Halysaah Page 114 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 114Khaleesat dai na tsaye tana ta kallon yanda motoci ke ta zuwa daukan masu sarauta zuwa gida kuma babu wanda ya bi ta kanta, Hadiyah sai aikin makale ma Jay dake rike da graduation folder dinta da wayarta take duk inda yayi sai ta bi sa, a hankali Khaleesat ta bude jakarta ta ciro wayarta, call log dinta ta shiga tana ta kallon number Ajay, can dai tayi dialing number ya fara ringing amma har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa nan ma no reponse, jira tayi taga ko zai biyo kiran amma still har bayan 15 mins bai kira ba, mayar da wayar tayi cikin jaka cikin sanyin jiki, ta ci gaba da bin kowa na wajen da kallo, duk baƙin da suka zo taya Hadiyah murna sai da aka tabbatar an maida su masaukin su, ya rage iya Cousins dinta kawai da 3 of Her friends ne a wajen sai Jay, Jay na son ce ma Khaleesat ta je ta hau mota ganin she is just standing amma bai san ta ya ba saboda yanda Hadiyah ta makale masa not even giving him a breathing space, Khaleesat na hada ido da Walid da ya dawo wajen ta sauke idonta kasa, ya nufi har inda take tsaye yana kallon fuskarta yace “Hey, mu je inyi dropping din ki a gida ko?” Da kyar ta daga idonta tace “Yace min yana zuwa in jira sa” Yana mata wani kallo yace “A ina ku ka sauka?” Ta girgiza masa kai tace “Nima ban san wajen ba” Wani shegen murmushi yayi mata yace “Za mu hade….” Daga haka ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo zuciyarta na bugawa, har kasan ranta take tsoron Walid da Aunty, Duk Jay na lura da su kuma duk tunaninsa da Walid yaje wajenta zai ce mata su je yayi dropping dinta a gida ne amma sai kuma yaga ya tafi ya bar ta tsaye wajen, a hankali Khaleesat ta sake bude jakarta ta ciro wayarta tayi dialing number Ajay, har ya katse bai ɗaga ba nan ma, ta sake kiransa no response again, jiki a sanyaye ta mayar da wayar cikin jaka gashi ta gaji da tsayuwa, After some more minutes Jay ya juya ya kalleta, sai kuma ya dubi Hadiyah dake making phone call, ya jira har ta gama sannan yace “Hadiyah go and tell her to come over ku tafi gida it’s getting late, the second car is back….” Hadiyah na kallonsa tace “Who?” calmly yace “Halysaah” Da wani expression tace “Wacece kuma haka?” Bai sake tanka ta ba, ta juya masa kunnenta tace “Ni dai cire min dankunnen nan Honey, it’s very tight….” Yace “Ba gida za mu tafi ba why remove it?” Ta hade rai tace “A’a just take it off pls, I am not comfortable with it” Bai sake ce mata komai ba ya kai hannu ya fara cire mata dankunnen nata, yana cirewa ya daga kai ya kalli Khaleesat da tayi masu kallo daya ta dauke kai, ya gama cire earrings din ya mika ma Hadiyah tayi masa side hug tana kallonsa tace “Thanks love” Khadijah ya kira bayan ta iso wajensu yace “Je ki ce ma Halysaah ga mota yana jira za ku tafi gida” Hadiyah ta wani hade rai tana kallonsa tace “C’mon Honey ba fa tare muka zo nan da ita ba, definitely mijinta ne zai tafi da ita since they came together, jiya ma ai shi yaje ya dauketa daga can gida suka yi tafiyar su” Khadijah tace “Tare fa suke da Ya Junaid and he is somewhere around here, salon mu tafi da ita mu yi masa laifi, balle ma ya nuna baya