Mejo Najeeb Page 48 By Autar Alheri
“Wlh bazan iya sakinta ba domin rayuwatace sedai idan kunshirya kasheni daraina amma bakina baze taɓa furtawa mamana kallimar sakiba dan Allah kuyimun rai….dukkansu juyuwa sukayi suna kallon mejo da mamaki kwance akan fuskarsu, kamin wani samu zarafin yin magana sukaga yazo gun Isseta dake maƙale jikin Hajiya Hannah yariƙo duka hannayenta idonshi suncika tab da ƙwallah yace “sweet life kinajiko kinajin abinda suke faɗa wai rabamu zasuyi bazan juraba bazan iya rayuwa babukeba maryamm wlh idan suka rabamu mutuwa zanyi kuma koban mutuba zanyi abinda za’akasheni domin narantseda Allah bazan bari kowane namiji yakoda kallekaba balle yarayu dake amatsayin matarshi wlh kasheshi zany…cikin sauri isseta tafaɗa jikinshi tare da rufe Mishi baki tana sakin marayan kuka tace “wlh bawanda zerabamu yayana koda bansan kai ɗan uwana bane tunda kai ɗin zaɓin maah ne kaine zaɓina balle yanzu danasan cewar kai jinin Ammina ne wlh Nima mutuwa zanyi yah najeeb please kadena faɗar zasu rabamu..sekuma tamiƙe kamar wata zarriya tanufi Alhaji abdussalam tana ɗingishi cikin kuka tariƙo hannunshi amma takasa magana sabida kukan dayaci karfinta. Cikin sauri mejo yasameta awurin sekawai yarun gumeta ajikinshi shima yasaka kukan…gabaki ɗaya wanda ke wurin mutuwar zaune yayi musamman wanda sukasan waye mejo najeeb daga Abba har general Aliyu da dady mufeedah da Ummi su abun yafi ɗaurewa kai, nazeer da sapwan kuwa kamar suyi kuka domin suma sunbasu tausayi sabida sunsan minene so…halima kan tuni tashiga rusa kuka itada mufeedah da Ummi, hakan mama bintu da innar halima. Hajiya Hannah kam kallonsu kawai takeyi da murmushi kwance akan fuskarta, abinda yayi mugun ɗaurewa ƴaƴan nata kai kenan har sapwan yakasa hakuri yace mammey yafaɗa kamar zayi kuka. Kowa awurin su yake kallo da Alhaji abdussalam daya zuba musu ido kawai yana kallonsu wani irin kallo yake musu wanda baza iya fassarashiba. Kowaye kai idan ka kallesu sesun baka tausayi, tab ɗijam ashe akwai abinda zesaka mejo najeeb kuka aduniya haka cikin sauƙi, general Aliyu yafaɗa azuciarshi.Ahankali Alhaji abdussalam yariƙo hannayensu dake maƙele dajuna, azabure suka ƙara ƙanƙame jikinsu wuri ɗaya domin sun ɗauka tabasu zeyi, hakama mutanen dake wurin har nazeer yafara faɗar no Abey no please,,, shikanshi Alhaji abdussalam seda yasaki murmushi ganin yadda suka ƙara yiwa junansu…sekawai sukaga yasaka hannun Isseta acikinna mejo yana murmushi. Ɗagowa sukayi atare suna kallonshi fuska gaja’gaja da hawaye😹 “jinjina musu kai yayi kana yafara magana cikin Dattako “haba yaran kirki miye nakuka kuma ai dama kaine mijin nata niban san cewar kaine aka aurawa itaba tabbas wannan haɗin naku na Allah ne domin tun ranarda aka haifeta nace anhaifawa najeeb ɗin Maryama mata kuma nagayawa mahaifiyarta koda bana raye idan tagirma batada wani miji se kai segashi kuma dudda cewar ba’ahannun mu tagirmanba Allah yayi cewar kaine mijin nata, Masha allah haƙiƙa wannan abun yayimun daɗin fiyeda tunaninku irin wannan soyayyar haka, uhm Maryama kinsakamun yaro kuka duk sabida ke? Yafaɗa cikin zolaya yana murmushi…ganin haka yasa mutane dayawa awurin sauke ajiyar zuciya cikin farin ciki sunabinsu da kallon sha’awa…duƙarda kai