Karfe A Wuta Chapter 25 By Ayshercool
Dukan gefen katifar da take kai yayi, amma ba ta motsa ba, ya zura kai ya leƙa fuskarta, ya ga bacci take yi. Duk da bai saba zuwa ya tarar da ita tana bacci ba.Ficewa ya yi, ya bar ɗakin, shi babban takaicin sa, rashin samun abun da zai ci.Jauhar kuwa, tun dare ta kwana ta na fama da matsanancin ciwon mara, ga ulcer ta tayar mata, sai gudawa take fama da tashin zuciya, ta samu ya lafa mata, ta kwanta ta hau bacci ga gidan yau babu abun da za ta dafa, ɗan kuɗin hannunta sam ba su da yawa.Ƙarshe dai buredi ya fita ya samo, ya dawo ya zauna a falo yana ci.Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba ya ga kiran indabo ne, kallon wayar ya cigaba da yi, yana cin buredinsa, sai da ta kusa katsewa ya ɗaga ya saka a kunnensa, yayi shiru.”Aminu””Mmm””Na dawo, kai nake jira, haryanzu ba ka zo ba””Zan zo””Yaushe kenan? Haba kai kuwa dan Allah, ba ka san kiran me nake yi maka ba fa”Al’amin ya ce “Na ce zan zo ai””To shikenan, Allah ya kawo ka”Ya ajiye wayar, gaba ɗaya haushin buredin da yake ci ma yake ji, sam ba ya yi masa daɗi, har aka yi kiran la’asar, ba ta fito ba.Ya tashi yayi salla, ya fito falo ya sake zama, sai ga ta ta fito tana ɗan yamutsa fuska. Fuskar duk ta ɗan ɗaga tayi jawur.Ta zo ta nemi wuri ta kwanta, ba tare da ta ce masa komai ba.”Wai yau ba abinci ne?” Yayi maganar yana wani basarwa.Maimakon ta ce masa babu abun da za ta dafa ne, sai ta ce masa “Ba na jin daɗi ne”Ya taɓe baki, ya tashi ya saka takalmansa ya fice daga gidan, fitarsa ba kaɗan, ta ji horn da tsayuwar mota a ƙofar gidan, mintuna kaɗan ta ji ana bugun gate, ta saka hijjabi ta je ta buɗe.Baba ta gani a tsaye, cikin matsananciyar murna ta ce “Baba” yayi murmushi ta ba shi hanya ya shigo.Suka isa har falonta, ya samu wuri ya zauna ta ce “Baba meyasa baka kuma zuwa ba?” Tayi maganar hawaye na cika mata ido.Wani irin matsanancin tausayinta ya kama shi, har ya ji kamar shi ma ya yi kukan, amma ya danne ya ce “To ba gani na zo ba, Waliyiyya ‘yar baba””Baba babu wanda ya zo mini, sai yaya saifu da Anty lubabatu, kowa yaƙi zuwa in da nake, wai ba za su zo ba, mijina ɗan daba ne, kuma ba abun da zai yi musu, ba ruwan shi da su.Baba ya ce “Waliyiyya, ki daina saka irin wannan abubuwan a ranki, kar su dameki, ki yi haƙuri ke mai haƙuri ce, amma ki ƙara. Ya gidan ya mijin naki?”Cikin jin kunya ta ce “Yana nan lafiya, yanzun nan ya fita””Jauhar, ina fatan dai babu wata matsala dai ko?” Ta girgiza kai ta ce “Babu”.Turus yayi ganin takalma a ƙofar falo, amma ya ƙarasa ya shiga, ba tare da ya yi sallama ba.Kallo ɗaya ya yi wa mutumin, ya ga yana yanayi da jauhar ya ƙarasa cikin falon, hannunsa riƙe da baƙar leda.Durƙusawa yayi har ƙasa ya ce wa Baba “Ina wuni” hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa jauhar ba, dan tun da ta ji motsin shigowar sa, take fatan Allah ya sa kar ya yi wa baba wani abun na rashin ɗa’a.Baba ya ƙare masa kallo, kai ba ka ve mara ji bane ba, dan a cikin nutsuwarsa yake, ya ce “Lafiya ƙalau malam Aminu, yau dai Allah ya yi mun haɗu, ya