son ta zauna cikinmu, gwara kawai a bar masa ita kawai Ya Jay ba ruwana da jarabansa” Jay dai bai ce komai ba ya ciro wayarsa dake ringing yaga Mami ke kiransa, picking call din yayi ya koma wani wajen ya tsaya yana answering call din nata, bayan ya gama wayar kawai ya ɗan kalli side din su Hadiyah kafin ya juya ya nufi Khaleesat, har ya isa inda Khaleesat take tsaye bata yarda ta kallesa ba yace “Ga mota can ki tafi ki shiga a maida ke gida, or are you waiting for anyone to pick you up?” Tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta daga kai ta kallesa a hankali tace “Nace ina son magana da kai” He was quiet for few seconds bayan ya dauke idonsa daga kallonta, ganin Hadiyah ta nufosu don sai a sannan ta kula ya tafi wajen Khaleesat, yace “Let’s chat, ki je ki shiga mota kawai” Nuna mata inda motar yake yayi, ta juya ta nufi wajen tun Hadiyah bata karaso wajensu ba, shi kuma ya ciro wayarsa ya kira driver din ya ce masa ya tafi da ita kadai ba sai ya dauki kowa ba a motar, Hadiyah ta hade rai bayan ta iso gabansa tana kallonsa tace “Dole ne sai kayi magana da ita ne Baby? Shi mijin nata da ya kawota bai san zai maida ta ba? What’s ur business with her??” Jay ya kalleta strictly yace “It’s my duty to make sure everyone leaves here to their various destination Hadiyah, stop questioning me” Hadiyah ta ɓata fuska tana kallonsa, ya ja hancinta yace “To yi kukan mu ga” juya masa baya tayi, ya kamo hannunta ya juyo ta yace “Zaki fara ko” Ko da wasa Khaleesat bata yarda ta juya ba har ta isa gun motar, tana shiga ciki driver ya ja suka bar wajen, gaba daya jikinta a sanyaye yake, nan ta fara tunanin ko kawai ta gaya masa sunan hotel din da Ajay ya kai ta jiya yayi dropping dinta a can a maimakon gida don ita tsoron zuwa wannan apartment din take bata san me zata je ta tarar ba, gaba daya family din ma tsoro suke bata she is not comfortable staying together with them, tun bata bari sun yi nisa ba kawai ta gaya masa ya kai ta hotel din, haka kuwa aka yi bayan kusan tafiyar minti ashirin da biyar suka isa babban hotel din, ta bude motar ta sauka tayi masa sai anjima sannan ta shiga cikin hotel din ta wuce sama, a hankali ta bude kofar dakin ai kuwa taji sa a bude ta shiga cikin dakin closing the door gently tana kallon Ajay dake kwance kan gado yayi rub da ciki yana bacci ta can ɓangaren gadon ba inda ta kwanta ba daren jiya, haushi ya cikata lokaci daya ta hade rai, shine zai yi tafiyarsa ya bar ta ita kadai a wajen ya dawo nan yana bacci abunsa, shi yasa take ta kiransa no response, tana tafiya a hankali ta karasa cikin dakin ta ajiye handbag dinta ta cire mayafin kanta ta sauke gashinta da ta nannade sannan ta fara cire jewelries din jikinta gaba daya ta ajiye su saman bedside drawer, ta cire rigar jikinta kenan ta ajiye gefen gado zata dau doguwar rigarta dake linke ta ajiye saman akwati taga ya bude idonsa a hankali sae a cikin nata, zaro ido tayi with shock ta durkusa kasan dakin da sauri ta rufe fuskarta da gado taji kamar kasa ya bude ta shige don she is just wearing bra and pant, kauda kansa yayi daga kallonta ya mayar zuwa daya side din dakin ya lumshe idonsa, Khaleesat tafi minti uku bata dago kanta daga boyewar