mejo yayi ƙasa yana murmushi yayinda isseta taturo ɗan ƙaramin bakinta gaba. “Au ai itama yasaka kukan karkawani tutsiyemun ƴa kuma ai duk kaine kajanyo sunaji suna gani kana neman tabasu, Abba yafaɗa shima yana dariya. “Ahh ai kuma ban isaba khamis irin wannan so hakan idan nace narabashi ai Allah ma baze barniba koda kuwa bashine dama wanda zanbawa ba bazan rabasuba awannan yanayinkam balle kuma shine, sabida hakan ba’abinda zance sedai Allah yasanyawa rayuwar aurenku albarka tare da zuri’atagari…Ameen y jabbarul Aziz..cikin tsokana innar halima tace to yarinyar Ammi kuka yaƙare ko ga amminki kaguma ɗanta yazama naki duk ke kaɗai..aiko duk aka saka dariya musamman samarin wurin da yammatan kowannensu yana cikin farin ciki. Ita kuwa Isseta cikin sauri taɓoye fuskarta a ƙirjin mejo tana dariya, hakan yagame hannayenshi yaƙara sakata ajikin nashi nashi. Bawanda yace musu komai domin sunsan wannan duk aikin so ne idan akwaishi ba’aganin kowa da komai balle wata kunya tabiyo baya……ahakan akashiga sabuwar fira anata barkwanci da bada labarin abubuwan dasuka faru wa juna tsakaninsu, wani suyi dariya wani suyi alhini. Ahakan aka gabatar musu da abinci gakuma abubuwan sha anan tsakiyar general perlor megirma gwamna suka baje sunacin abincin suna nishaɗi da juna…innar halima da mama bintu se zancen zuci sukeyi aransu, komai dalili kan kawo dalili yanzu dalilin Maryama sunacin abinci acikin gidan gwamna kuma tareda shi da iyalinshi gakuma shugaban ƙasar Niger danashi iyalin sukuwa mizasuyi Allah inba godiyaba.Aranardai anan suka wuni maganar tafiya babuta doli se gobe, dadare yayi samarin sukace zasuje hotel sukwana zuwa gobe sunɗauki hanya domin akwai abinda zasuyi..iyayen sukace bakomai. Babu kunya mejo yace “mamana zomuje ko Kinga gobe da sassafe zamu wuce.. “taje ina? Ai kuma se bayan wata biyu keda ganinta domin se munji ɗiminta atare damu, cewar Ammi…ido yazaro cikin tashin hankali yace “nashiga ukku dan Allah kimin rai Abba kanajinta ko zata ɗaukemun mata please Abba kasaka baki dan Allah. Dariya dukkansu sukayi cikin Dattako Hajiya Hannah tace “rabuda ita ɗana bazata ɗauke ma mataba amma kayi haƙuri zamuje da ita Niger kaima sabida aikin dazakuyine yasa bazamuje dakaiba amma mako ɗaya kawai zatayi sabida family wanda basu samtaba kaga sunganta kuma inaso taje taga abbana idan tacika mako ɗaya kaje kaima mutane shuganka seka dawo da martaka kajiko..’toh mammey amma fa batada lafiya yafaɗa kamar yadda yaji fawan yakirata ɗazu amma sam bahakan yasoba…eh in sha Allah za’akula da ita karka damu..toh kawai yace domin ba yadda zeyi…cikin tsokana general Aliyu yace “au waida nufinka kajeda little mom mukuwa kabarmu ai wlh baka isa inkuwa hakane Nima zanje da halima Abba dan Allah Nima azo ayi magana nagafa matar aure anan domin naga alama idan banyiba wata rana mejo cewa zeyi yahaifeni..ido halima tazaro tana kallonshi. Shikuwa Abba cewa yayi Masha allah wacece kagani my son?? “Gata kuwa Abba wannan ƙawar ta little mom itace Nakeso Please dan kunema mun aurenta. “Ikon Allah to kai hakan akeyin abu kaitsaye bazaka fara neman yardar yarinyarba? Cewar Dady…shikuwa general Aliyu murmushi kawai yayi yana sosa ƙeyarshi….halima kuwa cikin sauri taɓoye fuskarta bayan