gidan ya iyalin naka”Ya amsa da “Lafiya ƙalau”.”To masha Allah, Ubangiji Allah ya yi muku albarka, ayi ta haƙuri, ka san ita rayuwar aure, zama da mace sai haƙuri, dole za ku saɓawa juna, ayi ta haƙuri. Ba yabon kai ba, na san Waliyiyya yarinyar kirki ce, amma duk da haka na san dole wataran a saɓa Allah ya yi muku albarka”Ya amsa da Amin, ya tashi ya bar wurin ya tafi ɗakinsa.Ta ce “Baba bari na dafa maka abinci” ta faɗi hakan, dan kar baba ya fahimta wani abu.Baba ya ce “A’a, zuwa na yi dama na ganki, ni da ba a san da zuwana ba”Jauhar ta ce “Dan Allah baba ka tsaya”Ya ce “Gidanku ba zan tsaya ba, kira mini mijinki, zamu yi magana”Ta tashi ta shiga ɗakinsa, ta ce “Master, baba yana son ganinka”.Ya jinjina mata kai, ya tashi ya fito, ya samu wuri a ƙasa ya zauna.Baba ya ce “Malam Aminu dan Allah alfarma zan nema, ka san jauhar ba ta kammala sakandare ba, an fara registration ɗin WAEC ne, shi ne na ce ina neman alfarma, zan biya mata tayi registration ta yi jarrabawa dan Allah”.Aminu ya ce “Babu damuwa, Allah ya bada sa’a”.”Amin Aminullahi, Allah ya saka da alkhairi” Baba ya miƙe ya ce zai tafi.Cikin rauni ta ce “Baba daga zuwanka sai tafiya kuma?”.”To Waliyiyya ba dai na ganki ba”.Kamar mara gaskiya, haka ta biyo bayan baba, a tsakar gida ya tsaya ya kalleta ya ce “Jauhar menene?” Ta girgiza masa kai alamar bakomai.Ya juya zai buɗe gate, ta riƙe rigarsa ta fashe da kuka.Ya ce “Subhanallah, gaya mini menene? Wani abun yake yi miki?” Girgiza masa kai ta sake yi.Ta cukuikuye rigarsa, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, shafa kanta ya dinga yi sai dai ya kasa hanata cigaba da kukan.Sai ma hannu da ya sa, yana goge hawayen da suke ƙoƙarin zubo masa, ya san ba zata faɗa masa koma menene ba, amma yanayinta ya nuna masa tana da damuwa.Dan kanta ta cika masa riga, ta goge hawayenta ta ce “Ka gaida gida baba, ka ce ina gaida su mama da Anty da kowa da kowa”Yayi ajiyar zuciya ya ce “Za su ji in sha Allah, gashi ke ba waya ba, ranar talata ki je ki samu malam Hadi, a office ɗin su, zaki yi thumb print, yayi miki registration”Ta ce “To baba, na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi” ya fita ta rufe gate ɗin, ta jingina da jikin gate ɗin, hawaye na cigaba da zuba daga idonta.Duk yadda suka yi, Al’amin yana kallonsu ta window, ta goge hawayenta kafin ta dawo ɗakin, ya bar falon. Haka ta koma bedroom ɗin ta, ta kwanta tana ta tunani daban-daban a cikin zuciyarta.****’yan uwan Alhaji mu’azzam kuwa, ba su gaya masa cewar an aurar da jauhar ba, suka ce masa babanta ya ce yayi haƙuri idan ya dawo ayi auren, abun ya bashi mamaki, ga wata irin kewar yarinyar da yake yi, yana jin son ta sosai da sosai a ransa, ya din ga addu’a da fatan Allah ya sa ba wani abun ne zai faru ba, saboda jinkirin da ake samu ba.Kusan kwanaki biyu kenan, jauhar bayan ta gama ciwon mara, ta koma zazzaɓi, gashi babu abincin kirki, kuɗin da take tarawa a kati, ba ta son ta je ta ce a bata, a fuskanci akwai matsala, hakan kamar tonon asiri ne ga mijinta, ‘yan unguwa su samu abun faɗa.Haka