da tayi jikin gado ba tsabar kunya, a hankali ta lalubo rigar da ta cire a gefen gado, tana durkushe a haka ta saka rigar don ta kasa tashi tsaye, bayan ta mayar da rigar ta dago kanta a hankali taga har sannan yana facing daya bangaren dakin, da kyar ta mike kamar munafuka ta shiga banɗaki don bata yi la’asar ba, ta kulle kofar bandakin ta jingina jiki tana turo baki, ta fi minti goma a toilet din ta kasa fitowa duk da ta gama alwala, daga ƙarshe ta dake ta fito sai taga ya ma fita daga dakin, ita dai har lokacin kunya bai saketa ba, da ta sani bandaki ta tafi ta canza kayan, she thought he was sleeping deeply shi yasa har ta cire kaya a dakin. Ajay na zaune dakin da Hajja take wajen karfe bakwai da rabi na dare yana sauraronta, Aunty da Gimbiya Firdausi da Hajiya A’isha duk suna zaune dakin su ma ko wacce ta murtuke fuska, rai bace Hajja taci gaba tace “To ina amfanin tahowa da ita in haka ne? Aikin banza kenan ai in dai zaka kai ta wani waje ka ajiye bayan kasan al’adar mu ba haka take ba, sam baka dau al’adun mu a bakin komai ba Junaid a haka wai kuma kai ne Yarima me jiran gado, ke kuma Fulani wannan maganar ma har sai kin gaya ma Sarki? Akan me zaki gaya masa?” Gimbiya Firdausi tace “To baya ganin kowa da gashi Hajja, baya mutunta kowa, gwara da ta gaya ma sarki don shi kadai yake gani da mutunci kuma bazai ki jin maganar sa ba, banda raini da walakanci yaushe zai dauki yarinya bai ji kunyan idonmu ba ya kai ta wani wajen ya ajiye bayan yasan duk waje daya ake sauka idan sha’ani irin haka ya tashi, ita yarinyar er gidan uban wacece ita da bazata zauna a gidan nan ba? Wani irin fi’ili ne wannan yake son shigo mana da shi family? Ko akan sa aka fara aure? Auren nasa ma auren joni” Hajja ta kalli Junaid tace “Ka je ka maidota gidan nan har zuwa sanda za ku bar kasar nan da daddaren nan ba sai gobe ba, in ka san bamu kai ta zauna gida daya da mu ba da ka bar ta can Amurka kayi tahowar ka kai kadai tunda kai ne dolen Hadiyah ba ita ba” Aunty da Hajiya A’isha suka gyada kai alamar dai dai kenan yaje ya dawo da ita, After few seconds Ajay ya kalli Hajja calmly yace “Why is it a must sai ta zauna gidan nan? What if I have my reasons for taking her away?” Gimbiya Firdausi tace “Kin ji ko Hajja? Ai in bai yi fitsara ya nuna ba a isa da shi ba bazai ji dadi ba, reasons dinsa na banza da hofi, ita din nace er gidan uban wacece da bazata zauna nan ba? Mu da muke jinin sarauta bamu ce baza mu zauna da ita ba sai ita da ba kowan kowa ba kowar wake? Who the hell is she? Wallahi kar ka bari in yi mugun saɓa maka a kasar nan idan kace zaka kawo min iskanci Ahmad, ni ba sauran iyayenka da ka raina bace yanxun nan zan gyara maka zama wallahi, kuma ka sanar mana er gidan uban wacece yarinyar da tafi karfin zama cikin mutane….” Ajay ya kalli Hajja yace “Saboda wata al’ada can idan ina bukatar matata sai in ki tafiya inda zan tafi da ita kenan? Al’adar ce ta haramta in kebe da ita if the need of that arise?” Kallonsa su Aunty suka dinga yi da mugun mamaki jin kalamansa, duk kowa yayi shiru a dakin kamar anyi ruwa an dauke, can Hajja ta gyara zama tace “To kun dai ji bukatar ta yake, yana bukatar matarsa a kusa da shi don haka sai ku hakura