Halysaah Page 138 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 138…Ajay na ta tsaye bakin kofar jin bata yi responding ba, ya sake knocking yace “Jeeddah” Still bata amsa ba, bayan kusan 3 minutes ya juya a hankali ya bar wajen ya koma parlonsa, wayarsa ya dauka ya zauna kan kujera yana dialing number…. Khaleesat ta fito daga bathroom tana kallon kofar dakin don tana wanka taji kamar anyi knocking, fuskarta babu walwala ta kauda ko kuka ta kasa yi balle ta dan ji saukin abinda take ji a ranta, nan ta dinga duba boxes din lefenta daya bayan daya har ta bude wanda kayan bacci ke ciki, ta dau doguwar rigar bacci da inner wear ta ajiye gefen gado, sannan ta bude box din cosmetics ta dau tsadaddun turarurrukan da aka zuba mata, ta dau cream din shafa da hair oil sai sabon comb ta tafi gaban mirror ta zauna, ta gama shafe shafenta ta daure gashinta kenan taji ana knocking kofar dakin, ta juya tana kallon kofar sai kuma taji sallaman Yakumbo, sau uku Yakumbo tayi sallama kafin ta mike a hankali ta tafi ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, Yakumbo ta yi kasa da kai cikin girmamawa tace “Barka da dare ranki shi dade, Allah ya sa baki fara bacci ba na tashe ki” Khaleesat na kallonta tace “Ban fara ba” ido hudú tayi da Ajay dake tahowa daga babban parlor bayan ya ta bude kofar, ta dauke idonta ta maida kan Yakumbo babu yabo babu fallasa tace “Ina jin ki Mama” Yakumbo na dan kame kame tace “A’a dama ba wani abu bane, zan tambaya ne ko da abinda kike bukata ranki shi dade?” Khaleesat na ganin Ajay ya iso wajen tace “Bana bukatar komai, sai da safe” Daga haka ta juya zata koma cikin dakin da nufin kulle kofar amma taga har ya shigo ciki, tana ganin haka ta nufi hanyar bandaki ya kulle kofar dakin sannan yayi saurin rikota, Yakumbo dai tuni ta juya ta bar bakin kofar sum sum ta fita daga part din, Khaleesat ta ki yarda ta kallesa duk da yana rike da hijab dinta, cikin sanyin murya barin su hada ido, manneta yayi da bango yana kallonta murya can kasa yace “Da aka kawo ki gidan nan dama an shigo dake dakin nan ne?” Kin cewa komai tayi, ya dago kanta yana kallonta babu ko kiftawa, ta fara kokarin barin wajen amma yaki saketa, kamar zata yi kuka ta kallesa tace “Don Allah ka kyaleni pls sallah zan yi fa” yayi kasa da murya yace “Why didn’t you open the door when I was knocking?” Da sauri ta girgiza kai tace “Wallahi ina bandaki ban sani ba” Shi dai kallonta kawai yake, ta sauke idonta a hankali, can ya saketa har sannan bai cire idonsa a kanta ba, ta bar jikin bangon ta tafi ta tsaya kan darduma zata tada sallah, makullin kofar dakin ya cire da na bandaki sannan ya fita, tana sallah ya kawo mata abinci da cup din tea ya ajiye mata, sannan ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa yana duba mai kiransa, kofa ya nufa ya fita daga dakin, ko da Khaleesat ta idar da sallah gaba daya taji ko appetite din cin abincin ma bata da shi, amma dai taji abinda take ji a zuciyarta ya ragu da almost 80 per cent, ta dan sha shayin kadan ta kwantar da kanta jikin gado a hankali ta lumshe idonta, a haka bacci ya dauketa, wajen karfe sha biyu taji an kwantar da ita sanan gadon dakin ta bude ido ta kallesa, sai kuma ta juya ya rufa mata duvet din da ya dauko daga dakinsa ta ci gaba da baccinta, ya kwashe abincin da bata ci ba da cup din tea ya kashe wutan dakin ya fita, dawowarsa part din kenan daga bangaren Mami. Da asuba Khaleesat na zaune kan darduma bavan ta yayi mata sallama akan zai fita Masallaci,daga can ta tashi tana tana murda handle din taji a bude ta kulle da makulli sannan ta juya ta tafi parlonsa, daga bedroom dinsa har zuwa parlon ta gyara ko ina sannan ta sa turaren wuta ta kunna AC, ta koma dakin da ta kwana