zata fita ya sayo gari, da gyaɗa ko suga babu ta sha, shi kuwa garujen ko a jikinsa, sai dai yana ankare da yanayin jikinta.Al’amin na zaune a katafaren falon honorable Indabo, yana jiransa.Babu jimawa ya iso falon, yana ganinsa yayi murmushi ya ce “Ango ka sha ƙamshi, da alama amarya ce ta ɓoye mana kai har haka”Shiru yayi, ya saka babban yatsansa yana sosa girarsa.Indabo ya zauna ya ce “Tun shekaranjiya na shigo, nake nemanka amma ka ƙi zuwa. Da farko dai ina yi maka murnar angwancewa da ka yi, ina Abuja aka sanar da ni an kama ka, ana gobe ɗaurin aure, na tura P.A . Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya””Amin” ya amsa a ciki kamar an yi masa dole.”To yaya shirye-shirye? Ina fatan kana ƙara shirya mini yaranka, babban zaɓe yana gabatowa, idan aka yi nasara aka samu kujerar nan, Aminu zaku warwasa daga kai har yaranka, har da na kusa da ku ma, dan Allah kar ka bani kunya, duk da ba ka saba bani ɗin ba”.”To” ya amsa yana kallon wani wurin daban.”Ka san meyasa na kira ka?””A’a””Akwai wani matashi, yana nan a social media, ba shi da wani aiki da ya wuce adawa da ni, da aibata mana jam’iyya,kuma hankalin matasa ya fara komawa kansa, na rasa yadda zan yi da yaron nan, duk wasu hanyoyi da zan bi a siyasance, na yi amma ya ƙi ganewa”.”Me ka ke so ayi?”.Ya jefowa Al’amin hoton matashin, an rubuta adress ɗin sa a jiki.Kallo ɗaya ya yi wa hoton, ba tare da ya ɗauka ba, ya ce “Me ka ke so ayi masa?””Ire-iren sa suna da yawa, amma sonake ayi musu misali a kansa. Ina son yayi ido biyu da Switzerland ɗin ka, ka yi masa shaida alamar kun haɗu”.Wani irin murmushi ya yi, ya fito da dogon harshen sa, ya lashi laɓaɓɓansa na ƙasa da suka yi duhu ya ce “Switzerland. Kamar ka ce idan aka samu kujerar nan, zamu warwasa da yarana da na kusa da ni, alƙawari ne ko zance?””Wace irin magana ka ke haka ne, ba zance bane ba, da gaske nake yi mana”.Al’amin ya ce “In ɗauke shi a matsayin alƙawari dai”Indabo ya yi turus, ya kasa bashi amsa.”Ba zan tura mota, ta tashi a bule ni da hayaƙi ba, ba senator ba wallahi ko shugaban ƙasa ka zama, ba za a bule ni da hayaƙi ba, dan haka maganar nan a matsayin alƙawari na ɗauketa””Kai fa matsalarka kenan Aminu”.”Menene sallamar aikina?””Masu kauri ne, ga wannan ka fara rage ta” yayi maganar yana ajiye masa envelopes.”Ka san dai in da ka tura ni ko? Wallahi idan ka bani abun da bai yi mini ba, ba zan yi ba”Indabo yayi murmushi ya ce “Ai somin taɓi na baka, akwai ciko”Ya miƙe tsaye ya ɗauki envelope ɗin sa ya fice.Sai da ya je can dabar su, ya sallame su, sannan ya nufi gida.Da ya je gidan a buɗe ya tarar da ƙofar gidan, kai tsaye ya shiga ya tarar duk ta cika igiya da kayansa, ta wanke masa su.Mamakin jauhar yake, rashin sanin ciwon kai ne, ko me yake damunta, ta ce ba ta da lafiya, amma ta zage ta yi masa wanki, hatta ɗakinsa da ya bari kaca-kaca ta gyara masa.Ya samu wuri ya zauna a kan kujera, ya kunna sigari yana sha.Sallamarta ya ji a tsakar gida, bai amsa ba ya cigaba da shan sigarinsa.A hankali take takawa, ga yunwa ga ciwo, ta shigo hannunta