfashina”Ya miƙe ya ce “Shikenan, tana gaishe ki, ki kwantar da hankalinki, tana cikin ƙoshin lafiya” ya ajiye mata kuɗi suka fice, ta bishi tana ya zo ya karɓi kuɗinsa amma yayi mata banza suka tafi.Salim ya din ga yi masa masifa a mota “Amma dai baka da hankali ko? Ka yi wa yarinyar fyaɗe, mu zo gaban babarta mu yi rashin mutunci, kuma mu dawo ka ce zaka aureta, wai ma ka gaya wa su daddy ne?”Abdul ya girgiza kai ya ce “A’a, yarinyar ce take bani tausayi irin sosai ɗin nan, virginity is very important to woman’s, i took it away just like that, she’s very young and innocent, ina jin babu daɗi, na san yadda zan ɓullowa lamarin”Tare da Salim suka cigaba da shige da fice, suka samo wani wan baban ramma, Abdul ya danƙara masa kuɗi, babar ramma bata sani ba, aka ɗaura musu aure, sai bayan an ɗaura ya je ya din ga yi wa babar ramma masifa, wai Allah zai rufa wa ramma asiri, amma tana ƙoƙarin tonewa, da ta samu ma mai kuɗi da kyau kamar wannan ya saurari yar ta ta, a wurin ɗan birni kamar Abdul ai ramma a bar ƙyama ce.Cikin kuka ta ce “Wallahi balarabe ba zai yiwu ba, ban san wani zancen aurar da ramma ba, lokacin da nake wahala ta da ya ta da me ka taimake ni, ina har gonar su ta gado ka cinye”.”Oho miki, koma menene rashin iya takaucinki, da son abun duniya ya sanya ki ka kaita aikatau” da kansa ya shiga ya kwaso wa Abdul kayan ramma, ya sake ba wa babar ramma kuɗi, ya ɗauki kaya suka tafi.Suna tafe Salim ya ce “Ranar da asirinka ya tonu ban sanka ba wallahi, ko kuma ka gama abun da zaka yi, salin alin ka sakar musu ‘ya”Abdul ya ce “Ban aureta dan na saketa ba, sai dai ayi wadda za ayi”Ya je ya samu ramma, ya kai mata kayanta, da goro da alawa ya ce “Gashi nan, hankalinki ya kwanta an ɗaura mana aure yau” cikin mamaki ta kalleshi ta ce “Aure kuma kamar yaya?””Ba damuwarki kenan ba? Ke ba zaki auru ba? To an ɗaura yau, yayan babanki wai malam bala, shi ne ya ɗaura mana aure””Wane irin aure ne babu istibura’i? Cewa nayi ina sonka ne ma?”Ya ce “Meye istibura’i?””Sai nayi jini uku a addinance, dan tsaftace mahaifata kan ka aureni, tun da zina kayi da ni, kuma ni bana sonka”.Abdul ya kalleta ya ce “Allah ya nuna mana wata ukun, kuma ni ina sonki ai, Shikenan an wuce wurin”.Ramma tayi kuka a kan wannan wulaƙanci da Abdul yayi mata, da nuna mata tsantsar isa da gadara, ta fara yi masa misbehaving ta daina tsoronsa, amma ko a jikinsa, sai dai zamansu tare ta gane yana da wasu ɗabi’u na tausayi da sauƙin kai, rashin tarbiyya da ilimin addini ne kawai yake ɗawainiya da shi, bai sake nemanta ba, sai da ta cika watanni uku, kamar yadda ta buƙata.Idan tana yi masa masifar ba dan Allah ya aure ta ba, ya kan ce mata “Ba dan ina sonki ba, babu dalilin da zai sanya na zauna da ke watanni uku ina kallonki, kina gindaya mini sharuɗa ina ƙyale ki”.