da mita kuma haka tun da ya bada uxurin sa, kin ga ba reason din banza da hofi bane kamar yanda kika ce ke Firdausi, yi tafiyar ka sai da safe Junaid, ga abinci nan ba ci zan yi ba sai ka tafi maku da shi, Allah ya tashe mu lafiya” Yace “Ameen, sai da safe” Mikewa yayi without looking at anybody ya dau warmer din abincin ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hajja tace “Tun da bukatar ta yake kun ga ko ai baza a tauyesa ba saboda wani dalili mara tushe, ku bar su kawai su yi zaman su a can, yaran yanxu ba kunya gare su ba kun dai ga kansa tsaye ya bada uxurin sa, yana kuma da gaskiya, shi yasa nace da ba a gaya ma Sarki ba, gashi nan dai kun ga yafi mu gaskiya….” Gimbiya Firdausi tace “Da yake shi fitsararre ne mara kunya ba, ya kamata ya kalle mu ya gaya mana wannan magana idan ba raini ba? Idan Jawwad ne yaushe zai yi haka?” Hajiya A’isha tace “Ai Jawwad bazai ma taɓa dauke matarsa idan ana sha’ani ba balle ya kawo mana zancen rashin kunya” Gimbiya Firdausi tace “Da yake shi ya koshi da tarbiyya ba, kin taɓa ganin yana musu da na gaba da shi ko kuma ace yayi abu yace bazai yi ba shi ga yanda zai yi?” Hajja ta hade rai don no matter what ta tsani a dinga maganganu kan Ajay, tace “Don yace yana bukatar matarsa sai kuma ya zama abun magana? Haramun ya aikata? Babu warce tafi sa gaskiya akan wannan batu duk inda za aje kuwa, laifi ne don ya fadi uxurinsa da za ku dinga hadasa da Jawwad? Naga dai halinsu ba daya ba, in Jawwad ne ko uxurin zai kashesa bazai yi magana ba, shi kuma Junaid bai yarda ya cuci kansa ba, he speaks for himself always, don haka bana son in kara jin maganar Yarima ya dauke matarsa a gidan nan” Babu wanda ya sake cewa komai a dakin ko wacce ranta babu dadi tsabar takaici da bakin ciki, can Gimbiya Firdausi ta mike ta fice daga dakin, Aunty dai takaici sai da ya saukar mata da wani mugun migraine headache nan take a wajen, kalmomin Ajay sai yawo suke mata a kai, wai yana bukatar matarsa, abun har ya girmama haka bayan duk shige shigen da take a can Nigeria, sosai hankalinta yayi matukar tashi a wajen… Ajay na sauka downstairs ya tarar babu kowa parlor duk yan matan gidan na Bedroom a sama, kitchen ya nufa zai dau plate da spoon, shi ba cin abincin zai yi ba don ya sha shayi, Khaleesat zai kai ma idan taga zata ci duk da bai ma yi niyyar kai mata ba, yana shiga kitchen din ya tarar da Jay da Hadiyah makale da juna, within seconds suka yi separating, Ajay dai har ya juya ya fita daga kitchen din ya bar warmer din abincin a nan parlon tunda babu plate yayi tafiyarsa… After a while Aunty ta tashi ta fita daga dakin Hajja tana jin ciwon kanta na tsananta, dakin da Gimbiya Firdausi suke ciki ta nufa amma sai taji kamar suna magana da Hajiya Sumayya kasa kasa, har sai da ta kasa kunne jikin kofar dake bude slightly bayan ta tabbatar babu wanda ke tahowa daga downstairs sannan ta iya jin abinda suke cewa, Ta ji Gimbiya Firdausi na cewa “To ai naga alamar wankin hula na neman kai ni dare ne Sumayyah, ina ga a duk masarautar mu babu wanda ya kai ni ƙin auren yarinyar nan da Junaid, yau ace yarinyar nan tayi ciki ta haihu a masarautar nan shikenan magana ta kare kuma, kin ga idan Allah ya bata namiji