riƙe da ‘yar leda.Ta zauna a kan carfet jiki a sanyaye ta ce “Ka yi haƙuri, baka nan ne ban tambayeka ba na fita, magani na je chemist ɗin bakin titi na sayo”Sai da yayi wani munafukin tari, saboda tun ranar da mai chemist ɗin nan yayi masa ɗinki, ya din ga jan ta da hira, ya ji ya tsane shi, amma ya fuske yayi mata shiru.”Kar ka ga ban yi girki ba tun jiya, kuɗin hannuna ne suka ƙare, amma ga gurasa na taho mana da ita daga titi” ƙara yawan hayaƙin da yake fitarwa daga bakinsa yayi, ba tare da ya ko kalleta ba.Jin ba shi da niyyar kulata, ya sanya ta yinƙura za ta tashi, sai dai ta yi wani irin razanannen ihu, kallonta yayi da sauri, ya ga ihun me take yi, dan ya san ba zai wuce wani abun haushin ne ba, dan kamar gyare haka take da ihu.Ashe ƙadangare ne a ƙarƙashin kujerar da ta zauna a gabanta, tun shigowarsa ya ganshi, amma bai damu ba, ƙadangaren na ta neman hanyar fita, jikinsa yayi baƙi sosai, kamar an ciro shi daga kwata, yayi ba kyan gani.Tuni ta suma a wurin, dan kuwa hannunta ta ɗora a kansa ba ta sani ba.Maimakon ya tashi, sai ya zuba mata ido, cikin takaici, abu kaɗan sai ta suma, ko ta hau ihu.Kamar ba zai tashi ba, sai kuma ya miƙe.Ya saka hannu ya ɗauketa ya kwantar da ita a kan kujera, sai dai jikinta ya yi zafi sosai, sai yanzu yake tunanin zazzaɓi take yi kenan?.Ya duba ledar magungunan da ta sayo, maganin ɗaya mai hoton sauro, ɗaya kuma pcm ne.Ya kama gefen hannunta, ya ji bugun zuciyar ta yana bugawa da sauri, ya saki hannun nata yana kallonta, ita a rayuwata komai ma tsoro yake ba ta kenan.A hankali ta fara motsawa, ta yinƙura za ta tashi, ya ce “Koma ki kwanta” ta ɗaga idonta a hankali ta kalleshi.”Tsoro nake ji” ta faɗa muryarta na rawa cikin tsoro.Ya sake kama hannunta, yana jin bugun zuciyar ta, ya saki ya ce “Tashi” ta yinƙura ta tashi a hankali, kanta na sara mata ga jiri saboda yunwar da take ji.Tana daga kan kujerar a kwance, ya ɗage ɗaya kujerar da ƙadangaren yake ƙarƙashin ta, kawai ya saka hannu ya danƙi ƙadangaren ya jefa shi waje.”Na shiga uku master, ƙadangaren ka ke kamawa da hannunka”Tsaki yayi, ya wuce ɗakinsa, jikinta ya din ga rawa, tsigar jikinta ta din ga tashi. Ya dawo ya dire mata leda, ya ce “Ki ci ki sha magani” ya jefa mata wani kwali sannan ya fita.Kwalin ne ya fara ɗaukar hankalinta, ta ɗauka da sauri tana dubawa, sabuwar mp ce kar ‘yar ƙarama mai kyau.Ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba, ta hau kukkunata tana dubawa, sai da ta gama, ta ajiye ta buɗe ledar.Irin meatpie ɗin nan ne oasis manya kusan biyar, da ƙatuwar robar fura da nono.Kasancewar a yunwace take kuwa ta hau ci, ta ji babu daɗi kwana biyu tana ciwo, amma bai iya yi mata sannu ba, dama magani ba ta saka ran ya saya mata ba, mutumin da bai ba ta abinci ba wane magani zai bata, ashe yana sane, sannu ce ko ya jiki ba zai iya ce mata ba.Sai dai da tuna yadda ya ɗauki ƙadangare da hannunsa, sai tsigar jikinta ta tashi.Ana yin sallar isha’i ya dawo, mp ɗin ta har da fitila.Ta tashi tana yi masa sannu da zuwa, ya wani maze ya bata wata ledar, sannan