****Mahaifiyar Abdul ta ce “Aure ka yi bamu sani ba Abdul, rashin muhimmancin namu har ya kai haka?”Ya kalleta ya ce “Ko zan mutu ba zaku yadda ku aura mini rahama ba, zaku yi iƙirarin yar talakawa ce, ba tare da la’akari da ɓarnar da na akata mata ba. Kuma sakawa zaka yi a kasheta, sannan mutumin nan da ka saka aka kashe, ba ruwana babu saka hannuna a ciki. Zan ɗauki matata mu bar garin nan, dan Allah kar ka neme ni, takara kuma ka bawa wani, ba zan iya ba” ya ɗauke wayarsa, mahaifiyarsa ta bishi tana ƙwala masa kira, amma yayi waje.***Viper ne ya shigo ɗakin da Nabila take, tana zaune ya shigo da waya a kunnensa ya ce “Eh na je wani wuri ne, ɗan mama ya dawo gidan nan ne, ya gudu na neme shi na rasa, ya kuma kashe wayarsa”Walid ya ce “A’a bai dawo ba, ko laifi yayi maka ka ce zaka hukunta shi?”Yayi murmushi ya ce “Laifi yayi, kuma duk in da ya shiga zan nemo shi, zamu gauraya da ni da shi”ya katse wayar ya ƙarasa gefen Nabilaya zauna.”Vi””Mmm””Wai dan Allah ina ne nan? Ina son na tafi gida ne””Ai ba zaki koma gida ba, kin zo kenan”Dariya tayi, dan ta zata da wasa yake yi.”Daga fitarka ka sha sigari ko?””Eh”Nabila ta ce “Au eh, baka jin kunya wai ka amsa ka tsaye, sai ƙauri ka ke yi, ba na son ƙaurin abar nan ko kaɗan wallahi”Ya tsura mata ido, ya girgiza kai ya ce “You can’t be her””Who?”Ya lanƙwasa ƙafarsa ɗaya a kan gadon ya ce “Jauhar, ba ta taɓa nuna warin sigarina da wiwi yana damunta ba, sai dai ta ce ; Master kar a sha da yawa, dan Allah a sha kaɗan, idan nayi shaye-shaye na dawo, ta bani ruwan wanka, ta bani wankakkun kaya, ta fesa mini turare, sai daga baya na fahimci, warin wiwi ne ba ta so, amma bata taɓa yi mini complain ba. Yanzu bana iya shan komai, na yadda ƙwaƙwalwata da lafiyata suna da amfani, ko dan ganin bayan wanda suka cutar da mu. Ke kuwa masifaffiya ce, always angry, ki ka gaya mini ina ƙaurin taba””Sai na zama irin ta zaka so ni? Gaskiya ba zan iya shiru ba, ni kawai ka daina gaba ɗaya”Viper ya ce “Ai babu wannan maganar tsakanina da ke, na gaya miki ki daina wahalar da kanki” ya yi maganar yana miƙa mata wayarta.Karɓa ta yi tana hararsa ta ga sunan sumayya ta ce “Ba zan ɗaga ba””No, ki ɗaga baki san me za ta ce miki ba”Ta ɗaga ta saka a kunnenta ta ce “Ina jinki””Nabila kina ina ne?””Menene?””Kawai malama kina ina?””Ki gaya mini meyafaru? Nayi nisa ne”Sumayya ta ce “Mahaifin Viper, ya zo gidan radionmu, ya ce yana son zai yi magana da ke, na ce masa zan haɗaku, zan yi miki magana”Nabila ta ce “Are you serious dan Allah da gaske?””Wallahi da gaske nake yi miki””Shikenan, in sha Allah zuwa gobe in Allah ya kaimu, zan zo zamu haɗu, kin karɓi lambarsa?””Eh na karɓa””Shikenan in sha Allah zan zo” ta katse wayar, ta ga wani irin kallo da yake yi mata.”Vi snake, menene? Abunka ne ya zo yana nemana, wataƙila…..”Silent. Kar ki kuskura ki fara, ke gaba ɗaya baki da lissafi, idan wani trap ɗin ne fa?” Yayi maganar cikin hargowa.”Bari na zama kamar jauhar, ba zan biye maka ba ai yanzu, hukuma sai da rarrashi, hadari malafar