ta shiga wanka, karfe bakwai saura ta gama shiryawa ta tafi main parlor ta kwanta don kar ya dawo yana knocking bata ji ba, har bacci ya dauketa taji knocking dinsa, ta mike ta bude kofar, yana kallonta yace “Why did you lock the door?” Girgiza masa kai kawai tayi, ya tafi parlonsa, after some seconds ta bi bayansa, zaune ta samesa parion yana duba wayarsa, ta zauna ta gaishesa without looking at him, jin bai amsa ba ta daga kai ta dan kallesa taga Kallonta yake, sosal taji gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta, ya mike yace “Mu je kina Mami bata da lafiya” Khaleesat ta daga kai ta kalles Jin abinda yace, a hankali tace “Ni dai bazan je ba, in kaje sai kace ina gaisheta….” Kallonta yake jin abinda tace, can kawai ya nufi kofa ta bi sa da kallo, sae kuma ta tashi ta bi bayansa tana tafiya a hankali, tare suka isa bangaren Mami tana biye da shi, ta zauna parlon Mami incident din jiya na dawo mata kamar lokacin aka yi, sunkuyar da kanta tayi shi kuma ya karasa Bedroom din Mami yayi sallama ya shiga, bayan few minutes ya fito ya zauna kan kujera without looking at her yace “Go inside” A hankali ta mike ta nufi Bedroom din ya bi ta da kallo har ta shiga da callama daki na nari murds that is wall furnished nan suka gaisuwarta cikin sanyin murya, Khaleesat tace “Ya jikin Mami?” Mami tace “Alhamdulillah da sauki” Khaleesat bata sake cewa komai ba tayi shiru tana ta zaune kasan carpet din dakin, after some minutes ta kalli kayan gugan Mami masu yawa dake ajiye kan kujera a ledojin su, tace “Mami a sa maki kayan a press ne?” Mami ta dan yi shiru don ba kowa take yarda ya gyara mata sip dinta ba, sai kuma tace “In zaki iya ki sa to” Mikewa Khaleesat tayi ta nufi gun kayan, Ajay na ta zaune parlor yana jiran fitowar Khaleesat, ganin bata fito ba har bayan minti sha biyar ya mike ya fita daga parlon kawai, har bayan minti talatin Khaleesat bata gama jera kayan ba don cikin nutsuwa take yi kamar yanda taga aka jera wer enda ke cikin press din, ko wanne da wajensa, Aunty ce ta shigo parlon da sallama cikin shiga ta allarma, da mamki ta dinga kallon Khaleesat da ta sunkuya da kai ganinta, Aunty ta karasa gun gadon Mami tace “Barkanmu da safiya Fulani, ya jikin?” Mami tace “Jik Alhamdulillah, ya kwanan su Maryam” Aunty tace “Lafiya lau” Dukawa Khaleesat tayi har kasa tana gaida Aunty, Aunty tayi kamar bata san da ita take ba tana dai tsaye fuskarta a murtuke, bayan few seconds Khaleesat ta mike ta ci gaba da abinda take, babu wanda ya sake cewa komai a dakin tsakanin Mami da Aunty, Aunty kuwa mamaki ne ya kasa barin zuciyarta, Mami da duk yanda take da mutum bata taba barin va shigar mata daki wai sai ga Khaleesat a dakin itama tana mai fadin ne na shigo in maki sannu ban san har da karin ruwa ba ma” Mami tace “Na ma ji sauki yanxu, ruwan ma ai ya kare kadan yayi saura” a takaice Aunty tace “Allah ya sauwake” Daga haka ta nufi kofa ta fice daga dakin, Khaleesat ta gama jera kayan gaba daya, sannan ta fara tidying din dakin duk da ko ina a gyara yake, ta kunna burner da ta gani ta saka turaren wuta, taji Mami tace “Kira Junaid ya zo ya cire min ruwan ya kare” Khaleesat ta mike ta karasa gun Mami tana kallon drip din tace “Zan iya cirewa” Mami na kallonta tace “Ke ma likitancin kika karanta” Murmushi Khaleesat tayi tana cire drip din tace “A’a Pharmacy nayi Mami bata ce komai ba, Khaleesat ta kalli flask din ruwan zafi da kayan shayi dake dako Daven ta gama cire drip din tace “Mami a hada maki shayin be ko kin sha?” Mami ta mike zaune tace “Ki dauko cup a kitchen” Mikewa tayi ta nufi kofa zata fita sai ga Jay zai shigo dakin, hade rai tayi without looking at him ta koma gefe ta basa hanya bayan ya wuceta tayi ficewarta daga