ya zauna ya ce “Ki nemi wata ma’aikaciyar idan akwai a nan kusa, tayi miki, idan ki ka je wurin wancan ɗan iskan na bakin hanya kuma ni da ke ne”Ta saka hannu biyu ta karɓa, allurar zazzaɓi ce mai tsada ya sayo ya kawo mata, amma bai iya cewa ya jiki ba.”To godiya nake master, Allah ya ƙara arziki ya sa a fi haka, na ga saƙo ma na gode sosai da sosai Allah ya sa afi haka”.”Amin”.Ta ce “Ga naka na ajiye maka” Ya ce “Idan zan ci ba sai kin ce na ci ba, ki daina kuma wannan mugun tsoron, komai ya baki tsoro, idan ba haka ba ki kashe kanki a banza”Jauhar ta rausayar da kai ta ce “Nima ban san ina jin tsoron ba ne. Amma kai ba ka jin tsoron sa ka riƙe shi da hannu?””Ban sani ba? Rannan kwaɗo yau ƙadangare, meye abun tsoro a jikinsu, har da suma saboda ƙadangare” tayi shiru ta sunkuyar da kai.Sai da ya gama sannan ta ce “Ka yi haƙuri to, ban san ya ake yi nake jin tsoron ba”.”Idan ma kina sane ki cigaba da yi mini ihu a gida kamar gyare”.Sai da ta yi murmushi ta ce “Zan koyi jarumta, zan daina jin tsoro in sha Allah. Yauwwa master yaushe zamu je ka kai ni na gaida su mama? Ba su taɓa ganina ba, ban taɓa ganinsu ba, su hajiya kawai na taɓa gani, yakamata ka kaini na gaishe su. Sai ayi girki mu je mu gaishe su, na ga haka ake yi”.Shiru yayi, yana tuna Ummansa, tana yawan cewa Allah ya raya mini babana na ga aurenka, in ga mai sa’ar da zata auri ɗan autan mazanaJauhar ta ce “Ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai ne maganar da na yi”Ya tashi tsam ya ce “Yauwwa, Ina sake jaddada miki, idan ba zaki iya zama ba, ko kin gaji zaki iya komawa gida, babu takura, na ga shekaranjiya kina ta koke-koke, idan da takura you are free to go” daga haka ya nufi ɗakinsa.Gabanta ya faɗi ta fara tunanin, me ta ce da zai ɓata masa rai har haka?.Haka nan ta ji ba ta fatan abun da zai sake mayar da ita gida yanzu, da sunan zawarci ko ace ta kasa zama, saboda ta san dama mugunta ce ta saka aka aura mata shi.A ranta ta ce ‘Zan jure, in sha Allah zan bawa mara ɗa kunya, in sha Allah, Allah ba zai kunyata ni ba, ba zan tagayyara ba”Lokaci-lokaci yake leƙowa falo, sai ya hangota tana aikin stone ɗin ta, tana jin radio a mp. Yana so yayi mata maganar ta je ayi mata allura, amma ya fasa.Bacci ta fara, ji ta tafi ta je ta kwanta, har ta fara bacci aka kawo wuta, hasken lantarki ya hasketa, ba shiri ta tashi, sai a yanzu ta tuna ba ta kashe ƙwayayen ba, ta fita falo dan ta kashe, taga Al’amin ya fito daga ɗakinsa, yana soke wuƙa a ƙugunsa.Ta tsura masa ido tana kallonsa, bai san tana falon ba, yana ɗaga ido, suka yi ido huɗu, ɗaure fuska yayi ya zo zai fice.Ta ce “Master ina zaka je a daren nan, kuma?”Ai ko sake kallonta bai yi ba, ya nufi ƙofar fita.”Dan Allah kar ka je in da za a illataka, zuciyata ba ta yi mini daɗi in ga kana zubar da jini”.Bai tsaya ba, sai da ya dangana da tsakar gida, ya kama katanga ya dira, ita kuma ta zauna a wurin ta fashe da kuka mai taɓa zuciya.Ko da ya fita titi, liti ya zo a kan babur ya ɗauke shi, suka tafi.Unguwar shiru, kowa ya shige gida, suka maƙale a wani wuri