duniya. Tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah. Nifa duk da ina da labarin abun da babanna yayi wa mahaifiyata, fata nake yi na ganshi, haka zaka cigaba da rayuwa ba dangi, kaikaɗai sai su oga Walid, sai kuma Ni” ta yi maganar tana murmushi.”Ka bari mu haɗu da Abbu dan Allah, na san maybe nemanka yake yi, so yake ya ganka, haba sweetheart, namijin duniya, kar ka saka muyi babu, kai ba uba nima haka, kayi haƙuri dan Allah, ka manta da komai My Vi. Magana fa nake yi an yi mini shiru, talk mana, ko sarautar ce ta motsa? Master magana nake” tsigar jikinsa ta mimmiƙe ya juya yana kallonta.”Ban taɓa kallon wani abu na ji ina son shi ba, sai kai Vi, duk a dalilinka na rasa ajina da jin kai na ‘ya mace. Gashi ka yi ta hantarata, baka tausayina ko kaɗan.Ɗan nuna mini hoton ‘yar madara mana, ko sau ɗaya ne””Hotonta mai tsada ne, yarinya mai haƙuri da aji””Ni kuma masifaffiya mara aji, daga nan kuma sai me?” Ya fuskanci kawai kunna shi take yi.Ya ajiye mata wata leda, ya ce “Gashi nan, abinci ne, za a kawo miki kaya””A’a nifa ban gane ba, gida fa?”Ya miƙe tsaye ya ce “Ba sa buƙatar ki, na fi su buƙatar ki a yanzu, muddin wani abu ya sameki, ni aka jiƙawa aiki”Nabila ta ce “Ban gane ba, garkuwa zaka yi da ni?””Na ma yi” yayi maganar tare da ficewa.****Hanklin can gidan su Nabila ya tashi, bayan an shafe kwana na biyu, ba a san in da take ba, Abba ya maze kamar ko a jikinsa, amma hankalinsa a matuƙar tashe yake. Nasir ma ya din ga up and down, haka ma sumayya dan sai da ta gaya wa Kankarofi an nemi Nabila an rasa.Ta gaya wa Nasir cewa, ranar da ta ɓata sun yi waya, bayan la’asar kuma da alama tana cikin ƙoshin lafiya.Nasir ya ce “Abu ne mawuyaci ace barin gidan nan tayi, wataƙila mutanen da take addabawa ne suka sace ta”Aka din ga kiran wayarta, amma a kashe.Kwana na uku, Nasir ya kira wayarta, ta shiga, amma ba a ɗagawa.Dan haka ya saka layin a tracker, ya fara tracking in da wayar take, sai dai ga mamakinsa, wayar tana cikin garin kano.****Abdul tamkar zai haukace, duk wani lungu da saƙo na gidan ya duba, amma bai ga ramma ba, ya dudduba ko ina da ina, amma bai ganta ba. Ya kira wayarta amma a kashe.Taka jikinsa ya hau tsuma, ya tabattar da cewa Indabo ne ya saka aka ɗauke ta, jikinsa na rawa ya ɗaukko mota ya fito, tare da sakawa a ransa komai zai faru sai dai ya faru, amma sai indabo ya fito masa da matarsa, ko kuma shi da kansa ya tona musu asiri kowa ya huta.****Nasir yayi mamakin surƙuƙin wurin da yake indicating in da wayar Nabila take, da shi da abokan aikinsa, ƙarshe ajiye motar suka yi, suka din ga shiga wurin da ƙafa, suna cigaba da dubawa.A tsaye suka tarar da shi ya juya baya, hayaƙi yana tashi.Nasir ya ce “Malam waye kai?”Sai da ya ja sakanni, sannan ya juyo a hankali, hannunsa ɗaya da wayar Nabila, ɗaya kuma riƙe da sigarinsa, gaban rigarsa ɗauke da sunansa Viper da hoton maciji a jiki.”Al’amin Viper, ko ka ce mai zamani”
Ayshercool 08081012143