Yarima ya samu Magaji kenan fa, wanda hakan na nufin wataran dole ɗan nan da zata haifa yayi sarauta, yaron da uwarsa ba kowa bace facce er matsiyata er talakawa mara asali, Sarki yaki fahimtar cewa yanzu ba a auro bare a shigo da ita gidan sarauta, an dena wannan gangancin, ga ‘ya yan ‘yan uwa kaca kaca da ya kamata ace ya aura ma Junaid daya kamar yanda Jawwad ya auri Hadiyah, sannan yarinyar nan fa Bazawara ce ba budurwa ba babban abun takaicin, Sumayyah har yanxu fa ban hakura batun sai Junaid ya auri Shahuda ba, yau ace Shahuda ta auri Junaid kin ga dai saurauta kara kusanto mu yayi ba nisa yayi mana ba….” Hajiya Sumayyah tace “Kwarai kuwa Gimbiya zancen ki hakkun, yanxu kamata yayi a tado da batun Shahuda gadan gadan idan mun koma gida, kin san dai kina daya daga mutanen da sarki ke jin maganar su, amma ki bari mu koma Nigeria sai mu tsara yanda za mu yi cikin tsanake, nasan kilishi ma baza ta rasa abinda zata ce ba akan lamarin nan don ita ma tana bakin ciki da wannan aure, nasan ita kanta zata kawo solution din matsalar nan” Gimbiya Firdausi tace “Haka ne, Allah ya maida mu gida lafiya” Hajiya Sumayyah tace “Ameen, ana wani cewa ai shi ma Junaid din bai san da auren ba sai bayan da aka daura, a yanxu kam na ƙaryata hakan, bana jin zanyi kaffara idan na rantse cewar Yarima na sane da shirin Sarki, sarai ya san da auren kuma alamu sun nuna yana son yarinyar shi ma, banda haka ki ga fa shigar yarinyar na yau, komai na jikinta designers ne tana er matsiyata da ita, kuma ba wai kayan cikin lefe ba, don kaf lefenta babu irin wannan kaya masu zunzurutun kudi haka, duk designers ne jikinta fa Gimbiya, da nayi estimating kudin shigar nan da tayi yau sai da nayi takaici, wallahi duk yanda za muyi ma dole mu yi a kawo karshenta a gidan nan don bata da ce da zama matar ɗan sarki me jiran Gado ba, Shahuda ce tayi deserving wannan matsayin ba ita ba” Gimbiya firdausi ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace “Allah ya maida mu gida lafiya Sumayyah” Aunty tayi wani makirin murmushi bayan duk ta gama jin conversation dinsu tana gyada kai a hankali, a ranta kuwa tace “Sai dai in ni Hafsah bana numfashi ne za ku aiwatar da wannan nufi naku, amma baku isa ku wargaza min nawa shirin ba wallahi, Shahudar banza, ban gama da dayan nan dake gabana ba ku ke neman karo masa daya, gwara da aka yi akan kunne na, mu zuba da ku…” Juyawa Aunty tayi da sauri jin Footsteps, ta hango Jay yana haurowa sama hakan yasa ta bar bakin kofar da sauri, ta karasa har wajen stairs din kamar sauka zata yi, cikin nutsuwa tace “Jawwad yau ɗan uwanka ya shayar da mu ruwan mamaki” Jay dai kallonta yake yana haurowa don yasan Ajay take nufi, Aunty tace “Muna ta fadan bai kamata ya dauke matarsa ba bayan ba haka al’adar mu yake ba ya kamata ace ita ma tana gidan nan ayi komai da ita, buden bakinsa sai cewa yayi shi yana bukatar kebewa da ita ne shi yasa ya tafi da ita saboda uxurinsa, bai ji kunyan idanuwanmu ba ya fadi haka kansa tsaye, Hajja kuwa ta hadasa da Warmer din abinci tace sae da safe, is this proper Jawwad?” Jay dai bai ce komai ba yana tafiya slowly bayan yaji abinda Aunty tace…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788*