su na shaye-shaye.Can sai ga wanda suke hari, ya kwararo layin a kan babur, Al’amin ne ya fita da sauri, ya daki tayar gaban babur ɗin, aikuwa ya faɗi ƙasa da shi da babur ɗin.Suka rirriƙe shi, Al’amin ya zagaya dai-dai kunnensa ya ce “Tijjani Faruk ko? Gargaɗi aka ce ayi maka, a kan rubuce-rubucen da ka ke yi a dandalin sa da zumunta, da waɗanda ka ke suka, da Switzerland na so na yi maka warning ɗin, amma a yadda ka ke ɗin nan, zaka iya ɗayewa idan nayi maka da ita, ko iraƙi na saka maka a jiki ba zaka shura ba.Liti, duba bayana, ka ciro Russia ka yi masa rijiya a cinya, ka yi masa eleven da iraƙi a gadon bayansa”.Tijjani yana ihu, yana kururuwa, yana komai, liti ya caka masa wuƙa a cinyarsa, ya yage masa riga, ya yanke shi sau biyu a baya, ya watsar da shi a wurin yana kururuwa.Can gida mama tana ta sintiri, har sha biyu saura, ba ta ji an ce Tijjani ya shigo gida ya ɗauki abinci ba, ta din ga kiran lambar wayarsa amma a kashe.Tana ta mita, aka kira baba a waya, aka sanar musu, an tsinto tijjani a hanyar dawowa gida, an yanke shi da makami, an tafi kai shi asibitin cikin gari, sashen bayar da agajin gaggawa.Ɗora hannu ta yi a ka, tana ihu tana ta shiga uku an kashe mata ɗa.Baba ya ce ‘Ba cewa aka yi ya mutu ba, an yanke shi aka ce, ƙila masu ƙwacen waya ne ki bari mu je mu gani mana”Ya fita ya kira maƙwabcinsa, ya ce ya raka shi asibiti, domin su ga a halin da Tijjani yake ciki.Ala’amin bayan ya koma gida, a falo ya tarar da jauhar, sauro yayi dandazo a kanta yana cizo, sai ajiyar zuciya take yi ta ci uban kuka.Tsayawa yayi yana kallonta, tare da jinjinawa taurin kanta.Kamar ya tsallaketa ya wuce, ya durƙusa ya kwasheta kamar tsuma ya nufi ɗakinta da ita, yana zuwa ya kwantar da ita a kan gadon, ta buɗe idonta tare da ƙura masa ido.Tsaki yayi ya fita, ta mayar da kanta ta kwantar a kan pillow.Al’amin sawun keke ne, Allah kaɗai ya san in da ya dosa, ɗazu ya gama cewa idan ba zata iya zama ba, ta tafi gida, amma yanzu ya tsinto ta a falo ya kawota ɗaki.Da safe ta dafa tea, ta kawo masa da sauran meatpie ɗin da ya so jiya, yau bai yi rejecting ba ya karɓa ya fara ci.”Master””Mmmm””Na iya irin wannan meatpie ɗin fa, idan ka na so ka sayo mini kayan, na iya sosai mai daɗi”.Ya ce “To”.Da tana jin kunyar cin abu a gabansa, amma zuwa yanzu ta saba, ta gama cin nata, ta je ta kwaso kayansa da suka bushe, tana ninkewa ta saka zare da allura, tana ɗinke masa waɗanda suka yage.Yana kallonta tana yi, shi kuma ya karkace zai kunna sigari.”Master, shan sigari yana cutar da lafiya fa, ka din ga ragewa dan Allah, kar ka yi rashin lafiya”.”Kin je an yi miki allurar?””Zan sha magani, ba na son allura ne tsoro nake ji”Tashi ya yi zaune ya ce “Ƙadangare, kwaɗo yanzu kuma allura, sannu ‘yar madara. Sai ki biyani kuɗin allurar da na saya” yayi maganar yana barsawa yana gyara gefen rigarsa.Tayi dariya, jin yau ya kulata, har ya ɗan yi doguwar magana da ita.”To nawa ne, sai na tara da kaɗan-kaɗan na biya ka” yayi shiru yana cigaba da sakin hayaƙi.Ta sake gyara zamanta ta ce “Master Mp nan fa