Ammin isseta domin wata irin kunya taji tarufeta….cikin farin ciki Abba yace “Masha allah aiko abu yayi kyau in kuwa hakane zamu nemi iyayen yarinyar gobe kafin muwuce kaiko seka nemi yar dar ta..”wayyo Abba na shiyasa nake sanka wlh ngd sosai my sweet Abba, yafaɗa cikin farin ciki. “Abba to nifa, cewar general Faruk? Ikon Allah kaima ummaru Kanada wadda kakeson ne? Abba ya tambaya…cikin jin kunya general Faruk yace “ai doline nayi Abba kar waƴannan sufaramin gori inada ita. “To wacece? Cewar Dady… ahankali yanuna musu ummi dakecan gefe suna fira itada mufeedah…tofa ummi cewar Abba. “Eh Abba..Masha allah to ai Ummi kam ƙanwarku ce kanemi yadda ta kawai idan ta amince semu saka ranar aure. Wani irin daɗi ne ya lulluɓe general Faruk har besan lokacinda yafara yiwa Abba godiyaba……cikin kwaɓe fuska nazeer yace tonima Abba abani Allah dan bazsn yadda ba kuma Nima cikin waƴannan za’abani gatanan me green color ɗin kaya..ido suka zubawa ƴammatan sunaso suga me green ɗin kaya, itake idonsu ya hango musu mufeedah datayi wani tsuru tsuru da ita duk tashige gashi…ikon Allah kucedai duk kwashe mana ƴammatan zakuyi to ai kaima nazeer ƙanwarku ce kanemi yardar ta kawai. Ahankali isseta yaɗago daga jikin Ammi tana kallon fawan dakebinsu kawai da ido “yayana. Takirashi sabida sunada kusanci sosai da ita yasa yagane dashi take. “Na’am lattey ya’akayi ne? Murmushi tayi kana tace bakomai “naga duk sun ɗauke mun ƙawaye ne amma kai baka ɗauki ko ɗaya ba ko Kanada mata ne?? “Murmushi yayi shima kana ya marairaice fuska yace “a’a ƙanwata banida ita ko budurwa banada kuma Kinga sunmin wayo kowa yasamu anan. “To shikenan idan kanaso zan samoma dakaina inada ƙanne biyu acikinsu kaɗauki ɗaya zubaida da jidda amma zubaida itace sa’ata jidda ƙarama ce sosai. “Wow ƙanwata garadai zubaidan tunda itace babba amma kyakkyawa ce kamar ke da kyawun hali? Ya tambayar cikin tsokana. “Eh mana tama fini kyau sosai ma. “Kai mamana banyanda ba nikam babu macenda tafi matata kyau kima dena haɗa ta dake please kilawa mummuna ce, mejo yafaɗa shima yana dariya. Dasauri fawan ya kalli Alhaji Abubakar yace “Dady kagsnshi ko. “Najeeb zansaɓa maka fa matar yarona kyakkyawa ce itama…aiko duk aka saka dariya…shidai Alhaji abdussalam da ido kawai yake binsu yana murmushi yayinda yakejin kamar su dawwama ahakan…mlm Musa kuwa da mama bintu kallo isseta kawai sukeyi suna jinjina girman kyawun halinta wato dudda cutarda ita da matan gidan sukayi yau ƴaƴan su take nemawa mijin aure mijinma na nunawa sa’a ga kuɗi ga kyau ga ilimi, Allah ya saka mata da alkhairi..ahakandai su mejo suka tafi hotel dukkansu harsu nazeer. Yayinda mama bintu da mlm harda innar halima suka koma gida amma Ammin isseta da halima basubi inna ba. Ɗaki ɗaya aka basu. Dukkansu ƴammata isseta halima mufeedah Ummi, anan suka buɗe sabon babin fira se zancen zaratan samarin suke suna dariya yayinda ƙasan zuciyar ko wacce take marhabin da nata gwanin…..seda dare yayi sosai kana Ammi tashigo takira isseta domin kayan gyaran mata ne suka saka akasiyo musu itada Hajiya Hannah sabida sun ɗan ɗauki hasashen abinda ke damun ƴar tasu, Ammi dakanta tashiga gasawa isseta jikinta seda taji Takoma dede tukunnah tabarta.Acan hotel ɗin ma sabon babin fira