dakin ta tafi kitchen din Marni, ba a dau lokaci ba ta dawo dakin ta tafi ta duka gun flask ta bude tana zuba ruwan zafin a Mug, shi dai Jay na zaune dakin Mami taki ma kallon inda yake tun daga gaisuwarsa da ta amsa shima kuma bai sake cewa komai ba a dakin, Khaleesat ta gama hada shayin ta mika ma Mami ta amsa tace “Nagode” Khaleesat na durkushe har sannan tace “Zan tafi sai anjima Mami” Mami tace “To bi tum min lunaid Khaleecat taco “Tomua jay yang wala yi wa, ya wa la wa nanun yeICH INU har ta fita. Khaleesat na fita parlon Marni ta hadu da Walid da Mukhtar sun zo duba Mami su ma, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Walid, Mukhtar ya gaisheta, ta mayar masa gaisuwan kanta a kasa, Walid kuwa sai kallonta yake kasa kasa suka shiga parlon da Mukhtar, tana tafiya da sauri ta koma bangaren Ajay, tsabar yanda zuciyarta ya tsinke sai da ta zauna babban parlor to calm her self down, ko dai Mami zata yi ma maganar Walid don ita tsoronsa take ji sosai, tana ta zaune a parlon har bayan minti goma sannan ta mike tana tafiya a hankali ta nufi parlon Ajay, baya parlon hakan yasa ta karasa bedroom dinsa ta gansa kwance yana bacci, juyawa tayi a hankali ta koma parlor ta kwanta. Yakumbo ce ta shigo bangaren wajen karfe sha biyu da rabi, Khaleesat ta fita babban parlor ta zauna tana gaidata, Yakumbo tace “Allah ya taimake ki, nace bari in zo in ji ko kina da bukatar wani abu dai” Khaleesat tace “A’a ba komai Mama” Yakumbo tace “To amma ranki shi dade in dai da wani abu da kike son ci a ranki ki dinga sanar min ko a kitchen dinki ne sal in maki, naga bakya wani cin abincin da ake kawo wa, ko kumallon dazu ma naga tabawa kawai kika yi, haka ma dinner din jiya, shi dama Yarima nasan bai wani damu ya ci abinci da yawa ba, amma ke sai nake ga kamar cimar da ake kawo maku ne baki so” Khaleesat tace “A’a duk ina cin komai indan ina hukatar wani ahu ma zan yi magana. Kina nufin zaki kiyi da kanki” Ita dai Khaleesat tayi shiru, Yakumbo ta karasa kusa da ita tana mika mata wani package da hannu biyu tace “Yanxu na shiga duba Mami da jiki ta bada wannan a kawo maki” Khaleesat na kallon package din ta amsa hannun Yakumbo tace “To” ajiyewa tayi kusa da ita don bata san ko menene ba shi yasa bata bude gaban Yakumbo ba, Yakumbo ta koma ta zauna tana kara sauke kai kasa tace “Sannan idan babu damuwa ina son wata er magana da ke Gimbiya amma sai kin ban dama….” Khaleesat na kallonta tace “ina jin ki” Yakumbo tayi kasa da murya tace “Ki gafarceni ranki shi dade, amma a matsayina na me shekaru kuma duba da yanda kike mutunita ni da girmama ni ba tare da kin duba naki matsayın ba yasa har na samu kwarin gwiwan yi maki wannan maganar, Allah ya taimake ki ina son baki shawara ba don na isa ba amma don Allah duk abun da zai hadaki da Yarima kiyi hakuri kar ki sake cewa za ki rufe masa kofa, ba a yi ma miji haka balle ma miji irin Yarima….” Fitowar Ajay zai je masallaci yasa Yakumbo tayi shiru kanta a kasa tana qaishesa da ladabi, Ya amsa va nufi wajen motarsa “A’a, hasali ma ni ban kulle masa kofa ba” Yakumbo tace “To Allah ya huci zuciyarki Gimbiya, na maki mummunan fahimta a gafarce ni” Khaleesat tace “Ina son dama in tambayeki, don Allah bazai yiwu ki dawo nan ki dinga zama ba har dare?” Ba komai yasa Khaleesat tace haka ba sai don kawai tana son mutum ya kasance da ita a part din, don tun daxu ta kasa samun sukuni bayan haduwarta da Walid a part din Mami, Yakumbo tace “Sai abinda Yarima yace Gimbiya, ke zaki sanar masa da abinda kike so kiji abinda zai ce, amma don ta ni banda matsala na ma fi son kasancewa tare dake ina maki duk abinda kike so, balle naga har yanxu baki gama sakin jiki da gidan ba” Khaleesat tace “To zan masa magana…..”