tayi kyau sosai, Allah ya ƙara maka buɗi” Ya jinjina mata kai.Tijjani kuwa ba ma ya hayyacinsa, saboda ya zubar da jini sosai da sosai saran da su Viper suka yi masa, da ƙyar aka samu ya farfaɗo.Cinyarsa sun yi masa rami da ɗan buda, likitoci sai ƙoƙarin ceto ransa yake yi.”Sai oga””Yaya na ji shiru fa, haryanzu kuna tsare da yarona”.”Na sani, trape ɗin muke setting, idan muka yi gaggawa aikinmu zai kwaɓe””Ok ina saurarenku”.Jauhar sai murna take yi, zata je registration makarantar su, dama tun da aka kawota ba ta je unguwar ba.Da safe tana ta shiri, ya fito zai fita ya ajiye mata dubu ɗaya ya ce “Ki hau mota””Na gode sosai da sosai, Allah ya sa a fi haka, ya ƙara buɗi, ya tsare mini kai” ba shiri ya kalleta, ya ga ba shi take kallo ba, sai jujjuya dubun take yi tana murmushi.”Da ina da wata ba zan kasheta ba, ina son sabon kuɗi sosai” tayi maganar tana ƙara faɗaɗa murmushin ta.”Sai ki ɗinka ta ki saka tun da riga ce””Kuma zata yi mini kyau fa, adawo lafiya, Allah ya tsareka”Ya amsa da “Amin”Jauhar ta ƙarasa shirinta, ta tafi makaranta, kamar yadda Baba ya ce mata ta je tayi registration, a nan ta haɗu da ‘yan makarantar su, ta din ga murna sun haɗu da ‘yan makarantar su, da malaman makarantar ma.Ta din ga yi wa ƙawayenta mitar ba su je gidanta ba.”Jauhar wa zai zo gidanki kina auren ɗan daba? Ba ma za a bar mu mu zo ba”Jauhar ta yi murmushi ta ce “Ku daina fakewa da haka, ni da muke tare, ya aka yi bai yi mini komai ba?””A’a ai ke matarsa ce, mu kuwa fa”Duk da ba ta gaya masa ba, haka kawai ta ji tana son ta je gida.Ganin ko ta fita ba hanata yake yi ba, ya sanya ta nufi hanyar gida.Gaba ɗaya sun yi mamakin ganinta, Anty ta ce “Yaya, ya na ganki yanzu meyafaru?”Jauhar ta yi murmushi ta ce “Lafiya lau anty, registration na zo na ce bari na biyo, tun da kun ƙi zuwa”.Kallon jauhar suke yi, su ga ko akwai wani abu na tashin hankali a tare da ita, ko alamar duka ko makamancin haka, amma ba su gani ba, sai ma wata nutsuwa ta mussaman da suka gani a tare da ita.Mama ta ce ‘m”Jauhar kin kyauta, wato miji daɗi, ki ka kasa zuwa ki duba ɗan uwanki, ya kusa mutuwa”Cikin tashin hankali jauhar ta ce “Subhanallah, mama ban sani ba ba shi da lafiya ne?””Ina fa, ya dawo daga aiki, aka samu wasu suka sassare shi”.Abun ya ɗagawa jauhar hankali, ta ce musu ba ta sani ba.Al’amin yana can wurin su Walid, kansa yana yi masa ciwo, ga yana jin yanayin jikinsa kamar zazzaɓi yana son kama shi.Yana jin wayarsa na ta vibrating yayi banza.”Viper wayarka fa ta cika mini kunne, dan Allah ka ɗaga””Ƙyale ni, kamar zazzaɓi ne zai kama ni””To ka kashe wayar mana”.”Ba zan kashe ba””Ka duba mana ko beb ɗin ka ce take nemanka, yarinyar nan ta na kula mana da kai yasin”.Viper yayi tsaki, ya sake gyara kwanciyar sa.Walid ya miƙa hannu, ya ɗauki wayar ya ɗaga ya ce “Ya aka yi?””Ka gaya wa uban gidanka, na ga cikarsa ta shigo mana arear, duk da kashedin da na yi kar ta sake zuwa, tun da ya kwasheta. Yayi ganganci mafi girma da muni, tun tun da ya bari ta shigo, ya zo ya ɗauki gawarta a dabata!.
Ayshercool 08081012143