suka buɗe kamar damacan sun saba dajuna abin mamaki yau ga mejo najeeb da fira haddasu dariya…sukuwa se tsokanarshi sukeyi wai yazama Romeo basu saniba.LagosTunda Hajiya umma tafita bata dawo gidanba se cikin dare tadawo wujiga wujiga,,, Hajiya mama na general perlor itada su munir tana basu labarin tafiyarsu mejo tashigo duka yaran da kallo suka bita Munir da sajad hakama auta siyana amma ba wanda yayi yun ƙarin Binta. “Wai mama lafiya dai naga umma tafita tunɗazu se yanzu tadawo? Cewar sajad. “Wlh bansaniba sajad amma ina tunanin maybe lafiya sabida batacemun wani abun yafaruba. To Allah yasa lafiyan..ameen, ta amsa mishi…shidai munir bece musu komai ba domin shi wasu lokutan mamaki lamarin mahaifiyar tashi kebashi..Gombewashe gari da sassafe sukayi shirin tafiya dukkansu seda sukaje gidan gwamna sukayi sallama dasu Alhaji abdussalam kana samarin duka suka karɓi nomber ƴammatan tukunnah su mejo dasu Abba suka ɗauki hanyar Lagos..Bayan tafiyarsu suma su Alhaji abdussalam suka shirya tafiya anan sukayiwa megirma gwamna godiya akan karamawar dayayi Mishi dakuma gudun muwarda yabada wurin neman ƴarshi. Sosai megirma gwamna yaji daɗin ziyarar Alhaji abdussalam haka suka rabu cikin aminci dakewar juna….daga gidan gwamna basu wuce airport ba cikin gari suka wuce inda kaitsaye sukaje gidansu isseta…sosai mutanen gidan sukayi mamakin ganin iyayen isseta na asili tuni suka rena kansu..anty hawwa ma datayi wani zuru’zuru da ita sabida kukan datasha narashin mejo ajiya kawai ta ƙuntata rayuwarta dan seda sukaci uban dambe itada juwaira daga baya kowannesu yarungumi sorry…jidda da zubaida kuwa baƙaramin farin cikin ganin isseta sukayiba kuma sunji daɗi sosai da mijinta yakoma mata kamar yadda suke fata bayazauna da Anty hawwa ba…su iyya hassi da mamansu ya balah hadda kuka wurin neman isseta gafara. Ita dai batace musu komai ba se Hajiya Hannah ce tace suje bakomai komai yawuce…anan suka gayawa mama bintu zasuwuce ne Niger sukayi mata goma sha biyu na azziki tukunnah suka fito, isseta ta haɗa yayanta fawan da zubaida kuma tanemi alfarma agun mama salmu nacewar zataje da jidda garinsu. Mama salmu kan baki har kunne ta amince. Yaya balah da sauran yaran gidan duk sunrena kansu sabida abinda suka riƙa yiwa baiwar Allah gashi yanzu ko takalmin ƙafarta yayi musu nisa…yaya Kabir kam baki har kunne yaron wurin mama bintu sabida yaga ƙanwarshi kuma cikin kyakkyawar kama….haka suka baro gidansu isseta sukaje gidansu halima. Sosai Alhaji abdussalam yayiwa innar halima alkhairi wanda baze faɗuba hadda su kujerar hajji yakuma gaya mata zeturo acanza mata gida..daganan suka nemi alfarman tafiya da halima sabida taga dangin isseta.. ai kuwa babu mata lokaci inna ta amince, sosai sukayi kukan rabuwa tsakanin innar halima da Ammin Isseta daganan suka ɗauki hanyar airport suna zuwa basu wani jimaba jirginsu yatashi zuwa Niger..Su mejo kuwa seda sukayi nisa atafiyarsu sunshigo cikin jeji kenan sukaga an tare musu hanya an ɗora manyan itatuwa ahanyarsu…cikin mamaki suka fito suna tunanin mi hakan kenufi badai ƴan fashine suka taresuba, kowannensu dayayi wannan tunanin seda yasaki murmushin gefen baki, kafin susamu amsar tambayarsu kawai sukaji ana musu ruwan alburushi tako ina…..!


